Muhawara Hausa
 
Fassarar Sheikh Is'hak Yunus Almashgool, Bauchi
 
Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai Daga Salihu Makera

Fassarar Sheikh Is'hak Yunus Almashgool, Bauchi

Babi na Ashirin: Kamar abin da ya gabata:

79. An karbo daga Muhammad dan Dinar ya ce: ''Fulaihu ya ba mu labari ya ce, Hilal ya ba mu labari -Hawwal Sanad- ya ce, ''Abdullahi dan Muhammad ya ce, Abu Amir ya ba mu labari ya ce, Fulaihu ya ba mu labari daga Hilal dan Aliyu daga Adda'u dan Yassar daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: ''Hakika Annabi (SAW) ya kasance wata rana yana bayar da labari lokacin da wani mutum daga mutanen kauye masu aikin lambu na tare da shi (Annabi). Ya ce: ''Wani manomi daga mutanen Aljanna zai nemi izinin Ubangijinsa a game da yin shuka, sai (Allah) Ya ce, masa: Shin ba kana cikin abin da kake so ba? Ya ce, ''Gaskiya ne, amma dai ni, ina son noman ne kawai. Sai ya ce, ''Ka yi shuka, idan ya shuka sai tsiron ya fito ya girma (ya nuna ya isa girbi) cikin sa'a daya, ya girma sai ka ce misalin dutse. Sai Allah Madaukaki Ya ce: ''Karbi ya kai dan Adamu babu abin da zai kosar da kai. ''Sai wani Balaraben kauye ya ce, ''Wallahi ba mu ganin wanda zai aikata haka face Bakuraishe (mutumin Makka) ko mutumin Madina, su ne za su nemi aikata haka saboda manoma su. Amma mu, ba manoma ba ne, sai Annabi (SAW) ya yi dariya.''

Babi na Ashirin da daya:

Abin da ya zo cikin hukuncin dashe:

80. An karbo daga kutaiba dan Sa'id ya ce: ''Yakub ya ba mu labari daga Abu Hazim daga Sahlu dan Sa'ad (Allah Ya yarda da shi) cewa: ''Lallai shi ya ce, ''Lallai mu, mun kasance mukan yi farin ciki da kewayowar wunin Juma'a saboda wata mace tsohuwa tana dibar jijiyar (saiwar) Silk dinmu da muke dasa shi a gabar koginmu, sai ta rika sanya shi cikin tukunyarta ta hada shi da wasu hatsi na sha'iri ban san ko yaya take yi ba face shi ya ce: ''Babu kitse a cikinsa kuma babu wani romo, idan muka yi Sallar Juma'a sai mu ziyarce ta, sai ta rika ba mu, don haka muka kasance muna farin cikin da kewayowar wunin Juma'a saboda haka, kuma ba mu cin abincin rana kuma ba mu barcin rana face bayan Juma'a.''

81. An karbo daga Musa dan Isma'il ya ce: Ibrahim dan Sa'ad ya ba mu labari daga dan Shihab daga A'raji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ''Sahabbai sun kasance suna cewa, lallai Abu Huraira ya yawaita game da hadisai. Amma dai Allah Ya sani ko gaskiya nake fadi ko a'a. Ya ce, ''Suna cewa, me ya hana Muhajirai (mutanen Makka) da Ansar (mutanen Madina) su rika bayar da hadisai misalin hadisansa? Amma lallai 'yan uwana masu hijira tafiya fatauci a kasuwanni ya shagaltar da su, kuma 'yan uwana mutanen Madina ayyuka cikin dukiyaoyinsu ya shagaltar da su. Amma ni, na kasance wani mutum ne miskini ina lazimtar Manzon Allah (SAW) bisa cikar cikina da abinci. Ina halarta lokacin da ba su nan, ina kiyaye abu lokacin da suka manta. Annabi (SAW) ya ce, wata rana: ''Babu wani daga cikinku wanda zai shimfida tufafinsa har sai na kare magana ta wannan, sa'an nan ya tara shi bisa kirjinsa a ce ya manta wani abu daga maganata har abada. Sai na shimfida mayafina don ba ni da wata tufa ban da ita har sai da Annabi (SAW) ya kare daga maganarsa, sa'an nan na tara ta zuwa ga kirjina. Ina rantsuwa da Wanda Ya aiko shi (Annabi) da gaskiya ban mantawa da maganarsa har zuwa wunina wannan. Wallahi ba domin ayoyi biyu da suke cikin Littafin Allah ba da ban ba ku labari da komai ba har abada, su ne: ''Lallai wadanda suke boye abin da Muka saukar daga hujjojinMu da shiriya….. har zuwa….Mai Jinkai (2:159).''

 Posted By Aka Sanya A Saturday, May 21 @ 20:57:53 PDT Da MediaHausaTeam

Comments 💬 التعليقات
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad

Zabuka

 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki

Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

"Fassarar Sheikh Is'hak Yunus Almashgool, Bauchi" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata

Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 
Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu

Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com