Prev  

19. Surah Maryam سورة مريم

  Next  
Ayah  19:1  الأية
    +/- -/+  
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ

Ayah  19:2  الأية
    +/- -/+  
ذِكْرُ رَحْمَتِ رَبِّكَ عَبْدَهُ زَكَرِيَّا
Hausa
 
Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya.

Ayah  19:3  الأية
    +/- -/+  
إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ نِدَاءً خَفِيًّا
Hausa
 
A lőkacin da ya kirăyi Ubangijinsa, kira ɓőyayye.

Ayah  19:4  الأية
    +/- -/+  
قَالَ رَبِّ إِنِّي وَهَنَ الْعَظْمُ مِنِّي وَاشْتَعَلَ الرَّأْسُ شَيْبًا وَلَمْ أَكُن بِدُعَائِكَ رَبِّ شَقِيًّا
Hausa
 
Ya ce: "Yă Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yă Ubangiji!"

Ayah  19:5  الأية
    +/- -/+  
وَإِنِّي خِفْتُ الْمَوَالِيَ مِن وَرَائِي وَكَانَتِ امْرَأَتِي عَاقِرًا فَهَبْ لِي مِن لَّدُنكَ وَلِيًّا
Hausa
 
"Kuma lalle nĩ, na ji tsőron dangi a băyăna, kuma mătăta ta kasance bakarăriya! Sai ka bă ni wani mataimaki daga wajenKa."

Ayah  19:6  الأية
    +/- -/+  
يَرِثُنِي وَيَرِثُ مِنْ آلِ يَعْقُوبَ ۖ وَاجْعَلْهُ رَبِّ رَضِيًّا
Hausa
 
"Ya găjẽ ni, kuma ya yi gădo daga gidan Yăƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yă Ubangiji!"

Ayah  19:7  الأية
    +/- -/+  
يَا زَكَرِيَّا إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَامٍ اسْمُهُ يَحْيَىٰ لَمْ نَجْعَل لَّهُ مِن قَبْلُ سَمِيًّا
Hausa
 
(Allah Ya karɓa) "Yă zakariyya! Lalle ne Mũ, Mună yi maka bushăra da wani yăro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabăni."

Ayah  19:8  الأية
    +/- -/+  
قَالَ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَامٌ وَكَانَتِ امْرَأَتِي عَاقِرًا وَقَدْ بَلَغْتُ مِنَ الْكِبَرِ عِتِيًّا
Hausa
 
Ya ce: "Yă Ubangijĩna! Yăya wani yăro zai kasance a gare ni, alhăli kuwa mătăta ta kasance bakarăriya, kuma gă shi nă kai ga matuƙa ta tsũfa?"

Ayah  19:9  الأية
    +/- -/+  
قَالَ كَذَٰلِكَ قَالَ رَبُّكَ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٌ وَقَدْ خَلَقْتُكَ مِن قَبْلُ وَلَمْ تَكُ شَيْئًا
Hausa
 
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabănin haka, alhăli ba ka kasance kőme ba."

Ayah  19:10  الأية
    +/- -/+  
قَالَ رَبِّ اجْعَل لِّي آيَةً ۚ قَالَ آيَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ النَّاسَ ثَلَاثَ لَيَالٍ سَوِيًّا
Hausa
 
Ya ce: "Yă Ubangijina! Ka sanya mini alăma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kăsa yi wa mutăne magana a darũruwa uku daidai."

Ayah  19:11  الأية
    +/- -/+  
فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوْمِهِ مِنَ الْمِحْرَابِ فَأَوْحَىٰ إِلَيْهِمْ أَن سَبِّحُوا بُكْرَةً وَعَشِيًّا
Hausa
 
Sai ya fita a kan mutănensa daga masallăci, sa'an nan ya yi ishăra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi săfe da yamma."

Ayah  19:12  الأية
    +/- -/+  
يَا يَحْيَىٰ خُذِ الْكِتَابَ بِقُوَّةٍ ۖ وَآتَيْنَاهُ الْحُكْمَ صَبِيًّا
Hausa
 
Yă Yahaya! Ka kăma littăfi da ƙarfi. Kuma Muka bă shi hukunci yană yăro.

Ayah  19:13  الأية
    +/- -/+  
وَحَنَانًا مِّن لَّدُنَّا وَزَكَاةً ۖ وَكَانَ تَقِيًّا
Hausa
 
Kuma (Muka sanya shi) abin girmamăwa daga gunMu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗă'ă da taƙawa.

Ayah  19:14  الأية
    +/- -/+  
وَبَرًّا بِوَالِدَيْهِ وَلَمْ يَكُن جَبَّارًا عَصِيًّا
Hausa
 
Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai săɓo ba.

Ayah  19:15  الأية
    +/- -/+  
وَسَلَامٌ عَلَيْهِ يَوْمَ وُلِدَ وَيَوْمَ يَمُوتُ وَيَوْمَ يُبْعَثُ حَيًّا
Hausa
 
Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rănar da aka haife shi da rănar da yake mutuwa da rănar da ake tăyar da shi yană mai rai.

Ayah  19:16  الأية
    +/- -/+  
وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ مَرْيَمَ إِذِ انتَبَذَتْ مِنْ أَهْلِهَا مَكَانًا شَرْقِيًّا
Hausa
 
Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littăfi, a lőkacin da ta tsallake daga mutănenta a wani wuri, a gẽfen gabas.

Ayah  19:17  الأية
    +/- -/+  
فَاتَّخَذَتْ مِن دُونِهِمْ حِجَابًا فَأَرْسَلْنَا إِلَيْهَا رُوحَنَا فَتَمَثَّلَ لَهَا بَشَرًا سَوِيًّا
Hausa
 
Sa'an nan ta riƙi wani shămaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.

Ayah  19:18  الأية
    +/- -/+  
قَالَتْ إِنِّي أَعُوذُ بِالرَّحْمَٰنِ مِنكَ إِن كُنتَ تَقِيًّا
Hausa
 
Ta ce: "Lalle nĩ ină nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!"

Ayah  19:19  الأية
    +/- -/+  
قَالَ إِنَّمَا أَنَا رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَامًا زَكِيًّا
Hausa
 
Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dőmin in băyar da wani yăro tsarkakke gare ki."

Ayah  19:20  الأية
    +/- -/+  
قَالَتْ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَامٌ وَلَمْ يَمْسَسْنِي بَشَرٌ وَلَمْ أَكُ بَغِيًّا
Hausa
 
Ta ce: "A ină yăro zai kasance a gare ni alhăli kuwa wani mutum bai shăfe ni ba, kuma ban kasance kăruwa ba?"

Ayah  19:21  الأية
    +/- -/+  
قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٌ ۖ وَلِنَجْعَلَهُ آيَةً لِّلنَّاسِ وَرَحْمَةً مِّنَّا ۚ وَكَانَ أَمْرًا مَّقْضِيًّا
Hausa
 
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dőmin Mu sanya shi wata alăma ga mutăne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yă kasance wani al'amari hukuntacce."

Ayah  19:22  الأية
    +/- -/+  
فَحَمَلَتْهُ فَانتَبَذَتْ بِهِ مَكَانًا قَصِيًّا
Hausa
 
Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa.

Ayah  19:23  الأية
    +/- -/+  
فَأَجَاءَهَا الْمَخَاضُ إِلَىٰ جِذْعِ النَّخْلَةِ قَالَتْ يَا لَيْتَنِي مِتُّ قَبْلَ هَٰذَا وَكُنتُ نَسْيًا مَّنسِيًّا
Hausa
 
Sai năƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dă dai na mutu a gabănin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!"

Ayah  19:24  الأية
    +/- -/+  
فَنَادَاهَا مِن تَحْتِهَا أَلَّا تَحْزَنِي قَدْ جَعَلَ رَبُّكِ تَحْتَكِ سَرِيًّا
Hausa
 
Sai (yăron da ta haifa) ya kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.

Ayah  19:25  الأية
    +/- -/+  
وَهُزِّي إِلَيْكِ بِجِذْعِ النَّخْلَةِ تُسَاقِطْ عَلَيْكِ رُطَبًا جَنِيًّا
Hausa
 
"Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yană 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu."

Ayah  19:26  الأية
    +/- -/+  
فَكُلِي وَاشْرَبِي وَقَرِّي عَيْنًا ۖ فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ الْبَشَرِ أَحَدًا فَقُولِي إِنِّي نَذَرْتُ لِلرَّحْمَٰنِ صَوْمًا فَلَنْ أُكَلِّمَ الْيَوْمَ إِنسِيًّا
Hausa
 
"Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idănunki. To, idan kin ga wani aya daga mutăne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwăshin azumi dőmin Mai rahama sabőda haka bă zan yi wa wani mutum magana ba."

Ayah  19:27  الأية
    +/- -/+  
فَأَتَتْ بِهِ قَوْمَهَا تَحْمِلُهُ ۖ قَالُوا يَا مَرْيَمُ لَقَدْ جِئْتِ شَيْئًا فَرِيًّا
Hausa
 
Sai ta je wa mutănenta tană auke da shi. Suka ce: "Yă Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!

Ayah  19:28  الأية
    +/- -/+  
يَا أُخْتَ هَارُونَ مَا كَانَ أَبُوكِ امْرَأَ سَوْءٍ وَمَا كَانَتْ أُمُّكِ بَغِيًّا
Hausa
 
"Yă 'yar'uwar Hărũna! Ubanki bai kasance mutumin alfăsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kăruwa ba."

Ayah  19:29  الأية
    +/- -/+  
فَأَشَارَتْ إِلَيْهِ ۖ قَالُوا كَيْفَ نُكَلِّمُ مَن كَانَ فِي الْمَهْدِ صَبِيًّا
Hausa
 
Sai ta yi ishăra zuwa gare shi, suka ce: "Yăya ză mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yană jărĩri?"

Ayah  19:30  الأية
    +/- -/+  
قَالَ إِنِّي عَبْدُ اللهِ آتَانِيَ الْكِتَابَ وَجَعَلَنِي نَبِيًّا
Hausa
 
Ya ce: "Lalle ne, nĩ băwan Allah ne Allah Yă bă ni Littăfi kuma Ya sanya ni Annabi."

Ayah  19:31  الأية
    +/- -/+  
وَجَعَلَنِي مُبَارَكًا أَيْنَ مَا كُنتُ وَأَوْصَانِي بِالصَّلَاةِ وَالزَّكَاةِ مَا دُمْتُ حَيًّا
Hausa
 
"Kuma Yă sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar ină da rai."

Ayah  19:32  الأية
    +/- -/+  
وَبَرًّا بِوَالِدَتِي وَلَمْ يَجْعَلْنِي جَبَّارًا شَقِيًّا
Hausa
 
"Kuma mai biyayya ga uwăta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri."

Ayah  19:33  الأية
    +/- -/+  
وَالسَّلَامُ عَلَيَّ يَوْمَ وُلِدتُّ وَيَوْمَ أَمُوتُ وَيَوْمَ أُبْعَثُ حَيًّا
Hausa
 
"Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rănar da aka haife ni da rănar da nake mutũwa da rănar da ake tăyar da ni ină mai rai."

Ayah  19:34  الأية
    +/- -/+  
ذَٰلِكَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ ۚ قَوْلَ الْحَقِّ الَّذِي فِيهِ يَمْتَرُونَ
Hausa
 
Wancan ne Ĩsă ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.

Ayah  19:35  الأية
    +/- -/+  
مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٍ ۖ سُبْحَانَهُ ۚ إِذَا قَضَىٰ أَمْرًا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُ كُن فَيَكُونُ
Hausa
 
Bă ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗă. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yă hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa.

Ayah  19:36  الأية
    +/- -/+  
وَإِنَّ اللهَ رَبِّي وَرَبُّكُمْ فَاعْبُدُوهُ ۚ هَٰذَا صِرَاطٌ مُّسْتَقِيمٌ
Hausa
 
"Kuma lalle Allah ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici."

Ayah  19:37  الأية
    +/- -/+  
فَاخْتَلَفَ الْأَحْزَابُ مِن بَيْنِهِمْ ۖ فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا مِن مَّشْهَدِ يَوْمٍ عَظِيمٍ
Hausa
 
Sai ƙungiyőyin suka săɓă wa jũna a tsakăninsu. To, bőne ya tabbata ga waɗanda suka kăfirta daga halartar yini mai girma.

Ayah  19:38  الأية
    +/- -/+  
أَسْمِعْ بِهِمْ وَأَبْصِرْ يَوْمَ يَأْتُونَنَا ۖ لَٰكِنِ الظَّالِمُونَ الْيَوْمَ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Hausa
 
Mẽne ne ya yi jinsu, kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rănar da suke zo Mana! Amma azzălumai sună a cikin ɓata bayyananna.

Ayah  19:39  الأية
    +/- -/+  
وَأَنذِرْهُمْ يَوْمَ الْحَسْرَةِ إِذْ قُضِيَ الْأَمْرُ وَهُمْ فِي غَفْلَةٍ وَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
Hausa
 
Kuma ka yi musu gargaɗi da rănar nadăma a lőkacin da aka hukunta al'amari alhăli kuwa sună a cikin ɓăta, kuma sũ bă su yin ĩmăni.

Ayah  19:40  الأية
    +/- -/+  
إِنَّا نَحْنُ نَرِثُ الْأَرْضَ وَمَنْ عَلَيْهَا وَإِلَيْنَا يُرْجَعُونَ
Hausa
 
Lalle ne Mũ, Mũ ne ke gădon ƙasa da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su.

Ayah  19:41  الأية
    +/- -/+  
وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ إِبْرَاهِيمَ ۚ إِنَّهُ كَانَ صِدِّيقًا نَّبِيًّا
Hausa
 
Kuma ambaci Ibrăhĩm a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatăwa, Annabi.

Ayah  19:42  الأية
    +/- -/+  
إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ يَا أَبَتِ لِمَ تَعْبُدُ مَا لَا يَسْمَعُ وَلَا يُبْصِرُ وَلَا يُغْنِي عَنكَ شَيْئًا
Hausa
 
A lőkacin da ya ce wa ubansa, "Yă băba! Don me kake bauta wa abin da bă ya ji, kuma bă ya ga ni, kuma ba ya wadătar da kőme daga barinka?"

Ayah  19:43  الأية
    +/- -/+  
يَا أَبَتِ إِنِّي قَدْ جَاءَنِي مِنَ الْعِلْمِ مَا لَمْ يَأْتِكَ فَاتَّبِعْنِي أَهْدِكَ صِرَاطًا سَوِيًّا
Hausa
 
"Yă băba! Lalle ni, haƙĩƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabőda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici."

Ayah  19:44  الأية
    +/- -/+  
يَا أَبَتِ لَا تَعْبُدِ الشَّيْطَانَ ۖ إِنَّ الشَّيْطَانَ كَانَ لِلرَّحْمَٰنِ عَصِيًّا
Hausa
 
"Yă băba! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓăwa ga Mai rahama."

Ayah  19:45  الأية
    +/- -/+  
يَا أَبَتِ إِنِّي أَخَافُ أَن يَمَسَّكَ عَذَابٌ مِّنَ الرَّحْمَٰنِ فَتَكُونَ لِلشَّيْطَانِ وَلِيًّا
Hausa
 
"Yă băba! Lalle ne ni ină tsőron wata azăba daga Mai rahama ta shăfe ka, har ka zama masőyi ga Shaiɗan."

Ayah  19:46  الأية
    +/- -/+  
قَالَ أَرَاغِبٌ أَنتَ عَنْ آلِهَتِي يَا إِبْرَاهِيمُ ۖ لَئِن لَّمْ تَنتَهِ لَأَرْجُمَنَّكَ ۖ وَاهْجُرْنِي مَلِيًّا
Hausa
 
Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumăkăna? Yă Ibrăĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kană mai mutunci."

Ayah  19:47  الأية
    +/- -/+  
قَالَ سَلَامٌ عَلَيْكَ ۖ سَأَسْتَغْفِرُ لَكَ رَبِّي ۖ إِنَّهُ كَانَ بِي حَفِيًّا
Hausa
 
Ya ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya găfarta maka. Lalle Shi Ya kasance Mai girmamăwa gare ni."

Ayah  19:48  الأية
    +/- -/+  
وَأَعْتَزِلُكُمْ وَمَا تَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ وَأَدْعُو رَبِّي عَسَىٰ أَلَّا أَكُونَ بِدُعَاءِ رَبِّي شَقِيًّا
Hausa
 
"Kuma ină nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma ină kiran Ubangijina, tsammănin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina."

Ayah  19:49  الأية
    +/- -/+  
فَلَمَّا اعْتَزَلَهُمْ وَمَا يَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللهِ وَهَبْنَا لَهُ إِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ ۖ وَكُلًّا جَعَلْنَا نَبِيًّا
Hausa
 
To, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautăwa baicin Allah, Muka bă shi Is'hăƙa da Ya'aƙuba alhăli kuwa kőwanensu Mun mayar da shi Annabi.

Ayah  19:50  الأية
    +/- -/+  
وَوَهَبْنَا لَهُم مِّن رَّحْمَتِنَا وَجَعَلْنَا لَهُمْ لِسَانَ صِدْقٍ عَلِيًّا
Hausa
 
Kuma Muka yi musu kyauta daga RahamarMu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya maɗaukaki.

Ayah  19:51  الأية
    +/- -/+  
وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ مُوسَىٰ ۚ إِنَّهُ كَانَ مُخْلَصًا وَكَانَ رَسُولًا نَّبِيًّا
Hausa
 
Kuma ka ambaci Mũsă a cikin Littăfi. Lalle ne shi, yă kasance zăɓaɓɓe, kuma yă kasance Manzo, Annabi.

Ayah  19:52  الأية
    +/- -/+  
وَنَادَيْنَاهُ مِن جَانِبِ الطُّورِ الْأَيْمَنِ وَقَرَّبْنَاهُ نَجِيًّا
Hausa
 
Kuma Muka kira shi daga gẽfen dũtse na dăma kuma Muka kusanta shi yană abőkin gănăwa.

Ayah  19:53  الأية
    +/- -/+  
وَوَهَبْنَا لَهُ مِن رَّحْمَتِنَا أَخَاهُ هَارُونَ نَبِيًّا
Hausa
 
Kuma Muka yi masa kyauta daga RahamarMu da ɗan'uwansa Hărũna, ya zama Annabi.

Ayah  19:54  الأية
    +/- -/+  
وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ إِسْمَاعِيلَ ۚ إِنَّهُ كَانَ صَادِقَ الْوَعْدِ وَكَانَ رَسُولًا نَّبِيًّا
Hausa
 
Kuma ka ambaci Ismă'ila a cikin Littăfi. Lalle shi, yă kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yă kasance Manzo, Annabi.

Ayah  19:55  الأية
    +/- -/+  
وَكَانَ يَأْمُرُ أَهْلَهُ بِالصَّلَاةِ وَالزَّكَاةِ وَكَانَ عِندَ رَبِّهِ مَرْضِيًّا
Hausa
 
Kuma yă kasance yană umurnin mutănens da salla da zakka. Kuma yă kasance yardajje a wurin Ubangijinsa.

Ayah  19:56  الأية
    +/- -/+  
وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ إِدْرِيسَ ۚ إِنَّهُ كَانَ صِدِّيقًا نَّبِيًّا
Hausa
 
Kuma ka ambaci Idrĩsa a cikin Littăfi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatăwa, Annabi.

Ayah  19:57  الأية
    +/- -/+  

Ayah  19:58  الأية
    +/- -/+  
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ أَنْعَمَ اللهُ عَلَيْهِم مِّنَ النَّبِيِّينَ مِن ذُرِّيَّةِ آدَمَ وَمِمَّنْ حَمَلْنَا مَعَ نُوحٍ وَمِن ذُرِّيَّةِ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْرَائِيلَ وَمِمَّنْ هَدَيْنَا وَاجْتَبَيْنَا ۚ إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُ الرَّحْمَٰنِ خَرُّوا سُجَّدًا وَبُكِيًّا ۩
Hausa
 
Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabăwa daga zurriyar Ădamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tăre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrăhĩm da Isră'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zăɓe su. Idan ană karătun ăyőyin Mai rahama a kansu, sai su făɗi sună măsu sujada kuma măsu kũka.

Ayah  19:59  الأية
    +/- -/+  
فَخَلَفَ مِن بَعْدِهِمْ خَلْفٌ أَضَاعُوا الصَّلَاةَ وَاتَّبَعُوا الشَّهَوَاتِ ۖ فَسَوْفَ يَلْقَوْنَ غَيًّا
Hausa
 
Sai waɗansu 'yan băya suka maye a băyansu suka tőzarta salla, kuma suka bi sha'awőwinsu. To, da sannu ză su hau da wani sharri.

Ayah  19:60  الأية
    +/- -/+  
إِلَّا مَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا فَأُولَٰئِكَ يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ وَلَا يُظْلَمُونَ شَيْئًا
Hausa
 
Făce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmăni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sună shiga Aljanna, kuma bă a zăluntar su da kőme.

Ayah  19:61  الأية
    +/- -/+  
جَنَّاتِ عَدْنٍ الَّتِي وَعَدَ الرَّحْمَٰنُ عِبَادَهُ بِالْغَيْبِ ۚ إِنَّهُ كَانَ وَعْدُهُ مَأْتِيًّا
Hausa
 
Gidăjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin băyarwa ga băyinSa (măsu aikin ĩmăni) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa.

Ayah  19:62  الأية
    +/- -/+  
لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا إِلَّا سَلَامًا ۖ وَلَهُمْ رِزْقُهُمْ فِيهَا بُكْرَةً وَعَشِيًّا
Hausa
 
Bă su jin yasassar magana a cikinta, făce sallama. Kuma sună da abinci, a cikinta, săfe da maraice.

Ayah  19:63  الأية
    +/- -/+  
تِلْكَ الْجَنَّةُ الَّتِي نُورِثُ مِنْ عِبَادِنَا مَن كَانَ تَقِيًّا
Hausa
 
Wancan Aljannar ce wadda Muke gădar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga băyiNa.

Ayah  19:64  الأية
    +/- -/+  
وَمَا نَتَنَزَّلُ إِلَّا بِأَمْرِ رَبِّكَ ۖ لَهُ مَا بَيْنَ أَيْدِينَا وَمَا خَلْفَنَا وَمَا بَيْنَ ذَٰلِكَ ۚ وَمَا كَانَ رَبُّكَ نَسِيًّا
Hausa
 
(Sună măsu cẽwa) "Kuma bă mu sauka Făce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a băyanmu da abin da ke a tsakănin wannan." Kuma (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantăwa ba.

Ayah  19:65  الأية
    +/- -/+  
رَّبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا فَاعْبُدْهُ وَاصْطَبِرْ لِعِبَادَتِهِ ۚ هَلْ تَعْلَمُ لَهُ سَمِيًّا
Hausa
 
Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakăninsu. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautarsa. Shin kă san wani takwara a gare shi?

Ayah  19:66  الأية
    +/- -/+  
وَيَقُولُ الْإِنسَانُ أَإِذَا مَا مِتُّ لَسَوْفَ أُخْرَجُ حَيًّا
Hausa
 
Kuma mutum yana cẽwa, "Shin idan na mutu lalle ne haƙĩ ƙa da sannu ză a fitar da ni ină mai rai?"

Ayah  19:67  الأية
    +/- -/+  
أَوَلَا يَذْكُرُ الْإِنسَانُ أَنَّا خَلَقْنَاهُ مِن قَبْلُ وَلَمْ يَكُ شَيْئًا
Hausa
 
Shin, kuma mutum bă zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabăni, alhăli kuwa bai kasance kőme ba?

Ayah  19:68  الأية
    +/- -/+  
فَوَرَبِّكَ لَنَحْشُرَنَّهُمْ وَالشَّيَاطِينَ ثُمَّ لَنُحْضِرَنَّهُمْ حَوْلَ جَهَنَّمَ جِثِيًّا
Hausa
 
To, Mună rantsuwa da Ubangijinka, lalle ne, Muna tăyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sună gurfăne.

Ayah  19:69  الأية
    +/- -/+  
ثُمَّ لَنَنزِعَنَّ مِن كُلِّ شِيعَةٍ أَيُّهُمْ أَشَدُّ عَلَى الرَّحْمَٰنِ عِتِيًّا
Hausa
 
Sa'an nan kuma lalle Mună fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kőwace ƙungiya.

Ayah  19:70  الأية
    +/- -/+  
ثُمَّ لَنَحْنُ أَعْلَمُ بِالَّذِينَ هُمْ أَوْلَىٰ بِهَا صِلِيًّا
Hausa
 
Sa'an nan kuma lalle Mũ ne Mafi sani ga waɗanda suke sũ ne mafiya cancantar ƙőnuwa da ita.

Ayah  19:71  الأية
    +/- -/+  
وَإِن مِّنكُمْ إِلَّا وَارِدُهَا ۚ كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ حَتْمًا مَّقْضِيًّا
Hausa
 
Kuma băbu kőwa daga gare ku sai mai tuzga mata. Yă kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce.

Ayah  19:72  الأية
    +/- -/+  
ثُمَّ نُنَجِّي الَّذِينَ اتَّقَوا وَّنَذَرُ الظَّالِمِينَ فِيهَا جِثِيًّا
Hausa
 
Sa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzălumai a cikinta gurfăne.

Ayah  19:73  الأية
    +/- -/+  
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ قَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلَّذِينَ آمَنُوا أَيُّ الْفَرِيقَيْنِ خَيْرٌ مَّقَامًا وَأَحْسَنُ نَدِيًّا
Hausa
 
Kuma idan ană karatun ăyőyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kăfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmăni, "Wanne daga ƙungiyőyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa?"

Ayah  19:74  الأية
    +/- -/+  
وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هُمْ أَحْسَنُ أَثَاثًا وَرِئْيًا
Hausa
 
Kuma da yawa daga mutănen ƙarni Muka halakar a gabăninsu sũ (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kăyan ăki da magănă.

Ayah  19:75  الأية
    +/- -/+  
قُلْ مَن كَانَ فِي الضَّلَالَةِ فَلْيَمْدُدْ لَهُ الرَّحْمَٰنُ مَدًّا ۚ حَتَّىٰ إِذَا رَأَوْا مَا يُوعَدُونَ إِمَّا الْعَذَابَ وَإِمَّا السَّاعَةَ فَسَيَعْلَمُونَ مَنْ هُوَ شَرٌّ مَّكَانًا وَأَضْعَفُ جُندًا
Hausa
 
Ka ce: "Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatăwa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azăba kő să'a, to ză su sani, wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna!"

Ayah  19:76  الأية
    +/- -/+  
وَيَزِيدُ اللهُ الَّذِينَ اهْتَدَوْا هُدًى ۗ وَالْبَاقِيَاتُ الصَّالِحَاتُ خَيْرٌ عِندَ رَبِّكَ ثَوَابًا وَخَيْرٌ مَّرَدًّا
Hausa
 
Kuma Allah na ƙăra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka măsu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lăda, kuma mafi alhẽri ga makőma.

Ayah  19:77  الأية
    +/- -/+  
أَفَرَأَيْتَ الَّذِي كَفَرَ بِآيَاتِنَا وَقَالَ لَأُوتَيَنَّ مَالًا وَوَلَدًا
Hausa
 
Shin, ka ga wanda ya kăfirta da ayőyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne ză a bă ni dũkiya da ɗiya?"

Ayah  19:78  الأية
    +/- -/+  
أَطَّلَعَ الْغَيْبَ أَمِ اتَّخَذَ عِندَ الرَّحْمَٰنِ عَهْدًا
Hausa
 
Shin, yă tsinkăyi gaibi ne, kő kuwa yă ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne?

Ayah  19:79  الأية
    +/- -/+  
كَلَّا ۚ سَنَكْتُبُ مَا يَقُولُ وَنَمُدُّ لَهُ مِنَ الْعَذَابِ مَدًّا
Hausa
 
Ă'aha! ză mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azăba, yalwatăwa.

Ayah  19:80  الأية
    +/- -/+  
وَنَرِثُهُ مَا يَقُولُ وَيَأْتِينَا فَرْدًا
Hausa
 
Kuma Mu găde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yană shi kɗai.

Ayah  19:81  الأية
    +/- -/+  
وَاتَّخَذُوا مِن دُونِ اللهِ آلِهَةً لِّيَكُونُوا لَهُمْ عِزًّا
Hausa
 
Kuma suka riƙi gumăka, baicin Allah, dőmin su kăsance mataimaka a gare su.

Ayah  19:82  الأية
    +/- -/+  
كَلَّا ۚ سَيَكْفُرُونَ بِعِبَادَتِهِمْ وَيَكُونُونَ عَلَيْهِمْ ضِدًّا
Hausa
 
Ă'aha! Ză su kăfirta da ibădarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu.