Shĩ ne wanda Ya fitar da waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littãfi, daga
gidãjẽnsu da kõra ta farko. Ba ku yi zaton sunã fita ba, kuma sun tabbata cẽwa
gãnuwõwinsu mãsu tsare su ne daga Allah, sai Allah Ya jẽ musu daga wajen da ba
su yi zato ba, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukãtansu, sunã rushe gidãjensu da
hannãyensu da kuma hannãyen mũminai. To, ku lũra fa, ya mãsu basĩrõri.
Kuma abin da Allah Ya sanya ya zama ganĩma ga ManzonSa, daga gare su, to, ba ku
yi hari a kansa da dawãki ko rãƙuma ba amma Allah ne Ya rinjãyar da ManzanninSa
a kan wanda Yake so, kuma Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme.
Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga ManzonSa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na
Allah ne, kuma na ManzonSa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da
ɗan hanya ( matafiyi) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta
daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane
ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba
ne.
(Ku yi mãmãki) Ga matalauta mãsu hijira waɗanda aka fitar daga gidãjẽnsu da
dũkiyõyinsu, sunã nẽman falala daga Allah da kuma yarda, kuma sunã taimakon
Allah da ManzonSa! Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya.
Da waɗanda suka zaunar da gidãjensu (ga Musulunci) kuma (suka zãɓi) ĩmãni, a
gabãnin zuwansu, sunã son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma bã su tunãnin
wata bukãta a cikin ƙirãzansu daga abin da aka bai wa muhãjirĩna, kuma sunã
fĩfĩta waɗansu a kan kãwunansu, kuma ko dã sunã da wata larũra. Wanda ya sãɓã wa
rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
Kuma waɗanda suka zõ daga bãyansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a
gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya
wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Lalle Kai
ne Mai tausayi, Mai jin ƙai.
Ashe, ba ka ga waɗanda suka yi munãfinci ba, sunã cẽwa ga 'yan'uwansu, waɗanda
suka kãfirta daga Mazõwa Littafi, "Lalle idan an fitar da ku, lalle zã mu fita
tãre da ku, kuma bã zã mu yi ɗã'a ga kõwa ba game da ku, har abada, kuma lalle
idan an yãƙe ku, lalle zã mu taimake ku haƙĩƙatan?" Alhãli kuwa Allah na shaidar
cẽwa lalle sũ tabbas, maƙaryata ne.
Lalle idan an fitar da su, bã zã su fita tãre da su ba kuma lalle idan an yãƙe
su bã zã su taimake su ba, kuma lalle idan sun taimake su lalle ne, haƙĩƙatan,
zã su jũyar da bãyansu dõmin gudu, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba.
Bã su iya yãƙar ku gabã ɗaya, fãce a cikin garũruwa mãsu gãnuwa da gãruna, kõ
kuma daga bãyan katangu. Yãkinsu a tsãkaninsu mai tsanani ne, kanã zaton su a
haɗe, alhãli kuwa zukãtansu dabam- dabam suke. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle wasu
irin mutane ne da bã su hankalta.
Kamar misãlin Shaiɗan a lõkacin da yake cẽ wa mutum, "Ka kãfirta," To, a lõkacin
da ya kãfirta ɗin, ya ce (masa): "Lalle bãbu ruwãna da kai. Lalle ni inã tsõron
Allah Ubangijin halitta!"
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma rai ya dũbi abin da ya
gabãtar dõmin gõbe, kuma ku bi Allah da taƙawa. lalle Allah, Mai ƙididdigewa ne
ga abin da kuke aikatãwa.
Dã Mun saukar da wannan Alƙur'ani a kan dũtse, dã lalle kã ga dũtsen yanã mai
tawãli'u, mai tsattsãgẽwa sabõda tsõron Allah, kuma waɗancan misãlai Munã
bayyana su ne ga mutãne, da fatan za su yi tunãni.
Shĩ ne Allah, wanda bãbu abin bautãwa fãce shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci,
Mai amintarwa, Mai Tsarẽwa, Mabuwãyi, Mai tastãwa Mai nuna isa, tsarki ya
tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirki da Shi.
Shĩ ne Allah, Mai halitta, Mai ginãwa, Mai sũrantãwa.Yanã da sũnãye mãsu kyau,
abin da ke a cikin sammai da ƙasa sunã tsarkake Shi, kuma Shĩ ne Mabuwãyi,Mai
hikima.