Muhawara Hausa
 



Abin da za mu yiAllah Ya so mu (1)
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Abin da za mu yiAllah Ya so mu (1)

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai. Mai nuna mulki Ranar Sakamako. Kai kadai muke bautawa kuma gare Ka kadai muke neman taimako. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da sauran masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Bayan haka ganin halin da mu Musulmi muka samu kanmu a ciki a wannan lokaci, ya kamata mu rika wa kanmu wannan tambaya ta sama. "Shin Allah Yana sonmu kuwa?"

Yin Tambayar zai sa mu yi kokarin gano amsa kuma ta haka ne za mu iya gane ko muna tafiya a kan hanyar da Allah Yake so ko a'a. Na fadi haka ne saboda yadda muka iske kanmu a cikin wani yanayi na rana kuna inuwa zafi a kusan duk duniyar Musulmi.

Domin amsa wannan tambaya za mu leka tarihi mu ga yadda magabatan kwarai (Salafus Salih) da mamayan kwarai (Khalfus Salih) suka gudanar da rayuwarsu har suka samu daukakar da yanzu muke ta karantawa a littattafan tarihi da na addini, kuma suka zama su ne suke juya duniya a zamaninsu.

Bayan wafatin Annabi (SAW) ba da dogon lokaci ba, Abu Idris Alkhaulani (wanda ya rasu a shekara ta 80 Bayan Hijira daidai da shekara ta 699-700 Miladiyya) a Damaskus ta kasar Syriya ya tafi Masallacin Al-Kabir. A cikin masallacin ya iske rukunin mutane sun kewaye wani mutum. Ya bayyana siffar mutumin da mutum mai yawan murmushi kuma mutanen sun kewaye shi suna yi masa tambayoyi. Sai Abu Idris Al-Khaulani ya tambaya: "Wane ne wannan mutum?" Sai suka amsa: "Mu'azu bin Jabal ne (RA), sahabin Manzon Allah (SAW)."

Washegari Abu Idris ya sake zuwa masallacin da jijjifi kafin Sallar Asuba, tunaninsa ya zamo mutum na farko da zai fara shiga masallacin. Amma sai ya iske Mu'azu bin Jabal (RA) yana nafila kafin Sallar. Sai Abu Idris ya isa ga Mu'azu (RA) ya zauna a bayansa ya jira ya idar da Sallarsa, Abu Idris ya matsa kusa da shi ya ce: "Ya Mu'azu! Lallai ni ina sonka saboda Allah Madaukaki!"

Sai Mu'azu Ibnu Jabal (RA) ya jawo Abu Idris kusa da shi, ya tambaye shi cewa: "Shin da gaske don Allah Madaukaki kawai kake sona?"

Abu Idris ya ce: "Eh!"

Sai Mu'az bin Jabal ya yi murmushi ya sake jawo shi kusa ya ce masa: "Zo in ba ka kyakkyawan labari, hakika na ji Annabi (SAW) ya ce: "Allah Madaukaki Ya ce: "Wajabat Muhabbati Li Mutahabina fiya." Ma'ana "SoyayyaTa ta wajaba ga masu soyayya domiNa."

'Yan Musulmi! Tarihin dan Adam cike yake da yadda mutane suke cewa suna son Allah Madaukaki kuma Allah Yana sonsu. Kiristoci suna da'awar cewa Allah Madaukaki Yana sonsu, amma sai ga shi Allah Subhanahu Wa Ta'ala Ya kira su da batattu (k:1:7). Haka Yahudawa suna da'awar suna son Allah, amma Allah Subhanahu Wa Ta'ala ya ce da su: "Wadanda Allah Ya yi fushi da su." (k:1:7).

To, haka akwai Musulmin da suke da'awar suna son Allah Subhanahu Wa Ta'ala, sai dai abin tambaya shin Allah (SWT) Yana sonsu? Shin da gaske Allah Madaukaki Yana sonmu?

Ya zo a cikin Sahihul Buhari, Annabi (SAW) ya ce: "A duk lokacin da Allah Ya so wani, sai Ya kira Mala'ika Jibrilu Ya ce, "Ya Jibril! Inni uhibbu Fulani…!" Ma'ana "Ya Jibril! Lallai Ni ina son wane dan wane don haka kai ma ka so shi!" Sai Allah Ya ambaci sunan mutumin , sai Jibril ya so wannan mutum. Sannan Jibril (AS) ya yi shela ga dukkan Mala'ikun da ke cikin sammai bakwai ya ce: "Allah Yana son wane dan wane, don haka ku so shi. Sai Allah Ya sanya son wannan mutum a cikin zukatan mutane!"

To, mu tsaya kowa ya tambayi kansa, me ya sa nake da bakin jini a wurin mutane? Shin me ya sa mutane ba sa sona? Shin wannan ba alamar Allah bai sonmu ba ne a daidaikunmu da kuma a kungiyancenmu?

A wani Hadisi Annabi (SAW) ya ce: "Bawa ba zai gushe ba yana neman kusanci da Allah; yana neman soyayyar Allah, har sai Allah Ya kira Jibril (AS) Ya ce: masa, "Ya Jibril! BawaNa wane dan wane yana ta kokarin neman yardaTa da kusantaTa. To hakika soyayyaTa ta tabbata a gare shi."

Alkur'ani da Sunnar Annabi (SAW) sun nuna mana irin mutanen da Allah (SWT) Yake so. Kuma daga cikin mafifitan mutanen da Allah Ya fi so, akwai Annabi Ibrahim (AS). Allah Subhanahu Wa Ta'ala Ya ce: "Kuma Allah Ya riki Ibrahim a matsayin Khalil (makusanci kuma amini)." (k:4:125).

Kuma daga cikin mutanen da Allah Subhanahu Wa Ta'ala Yake so, akwai Annabi Ayyub (AS). Allah Madaukaki Ya ce: "Mun same shi mai hakuri… Madalla da wannan bawa."

A cikin Sahihu Muslim Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya shaida mana yadda wata rana wani mutum ya tafi ziyarar dan uwansa saboda Allah Subhanahu Wa Ta'ala. A kan hanyarsa ta zuwa, sai Allah Ya aika masa da wani Mala'ika ya tambaye shi inda zai je, sai ya ce: "Zan je ziyarar dan uwana ne saboda Allah Subhanahu Wa Ta'ala." Sai Mala'ikan ya ce: "Ba ka da wani dalili na zuwan gidansa bayan wannan?" Sai mutumin ya ce: "Ba ni da wani dalili na zuwa sai saboda Allah Subhanahu Wa Ta'ala." Sai Mala'ikan ya ce: "Hakika ni Mala'ika ne daga Allah Subhaanahu Wa Ta'ala, kuma ina yi maka bushara cewa Allah Yana sonka!"

Kuma daga cikin mutanen da Allah Subhanahu Wa Ta'ala Yake so, akwai Nana Khadija (Radiyallahu Anha). Ya zo a cikin Sahihul-Bukhari cewa Annabi (SAW), yana zaune tare da Mala'ika Jibril suna karantun Alkur'ani, sai Nana Khadija (RA) ta zo. Sai Jibril (AS) ya juya ga Annabi (SAW) ya ce: "Wannan Khadija ce ta kawo maka abinci. Ka isar mata da sallamata!"

A nan Mala'ika Jibril (AS) ne yake mika gaisuwa ga Nana Khadija (RA), sannan sai Jibril ya ce: "Ka yi mata bushara tana da gida a Aljanna!"

Me zai faru idan Allah Yana sonmu?

Da farko dai Allah Madaukaki zai ambaci sunan mutum Ya ce, wane dan wane, sannan Allah Ya kira Mala'ika Jibril (AS) Ya shaida masa cewa shi Allah Yana son wancan mutum. Kuma ba so kawai Allah zai nuna wa mutumin ba, zai umarci Jibrila (AS) ya so wannan mutum. Baya ga Jibril Mala'ikun da suke cikin sama da na kasa za su so wannan mutum. Sannan Allah Ya sanya kauna da soyayyar wannan mutum a zukatan mutane.

To, idan irin wannan mutum ya roki Allah komai, Allah zai ba shi, idan kuma ya nemi tsarin Allah daga kowane abu, Allah zai tsare shi. Kuma duk mutumin da ya samu irin wannan matsayi yanke dan Aljanna ne.

Mu sake tambayar kanmu, "Shin Allah Yana sonmu?" Idan har muna ji a jikinmu cewa Allah ba Ya son mu saboda ba mu aikata abin da ya dace, to 'yan uwa mu yi wa kanmu kiyamul laili, mu tuna da karashen wannan Hadisi da muka fara kawowa, mu guje wa abin da zai fusata Allah. Mu guji mutanen da suke aikata ayyukan da ke fusata Allah.

 Posted By Aka Sanya A Monday, September 09 @ 02:42:53 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc



"Abin da za mu yiAllah Ya so mu (1)" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 



Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com