Prev  

7. Surah Al-A'râf سورة الأعراف

  Next  
Ayah  7:1  الأية
    +/- -/+  
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ

Ayah  7:2  الأية
    +/- -/+  
كِتَابٌ أُنزِلَ إِلَيْكَ فَلَا يَكُن فِي صَدْرِكَ حَرَجٌ مِّنْهُ لِتُنذِرَ بِهِ وَذِكْرَىٰ لِلْمُؤْمِنِينَ
Hausa
 
Littăfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dőmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunătarwa ne ga mũminai.

Ayah  7:3  الأية
    +/- -/+  
اتَّبِعُوا مَا أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ وَلَا تَتَّبِعُوا مِن دُونِهِ أَوْلِيَاءَ ۗ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ
Hausa
 
Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunăwa.

Ayah  7:4  الأية
    +/- -/+  
وَكَم مِّن قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا فَجَاءَهَا بَأْسُنَا بَيَاتًا أَوْ هُمْ قَائِلُونَ
Hausa
 
Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azăbarMu ta jẽ mata da dare kő kuwa sună măsu ƙailũla.

Ayah  7:5  الأية
    +/- -/+  
فَمَا كَانَ دَعْوَاهُمْ إِذْ جَاءَهُم بَأْسُنَا إِلَّا أَن قَالُوا إِنَّا كُنَّا ظَالِمِينَ
Hausa
 
Sa'an nan băbu abin da yake da'awarsu, a lőkacin da azăbarMu ta jẽ musu, făce suka ce: "Lalle ne mũ muka kasance măsu zălunci,"

Ayah  7:6  الأية
    +/- -/+  
فَلَنَسْأَلَنَّ الَّذِينَ أُرْسِلَ إِلَيْهِمْ وَلَنَسْأَلَنَّ الْمُرْسَلِينَ
Hausa
 
Sa'an nan lalle ne Mună tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Mună tambayar Manzannin.

Ayah  7:7  الأية
    +/- -/+  
فَلَنَقُصَّنَّ عَلَيْهِم بِعِلْمٍ ۖ وَمَا كُنَّا غَائِبِينَ
Hausa
 
Sa'an nan haƙĩƙa Mună bă su lăbări da ilmi kuma ba Mu kasance măsu fakowa ba.

Ayah  7:8  الأية
    +/- -/+  
وَالْوَزْنُ يَوْمَئِذٍ الْحَقُّ ۚ فَمَن ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
Hausa
 
Kuma awo a rănar nan ne gaskiya. To, wanda sikẽlansasuka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne măsu cin nasara.

Ayah  7:9  الأية
    +/- -/+  
وَمَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ فَأُولَٰئِكَ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنفُسَهُم بِمَا كَانُوا بِآيَاتِنَا يَظْلِمُونَ
Hausa
 
Kuma wanda sikẽlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabőda abin da suka kasance, da ăyőyinMu, sună yi na zălunci.

Ayah  7:10  الأية
    +/- -/+  
وَلَقَدْ مَكَّنَّاكُمْ فِي الْأَرْضِ وَجَعَلْنَا لَكُمْ فِيهَا مَعَايِشَ ۗ قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ
Hausa
 
Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan răyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gődẽwa.

Ayah  7:11  الأية
    +/- -/+  
وَلَقَدْ خَلَقْنَاكُمْ ثُمَّ صَوَّرْنَاكُمْ ثُمَّ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ لَمْ يَكُن مِّنَ السَّاجِدِينَ
Hausa
 
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittă ku sa'an nan kuma Mun sũrantă ku, sa'an nan kumaMun ce wa mală'iku: "Ku yi sujada ga Ădam." Sai suka yi sujada făce Iblĩs, bai kasance daga măsuyin sujadar ba.

Ayah  7:12  الأية
    +/- -/+  
قَالَ مَا مَنَعَكَ أَلَّا تَسْجُدَ إِذْ أَمَرْتُكَ ۖ قَالَ أَنَا خَيْرٌ مِّنْهُ خَلَقْتَنِي مِن نَّارٍ وَخَلَقْتَهُ مِن طِينٍ
Hausa
 
Ya ce: "Mẽne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alőkacin da Na umurce ka?" Ya ce: "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhăli kuwa Kă halitta shi daga lăka."

Ayah  7:13  الأية
    +/- -/+  
قَالَ فَاهْبِطْ مِنْهَا فَمَا يَكُونُ لَكَ أَن تَتَكَبَّرَ فِيهَا فَاخْرُجْ إِنَّكَ مِنَ الصَّاغِرِينَ
Hausa
 
Ya ce: "To, ka sauka daga gare ta; dőmin bă, ya kasancẽwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kană daga măsu ƙasƙanci."

Ayah  7:14  الأية
    +/- -/+  
قَالَ أَنظِرْنِي إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ
Hausa
 
Ya ce: "Ka yi mini jinkiri zuwa ga rănar da ake tăyar da su."

Ayah  7:15  الأية
    +/- -/+  
قَالَ إِنَّكَ مِنَ الْمُنظَرِينَ
Hausa
 
Ya ce: "Lalle ne, kană daga waɗanda aka yi wa jinkiri."

Ayah  7:16  الأية
    +/- -/+  
قَالَ فَبِمَا أَغْوَيْتَنِي لَأَقْعُدَنَّ لَهُمْ صِرَاطَكَ الْمُسْتَقِيمَ
Hausa
 
Ya ce: "To ină rantsuwa da halakarwar da Ka yi mini, lalle ne, ină zaune musu tafarkinKa madaidaici."

Ayah  7:17  الأية
    +/- -/+  
ثُمَّ لَآتِيَنَّهُم مِّن بَيْنِ أَيْدِيهِمْ وَمِنْ خَلْفِهِمْ وَعَنْ أَيْمَانِهِمْ وَعَن شَمَائِلِهِمْ ۖ وَلَا تَجِدُ أَكْثَرَهُمْ شَاكِرِينَ
Hausa
 
"Sa'an nan kuma haƙĩƙa, Ină je musu daga gaba gare su, kuma daga băya gare su, kuma daga jihőhin damansu da jihőhin hagunsu; Kuma bă ză ka sămi mafi yawansu măsu gődiya ba."

Ayah  7:18  الأية
    +/- -/+  
قَالَ اخْرُجْ مِنْهَا مَذْءُومًا مَّدْحُورًا ۖ لَّمَن تَبِعَكَ مِنْهُمْ لَأَمْلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكُمْ أَجْمَعِينَ
Hausa
 
Ya ce: "Ka fita daga gare ta kană abin zargi kőrarre. Lalle ne wanda ya bĩ ka daga gare su, haƙĩƙa, ză Ni cika jahannama daga gare ku, gabă ɗaya."

Ayah  7:19  الأية
    +/- -/+  
وَيَا آدَمُ اسْكُنْ أَنتَ وَزَوْجُكَ الْجَنَّةَ فَكُلَا مِنْ حَيْثُ شِئْتُمَا وَلَا تَقْرَبَا هَٰذِهِ الشَّجَرَةَ فَتَكُونَا مِنَ الظَّالِمِينَ
Hausa
 
"Kuma ya Ădam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan ităciya, har ku kasance daga azzălumai."

Ayah  7:20  الأية
    +/- -/+  
فَوَسْوَسَ لَهُمَا الشَّيْطَانُ لِيُبْدِيَ لَهُمَا مَا وُورِيَ عَنْهُمَا مِن سَوْآتِهِمَا وَقَالَ مَا نَهَاكُمَا رَبُّكُمَا عَنْ هَٰذِهِ الشَّجَرَةِ إِلَّا أَن تَكُونَا مَلَكَيْنِ أَوْ تَكُونَا مِنَ الْخَالِدِينَ
Hausa
 
Sai Shaiɗan ya sanya musu waswăsi dőmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hană ku daga wannan ităciya ba făce dőmin kada ku kasance mală'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama."

Ayah  7:21  الأية
    +/- -/+  
وَقَاسَمَهُمَا إِنِّي لَكُمَا لَمِنَ النَّاصِحِينَ
Hausa
 
Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga măsu nasĩha ne.

Ayah  7:22  الأية
    +/- -/+  
فَدَلَّاهُمَا بِغُرُورٍ ۚ فَلَمَّا ذَاقَا الشَّجَرَةَ بَدَتْ لَهُمَا سَوْآتُهُمَا وَطَفِقَا يَخْصِفَانِ عَلَيْهِمَا مِن وَرَقِ الْجَنَّةِ ۖ وَنَادَاهُمَا رَبُّهُمَا أَلَمْ أَنْهَكُمَا عَن تِلْكُمَا الشَّجَرَةِ وَأَقُل لَّكُمَا إِنَّ الشَّيْطَانَ لَكُمَا عَدُوٌّ مُّبِينٌ
Hausa
 
Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa'an nan a lőkacin da suka ɗanɗani ităciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sună lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hană ku ba daga waccan ităciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?"

Ayah  7:23  الأية
    +/- -/+  
قَالَا رَبَّنَا ظَلَمْنَا أَنفُسَنَا وَإِن لَّمْ تَغْفِرْ لَنَا وَتَرْحَمْنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Hausa
 
Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zălunci kanmu. Kuma idan ba Ka găfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Mună kasancẽwa daga măsu hasăra."

Ayah  7:24  الأية
    +/- -/+  
قَالَ اهْبِطُوا بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ ۖ وَلَكُمْ فِي الْأَرْضِ مُسْتَقَرٌّ وَمَتَاعٌ إِلَىٰ حِينٍ
Hausa
 
Ya ce: "Ku sauka, săshenku zuwa ga săshe yană maƙiyi, kuma kună da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dăɗi zuwa ga wani lőkabi."

Ayah  7:25  الأية
    +/- -/+  
قَالَ فِيهَا تَحْيَوْنَ وَفِيهَا تَمُوتُونَ وَمِنْهَا تُخْرَجُونَ
Hausa
 
Ya ce: "A cikinta kuke răyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku."

Ayah  7:26  الأية
    +/- -/+  
يَا بَنِي آدَمَ قَدْ أَنزَلْنَا عَلَيْكُمْ لِبَاسًا يُوَارِي سَوْآتِكُمْ وَرِيشًا ۖ وَلِبَاسُ التَّقْوَىٰ ذَٰلِكَ خَيْرٌ ۚ ذَٰلِكَ مِنْ آيَاتِ اللهِ لَعَلَّهُمْ يَذَّكَّرُونَ
Hausa
 
Yă ɗiyan Ădam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tană rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawă. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ăyőyin Allah ne, tsammăninsu sună tunăwa!

Ayah  7:27  الأية
    +/- -/+  
يَا بَنِي آدَمَ لَا يَفْتِنَنَّكُمُ الشَّيْطَانُ كَمَا أَخْرَجَ أَبَوَيْكُم مِّنَ الْجَنَّةِ يَنزِعُ عَنْهُمَا لِبَاسَهُمَا لِيُرِيَهُمَا سَوْآتِهِمَا ۗ إِنَّهُ يَرَاكُمْ هُوَ وَقَبِيلُهُ مِنْ حَيْثُ لَا تَرَوْنَهُمْ ۗ إِنَّا جَعَلْنَا الشَّيَاطِينَ أَوْلِيَاءَ لِلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ
Hausa
 
Yă ɗiyan Ădam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyăyenku, biyu daga Aljanna, yană fizge tufarsu daga gare su, dőmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yană ganin ku,shi da rundunarsa, daga inda bă ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bă su yin ĩmăni.

Ayah  7:28  الأية
    +/- -/+  
وَإِذَا فَعَلُوا فَاحِشَةً قَالُوا وَجَدْنَا عَلَيْهَا آبَاءَنَا وَاللهُ أَمَرَنَا بِهَا ۗ قُلْ إِنَّ اللهَ لَا يَأْمُرُ بِالْفَحْشَاءِ ۖ أَتَقُولُونَ عَلَى اللهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Hausa
 
Kuma idan suka aikata alfăsha su ce: "Mun sămi ubanninmu akanta." Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah bă Ya umurni da alfăsha. Shin kună faɗar abin da bă ku da saninsa ga Allah?"

Ayah  7:29  الأية
    +/- -/+  
قُلْ أَمَرَ رَبِّي بِالْقِسْطِ ۖ وَأَقِيمُوا وُجُوهَكُمْ عِندَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ ۚ كَمَا بَدَأَكُمْ تَعُودُونَ
Hausa
 
Ka ce: "Ubangjina Yă yi umurni da ădalci; kuma ku tsayar da fuskőkinku a wurin kőwane masallăci, kuma ku rőƙẽ Shi, kună măsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya făra halittarku kuke kőmăwa."

Ayah  7:30  الأية
    +/- -/+  
فَرِيقًا هَدَىٰ وَفَرِيقًا حَقَّ عَلَيْهِمُ الضَّلَالَةُ ۗ إِنَّهُمُ اتَّخَذُوا الشَّيَاطِينَ أَوْلِيَاءَ مِن دُونِ اللهِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُم مُّهْتَدُونَ
Hausa
 
Wata ƙungiya (Allah) Yă shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tă wajaba a kansu; lalle ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sună zaton, lalle sũ, măsu shiryuwa ne.

Ayah  7:31  الأية
    +/- -/+  
يَا بَنِي آدَمَ خُذُوا زِينَتَكُمْ عِندَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَكُلُوا وَاشْرَبُوا وَلَا تُسْرِفُوا ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُسْرِفِينَ
Hausa
 
Yă ɗiyan Ădam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kőwane masallăci kuma ku ci, kuma ku sha; Kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ (Allah), bă Ya son măsu ɓarna.

Ayah  7:32  الأية
    +/- -/+  
قُلْ مَنْ حَرَّمَ زِينَةَ اللهِ الَّتِي أَخْرَجَ لِعِبَادِهِ وَالطَّيِّبَاتِ مِنَ الرِّزْقِ ۚ قُلْ هِيَ لِلَّذِينَ آمَنُوا فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا خَالِصَةً يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ
Hausa
 
Ka ce: "Wăne ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar sabőda băyinSa, da măsu dăɗi daga abinci?" Ka ce: "Sũ, dőmin waɗanda suka yi ĩmani suke a cikin răyuwar dũniya, suna keɓantattu a Rănar Kiyăma. "Kamar wannan ne Muke bayyana ăyőyi, daki-daki, ga mutănen da suke sani.

Ayah  7:33  الأية
    +/- -/+  
قُلْ إِنَّمَا حَرَّمَ رَبِّيَ الْفَوَاحِشَ مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَمَا بَطَنَ وَالْإِثْمَ وَالْبَغْيَ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَأَن تُشْرِكُوا بِاللهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ سُلْطَانًا وَأَن تَقُولُوا عَلَى اللهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Hausa
 
Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yă hana abũbuwanalfăsha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓőyu, da zunubi da rarraba jama'a, bă da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah."

Ayah  7:34  الأية
    +/- -/+  
وَلِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌ ۖ فَإِذَا جَاءَ أَجَلُهُمْ لَا يَسْتَأْخِرُونَ سَاعَةً ۖ وَلَا يَسْتَقْدِمُونَ
Hausa
 
Kuma ga kőwace al'umma akwai ajali. Sa'an nan idan ajalinsu ya je, bă ză a yi musu jinkiri ba, sa'a guda, kuma bă ză su gabăce shi ba.

Ayah  7:35  الأية
    +/- -/+  
يَا بَنِي آدَمَ إِمَّا يَأْتِيَنَّكُمْ رُسُلٌ مِّنكُمْ يَقُصُّونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِي ۙ فَمَنِ اتَّقَىٰ وَأَصْلَحَ فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ
Hausa
 
Yă ɗiyan Ădam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jẽ muku, sună gaya muku ayőyiNato, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, băbu tsoro a kansu, kuma bă su yin baƙin ciki.

Ayah  7:36  الأية
    +/- -/+  
وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَاسْتَكْبَرُوا عَنْهَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Hausa
 
Kuma waɗanda suka ƙaryată game da ăyőyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne abőkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne.

Ayah  7:37  الأية
    +/- -/+  
فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَىٰ عَلَى اللهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِآيَاتِهِ ۚ أُولَٰئِكَ يَنَالُهُمْ نَصِيبُهُم مِّنَ الْكِتَابِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا جَاءَتْهُمْ رُسُلُنَا يَتَوَفَّوْنَهُمْ قَالُوا أَيْنَ مَا كُنتُمْ تَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ ۖ قَالُوا ضَلُّوا عَنَّا وَشَهِدُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ أَنَّهُمْ كَانُوا كَافِرِينَ
Hausa
 
To, wăne ne mafi zălunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kő kuwa ya ƙaryata game da ăyőyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littăfi yană sămunsu, har a lőkacin da ManzanninMu suka je musu, sună karɓar răyukansu, su ce: "Ĩnă abin da kuka kasance kună kira, baicin Allah?" Su ce: "Sun ɓace daga gare mu, "Kuma su yi shaida a kansu cẽwa lalle sũ, sun kasance kăfirai."

Ayah  7:38  الأية
    +/- -/+  
قَالَ ادْخُلُوا فِي أُمَمٍ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِكُم مِّنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ فِي النَّارِ ۖ كُلَّمَا دَخَلَتْ أُمَّةٌ لَّعَنَتْ أُخْتَهَا ۖ حَتَّىٰ إِذَا ادَّارَكُوا فِيهَا جَمِيعًا قَالَتْ أُخْرَاهُمْ لِأُولَاهُمْ رَبَّنَا هَٰؤُلَاءِ أَضَلُّونَا فَآتِهِمْ عَذَابًا ضِعْفًا مِّنَ النَّارِ ۖ قَالَ لِكُلٍّ ضِعْفٌ وَلَٰكِن لَّا تَعْلَمُونَ
Hausa
 
Ya ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabăninku, daga aljannu da mutăne, a cikin Wuta. A kő da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabă ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kăwo musu azăba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kőwane akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba."

Ayah  7:39  الأية
    +/- -/+  
وَقَالَتْ أُولَاهُمْ لِأُخْرَاهُمْ فَمَا كَانَ لَكُمْ عَلَيْنَا مِن فَضْلٍ فَذُوقُوا الْعَذَابَ بِمَا كُنتُمْ تَكْسِبُونَ
Hausa
 
Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: "To, bă ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azăba sabőda abin da kuka kasance kună tărăwa!"

Ayah  7:40  الأية
    +/- -/+  
إِنَّ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَاسْتَكْبَرُوا عَنْهَا لَا تُفَتَّحُ لَهُمْ أَبْوَابُ السَّمَاءِ وَلَا يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ حَتَّىٰ يَلِجَ الْجَمَلُ فِي سَمِّ الْخِيَاطِ ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُجْرِمِينَ
Hausa
 
Lalle ne waɗanda suka ƙaryată game da ăyőyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bă ză a bubbuɗe musu kőfőfin sama ba, kuma bă su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke săka wa măsu laifi.

Ayah  7:41  الأية
    +/- -/+  
لَهُم مِّن جَهَنَّمَ مِهَادٌ وَمِن فَوْقِهِمْ غَوَاشٍ ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِي الظَّالِمِينَ
Hausa
 
Sună da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke săka wa azzălumai.

Ayah  7:42  الأية
    +/- -/+  
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَا نُكَلِّفُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bă Mu ƙallafa wa rai făce iyăwarsa, Waɗannan ne abőkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne.

Ayah  7:43  الأية
    +/- -/+  
وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنْ غِلٍّ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمُ الْأَنْهَارُ ۖ وَقَالُوا الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي هَدَانَا لِهَٰذَا وَمَا كُنَّا لِنَهْتَدِيَ لَوْلَا أَنْ هَدَانَا اللهُ ۖ لَقَدْ جَاءَتْ رُسُلُ رَبِّنَا بِالْحَقِّ ۖ وَنُودُوا أَن تِلْكُمُ الْجَنَّةُ أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hausa
 
Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirăzansu, daga ƙiyayya, ƙőramu sună gudăna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: "Gődiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance mună iya shiryuwa ba, bă dőmin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jẽ mana da gaskiya." Kuma aka kira su, cẽwa: "Waccan Aljlnna an gădar da ku ita, sabőda abin da kuka kasance kună aikatăwa."

Ayah  7:44  الأية
    +/- -/+  
وَنَادَىٰ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ أَصْحَابَ النَّارِ أَن قَدْ وَجَدْنَا مَا وَعَدَنَا رَبُّنَا حَقًّا فَهَلْ وَجَدتُّم مَّا وَعَدَ رَبُّكُمْ حَقًّا ۖ قَالُوا نَعَمْ ۚ فَأَذَّنَ مُؤَذِّنٌ بَيْنَهُمْ أَن لَّعْنَةُ اللهِ عَلَى الظَّالِمِينَ
Hausa
 
Kuma 'yan Aljanna suka kirăyi 'yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sămi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sămi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya?" Suka ce: "Na'am." Sai mai sanarwa ya yi yẽkuwa, cẽwa: "La'anar Allah ta tabbata a kan azzălumai."

Ayah  7:45  الأية
    +/- -/+  
الَّذِينَ يَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللهِ وَيَبْغُونَهَا عِوَجًا وَهُم بِالْآخِرَةِ كَافِرُونَ
Hausa
 
"Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sună nẽman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lăhira, kăfirai ne."

Ayah  7:46  الأية
    +/- -/+  
وَبَيْنَهُمَا حِجَابٌ ۚ وَعَلَى الْأَعْرَافِ رِجَالٌ يَعْرِفُونَ كُلًّا بِسِيمَاهُمْ ۚ وَنَادَوْا أَصْحَابَ الْجَنَّةِ أَن سَلَامٌ عَلَيْكُمْ ۚ لَمْ يَدْخُلُوهَا وَهُمْ يَطْمَعُونَ
Hausa
 
Kuma a tsakăninsu akwai wani shămaki, kuma a kan A'arăf akwai wasu maza sună sanin kőwa da alămarsu; Kuma suka kirăyi abőkan Aljamia cẽwa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhăli kuwa sũ, sună tsammăni.

Ayah  7:47  الأية
    +/- -/+  
وَإِذَا صُرِفَتْ أَبْصَارُهُمْ تِلْقَاءَ أَصْحَابِ النَّارِ قَالُوا رَبَّنَا لَا تَجْعَلْنَا مَعَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ
Hausa
 
Kuma idan an jũyar da gannansu wajen abőkan wuta, su ce: "Yă Ubangijinmu! Kada Ka sanyă mu tăre da mutăne azzălumai."

Ayah  7:48  الأية
    +/- -/+  
وَنَادَىٰ أَصْحَابُ الْأَعْرَافِ رِجَالًا يَعْرِفُونَهُم بِسِيمَاهُمْ قَالُوا مَا أَغْنَىٰ عَنكُمْ جَمْعُكُمْ وَمَا كُنتُمْ تَسْتَكْبِرُونَ
Hausa
 
Kuma abőkan A'araf suka kirăyi wasu maza, sună sanin su da alămarsu, suka ce: "Tărawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kună yi na girman kai, bai wadătar ba daga barinku?"

Ayah  7:49  الأية
    +/- -/+  
أَهَٰؤُلَاءِ الَّذِينَ أَقْسَمْتُمْ لَا يَنَالُهُمُ اللهُ بِرَحْمَةٍ ۚ ادْخُلُوا الْجَنَّةَ لَا خَوْفٌ عَلَيْكُمْ وَلَا أَنتُمْ تَحْزَنُونَ
Hausa
 
"Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah bă zai săme su da rahama ba? Ku shiga Aljanna, băbu tsőro akanku, kuma ba ku zama kună baƙin ciki ba."

Ayah  7:50  الأية
    +/- -/+  
وَنَادَىٰ أَصْحَابُ النَّارِ أَصْحَابَ الْجَنَّةِ أَنْ أَفِيضُوا عَلَيْنَا مِنَ الْمَاءِ أَوْ مِمَّا رَزَقَكُمُ اللهُ ۚ قَالُوا إِنَّ اللهَ حَرَّمَهُمَا عَلَى الْكَافِرِينَ
Hausa
 
Kuma 'yan wuta suka kirăyi 'yan Aljanna cẽwa: "Ku zubo a kaumu daga ruwa kő kuwa daga abin da Allah Ya azurta ku." Su ce: "Lalle ne Allah Ya haramtă su a kan kăfirai."

Ayah  7:51  الأية
    +/- -/+  
الَّذِينَ اتَّخَذُوا دِينَهُمْ لَهْوًا وَلَعِبًا وَغَرَّتْهُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا ۚ فَالْيَوْمَ نَنسَاهُمْ كَمَا نَسُوا لِقَاءَ يَوْمِهِمْ هَٰذَا وَمَا كَانُوا بِآيَاتِنَا يَجْحَدُونَ
Hausa
 
"Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wăsa, kuma răyuwar dũniya ta rũɗe su." To, a yau Mună mantăwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ăyoyinMu sună musu.

Ayah  7:52  الأية
    +/- -/+  
وَلَقَدْ جِئْنَاهُم بِكِتَابٍ فَصَّلْنَاهُ عَلَىٰ عِلْمٍ هُدًى وَرَحْمَةً لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Hausa
 
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun jẽ musu da Littăfi, Mun bayyana Shi, daki-daki, a kan ilmi, yană shiriya da rahama ga mutăne waɗanda suke yin ĩmani.

Ayah  7:53  الأية
    +/- -/+  
هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا تَأْوِيلَهُ ۚ يَوْمَ يَأْتِي تَأْوِيلُهُ يَقُولُ الَّذِينَ نَسُوهُ مِن قَبْلُ قَدْ جَاءَتْ رُسُلُ رَبِّنَا بِالْحَقِّ فَهَل لَّنَا مِن شُفَعَاءَ فَيَشْفَعُوا لَنَا أَوْ نُرَدُّ فَنَعْمَلَ غَيْرَ الَّذِي كُنَّا نَعْمَلُ ۚ قَدْ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ
Hausa
 
Shin, sună jira, făce fassararsa, a rănar da fassararsa take zuwa, waɗanda saka manta da Shi daga gabăni, sună cẽwa: "Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu svun jẽ da gaskiya. To, shin, mună da wasu măsu cẽto, su yi cẽto gare mu, kő kuwa a mayar da mũ, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatăwa?" Lalle ne sun yi hasărar răyukansu, kuma abin da suka kasance sună ƙĩrƙirawa yă ɓace musu.

Ayah  7:54  الأية
    +/- -/+  
إِنَّ رَبَّكُمُ اللهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ يُغْشِي اللَّيْلَ النَّهَارَ يَطْلُبُهُ حَثِيثًا وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ وَالنُّجُومَ مُسَخَّرَاتٍ بِأَمْرِهِ ۗ أَلَا لَهُ الْخَلْقُ وَالْأَمْرُ ۗ تَبَارَكَ اللهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ
Hausa
 
Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwănaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yană sanya dare ya rufa yini, yană nẽman sa da gaggawa, kuma rănă da wată da taurări hőrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tă bayyana!

Ayah  7:55  الأية
    +/- -/+  
ادْعُوا رَبَّكُمْ تَضَرُّعًا وَخُفْيَةً ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ
Hausa
 
Ku kirăyi Ubangijinku da ƙanƙan da kai, da kuma a ɓőye: lalle ne Shĩ, bă Yă son măsuwuce iyăka.

Ayah  7:56  الأية
    +/- -/+  
وَلَا تُفْسِدُوا فِي الْأَرْضِ بَعْدَ إِصْلَاحِهَا وَادْعُوهُ خَوْفًا وَطَمَعًا ۚ إِنَّ رَحْمَتَ اللهِ قَرِيبٌ مِّنَ الْمُحْسِنِينَ
Hausa
 
Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a băyan gyaranta. Kuma ku kirăye shi sabőda tsőro da tsammăni; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga măsu kyautatăwa.

Ayah  7:57  الأية
    +/- -/+  
وَهُوَ الَّذِي يُرْسِلُ الرِّيَاحَ بُشْرًا بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا أَقَلَّتْ سَحَابًا ثِقَالًا سُقْنَاهُ لِبَلَدٍ مَّيِّتٍ فَأَنزَلْنَا بِهِ الْمَاءَ فَأَخْرَجْنَا بِهِ مِن كُلِّ الثَّمَرَاتِ ۚ كَذَٰلِكَ نُخْرِجُ الْمَوْتَىٰ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
Hausa
 
Kuma Shĩ ne wanda Yake aika iskőki, sună bishăra gaba ga rahamarSa, har idan sun ɗauki gizăgizai măsu nauyi, sai Mu kőra su ga wani gari matacce, sa'an nan Mu saukar da ruwa gare shi, sa'an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan 'ya'yan itĩce. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammăninku, kună tunăni.

Ayah  7:58  الأية
    +/- -/+  
وَالْبَلَدُ الطَّيِّبُ يَخْرُجُ نَبَاتُهُ بِإِذْنِ رَبِّهِ ۖ وَالَّذِي خَبُثَ لَا يَخْرُجُ إِلَّا نَكِدًا ۚ كَذَٰلِكَ نُصَرِّفُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَشْكُرُونَ
Hausa
 
Kuma gari mai kyau, tsirinsa yană fita da iznin Ubangijinsa, kuma wanda ya mũnana, (tsirinsa) bă ya fita, făce da wahala; kamar wannan ne, Muka sarrafa ăyőyi dőmin mutăne waɗanda suke gődẽwa.

Ayah  7:59  الأية
    +/- -/+  
لَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِ فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ
Hausa
 
Lalle ne, haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutănẽnsa, sai ya ce: "Yă mutănẽna! Ku bauta waAllah! Bă ku da wani abin bautăwa waninSa. Lalle ne nĩ, ină yimuku tsőron azăbar wani Yini mai girma."

Ayah  7:60  الأية
    +/- -/+  
قَالَ الْمَلَأُ مِن قَوْمِهِ إِنَّا لَنَرَاكَ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Hausa
 
Mashawarta daga mutănensa suka ce: "Lalle ne mu, haƙĩƙa, Mună ganin ka a cikin ɓata bayyananniya."

Ayah  7:61  الأية
    +/- -/+  
قَالَ يَا قَوْمِ لَيْسَ بِي ضَلَالَةٌ وَلَٰكِنِّي رَسُولٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ
Hausa
 
Ya ce: "Yă mutănena! Băbu ɓata guda gare ni, kuma amma nĩ Manzo ne daga ubangijin halittu !"

Ayah  7:62  الأية
    +/- -/+  
أُبَلِّغُكُمْ رِسَالَاتِ رَبِّي وَأَنصَحُ لَكُمْ وَأَعْلَمُ مِنَ اللهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Hausa
 
"Ină iyar muku da săƙonnin Ubangijina; kuma ină yi muku nasĩha, kuma ină sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba.

Ayah  7:63  الأية
    +/- -/+  
أَوَعَجِبْتُمْ أَن جَاءَكُمْ ذِكْرٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَلَىٰ رَجُلٍ مِّنكُمْ لِيُنذِرَكُمْ وَلِتَتَّقُوا وَلَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ
Hausa
 
"Shin, kună mămăkin cẽwa ambato yă zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji, daga gare ku, dőmin ya yi muku gargaɗi, kuma dőmin ku yi taƙawa, kuma tsammăninku ană jin ƙanku?"

Ayah  7:64  الأية
    +/- -/+  
فَكَذَّبُوهُ فَأَنجَيْنَاهُ وَالَّذِينَ مَعَهُ فِي الْفُلْكِ وَأَغْرَقْنَا الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا عَمِينَ
Hausa
 
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka tsĩrar da shi da waɗanda suke tăre da shi, a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ăyőyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance wasu mutăne ɗĩmautattu.

Ayah  7:65  الأية
    +/- -/+  
وَإِلَىٰ عَادٍ أَخَاهُمْ هُودًا ۗ قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Hausa
 
Kuma zuwa ga Ădăwa, ɗan'uwansu Hudu, ya ce: "Ya mutănena! Ku baută wa Allah! Bă ku da wani abin baută wa, waninSa. Shin fa, bă ză ku yi taƙawa ba?"

Ayah  7:66  الأية
    +/- -/+  
قَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَوْمِهِ إِنَّا لَنَرَاكَ فِي سَفَاهَةٍ وَإِنَّا لَنَظُنُّكَ مِنَ الْكَاذِبِينَ
Hausa
 
Mashawarta waɗanda suka kăfirta daga mutănensa suka ce: "Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Mună ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, Mună zaton ka daga maƙaryata."

Ayah  7:67  الأية
    +/- -/+  
قَالَ يَا قَوْمِ لَيْسَ بِي سَفَاهَةٌ وَلَٰكِنِّي رَسُولٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ
Hausa
 
Ya ce: "Yă mutănena! Băbu wata wauta a gare ni, kuma amma nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu!"

Ayah  7:68  الأية
    +/- -/+  
أُبَلِّغُكُمْ رِسَالَاتِ رَبِّي وَأَنَا لَكُمْ نَاصِحٌ أَمِينٌ
Hausa
 
Ină iyar muku da săƙonnin Ubangijina, kuma nĩ, gare ku, mai nasĩha ne amintacce.

Ayah  7:69  الأية
    +/- -/+  
أَوَعَجِبْتُمْ أَن جَاءَكُمْ ذِكْرٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَلَىٰ رَجُلٍ مِّنكُمْ لِيُنذِرَكُمْ ۚ وَاذْكُرُوا إِذْ جَعَلَكُمْ خُلَفَاءَ مِن بَعْدِ قَوْمِ نُوحٍ وَزَادَكُمْ فِي الْخَلْقِ بَسْطَةً ۖ فَاذْكُرُوا آلَاءَ اللهِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Hausa
 
"Shin, kuma kun yi mămăki cẽwa ambato daga Ubangijinku ya zo muku a kan wani namiji daga gare ku, dőmin ya yi muku gargaɗi? Kuma ku tună a lőkacin da Ya sanyă ku măsu mayẽwa daga băyan mutănen Nũhu, kuma Ya ƙăra muku zăti a cikin halitta. Sabőda haka ku tuna ni'imőmin Allah; tsammăninku kună cin nasara."

Ayah  7:70  الأية
    +/- -/+  
قَالُوا أَجِئْتَنَا لِنَعْبُدَ اللهَ وَحْدَهُ وَنَذَرَ مَا كَانَ يَعْبُدُ آبَاؤُنَا ۖ فَأْتِنَا بِمَا تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Hausa
 
Suka ce: "Shin, kă zo mana ne dőmin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance sună bauta wa? To, ka ző mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi idan kă kasance daga măsu gaskiya."

Ayah  7:71  الأية
    +/- -/+  
قَالَ قَدْ وَقَعَ عَلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ رِجْسٌ وَغَضَبٌ ۖ أَتُجَادِلُونَنِي فِي أَسْمَاءٍ سَمَّيْتُمُوهَا أَنتُمْ وَآبَاؤُكُم مَّا نَزَّلَ اللهُ بِهَا مِن سُلْطَانٍ ۚ فَانتَظِرُوا إِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُنتَظِرِينَ
Hausa
 
Ya ce: "Haƙĩƙa azăba da fushi sun auku a kanku daga Ubangijinku! Shin, kună jăyayya da ni a cikin wasu sunăye waɗanda kũ ne kuka yi musu sunăyen, kũ da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su? To, ku yi jira. Lalle ne ni, tăre da ku mai jira ne."

Ayah  7:72  الأية
    +/- -/+  
فَأَنجَيْنَاهُ وَالَّذِينَ مَعَهُ بِرَحْمَةٍ مِّنَّا وَقَطَعْنَا دَابِرَ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۖ وَمَا كَانُوا مُؤْمِنِينَ
Hausa
 
To, sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da waɗanda suke tăre da shi sabőda wata rahama daga gare Mu, kuma Muka katse ƙarshen waɗanda suka ƙaryata game da ăyőyinMu, kuma ba su kasance mũminaiba.

Ayah  7:73  الأية
    +/- -/+  
وَإِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحًا ۗ قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ قَدْ جَاءَتْكُم بَيِّنَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ ۖ هَٰذِهِ نَاقَةُ اللهِ لَكُمْ آيَةً ۖ فَذَرُوهَا تَأْكُلْ فِي أَرْضِ اللهِ ۖ وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوءٍ فَيَأْخُذَكُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Hausa
 
Kuma zuwa ga Samũdăwa ɗan'uwansu, Sălihu, ya ce: "Yă mutănena! Ku bauta wa Allah; bă ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙĩƙa hujja bayyananniya tă zo muku daga Ubangijinku! wannan răƙumar Allah ce, a gare ku, wata ăyă ce. Sai ku bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shăfe ta da wata cũta har azăba mai raɗaɗi ta kămă ku."

Ayah  7:74  الأية
    +/- -/+  
وَاذْكُرُوا إِذْ جَعَلَكُمْ خُلَفَاءَ مِن بَعْدِ عَادٍ وَبَوَّأَكُمْ فِي الْأَرْضِ تَتَّخِذُونَ مِن سُهُولِهَا قُصُورًا وَتَنْحِتُونَ الْجِبَالَ بُيُوتًا ۖ فَاذْكُرُوا آلَاءَ اللهِ وَلَا تَعْثَوْا فِي الْأَرْضِ مُفْسِدِينَ
Hausa
 
"Kuma ku tuna a lőkacin da Ya sanyă ku mamaya daga băyan Ădăwa kuma Ya zaunar da ku a cikin ƙasa, kună riƙon manyan gidăje daga tuddanta, kuma kună sassaƙar ɗăkuna daga duwătsu; sabőda haka ku tuna ni'imőmin Allah, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuna măsu fasădi."

Ayah  7:75  الأية
    +/- -/+  
قَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا مِن قَوْمِهِ لِلَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا لِمَنْ آمَنَ مِنْهُمْ أَتَعْلَمُونَ أَنَّ صَالِحًا مُّرْسَلٌ مِّن رَّبِّهِ ۚ قَالُوا إِنَّا بِمَا أُرْسِلَ بِهِ مُؤْمِنُونَ
Hausa
 
Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka raunanar, ga waɗanda suka yi ĩmăni daga gare su: "Shin, kună sanin cẽwaSălihu manzo ne daga Ubangijinsa?" Suka ce: "Lalle ne mũ, da abin daaka aiko shi, măsu ĩmăni ne."

Ayah  7:76  الأية
    +/- -/+  
قَالَ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا إِنَّا بِالَّذِي آمَنتُم بِهِ كَافِرُونَ
Hausa
 
Waɗanda suka yi girman kai suka ce: "Lalle ne mu, ga abin da kuka yi ĩmăni da shi kăfirai ne."

Ayah  7:77  الأية
    +/- -/+  
فَعَقَرُوا النَّاقَةَ وَعَتَوْا عَنْ أَمْرِ رَبِّهِمْ وَقَالُوا يَا صَالِحُ ائْتِنَا بِمَا تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ الْمُرْسَلِينَ
Hausa
 
Sai suka sőke răƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: "Yă Sălihu! Ka ző mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi, idan kă kasance daga manzanni !"

Ayah  7:78  الأية
    +/- -/+  
فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ
Hausa
 
Sai tsăwa ta kămă su, sabőda haka suka wăyi gari a cikin gidansu guggurfăne!

Ayah  7:79  الأية
    +/- -/+  
فَتَوَلَّىٰ عَنْهُمْ وَقَالَ يَا قَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَالَةَ رَبِّي وَنَصَحْتُ لَكُمْ وَلَٰكِن لَّا تُحِبُّونَ النَّاصِحِينَ
Hausa
 
Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Ya mutănena! Lalle ne, haƙĩƙa, nă iyar muku damanzancin Ubangijina. Kuma nă yi muku nasĩha kuma amma bă ku son măsu nasĩha!"