Prev  

22. Surah Al-Hajj سورة الحج

  Next  
1st Ayah  1  الأية ١الأولي
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمْ ۚ إِنَّ زَلْزَلَةَ السَّاعَةِ شَيْءٌ عَظِيمٌ
Ya ayyuha annasuittaqoo rabbakum inna zalzalata assaAAati shay-onAAatheem

Hausa
 
Yă ku mutăne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Lalle ne girgizar ƙasa ta tsayuwar Sa'a wata aba ce mai girma.

Ayah  22:2  الأية
يَوْمَ تَرَوْنَهَا تَذْهَلُ كُلُّ مُرْضِعَةٍ عَمَّا أَرْضَعَتْ وَتَضَعُ كُلُّ ذَاتِ حَمْلٍ حَمْلَهَا وَتَرَى النَّاسَ سُكَارَىٰ وَمَا هُم بِسُكَارَىٰ وَلَٰكِنَّ عَذَابَ اللهِ شَدِيدٌ
Yawma tarawnaha tathhalu kullumurdiAAatin AAamma ardaAAat watadaAAukullu thati hamlin hamlaha wataraannasa sukara wama hum bisukarawalakinna AAathaba Allahi shadeed

Hausa
 
A rănar da kuke ganin ta dukan mai shăyar da măma tană shagala daga abin da ta shăyar, kuma dukan mai ciki tană haihuwar cikinta, kuma kană ganin mutăne sună măsu măyẽ alhăli kuwa su bă măsu măye ba, amma azăbar Allah ce mai tsanani.

Ayah  22:3  الأية
وَمِنَ النَّاسِ مَن يُجَادِلُ فِي اللهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَيَتَّبِعُ كُلَّ شَيْطَانٍ مَّرِيدٍ
Wamina annasi man yujadilufee Allahi bighayri AAilmin wayattabiAAu kulla shaytaninmareed

Hausa
 
Akwai daga mutăne wanda yake yin musũ ga sha'anin Allah bă da wani ilmi ba, kuma yană biyar kőwane Shaiɗan mai taurin kai.

Ayah  22:4  الأية
كُتِبَ عَلَيْهِ أَنَّهُ مَن تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُ يُضِلُّهُ وَيَهْدِيهِ إِلَىٰ عَذَابِ السَّعِيرِ
Kutiba AAalayhi annahu man tawallahufaannahu yudilluhu wayahdeehi ila AAathabi assaAAeer

Hausa
 
An wajabta masa cẽwa wanda ya jiɓince shi, to, lalle ne sai ya ɓatar da shi, kuma ya shiryar da shi zuwa ga azăbar sa'ĩr.

Ayah  22:5  الأية
يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِن كُنتُمْ فِي رَيْبٍ مِّنَ الْبَعْثِ فَإِنَّا خَلَقْنَاكُم مِّن تُرَابٍ ثُمَّ مِن نُّطْفَةٍ ثُمَّ مِنْ عَلَقَةٍ ثُمَّ مِن مُّضْغَةٍ مُّخَلَّقَةٍ وَغَيْرِ مُخَلَّقَةٍ لِّنُبَيِّنَ لَكُمْ ۚ وَنُقِرُّ فِي الْأَرْحَامِ مَا نَشَاءُ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى ثُمَّ نُخْرِجُكُمْ طِفْلًا ثُمَّ لِتَبْلُغُوا أَشُدَّكُمْ ۖ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰ أَرْذَلِ الْعُمُرِ لِكَيْلَا يَعْلَمَ مِن بَعْدِ عِلْمٍ شَيْئًا ۚ وَتَرَى الْأَرْضَ هَامِدَةً فَإِذَا أَنزَلْنَا عَلَيْهَا الْمَاءَ اهْتَزَّتْ وَرَبَتْ وَأَنبَتَتْ مِن كُلِّ زَوْجٍ بَهِيجٍ
Ya ayyuha annasuin kuntum fee raybin mina albaAAthi fa-inna khalaqnakummin turabin thumma min nutfatin thumma minAAalaqatin thumma min mudghatin mukhallaqatin waghayrimukhallaqatin linubayyina lakum wanuqirru fee al-arhami manashao ila ajalin musamman thumma nukhrijukum tiflanthumma litablughoo ashuddakum waminkum man yutawaffawaminkum man yuraddu ila arthali alAAumuri likaylayaAAlama min baAAdi AAilmin shay-an watara al-ardahamidatan fa-itha anzalna AAalayhaalmaa ihtazzat warabat waanbatat min kulli zawjin baheej

Hausa
 
Ya ku mutăne! Idan kun kasance a cikin shakka a Tăshin ˇiyăma, to, lalle ne Mũ, Man halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudăjin jini, sa'an nan kuma daga taőka wadda ake halittăwa da wadda ba a halittawa dőmin, Mu bayyana muku. Kuma Mună tab batar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma Mună fitar da ku kună jărĩri, sa'an nan kuma dőmin ku kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin răyuwa dőmin kada ya san kőme a băyan ya sani. Kuma kană ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kőwane nau'i mai ban sha'awa.

Ayah  22:6  الأية
ذَٰلِكَ بِأَنَّ اللهَ هُوَ الْحَقُّ وَأَنَّهُ يُحْيِي الْمَوْتَىٰ وَأَنَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Thalika bi-anna Allaha huwa alhaqquwaannahu yuhyee almawta waannahu AAala kullishay-in qadeer

Hausa
 
Wancan ne dőmin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne shi Yake răyar da matattu, kuma lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kőme.

Ayah  22:7  الأية
وَأَنَّ السَّاعَةَ آتِيَةٌ لَّا رَيْبَ فِيهَا وَأَنَّ اللهَ يَبْعَثُ مَن فِي الْقُبُورِ
Waanna assaAAata atiyatunla rayba feeha waanna Allaha yabAAathu manfee alquboor

Hausa
 
Kuma lalle ne Sa'ar Tăshin ˇiyăma mai zuwa ce, băbu shakka a cikinta kuma lalle ne Allah Yană tăyar da waɗanda suke a cikin ƙaburbura.

Ayah  22:8  الأية
وَمِنَ النَّاسِ مَن يُجَادِلُ فِي اللهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَلَا هُدًى وَلَا كِتَابٍ مُّنِيرٍ
Wamina annasi man yujadilufee Allahi bighayri AAilmin wala hudan walakitabin muneer

Hausa
 
Kuma daga mutăne akwai mai yin musu ga Allah bă da wani ilmi ba kuma bă da wata shiriya ba, kuma bă da wani littăfi mai haskakăwa ba.

Ayah  22:9  الأية
ثَانِيَ عِطْفِهِ لِيُضِلَّ عَن سَبِيلِ اللهِ ۖ لَهُ فِي الدُّنْيَا خِزْيٌ ۖ وَنُذِيقُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَذَابَ الْحَرِيقِ
Thaniya AAitfihi liyudillaAAan sabeeli Allahi lahu fee addunyakhizyun wanutheequhu yawma alqiyamati AAathabaalhareeq

Hausa
 
Yană mai karkatar da săshensa dőmin ya ɓatar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yană da wani wulăkanci a dũniya, kuma Mună ɗanɗana masa azăbar gőbara a Rănar ˇiyăma.

Ayah  22:10  الأية
ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتْ يَدَاكَ وَأَنَّ اللهَ لَيْسَ بِظَلَّامٍ لِّلْعَبِيدِ
Thalika bima qaddamat yadakawaanna Allaha laysa bithallaminlilAAabeed

Hausa
 
(A ce masa): "Wancan azaba sabőda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma lalle ne Allah bai zama Mai zălunci ga băyinSa ba."

Ayah  22:11  الأية
وَمِنَ النَّاسِ مَن يَعْبُدُ اللهَ عَلَىٰ حَرْفٍ ۖ فَإِنْ أَصَابَهُ خَيْرٌ اطْمَأَنَّ بِهِ ۖ وَإِنْ أَصَابَتْهُ فِتْنَةٌ انقَلَبَ عَلَىٰ وَجْهِهِ خَسِرَ الدُّنْيَا وَالْآخِرَةَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْخُسْرَانُ الْمُبِينُ
Wamina annasi man yaAAbuduAllaha AAala harfin fa-in asabahukhayrun itmaanna bihi wa-in asabat-hu fitnatuninqalaba AAala wajhihi khasira addunya wal-akhiratathalika huwa alkhusranu almubeen

Hausa
 
Kuma daga mutăne akwai mai bauta wa Allah a kan wani gefe. Sa'an nan idan wani alhẽri ya săme shi, sai ya natsu da shi, kuma idan wata fitina ta săme shi, sai ya jũya băya a kan fuskarsa. Yă yi hasărar dũniya da Lăhira. Waccan ita ce hasăra bayyananna.

Ayah  22:12  الأية
يَدْعُو مِن دُونِ اللهِ مَا لَا يَضُرُّهُ وَمَا لَا يَنفَعُهُ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الضَّلَالُ الْبَعِيدُ
YadAAoo min dooni Allahi ma layadurruhu wama la yanfaAAuhu thalikahuwa addalalu albaAAeed

Hausa
 
Yană kiran baicin Allah, abin da bă ya cũtarsa da abin da bă ya amfăninsa! waccan ita ce ɓata mai nĩsa.

Ayah  22:13  الأية
يَدْعُو لَمَن ضَرُّهُ أَقْرَبُ مِن نَّفْعِهِ ۚ لَبِئْسَ الْمَوْلَىٰ وَلَبِئْسَ الْعَشِيرُ
YadAAoo laman darruhu aqrabu minnafAAihi labi/sa almawla walabi/sa alAAasheer

Hausa
 
Yană kiran wanda yake lalle cũtarwarsa ce mafi kusa daga amfăninsa! Lalle ne, tir da shi ya zama majiɓinci, kuma tir da ya zama abőkin zama!

Ayah  22:14  الأية
إِنَّ اللهَ يُدْخِلُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ۚ إِنَّ اللهَ يَفْعَلُ مَا يُرِيدُ
Inna Allaha yudkhilu allatheenaamanoo waAAamiloo assalihati jannatintajree min tahtiha al-anharu inna AllahayafAAalu ma yureed

Hausa
 
Lalle ne Allah Yană shigar da waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidăjen Aljanna, ƙoramu na gudăna daga ƙarƙashinsu. Lalle ne Allah Yană aikata abin da Yake nufi.

Ayah  22:15  الأية
مَن كَانَ يَظُنُّ أَن لَّن يَنصُرَهُ اللهُ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ فَلْيَمْدُدْ بِسَبَبٍ إِلَى السَّمَاءِ ثُمَّ لْيَقْطَعْ فَلْيَنظُرْ هَلْ يُذْهِبَنَّ كَيْدُهُ مَا يَغِيظُ
Man kana yathunnu anlan yansurahu Allahu fee addunya wal-akhiratifalyamdud bisababin ila assama-i thummaliyaqtaAA falyanthur hal yuthhibannakayduhu ma yagheeth

Hausa
 
Wanda ya kasance yană zaton cẽwa Allah bă zai taimake shi ba a cikin dũniya da Lăhira to sai ya mĩƙa wata igiya zuwa sama, sa'an nan kuma ya yanke ta, sa'an nan ya dũba. Shin, ko lalle kaidinsa zai gusar da abin da yake ji na takaici?

Ayah  22:16  الأية
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلْنَاهُ آيَاتٍ بَيِّنَاتٍ وَأَنَّ اللهَ يَهْدِي مَن يُرِيدُ
Wakathalika anzalnahu ayatinbayyinatin waanna Allaha yahdee man yureed

Hausa
 
Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alƙur'ăni) yană ăyőyi bayyanannu. Kuma lalle ne Allah Yană shiryar da wanda Yake nufi.

Ayah  22:17  الأية
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَادُوا وَالصَّابِئِينَ وَالنَّصَارَىٰ وَالْمَجُوسَ وَالَّذِينَ أَشْرَكُوا إِنَّ اللهَ يَفْصِلُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۚ إِنَّ اللهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ
Inna allatheena amanoo wallatheenahadoo wassabi-eena wannasarawalmajoosa wallatheena ashrakoo inna Allahayafsilu baynahum yawma alqiyamati inna AllahaAAala kulli shay-in shaheed

Hausa
 
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmăni da waɗanda suka tũba (Yahũdu) da waɗanda suka karkace (Saba'ăwa) da Nasăra da Majũsăwa da waɗanda suka yi shirka, lalle ne Allah Yană yin hukunci a tsakăninsu a Ranăr ˇiyăma.Lalle ne Allah Mahalarci ne a kan dukkan kőme.

Ayah  22:18  الأية
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللهَ يَسْجُدُ لَهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَمَن فِي الْأَرْضِ وَالشَّمْسُ وَالْقَمَرُ وَالنُّجُومُ وَالْجِبَالُ وَالشَّجَرُ وَالدَّوَابُّ وَكَثِيرٌ مِّنَ النَّاسِ ۖ وَكَثِيرٌ حَقَّ عَلَيْهِ الْعَذَابُ ۗ وَمَن يُهِنِ اللهُ فَمَا لَهُ مِن مُّكْرِمٍ ۚ إِنَّ اللهَ يَفْعَلُ مَا يَشَاءُ ۩
Alam tara anna Allaha yasjudu lahuman fee assamawati waman fee al-ardiwashshamsu walqamaru wannujoomu waljibaluwashshajaru waddawabbu wakatheerun minaannasi wakatheerun haqqa AAalayhi alAAathabuwaman yuhini Allahu fama lahu min mukrimin inna AllahayafAAalu ma yasha/

Hausa
 
Ashe, ba ka gani ba, lalle Allah, wanda yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasa yană yin sujada a gare shi, da kuma răna da wată da taurări da duwătsu da ităce da dabbőbi, da kuma măsu yawa daga mutăne? Kuma waɗansu măsu yawa azăba tă tabbata a kansu. Kuma wanda Allah Ya wulăkantar, to, bă ya da wani mai girmamăwa. Kuma Lalle ne Allah Yană aikata abin da Yake so.

Ayah  22:19  الأية
هَٰذَانِ خَصْمَانِ اخْتَصَمُوا فِي رَبِّهِمْ ۖ فَالَّذِينَ كَفَرُوا قُطِّعَتْ لَهُمْ ثِيَابٌ مِّن نَّارٍ يُصَبُّ مِن فَوْقِ رُءُوسِهِمُ الْحَمِيمُ
Hathani khasmani ikhtasamoofee rabbihim fallatheena kafaroo quttiAAatlahum thiyabun min narin yusabbu min fawqiruoosihimu alhameem

Hausa
 
waɗannan ƙungiyőyi biyu ne măsu husũma, sun yi husũma ga sha'anin Ubangijinsu. To, waɗanda suka kăfirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, ană zuba tafasasshen ruwa daga bisa kăwunansu.

Ayah  22:20  الأية
يُصْهَرُ بِهِ مَا فِي بُطُونِهِمْ وَالْجُلُودُ
Yusharu bihi ma fee butoonihimwaljulood

Hausa
 
Da shĩ ake narkar da abin da yake a cikin cikunansu da fătun jikinsu.

Ayah  22:21  الأية
وَلَهُم مَّقَامِعُ مِنْ حَدِيدٍ
Walahum maqamiAAu min hadeed

Hausa
 
Kuma sună da waɗansu gwalmőmin dũka na baƙin ƙarfe.

Ayah  22:22  الأية
كُلَّمَا أَرَادُوا أَن يَخْرُجُوا مِنْهَا مِنْ غَمٍّ أُعِيدُوا فِيهَا وَذُوقُوا عَذَابَ الْحَرِيقِ
Kullama aradoo an yakhrujoominha min ghammin oAAeedoo feeha wathooqooAAathaba alhareeq

Hausa
 
A kőyaushe suka yi nufin fita daga gare ta, daga baƙin ciki, sai a mayar da su a cikinta, (a ce musu) "Ku ɗanɗani azăbar gőbara."

Ayah  22:23  الأية
إِنَّ اللهَ يُدْخِلُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ يُحَلَّوْنَ فِيهَا مِنْ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٍ وَلُؤْلُؤًا ۖ وَلِبَاسُهُمْ فِيهَا حَرِيرٌ
Inna Allaha yudkhilu allatheenaamanoo waAAamiloo assalihati jannatintajree min tahtiha al-anharu yuhallawnafeeha min asawira min thahabin walu/lu-anwalibasuhum feeha hareer

Hausa
 
Lalle ne, Allah Yana shigar da waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidăjen Aljanna, ƙoramu sună gudăna daga ƙarƙashinsu, ană ƙawăta su, a cikinsu, da waɗansu mundăye na zĩnări da lu'u-lu'u. Kuma tufăfinsu a cikinsu alharĩni ne.

Ayah  22:24  الأية
وَهُدُوا إِلَى الطَّيِّبِ مِنَ الْقَوْلِ وَهُدُوا إِلَىٰ صِرَاطِ الْحَمِيدِ
Wahudoo ila attayyibimina alqawli wahudoo ila sirati alhameed

Hausa
 
Kuma an shiryar da su zuwa ga mai kyau na zance kuma an shiryar da su zuwa ga, hanyar wanda ake gode wa.

Ayah  22:25  الأية
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللهِ وَالْمَسْجِدِ الْحَرَامِ الَّذِي جَعَلْنَاهُ لِلنَّاسِ سَوَاءً الْعَاكِفُ فِيهِ وَالْبَادِ ۚ وَمَن يُرِدْ فِيهِ بِإِلْحَادٍ بِظُلْمٍ نُّذِقْهُ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ
Inna allatheena kafaroo wayasuddoonaAAan sabeeli Allahi walmasjidi alharamiallathee jaAAalnahu linnasi sawaanalAAakifu feehi walbadi waman yurid feehibi-ilhadin bithulmin nuthiqhu min AAathabinaleem

Hausa
 
Lalle ne waɗanda suka kăfirta kuma suka taushe (mutăne) daga hanyar Allah da masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutăne alhăli kuwa mazauni a ciki da baƙauye daidai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar da gaskiya a cikinsa da zălunci ză Mu ɗanɗana masa daga wata azăba mai raɗadi.

Ayah  22:26  الأية
وَإِذْ بَوَّأْنَا لِإِبْرَاهِيمَ مَكَانَ الْبَيْتِ أَن لَّا تُشْرِكْ بِي شَيْئًا وَطَهِّرْ بَيْتِيَ لِلطَّائِفِينَ وَالْقَائِمِينَ وَالرُّكَّعِ السُّجُودِ
Wa-ith bawwa/na li-ibraheemamakana albayti an la tushrik bee shay-an watahhirbaytiya litta-ifeena walqa-imeenawarrukkaAAi assujood

Hausa
 
Kuma a lőkacin da Muka iyăkance wa Ibrăhim wurin ¦akin (Muka ce masa), "Kada ka haɗa kőme da Ni ga bauta, kuma ka tsarkake ¦ăkiNa dőmin măsu ɗawăfi da măsu tsayuwa da măsu ruku'u da măsu sujada.

Ayah  22:27  الأية
وَأَذِّن فِي النَّاسِ بِالْحَجِّ يَأْتُوكَ رِجَالًا وَعَلَىٰ كُلِّ ضَامِرٍ يَأْتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٍ
Waaththin fee annasibilhajji ya/tooka rijalan waAAalakulli damirin ya/teena min kulli fajjin AAameeq

Hausa
 
"Kuma ka yi yẽkuwa ga mutăne da wajabcin Hajji su je maka suna măsu tafiya da ƙafăfu da kuma a kan kőwane maɗankwarin răƙumi măsu zuwa daga kőwane rango mai zurfi."

Ayah  22:28  الأية
لِّيَشْهَدُوا مَنَافِعَ لَهُمْ وَيَذْكُرُوا اسْمَ اللهِ فِي أَيَّامٍ مَّعْلُومَاتٍ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّن بَهِيمَةِ الْأَنْعَامِ ۖ فَكُلُوا مِنْهَا وَأَطْعِمُوا الْبَائِسَ الْفَقِيرَ
Liyashhadoo manafiAAa lahum wayathkurooisma Allahi fee ayyamin maAAloomatin AAalama razaqahum min baheemati al-anAAami fakuloo minhawaatAAimoo alba-isa alfaqeer

Hausa
 
"Dőmin su halarci abũbuwan amfăni a gare su, kuma su ambăci sunan Allah a cikin 'yan kwănuka sanannu sabőda abin da Ya azurta su da shĩ daga dabbőbin jin dăɗi. Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci."

Ayah  22:29  الأية
ثُمَّ لْيَقْضُوا تَفَثَهُمْ وَلْيُوفُوا نُذُورَهُمْ وَلْيَطَّوَّفُوا بِالْبَيْتِ الْعَتِيقِ
Thumma lyaqdoo tafathahum walyoofoonuthoorahum walyattawwafoo bilbaytialAAateeq

Hausa
 
"Sa'an nan kuma sai su ƙăre ibădarsu da gusar da ƙazanta, knma sai su cika alkawuransu kuma sai su yi ɗawăfi (sună gẽwaya) ga ¦ăkin nin 'yantacce."

Ayah  22:30  الأية
ذَٰلِكَ وَمَن يُعَظِّمْ حُرُمَاتِ اللهِ فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ عِندَ رَبِّهِ ۗ وَأُحِلَّتْ لَكُمُ الْأَنْعَامُ إِلَّا مَا يُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ ۖ فَاجْتَنِبُوا الرِّجْسَ مِنَ الْأَوْثَانِ وَاجْتَنِبُوا قَوْلَ الزُّورِ
Thalika waman yuAAaththimhurumati Allahi fahuwa khayrun lahu AAindarabbihi waohillat lakumu al-anAAamu illa mayutla AAalaykum fajtaniboo arrijsa minaal-awthani wajtaniboo qawla azzoor

Hausa
 
Wancan ne. Kuma wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah to shĩ ne mafĩfĩci a gare shi, a wurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbőbin ni'ima făce abin da ake karantăwa a kanku. Sabőda haka ku nĩsanci ƙazanta daga gumăka kuma ku nĩsanci ƙazanta daga shaidar zur.

Ayah  22:31  الأية
حُنَفَاءَ لِلَّهِ غَيْرَ مُشْرِكِينَ بِهِ ۚ وَمَن يُشْرِكْ بِاللهِ فَكَأَنَّمَا خَرَّ مِنَ السَّمَاءِ فَتَخْطَفُهُ الطَّيْرُ أَوْ تَهْوِي بِهِ الرِّيحُ فِي مَكَانٍ سَحِيقٍ
Hunafaa lillahi ghayramushrikeena bihi waman yushrik billahi fakaannamakharra mina assama-i fatakhtafuhu attayruaw tahwee bihi arreehu fee makanin saheeq

Hausa
 
Kuna măsu tsayuwa ga gaskiya dőmin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba. Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yană kamar abin da ya făɗo daga sama, sa'an nan tsuntsăye su cafe shi, ko iska ta făɗa da shi a cikin wani wuri mai nisa.

Ayah  22:32  الأية
ذَٰلِكَ وَمَن يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللهِ فَإِنَّهَا مِن تَقْوَى الْقُلُوبِ
Thalika waman yuAAaththimshaAAa-ira Allahi fa-innaha min taqwaalquloob

Hausa
 
Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibădődin Allah, to, lalle ne ita (girmamăwar) tană daga ayyukan zukăta na ibăda.

Ayah  22:33  الأية
لَكُمْ فِيهَا مَنَافِعُ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى ثُمَّ مَحِلُّهَا إِلَى الْبَيْتِ الْعَتِيقِ
Lakum feeha manafiAAu ilaajalin musamman thumma mahilluha ila albaytialAAateeq

Hausa
 
Kuna da waɗansu abũbuwan amfăni a cikinta (dabbar hadaya) har ya zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma wurin halattăta zuwa ga ¦ăkin 'yantacce ne.

Ayah  22:34  الأية
وَلِكُلِّ أُمَّةٍ جَعَلْنَا مَنسَكًا لِّيَذْكُرُوا اسْمَ اللهِ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّن بَهِيمَةِ الْأَنْعَامِ ۗ فَإِلَٰهُكُمْ إِلَٰهٌ وَاحِدٌ فَلَهُ أَسْلِمُوا ۗ وَبَشِّرِ الْمُخْبِتِينَ
Walikulli ommatin jaAAalna mansakanliyathkuroo isma Allahi AAala marazaqahum min baheemati al-anAAami fa-ilahukum ilahunwahidun falahu aslimoo wabashshiri almukhbiteen

Hausa
 
Kuma ga kőwace al'umma Mun sanya ibădar yanka, dőmin su ambaci sũnan Allah a kan abin da Ya azurta su da shi daga dabbőbin ni'ima. Sa'an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne Guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushăra ga măsu ƙanƙantar da kai.

Ayah  22:35  الأية
الَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ اللهُ وَجِلَتْ قُلُوبُهُمْ وَالصَّابِرِينَ عَلَىٰ مَا أَصَابَهُمْ وَالْمُقِيمِي الصَّلَاةِ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ
Allatheena itha thukiraAllahu wajilat quloobuhum wassabireenaAAala ma asabahum walmuqeemee assalatiwamimma razaqnahum yunfiqoon

Hausa
 
Waɗanda suke idan an ambaci Allah sai zukătansu su firgita, da măsu haƙuri a kan abin da ya săme su, da măsu tsayar da salla, kuma sună ciyarwa daga abin da Muka azurta su.

Ayah  22:36  الأية
وَالْبُدْنَ جَعَلْنَاهَا لَكُم مِّن شَعَائِرِ اللهِ لَكُمْ فِيهَا خَيْرٌ ۖ فَاذْكُرُوا اسْمَ اللهِ عَلَيْهَا صَوَافَّ ۖ فَإِذَا وَجَبَتْ جُنُوبُهَا فَكُلُوا مِنْهَا وَأَطْعِمُوا الْقَانِعَ وَالْمُعْتَرَّ ۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرْنَاهَا لَكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Walbudna jaAAalnahalakum min shaAAa-iri Allahi lakum feehakhayrun fathkuroo isma Allahi AAalayhasawaffa fa-itha wajabat junoobuhafakuloo minha waatAAimoo alqaniAAa walmuAAtarrakathalika sakhkharnaha lakum laAAallakumtashkuroon

Hausa
 
Kuma răƙuman, Mun sanya su a gare ku, a ibădőjin Allah. Kună da wani alhẽri babba a cikinsu. Sai ku ambaci sũnan Allah a kansu sună tsaye a kan ƙafăfu uku. Sa'an nan idan săsanninsu suka făɗi, to, ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mai wadar zũci da mai bara. Kamar haka Muka hőre muku su, tsammăninku kună gődẽwa.

Ayah  22:37  الأية
لَن يَنَالَ اللهَ لُحُومُهَا وَلَا دِمَاؤُهَا وَلَٰكِن يَنَالُهُ التَّقْوَىٰ مِنكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرَهَا لَكُمْ لِتُكَبِّرُوا اللهَ عَلَىٰ مَا هَدَاكُمْ ۗ وَبَشِّرِ الْمُحْسِنِينَ
Lan yanala Allaha luhoomuhawala dimaoha walakin yanaluhuattaqwa minkum kathalika sakhkharahalakum litukabbiroo Allaha AAala ma hadakumwabashshiri almuhsineen

Hausa
 
Nămőminsu bă za su sămi Allah ba haka jinainansu amma taƙawa daga gare ku tană, sămun Sa. Kamar haka Ya hőre su sabőda ku dőmin ku girmama Allah sabőda shiriyar da Ya yi muku. Kuma ka yi bushăra ga măsu kyautata yi.

Ayah  22:38  الأية
إِنَّ اللهَ يُدَافِعُ عَنِ الَّذِينَ آمَنُوا ۗ إِنَّ اللهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ خَوَّانٍ كَفُورٍ
Inna Allaha yudafiAAu AAaniallatheena amanoo inna Allaha la yuhibbukulla khawwanin kafoor

Hausa
 
Lalle ne, Allah Yană yin faɗa sabőda waɗanda suka yi ĩmăni. Lalle ne Allah bă Ya son dukkan mayaudari, mai yawan kăfirci.

Ayah  22:39  الأية
أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ بِأَنَّهُمْ ظُلِمُوا ۚ وَإِنَّ اللهَ عَلَىٰ نَصْرِهِمْ لَقَدِيرٌ
Othina lillatheena yuqataloonabi-annahum thulimoo wa-inna Allaha AAalanasrihim laqadeer

Hausa
 
An yi izni ga waɗanda ake yăƙar su da cẽwa lalle an zălunce su, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa,Mai ĩkon yi ne a kan taimakonsu.

Ayah  22:40  الأية
الَّذِينَ أُخْرِجُوا مِن دِيَارِهِم بِغَيْرِ حَقٍّ إِلَّا أَن يَقُولُوا رَبُّنَا اللهُ ۗ وَلَوْلَا دَفْعُ اللهِ النَّاسَ بَعْضَهُم بِبَعْضٍ لَّهُدِّمَتْ صَوَامِعُ وَبِيَعٌ وَصَلَوَاتٌ وَمَسَاجِدُ يُذْكَرُ فِيهَا اسْمُ اللهِ كَثِيرًا ۗ وَلَيَنصُرَنَّ اللهُ مَن يَنصُرُهُ ۗ إِنَّ اللهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ
Allatheena okhrijoo min diyarihimbighayri haqqin illa an yaqooloo rabbuna Allahuwalawla dafAAu Allahi annasa baAAdahumbibaAAdin lahuddimat sawamiAAu wabiyaAAun wasalawatunwamasajidu yuthkaru feeha ismu Allahikatheeran walayansuranna Allahu man yansuruhuinna Allaha laqawiyyun AAazeez

Hausa
 
Waɗanda aka fitina daga gidajensu bă da wani hakki ba făce sună cẽwa, Ubangijinmu Allah ne."Kuma ba dőmin tunkuɗẽwar Allah ga mutăne ba, săshensu da săshe, haƙĩƙa, da an rũsa sauma'ő'in (Ruhbănăwa) dă majămi'ő'in Nasăra da gidăjen ibădar Yahudu da masallatai waɗanda ake ambatar Allah a cikinsu da yawa. Kuma lalle, haƙĩƙa, Allah Yană taimakon wanda yake taimakon Sa. Lalle Allah ne haƙĩƙa Mai ƙarfi Mabuwăyi.

Ayah  22:41  الأية
الَّذِينَ إِن مَّكَّنَّاهُمْ فِي الْأَرْضِ أَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ وَأَمَرُوا بِالْمَعْرُوفِ وَنَهَوْا عَنِ الْمُنكَرِ ۗ وَلِلَّهِ عَاقِبَةُ الْأُمُورِ
Allatheena in makkannahum feeal-ardi aqamoo assalata waatawooazzakata waamaroo bilmaAAroofi wanahawAAani almunkari walillahi AAaqibatu al-omoor

Hausa
 
Waɗanda suke idan Muka bă su ĩko a cikin ƙasa sai su tsai da salla, kuma su baybr da zakka kuma su yi umurni da abin da aka sani, kuma su hana daga abin da ba a sani ba. Kuma ăƙibar al'amura ga Allah take.

Ayah  22:42  الأية
وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدْ كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَعَادٌ وَثَمُودُ
Wa-in yukaththibooka faqad kaththabatqablahum qawmu noohin waAAadun wathamood

Hausa
 
Kuma idan sun ƙaryata ka, to lalle haƙĩƙa, mutănen Nũhu da Ădăwa da Samũdawa, sun ƙaryata a gabaninsu.

Ayah  22:43  الأية
وَقَوْمُ إِبْرَاهِيمَ وَقَوْمُ لُوطٍ
Waqawmu ibraheema waqawmu loot

Hausa
 
Da mutănen Ibrahim da mutănen Lũɗu.

Ayah  22:44  الأية
وَأَصْحَابُ مَدْيَنَ ۖ وَكُذِّبَ مُوسَىٰ فَأَمْلَيْتُ لِلْكَافِرِينَ ثُمَّ أَخَذْتُهُمْ ۖ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ
Waas-habu madyana wakuththibamoosa faamlaytu lilkafireena thumma akhathtuhumfakayfa kana nakeer

Hausa
 
Da măsu Madyana, kuma an ƙaryata Mũsă. Sai Na jinkirtawa kăfiran, sa'an nan kuma Na kăma su. To, yăya musũNa (gare su) ya kasance?

Ayah  22:45  الأية
فَكَأَيِّن مِّن قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا وَهِيَ ظَالِمَةٌ فَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَبِئْرٍ مُّعَطَّلَةٍ وَقَصْرٍ مَّشِيدٍ
Fakaayyin min qaryatin ahlaknahawahiya thalimatun fahiya khawiyatunAAala AAurooshiha wabi/rin muAAattalatinwaqasrin masheed

Hausa
 
Sa'an nan da yawa daga alƙarya, Muka halaka ta, alhăli kuwa tană mai zalũnci sai ta zama făɗaɗɗa a kan rassanta, da yawa daga rĩjiya wadda aka wőfintar, da kuma gidăjen sarauta maɗaukaka.

Ayah  22:46  الأية
أَفَلَمْ يَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَتَكُونَ لَهُمْ قُلُوبٌ يَعْقِلُونَ بِهَا أَوْ آذَانٌ يَسْمَعُونَ بِهَا ۖ فَإِنَّهَا لَا تَعْمَى الْأَبْصَارُ وَلَٰكِن تَعْمَى الْقُلُوبُ الَّتِي فِي الصُّدُورِ
Afalam yaseeroo fee al-ardi fatakoonalahum quloobun yaAAqiloona biha aw athanunyasmaAAoona biha fa-innaha la taAAmaal-absaru walakin taAAma alquloobu allateefee assudoor

Hausa
 
Shin, to, ba su yi tafiya ba a cikin ƙasa dőmin zukăta waɗanda ză su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurăre da su su kasance a gare su? Dőmin lalle ne idănun ba su makanta, amma zukăta waɗanda ke a cikin ƙirăza sũ ke makanta.

Ayah  22:47  الأية
وَيَسْتَعْجِلُونَكَ بِالْعَذَابِ وَلَن يُخْلِفَ اللهُ وَعْدَهُ ۚ وَإِنَّ يَوْمًا عِندَ رَبِّكَ كَأَلْفِ سَنَةٍ مِّمَّا تَعُدُّونَ
WayastaAAjiloonaka bilAAathabiwalan yukhlifa Allahu waAAdahu wa-inna yawman AAindarabbika kaalfi sanatin mimma taAAuddoon

Hausa
 
Kuma sună nẽman ka yi gaggăwa da azăba, alhăli kuwa Allah bă zai săɓa wa'adinSa ba kuma lalle ne, yini ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shẽkara dubu yake daga abin da kuke ƙidăyăwa.

Ayah  22:48  الأية
وَكَأَيِّن مِّن قَرْيَةٍ أَمْلَيْتُ لَهَا وَهِيَ ظَالِمَةٌ ثُمَّ أَخَذْتُهَا وَإِلَيَّ الْمَصِيرُ
Wakaayyin min qaryatin amlaytu lahawahiya thalimatun thumma akhathtuhawa-ilayya almaseer

Hausa
 
Kuma da yawa daga alƙarya, Na yi jinkirin azăba gare ta (da laifinta) sa'an nan Na kăma ta, kuma zuwa gare Ni makőma take.

Ayah  22:49  الأية
قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّمَا أَنَا لَكُمْ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Qul ya ayyuha annasuinnama ana lakum natheerun mubeen

Hausa
 
Ka ce: "Ya ku mutăne! Nĩ wani mai gargaɗi ne kawai zuwa gare ku, mai bayyanawa."

Ayah  22:50  الأية
فَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ
Fallatheena amanoowaAAamiloo assalihati lahum maghfiratunwarizqun kareem

Hausa
 
To, waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, sună da găfara da arziki na karimci.

Ayah  22:51  الأية
وَالَّذِينَ سَعَوْا فِي آيَاتِنَا مُعَاجِزِينَ أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ
Wallatheena saAAaw fee ayatinamuAAajizeena ola-ika as-habu aljaheem

Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi aikin ɓătăwa a cikin ayőyinMu, sună măsu gajiyarwa, waɗancan 'yan Jahĩm ne.

Ayah  22:52  الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رَّسُولٍ وَلَا نَبِيٍّ إِلَّا إِذَا تَمَنَّىٰ أَلْقَى الشَّيْطَانُ فِي أُمْنِيَّتِهِ فَيَنسَخُ اللهُ مَا يُلْقِي الشَّيْطَانُ ثُمَّ يُحْكِمُ اللهُ آيَاتِهِ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Wama arsalna min qablika minrasoolin wala nabiyyin illa itha tamannaalqa ashshaytanu fee omniyyatihi fayansakhuAllahu ma yulqee ashshaytanu thummayuhkimu Allahu ayatihi wallahuAAaleemun hakeem

Hausa
 
Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabăninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba făce idan ya yi bũri, sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shăfe abin da Shaiɗan ke jefăwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ăyőyinSa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.

Ayah  22:53  الأية
لِّيَجْعَلَ مَا يُلْقِي الشَّيْطَانُ فِتْنَةً لِّلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ وَالْقَاسِيَةِ قُلُوبُهُمْ ۗ وَإِنَّ الظَّالِمِينَ لَفِي شِقَاقٍ بَعِيدٍ
LiyajAAala ma yulqee ashshaytanufitnatan lillatheena fee quloobihim maradun walqasiyatiquloobuhum wa-inna aththalimeenalafee shiqaqin baAAeed

Hausa
 
Dőmin Ya sanya abin da Shaiɗan ke jẽfăwa ya zama fitina ga waɗanda a cikin zukătansu akwai cũta, da măsu ƙẽƙasassun zukătansu. Kuma lalle ne azzălumai haƙĩƙa, sună a cikin săɓănimai nĩsa.

Ayah  22:54  الأية
وَلِيَعْلَمَ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ أَنَّهُ الْحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَيُؤْمِنُوا بِهِ فَتُخْبِتَ لَهُ قُلُوبُهُمْ ۗ وَإِنَّ اللهَ لَهَادِ الَّذِينَ آمَنُوا إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
WaliyaAAlama allatheena ootooalAAilma annahu alhaqqu min rabbika fayu/minoo bihifatukhbita lahu quloobuhum wa-inna Allaha lahadiallatheena amanoo ila siratinmustaqeem

Hausa
 
Kuma dőmin waɗanda aka bai wa ilmi su sani lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka dőmin su yi ĩmăni da shi sabőda zukătansu su natsu gare shi. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai shiryar da waɗanda suka yi ĩmăni ne zuwa ga hanya madaidaiciya.

Ayah  22:55  الأية
وَلَا يَزَالُ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي مِرْيَةٍ مِّنْهُ حَتَّىٰ تَأْتِيَهُمُ السَّاعَةُ بَغْتَةً أَوْ يَأْتِيَهُمْ عَذَابُ يَوْمٍ عَقِيمٍ
Wala yazalu allatheenakafaroo fee miryatin minhu hatta ta/tiyahumu assaAAatubaghtatan aw ya/tiyahum AAathabu yawmin AAaqeem

Hausa
 
Kuma waɗanda suka kăfirta bă ză su gushe ba sună a cikin shakka daga gare shi, har Sa'a ta jẽ musu bisa ga abke, kő kuwa azăbar wani yini bakarăre ta jẽ musu.

Ayah  22:56  الأية
الْمُلْكُ يَوْمَئِذٍ لِّلَّهِ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ ۚ فَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ
Almulku yawma-ithin lillahi yahkumubaynahum fallatheena amanoo waAAamiloo assalihatifee jannati annaAAeem

Hausa
 
Mulki a rănar nan ga Allah yake, Yană hukunci a tsakăninsu. To, waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sună a cikin gidăjen Aljannar ni'ima.

Ayah  22:57  الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا فَأُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ مُّهِينٌ
Wallatheena kafaroo wakaththaboobi-ayatina faola-ika lahum AAathabunmuheen

Hausa
 
Kuma waɗandra suka kăfirta kuma suka ƙaryata, game da ăyőyinMu, to, waɗannan sună da azăba mai wulăkantarwa.

Ayah  22:58  الأية
وَالَّذِينَ هَاجَرُوا فِي سَبِيلِ اللهِ ثُمَّ قُتِلُوا أَوْ مَاتُوا لَيَرْزُقَنَّهُمُ اللهُ رِزْقًا حَسَنًا ۚ وَإِنَّ اللهَ لَهُوَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ
Wallatheena hajaroofee sabeeli Allahi thumma qutiloo aw matoolayarzuqannahumu Allahu rizqan hasanan wa-inna Allahalahuwa khayru arraziqeen

Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin tafarkin Allah sa'an nan kuma aka kashe su, kő suka mutu, lalle ne Allah Yană azurta su da arziki mai kyau. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shĩ ne Mafi alhẽrin măsu azurtăwa.

Ayah  22:59  الأية
لَيُدْخِلَنَّهُم مُّدْخَلًا يَرْضَوْنَهُ ۗ وَإِنَّ اللهَ لَعَلِيمٌ حَلِيمٌ
Layudkhilannahum mudkhalan yardawnahuwa-inna Allaha laAAaleemun haleem

Hausa
 
Lalle ne, Yană shigar da su a wata mashiga wadda ză su yarda da ita. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa Masani ne, Mai haƙuri.

Ayah  22:60  الأية
ذَٰلِكَ وَمَنْ عَاقَبَ بِمِثْلِ مَا عُوقِبَ بِهِ ثُمَّ بُغِيَ عَلَيْهِ لَيَنصُرَنَّهُ اللهُ ۗ إِنَّ اللهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٌ
Thalika waman AAaqaba bimithlima AAooqiba bihi thumma bughiya AAalayhi layansurannahuAllahu inna Allaha laAAafuwwun ghafoor

Hausa
 
Wancan! Kuma wanda ya răma azăba da misălin abin da aka yi masa, sa'an nan kuma aka zălunce shi, lalle ne Allah Yană taimakon sa. Lalle ne Allah haƙĩƙa Mai yăfẽwa ne, Mai găfara.

Ayah  22:61  الأية
ذَٰلِكَ بِأَنَّ اللهَ يُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَيُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ وَأَنَّ اللهَ سَمِيعٌ بَصِيرٌ
Thalika bi-anna Allaha yoolijuallayla fee annahari wayooliju annaharafee allayli waanna Allaha sameeAAun baseer

Hausa
 
Wancan! sabőda Allah Yană shigar da dare a cikin yini, kuma Yană shigar da yini a cikin dare, kuma lalle, Allah Mai jĩ ne,Mai gani.

Ayah  22:62  الأية
ذَٰلِكَ بِأَنَّ اللهَ هُوَ الْحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدْعُونَ مِن دُونِهِ هُوَ الْبَاطِلُ وَأَنَّ اللهَ هُوَ الْعَلِيُّ الْكَبِيرُ
Thalika bi-anna Allaha huwa alhaqquwaanna ma yadAAoona min doonihi huwa albatiluwaanna Allaha huwa alAAaliyyu alkabeer

Hausa
 
Wancan! sabőda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma.

Ayah  22:63  الأية
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللهَ أَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَتُصْبِحُ الْأَرْضُ مُخْضَرَّةً ۗ إِنَّ اللهَ لَطِيفٌ خَبِيرٌ
Alam tara anna Allaha anzala mina assama-imaan fatusbihu al-ardu mukhdarrataninna Allaha lateefun khabeer

Hausa
 
Ashe, ba ka gani ba, lalle ne, Allah Yă saukar da ruwa daga sama, sai ƙasa ta wăyi gari kőriya? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Mai ƙididdigewa.

Ayah  22:64  الأية
لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ وَإِنَّ اللهَ لَهُوَ الْغَنِيُّ الْحَمِيدُ
Lahu ma fee assamawatiwama fee al-ardi wa-inna Allaha lahuwaalghaniyyu alhameed

Hausa
 
Abin da ke a cikin sammai, da abin da ke a cikin ƙasa, Nasa ne, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa,Shi ne wadatacce, Gődadde.

Ayah  22:65  الأية
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِي الْأَرْضِ وَالْفُلْكَ تَجْرِي فِي الْبَحْرِ بِأَمْرِهِ وَيُمْسِكُ السَّمَاءَ أَن تَقَعَ عَلَى الْأَرْضِ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۗ إِنَّ اللهَ بِالنَّاسِ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ
Alam tara anna Allaha sakhkhara lakumma fee al-ardi walfulka tajree fee albahribi-amrihi wayumsiku assamaa an taqaAAa AAalaal-ardi illa bi-ithnihi inna Allahabinnasi laraoofun raheem

Hausa
 
Shin ba ka gani ba, lalle ne Allah Ya hőre muku abin da yake a cikin ƙasa, kuma jirăge sună gudăna a cikin tẽku, da umurninSa kuma Yană riƙe sama dőmin kada ta făɗi a kan ƙasa făce da izninsa? Lalle ne Allah ga mutăne haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.

Ayah  22:66  الأية
وَهُوَ الَّذِي أَحْيَاكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يُحْيِيكُمْ ۗ إِنَّ الْإِنسَانَ لَكَفُورٌ
Wahuwa allathee ahyakumthumma yumeetukum thumma yuhyeekum inna al-insanalakafoor

Hausa
 
Kuma shĩ ne wanda Ya răya ku, sa'an nan kuma Yană matar da ku, sa'an nan kuma Yană răyar da ku. Lalle mutum, haƙĩƙa, mai kăfirci ne.

Ayah  22:67  الأية
لِّكُلِّ أُمَّةٍ جَعَلْنَا مَنسَكًا هُمْ نَاسِكُوهُ ۖ فَلَا يُنَازِعُنَّكَ فِي الْأَمْرِ ۚ وَادْعُ إِلَىٰ رَبِّكَ ۖ إِنَّكَ لَعَلَىٰ هُدًى مُّسْتَقِيمٍ
Likulli ommatin jaAAalna mansakan humnasikoohu fala yunaziAAunnaka fee al-amri wadAAuila rabbika innaka laAAala hudan mustaqeem

Hausa
 
Ga kőwace al'umma Mun sanya wurin yanka, su ne masu yin baiko gare Shi, sabőda haka, kada su yi maka jăyayya a cikin al'amarin (hadaya). Kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka lalle kai kana a kan shiriya madaidaiciya.

Ayah  22:68  الأية
وَإِن جَادَلُوكَ فَقُلِ اللهُ أَعْلَمُ بِمَا تَعْمَلُونَ
Wa-in jadalooka faquli AllahuaAAlamu bima taAAmaloon

Hausa
 
Kuma idan sun yi maka jidăli, sai ka ce: "Allah ne Mafi sani game da abin da kuke aikatăwa."

Ayah  22:69  الأية
اللهُ يَحْكُمُ بَيْنَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ
Allahu yahkumu baynakum yawmaalqiyamati feema kuntum feehi takhtalifoon

Hausa
 
"Allah ne zai yi hukunci a tsakăninku, a Rănar ˇiyăma a cikin abin da kuka kasance a cikinsa kună săɓawa jũna."

Ayah  22:70  الأية
أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ ۗ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَابٍ ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى اللهِ يَسِيرٌ
Alam taAAlam anna Allaha yaAAlamu mafee assama-i wal-ardi inna thalikafee kitabin inna thalika AAala Allahiyaseer

Hausa
 
Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yană sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yană cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne.

Ayah  22:71  الأية
وَيَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ سُلْطَانًا وَمَا لَيْسَ لَهُم بِهِ عِلْمٌ ۗ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِن نَّصِيرٍ
WayaAAbudoona min dooni Allahi malam yunazzil bihi sultanan wama laysa lahum bihiAAilmun wama liththalimeenamin naseer

Hausa
 
Kuma sună bautăwa baicin Allah, abin da (Allah) bai saukar da wani dalili ba game da shi, kuma abin da bă su da wani ilmi game da shi, kuma băbu wani mai taimako ga azzălumai.

Ayah  22:72  الأية
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ تَعْرِفُ فِي وُجُوهِ الَّذِينَ كَفَرُوا الْمُنكَرَ ۖ يَكَادُونَ يَسْطُونَ بِالَّذِينَ يَتْلُونَ عَلَيْهِمْ آيَاتِنَا ۗ قُلْ أَفَأُنَبِّئُكُم بِشَرٍّ مِّن ذَٰلِكُمُ ۗ النَّارُ وَعَدَهَا اللهُ الَّذِينَ كَفَرُوا ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ
Wa-itha tutla AAalayhim ayatunabayyinatin taAArifu fee wujoohi allatheena kafarooalmunkara yakadoona yastoona billatheenayatloona AAalayhim ayatina qulafaonabbi-okum bisharrin min thalikum annaruwaAAadaha Allahu allatheena kafaroo wabi/saalmaseer

Hausa
 
Kuma idan ană karanta ăyőyinMu bayyanannu a kansu kană sanin abin ƙyăma a cikin fuskőkin waɗanda suka kăfirta sună kusa su yi danƙa ga waɗanda ke karătun ayőyinMu a kansu. Ka ce: "Shin to in gaya muku abin da yake mafi sharri daga wannan? (Ita ce) Wuta." Allah Yă yi alkawarinta ga waɗanda suka kăfirta. Kuma makőmarsu ta mũnana.

Ayah  22:73  الأية
يَا أَيُّهَا النَّاسُ ضُرِبَ مَثَلٌ فَاسْتَمِعُوا لَهُ ۚ إِنَّ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ لَن يَخْلُقُوا ذُبَابًا وَلَوِ اجْتَمَعُوا لَهُ ۖ وَإِن يَسْلُبْهُمُ الذُّبَابُ شَيْئًا لَّا يَسْتَنقِذُوهُ مِنْهُ ۚ ضَعُفَ الطَّالِبُ وَالْمَطْلُوبُ
Ya ayyuha annasuduriba mathalun fastamiAAoo lahu inna allatheenatadAAoona min dooni Allahi lan yakhluqoo thubabanwalawi ijtamaAAoo lahu wa-in yaslubuhumu aththubabushay-an la yastanqithoohu minhu daAAufa attalibuwalmatloob

Hausa
 
"Ya ku mutăne! An buga wani misăli, sai ku saurăra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bă ză su halitta ƙudă ba, kő da sun tăru gare shi, kuma idan ƙudăn ya ƙwăce musu wani abu, bă ză su kuɓutar da shi ba daga gare shi. Mai nẽma da wanda ake nẽman gare shi sun raunana."

Ayah  22:74  الأية
مَا قَدَرُوا اللهَ حَقَّ قَدْرِهِ ۗ إِنَّ اللهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ
Ma qadaroo Allaha haqqaqadrihi inna Allaha laqawiyyun AAazeez

Hausa
 
Ba su ƙaddara wa Allah hakkin girmanSa ba. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ƙarfi ne, Mabuwăyi.

Ayah  22:75  الأية
اللهُ يَصْطَفِي مِنَ الْمَلَائِكَةِ رُسُلًا وَمِنَ النَّاسِ ۚ إِنَّ اللهَ سَمِيعٌ بَصِيرٌ
Allahu yastafee mina almala-ikatirusulan wamina annasi inna Allaha sameeAAunbaseer

Hausa
 
Allah nă zăɓen Manzanni daga mală'iku kuma daga mutăne. Lalle Allah, Mai ji ne, Mai gani.

Ayah  22:76  الأية
يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۗ وَإِلَى اللهِ تُرْجَعُ الْأُمُورُ
YaAAlamu ma bayna aydeehim wamakhalfahum wa-ila Allahi turjaAAu al-omoor

Hausa
 
Yană sanin abin da ke gaba gare su da abin da ke băyansu, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura.

Ayah  22:77  الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا ارْكَعُوا وَاسْجُدُوا وَاعْبُدُوا رَبَّكُمْ وَافْعَلُوا الْخَيْرَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ ۩
Ya ayyuha allatheena amanooirkaAAoo wasjudoo waAAbudoo rabbakum wafAAalooalkhayra laAAallakum tuflihoon

Hausa
 
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Ku yi rukũ'i, kuma ku yi sujada, kuma ku bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alhẽri, tsammăninku, ku sami babban rabo.

Ayah  22:78  الأية
وَجَاهِدُوا فِي اللهِ حَقَّ جِهَادِهِ ۚ هُوَ اجْتَبَاكُمْ وَمَا جَعَلَ عَلَيْكُمْ فِي الدِّينِ مِنْ حَرَجٍ ۚ مِّلَّةَ أَبِيكُمْ إِبْرَاهِيمَ ۚ هُوَ سَمَّاكُمُ الْمُسْلِمِينَ مِن قَبْلُ وَفِي هَٰذَا لِيَكُونَ الرَّسُولُ شَهِيدًا عَلَيْكُمْ وَتَكُونُوا شُهَدَاءَ عَلَى النَّاسِ ۚ فَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَاعْتَصِمُوا بِاللهِ هُوَ مَوْلَاكُمْ ۖ فَنِعْمَ الْمَوْلَىٰ وَنِعْمَ النَّصِيرُ
Wajahidoo fee Allahi haqqajihadihi huwa ijtabakum wama jaAAalaAAalaykum fee addeeni min harajin millata abeekumibraheema huwa sammakumu almuslimeena min qabluwafee hatha liyakoona arrasoolu shaheedanAAalaykum watakoonoo shuhadaa AAala annasifaaqeemoo assalata waatoo azzakatawaAAtasimoo billahi huwa mawlakumfaniAAma almawla waniAAma annaseer

Hausa
 
Kuma ku yi jihădi a cikin (al'amarin) Allah, hakkin JihădinSa. shĩ ne Ya zăɓe ku alhăli kuwa bai sanya wani ƙunci ba a kanku a cikin addĩni. Bisa ƙudurcẽwar ubanku Ibrăhĩm, shĩ ne ya yi muku sũna Musulmi daga gabănin haka. Kuma a cikin wannan (Littăfi ya yi muku sũna Musulmi), dőmin Manzo ya kasance mai shaida a kanku, kũ kuma ku kasancemăsu shaida a kan mutăne. Sabőda haka ku tsayar da salla kuma ku băyar da zakka kuma ku amince da Allah, Shi ne Majiɓincinku. Săbőda haka mădalla da Shi Ya zama Majiɓinci, mădalla da Shi ya zama Mai taimako.

© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us