Prev  

52. Surah At-Tűr سورة الطور

  Next  
1st Ayah  1  الأية ١الأولي
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
وَالطُّورِ
Wattoor

Hausa
 
Ină rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsă).

Ayah  52:2  الأية
وَكِتَابٍ مَّسْطُورٍ
Wakitabin mastoor

Hausa
 
Da wani littăfi rubũtacce.

Ayah  52:3  الأية
فِي رَقٍّ مَّنشُورٍ
Fee raqqin manshoor

Hausa
 
A cikin wata takardar făta shimfiɗaɗɗa.

Ayah  52:4  الأية
وَالْبَيْتِ الْمَعْمُورِ
Walbayti almaAAmoor

Hausa
 
Da Gidan da aka răyar da shi (da ibăda).

Ayah  52:5  الأية
وَالسَّقْفِ الْمَرْفُوعِ
Wassaqfi almarfooAA

Hausa
 
Da rufin nan da aka ɗaukaka.

Ayah  52:6  الأية
وَالْبَحْرِ الْمَسْجُورِ
Walbahri almasjoor

Hausa
 
Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa).

Ayah  52:7  الأية
إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَاقِعٌ
Inna AAathaba rabbika lawaqiAA

Hausa
 
Lalle, azăbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.

Ayah  52:8  الأية
مَّا لَهُ مِن دَافِعٍ
Ma lahu min dafiAA

Hausa
 
Bă ta da mai tunkuɗẽwa.

Ayah  52:9  الأية
يَوْمَ تَمُورُ السَّمَاءُ مَوْرًا
Yawma tamooru assamao mawra

Hausa
 
Rănar da samă ke yin mőtsi tană kai kăwo.

Ayah  52:10  الأية
وَتَسِيرُ الْجِبَالُ سَيْرًا
Wataseeru aljibalu sayra

Hausa
 
Kuma duwătsu nă tafiya sună shũɗẽwa.

Ayah  52:11  الأية
فَوَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Fawaylun yawma-ithin lilmukaththibeen

Hausa
 
To, bone yă tabbata a rănar nan ga măsu ƙaryatăwa.

Ayah  52:12  الأية
الَّذِينَ هُمْ فِي خَوْضٍ يَلْعَبُونَ
Allatheena hum fee khawdinyalAAaboon

Hausa
 
Waɗanda suke a cikin kududdufi sună wăsă.

Ayah  52:13  الأية
يَوْمَ يُدَعُّونَ إِلَىٰ نَارِ جَهَنَّمَ دَعًّا
Yawma yudaAAAAoona ila narijahannama daAAAAa

Hausa
 
Rănar da ză a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗăwa.

Ayah  52:14  الأية
هَٰذِهِ النَّارُ الَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ
Hathihi annaru allateekuntum biha tukaththiboon

Hausa
 
(A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kună ƙaryatăwa game da ita."

Ayah  52:15  الأية
أَفَسِحْرٌ هَٰذَا أَمْ أَنتُمْ لَا تُبْصِرُونَ
Afasihrun hatha am antum latubsiroon

Hausa
 
"To, shin wannan sihiri ne kő kuwa kũ ne bă ku gani?"

Ayah  52:16  الأية
اصْلَوْهَا فَاصْبِرُوا أَوْ لَا تَصْبِرُوا سَوَاءٌ عَلَيْكُمْ ۖ إِنَّمَا تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Islawha fasbirooaw la tasbiroo sawaon AAalaykum innamatujzawna ma kuntum taAAmaloon

Hausa
 
"Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai ană yi muku sakamakon abin da kuka kasance kună aikatăwa."

Ayah  52:17  الأية
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَنَعِيمٍ
Inna almuttaqeena fee jannatinwanaAAeem

Hausa
 
Lalle, măsu taƙawa, sună a cikin gidăjen Aljanna da wata ni'ima.

Ayah  52:18  الأية
فَاكِهِينَ بِمَا آتَاهُمْ رَبُّهُمْ وَوَقَاهُمْ رَبُّهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ
Fakiheena bima atahumrabbuhum wawaqahum rabbuhum AAathaba aljaheem

Hausa
 
Sună măsu jin dăɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsăre musu azăbar Jahĩm.

Ayah  52:19  الأية
كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Kuloo washraboo hanee-an bimakuntum taAAmaloon

Hausa
 
(A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dőmin abin da kuka kasance kună aikatăwa."

Ayah  52:20  الأية
مُتَّكِئِينَ عَلَىٰ سُرُرٍ مَّصْفُوفَةٍ ۖ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍ
Muttaki-eena AAala sururin masfoofatinwazawwajnahum bihoorin AAeen

Hausa
 
Sună kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mătă măsu farin idănu, măsu girmansu.

Ayah  52:21  الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَاتَّبَعَتْهُمْ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَانٍ أَلْحَقْنَا بِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَمَا أَلَتْنَاهُم مِّنْ عَمَلِهِم مِّن شَيْءٍ ۚ كُلُّ امْرِئٍ بِمَا كَسَبَ رَهِينٌ
Wallatheena amanoo wattabaAAat-humthurriyyatuhum bi-eemanin alhaqnabihim thurriyyatahum wama alatnahum minAAamalihim min shay-in kullu imri-in bima kasaba raheen

Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmănin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhăli kuwa bă da Mun rage musu kőme ba daga aikinsu, kőwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.

Ayah  52:22  الأية
وَأَمْدَدْنَاهُم بِفَاكِهَةٍ وَلَحْمٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ
Waamdadnahum bifakihatin walahminmimma yashtahoon

Hausa
 
Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan ităce da năma irin wanda suke marmari.

Ayah  52:23  الأية
يَتَنَازَعُونَ فِيهَا كَأْسًا لَّا لَغْوٌ فِيهَا وَلَا تَأْثِيمٌ
YatanazaAAoona feeha ka/san lalaghwun feeha wala ta/theem

Hausa
 
Sună mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjălan giya, wadda băbu yăsassar magana a cikinta, kuma băbu jin nauyin zunubi.

Ayah  52:24  الأية
وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ غِلْمَانٌ لَّهُمْ كَأَنَّهُمْ لُؤْلُؤٌ مَّكْنُونٌ
Wayatoofu AAalayhim ghilmanunlahum kaannahum lu/luon maknoon

Hausa
 
Kuma waɗansu samări nă gẽwayăwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle.

Ayah  52:25  الأية
وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَ
Waaqbala baAAduhum AAala baAAdinyatasaaloon

Hausa
 
Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sună tambayar jũna.

Ayah  52:26  الأية
قَالُوا إِنَّا كُنَّا قَبْلُ فِي أَهْلِنَا مُشْفِقِينَ
Qaloo inna kunna qablufee ahlina mushfiqeen

Hausa
 
Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabănin wannan (a dũniya ) a cikin iyălanmu mună jin tsőro."

Ayah  52:27  الأية
فَمَنَّ اللهُ عَلَيْنَا وَوَقَانَا عَذَابَ السَّمُومِ
Famanna Allahu AAalayna wawaqanaAAathaba assamoom

Hausa
 
"To, Allah Yă yi mana kyautar falala, kuma Yă tsare mana azăbar iskar zăfi."

Ayah  52:28  الأية
إِنَّا كُنَّا مِن قَبْلُ نَدْعُوهُ ۖ إِنَّهُ هُوَ الْبَرُّ الرَّحِيمُ
Inna kunna min qablu nadAAoohuinnahu huwa albarru arraheem

Hausa
 
"Lalle mũ mun kasance, a găbanin haka, mună kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatăwa, Mai rahama."

Ayah  52:29  الأية
فَذَكِّرْ فَمَا أَنتَ بِنِعْمَتِ رَبِّكَ بِكَاهِنٍ وَلَا مَجْنُونٍ
Fathakkir fama anta biniAAmatirabbika bikahin wala majnoon

Hausa
 
To, ka tunătar kai fa sabőda ni'imar Ubangjinka, bă bőka kake ba, kuma bă mahaukaci ba.

Ayah  52:30  الأية
أَمْ يَقُولُونَ شَاعِرٌ نَّتَرَبَّصُ بِهِ رَيْبَ الْمَنُونِ
Am yaqooloona shaAAirun natarabbasubihi rayba almanoon

Hausa
 
Shin ză su ce: "Mawăƙi ne, mună jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"?

Ayah  52:31  الأية
قُلْ تَرَبَّصُوا فَإِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُتَرَبِّصِينَ
Qul tarabbasoo fa-innee maAAakum minaalmutarabbiseen

Hausa
 
Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle ină a cikin măsu jira tăre da ku."

Ayah  52:32  الأية
أَمْ تَأْمُرُهُمْ أَحْلَامُهُم بِهَٰذَا ۚ أَمْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَ
Am ta/muruhum ahlamuhum bihathaam hum qawmun taghoon

Hausa
 
Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kő kuwa sũ wasu mutăne ne măsu ƙetare haddi?

Ayah  52:33  الأية
أَمْ يَقُولُونَ تَقَوَّلَهُ ۚ بَل لَّا يُؤْمِنُونَ
Am yaqooloona taqawwalahu bal layu/minoon

Hausa
 
Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙăga faɗarsa"? Ă'a ba su dai yi ĩmăni ba.

Ayah  52:34  الأية
فَلْيَأْتُوا بِحَدِيثٍ مِّثْلِهِ إِن كَانُوا صَادِقِينَ
Falya/too bihadeethin mithlihi in kanoosadiqeena

Hausa
 
Sai su ző da wani lăbări mai misălinsa idan sun kasance sũmăsu gaskiya ne.

Ayah  52:35  الأية
أَمْ خُلِقُوا مِنْ غَيْرِ شَيْءٍ أَمْ هُمُ الْخَالِقُونَ
Am khuliqoo min ghayri shay-in am humu alkhaliqoon

Hausa
 
Shin, an halitta su ne bă daga kőme ba, kő kuwa sũ ne măsu yin halitta?

Ayah  52:36  الأية
أَمْ خَلَقُوا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ ۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ
Am khalaqoo assamawatiwal-arda bal la yooqinoon

Hausa
 
Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ă'a ba su dai yi ĩmănin yaƙĩni ba.

Ayah  52:37  الأية
أَمْ عِندَهُمْ خَزَائِنُ رَبِّكَ أَمْ هُمُ الْمُصَيْطِرُونَ
Am AAindahum khaza-inu rabbika amhumu almusaytiroon

Hausa
 
Shin, taskőkin Ubangijinka, sună a wurinsu ne? Kő kuwa sũ ne măsu rinjăya?

Ayah  52:38  الأية
أَمْ لَهُمْ سُلَّمٌ يَسْتَمِعُونَ فِيهِ ۖ فَلْيَأْتِ مُسْتَمِعُهُم بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ
Am lahum sullamun yastamiAAoona feehifalya/ti mustamiAAuhum bisultanin mubeen

Hausa
 
Shin, sună da wani tsăni ne wanda suke (hawa sună) saurăron (lăbărin samă) a cikinsa? Sai mai saurarőnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne.

Ayah  52:39  الأية
أَمْ لَهُ الْبَنَاتُ وَلَكُمُ الْبَنُونَ
Am lahu albanatu walakumu albanoon

Hausa
 
Shin, Yană da 'ya'ya mătă ne kuma kũ, kună da ɗiya maza ne?

Ayah  52:40  الأية
أَمْ تَسْأَلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَ
Am tas-aluhum ajran fahum min maghraminmuthqaloon

Hausa
 
Shin, kană tambayar su wata ijăra ne, sabőda haka suka zama măsu jin nauyin biyan tărar?

Ayah  52:41  الأية
أَمْ عِندَهُمُ الْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ
Am AAindahumu alghaybu fahum yaktuboon

Hausa
 
Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabőda haka sună rubũtăwa?

Ayah  52:42  الأية
أَمْ يُرِيدُونَ كَيْدًا ۖ فَالَّذِينَ كَفَرُوا هُمُ الْمَكِيدُونَ
Am yureedoona kaydan fallatheenakafaroo humu almakeedoon

Hausa
 
Shin, sună nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kăfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi.

Ayah  52:43  الأية
أَمْ لَهُمْ إِلَٰهٌ غَيْرُ اللهِ ۚ سُبْحَانَ اللهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Am lahum ilahun ghayru Allahisubhana Allahi AAamma yushrikoon

Hausa
 
Shin, sună da wani abin bautăwa ne wanda bă Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki!

Ayah  52:44  الأية
وَإِن يَرَوْا كِسْفًا مِّنَ السَّمَاءِ سَاقِطًا يَقُولُوا سَحَابٌ مَّرْكُومٌ
Wa-in yaraw kisfan mina assama-isaqitan yaqooloo sahabun markoom

Hausa
 
Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samă yănă făɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna.

Ayah  52:45  الأية
فَذَرْهُمْ حَتَّىٰ يُلَاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي فِيهِ يُصْعَقُونَ
Fatharhum hatta yulaqooyawmahumu allathee feehi yusAAaqoon

Hausa
 
To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa.

Ayah  52:46  الأية
يَوْمَ لَا يُغْنِي عَنْهُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ
Yawma la yughnee AAanhum kayduhumshay-an wala hum yunsaroon

Hausa
 
Rănar da kaidinsu bă ya wadătar masu da kőme, kuma bă a taimakon su.

Ayah  52:47  الأية
وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا عَذَابًا دُونَ ذَٰلِكَ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Wa-inna lillatheena thalamooAAathaban doona thalika walakinna aktharahumla yaAAlamoon

Hausa
 
Kuma lalle, waɗannan da suka yi zăluncin, sună da azăba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba.

Ayah  52:48  الأية
وَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعْيُنِنَا ۖ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُ
Wasbir lihukmi rabbikafa-innaka bi-aAAyunina wasabbih bihamdirabbika heena taqoom

Hausa
 
Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kană idănunMu, kuma ka tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gőde Masa a lőkacin da kake tăshi tsaye (dőmin salla kő wani abu).

Ayah  52:49  الأية
وَمِنَ اللَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَإِدْبَارَ النُّجُومِ
Wamina allayli fasabbihhu wa-idbaraannujoom

Hausa
 
Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) dalőkacin jũyăwar taurări.531  الأية
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
1st Ayah  1  الأية ١الأولي
وَالنَّجْمِ إِذَا هَوَىٰ
Wannajmi itha hawa

Hausa
 
Ină rantsuwa da taurăron, a lőkacin da ya faku.

Ayah  53:2  الأية
مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمْ وَمَا غَوَىٰ
Ma dalla sahibukum wamaghawa

Hausa
 
Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.

Ayah  53:3  الأية
وَمَا يَنطِقُ عَنِ الْهَوَىٰ
Wama yantiqu AAani alhawa

Hausa
 
Kuma bă ya yin magana daga son zuciyarsa.

Ayah  53:4  الأية
إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْيٌ يُوحَىٰ
In huwa illa wahyun yooha

Hausa
 
(Maganarsa) ba ta zamo ba, făce wahayi ne da ake aikőwa.

Ayah  53:5  الأية
عَلَّمَهُ شَدِيدُ الْقُوَىٰ
AAallamahu shadeedu alquwa

Hausa
 
(Mală'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.

Ayah  53:6  الأية
ذُو مِرَّةٍ فَاسْتَوَىٰ
Thoo mirratin fastawa

Hausa
 
Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.

Ayah  53:7  الأية
وَهُوَ بِالْأُفُقِ الْأَعْلَىٰ
Wahuwa bil-ofuqi al-aAAla

Hausa
 
Alhăli kuwa yană a sararin samă mafi aukaka.

Ayah  53:8  الأية
ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ
Thumma dana fatadalla

Hausa
 
Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurőwa.

Ayah  53:9  الأية
فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ أَوْ أَدْنَىٰ
Fakana qaba qawsayni aw adna

Hausa
 
Har ya kasance gwargwadon ziră'i biyu, kő kuma abin da ya fi kusa.

Ayah  53:10  الأية
فَأَوْحَىٰ إِلَىٰ عَبْدِهِ مَا أَوْحَىٰ
Faawha ila AAabdihi maawha

Hausa
 
Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga băwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa ).

Ayah  53:11  الأية
مَا كَذَبَ الْفُؤَادُ مَا رَأَىٰ
Ma kathaba alfu-adu maraa

Hausa
 
Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.

Ayah  53:12  الأية
أَفَتُمَارُونَهُ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ
Afatumaroonahu AAala mayara

Hausa
 
Shin, ză ku yi masa musu a kan abin da yake gani?

Ayah  53:13  الأية
وَلَقَدْ رَآهُ نَزْلَةً أُخْرَىٰ
Walaqad raahu nazlatan okhra

Hausa
 
Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lőkacin saukarsa .

Ayah  53:14  الأية
عِندَ سِدْرَةِ الْمُنتَهَىٰ
AAinda sidrati almuntaha

Hausa
 
A wurin da magaryar tuƙẽwa take.

Ayah  53:15  الأية
عِندَهَا جَنَّةُ الْمَأْوَىٰ
AAindaha jannatu alma/wa

Hausa
 
A inda taken, nan Aljannar makoma take.

Ayah  53:16  الأية
إِذْ يَغْشَى السِّدْرَةَ مَا يَغْشَىٰ
Ith yaghsha assidratama yaghsha

Hausa
 
Lőkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.

Ayah  53:17  الأية
مَا زَاغَ الْبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ
Ma zagha albasaru wamatagha

Hausa
 
Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.

Ayah  53:18  الأية
لَقَدْ رَأَىٰ مِنْ آيَاتِ رَبِّهِ الْكُبْرَىٰ
Laqad raa min ayatirabbihi alkubra

Hausa
 
Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ăyőyin Ubangijinsa.

Ayah  53:19  الأية
أَفَرَأَيْتُمُ اللَّاتَ وَالْعُزَّىٰ
Afaraaytumu allata walAAuzza

Hausa
 
Shin, kun ga Lăta da uzza?

Ayah  53:20  الأية
وَمَنَاةَ الثَّالِثَةَ الْأُخْرَىٰ
Wamanata aththalithataal-okhra

Hausa
 
Da (wani gunki wai shi) Manăta, na ukunsu?

Ayah  53:21  الأية
أَلَكُمُ الذَّكَرُ وَلَهُ الْأُنثَىٰ
Alakumu aththakaru walahual-ontha

Hausa
 
Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?

Ayah  53:22  الأية
تِلْكَ إِذًا قِسْمَةٌ ضِيزَىٰ
Tilka ithan qismatun deeza

Hausa
 
Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe.

Ayah  53:23  الأية
إِنْ هِيَ إِلَّا أَسْمَاءٌ سَمَّيْتُمُوهَا أَنتُمْ وَآبَاؤُكُم مَّا أَنزَلَ اللهُ بِهَا مِن سُلْطَانٍ ۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا الظَّنَّ وَمَا تَهْوَى الْأَنفُسُ ۖ وَلَقَدْ جَاءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ الْهُدَىٰ
In hiya illa asmaonsammaytumooha antum waabaokum maanzala Allahu biha min sultanin inyattabiAAoona illa aththanna wamatahwa al-anfusu walaqad jaahum min rabbihimu alhuda

Hausa
 
Waɗannan bă kőme ba ne făce sũnăye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwăyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kăfirai) bă su biyar kőme făce zato da abin da răyukansu ke so, Alhăli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kőma wa zaton).

Ayah  53:24  الأية
أَمْ لِلْإِنسَانِ مَا تَمَنَّىٰ
Am lil-insani ma tamanna

Hausa
 
Ko (an fai cẽwa) mutum zai sămi abin da yake gũri?

Ayah  53:25  الأية
فَلِلَّهِ الْآخِرَةُ وَالْأُولَىٰ
Falillahi al-akhiratu wal-oola

Hausa
 
To, Lăhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yă yi kuskure).

Ayah  53:26  الأية
وَكَم مِّن مَّلَكٍ فِي السَّمَاوَاتِ لَا تُغْنِي شَفَاعَتُهُمْ شَيْئًا إِلَّا مِن بَعْدِ أَن يَأْذَنَ اللهُ لِمَن يَشَاءُ وَيَرْضَىٰ
Wakam min malakin fee assamawatila tughnee shafaAAatuhum shay-an illa minbaAAdi an ya/thana Allahu liman yashao wayarda

Hausa
 
Akwai mală'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bă ya wadătar da kőme făce băyan Allah Yă yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.

Ayah  53:27  الأية
إِنَّ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ لَيُسَمُّونَ الْمَلَائِكَةَ تَسْمِيَةَ الْأُنثَىٰ
Inna allatheena la yu/minoonabil-akhirati layusammoona almala-ikatatasmiyata al-ontha

Hausa
 
Lalle waɗannan da bă su yin ĩmăni da Lăhira, haƙĩƙa sună kiran mală'iku da sũnan mace.

Ayah  53:28  الأية
وَمَا لَهُم بِهِ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا الظَّنَّ ۖ وَإِنَّ الظَّنَّ لَا يُغْنِي مِنَ الْحَقِّ شَيْئًا
Wama lahum bihi min AAilmin inyattabiAAoona illa aththanna wa-innaaththanna la yughnee mina alhaqqishay-a

Hausa
 
Kuma bă su da wani ilmi game da shi, bă su bin kőme făce zato alhăli kuwa lalle zato bă ya amfănar da kőme daga gaskiya.

Ayah  53:29  الأية
فَأَعْرِضْ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكْرِنَا وَلَمْ يُرِدْ إِلَّا الْحَيَاةَ الدُّنْيَا
FaaAArid AAan man tawalla AAanthikrina walam yurid illa alhayataaddunya

Hausa
 
Sabőda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya băya daga ambatonMu kuma bai yi nufin kőme ba făce răyuwar kusa (dũniya).

Ayah  53:30  الأية
ذَٰلِكَ مَبْلَغُهُم مِّنَ الْعِلْمِ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِ وَهُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ اهْتَدَىٰ
Thalika mablaghuhum mina alAAilmiinna rabbaka huwa aAAlamu biman dalla AAan sabeelihiwahuwa aAAlamu bimani ihtada

Hausa
 
Wannan ita ce iyăkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.

Ayah  53:31  الأية
وَلِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ لِيَجْزِيَ الَّذِينَ أَسَاءُوا بِمَا عَمِلُوا وَيَجْزِيَ الَّذِينَ أَحْسَنُوا بِالْحُسْنَى
Walillahi ma fee assamawatiwama fee al-ardi liyajziya allatheena asaoobima AAamiloo wayajziya allatheena ahsanoobilhusna

Hausa
 
Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasă na Allah kawai ne, dőmin Yă săka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya săka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.

Ayah  53:32  الأية
الَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبَائِرَ الْإِثْمِ وَالْفَوَاحِشَ إِلَّا اللَّمَمَ ۚ إِنَّ رَبَّكَ وَاسِعُ الْمَغْفِرَةِ ۚ هُوَ أَعْلَمُ بِكُمْ إِذْ أَنشَأَكُم مِّنَ الْأَرْضِ وَإِذْ أَنتُمْ أَجِنَّةٌ فِي بُطُونِ أُمَّهَاتِكُمْ ۖ فَلَا تُزَكُّوا أَنفُسَكُمْ ۖ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ اتَّقَىٰ
Allatheena yajtaniboona kaba-iraal-ithmi walfawahisha illa allamama innarabbaka wasiAAu almaghfirati huwa aAAlamu bikum ithanshaakum mina al-ardi wa-ith antum ajinnatun feebutooni ommahatikum fala tuzakkoo anfusakumhuwa aAAlamu bimani ittaqa

Hausa
 
Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfăsha, făce ƙanănan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar găfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lőkacin da Ya ƙăga halittarku daga ƙasa, kuma a lőkacin da kuke tăyuna a cikin cikannan uwăyenku. Sabőda haka, kada ku tsarkake kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.

Ayah  53:33  الأية
أَفَرَأَيْتَ الَّذِي تَوَلَّىٰ
Afaraayta allathee tawalla

Hausa
 
Shin, ka ga wannan da ya jũya baya?

Ayah  53:34  الأية
وَأَعْطَىٰ قَلِيلًا وَأَكْدَىٰ
WaaAAta qaleelan waakda

Hausa
 
Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?

Ayah  53:35  الأية
أَعِندَهُ عِلْمُ الْغَيْبِ فَهُوَ يَرَىٰ
aAAindahu AAilmu alghaybi fahuwa yara

Hausa
 
Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabőda haka yană ganin gaibin?

Ayah  53:36  الأية
أَمْ لَمْ يُنَبَّأْ بِمَا فِي صُحُفِ مُوسَىٰ
Am lam yunabba/ bima fee suhufimoosa

Hausa
 
Ko kuwa ba a ba shi lăbări ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsă?

Ayah  53:37  الأية
وَإِبْرَاهِيمَ الَّذِي وَفَّىٰ
Wa-ibraheema allathee waffa

Hausa
 
Da Ibrăhĩm wanda ya cika alkawari?

Ayah  53:38  الأية
أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ
Alla taziru waziratun wizraokhra

Hausa
 
Cẽwa wani rai mai kăyan laifi bă ya ɗaukar kăyan laifin wani.

Ayah  53:39  الأية
وَأَن لَّيْسَ لِلْإِنسَانِ إِلَّا مَا سَعَىٰ
Waan laysa lil-insani illa masaAAa

Hausa
 
Kuma mutum bă shi da kőme făce abin da ya aikata.

Ayah  53:40  الأية
وَأَنَّ سَعْيَهُ سَوْفَ يُرَىٰ
Waanna saAAyahu sawfa yura

Hausa
 
Kuma lalle, aikinsa ză a gan shi.

Ayah  53:41  الأية
ثُمَّ يُجْزَاهُ الْجَزَاءَ الْأَوْفَىٰ
Thumma yujzahu aljazaa al-awfa

Hausa
 
Sa'an nan a săka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?

Ayah  53:42  الأية
وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ الْمُنتَهَىٰ
Waanna ila rabbika almuntaha

Hausa
 
Kuma lalle, makőmar zuwa Ubangijinka kawai take?

Ayah  53:43  الأية
وَأَنَّهُ هُوَ أَضْحَكَ وَأَبْكَىٰ
Waannahu huwa adhaka waabka

Hausa
 
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.

Ayah  53:44  الأية
وَأَنَّهُ هُوَ أَمَاتَ وَأَحْيَا
Waannahu huwa amata waahya

Hausa
 
Kuma lalle, Shĩ , Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya răyar.

Ayah  53:45  الأية
وَأَنَّهُ خَلَقَ الزَّوْجَيْنِ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰ
Waannahu khalaqa azzawjayni aththakarawal-ontha

Hausa
 
Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.

Ayah  53:46  الأية
مِن نُّطْفَةٍ إِذَا تُمْنَىٰ
Min nutfatin itha tumna

Hausa
 
Daga wani ɗigon ruwa guda a lőkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.

Ayah  53:47  الأية
وَأَنَّ عَلَيْهِ النَّشْأَةَ الْأُخْرَىٰ
Waanna AAalayhi annash-ata al-okhra

Hausa
 
Kuma a kansa ne ƙăga halitta ta biyu take.

Ayah  53:48  الأية
وَأَنَّهُ هُوَ أَغْنَىٰ وَأَقْنَىٰ
Waannahu huwa aghna waaqna

Hausa
 
Kuma lalle, Shĩ , Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadătar.

Ayah  53:49  الأية
وَأَنَّهُ هُوَ رَبُّ الشِّعْرَىٰ
Waannahu huwa rabbu ashshiAAra

Hausa
 
Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira .

Ayah  53:50  الأية
وَأَنَّهُ أَهْلَكَ عَادًا الْأُولَىٰ
Waannahu ahlaka AAadan al-oola

Hausa
 
Kuma lalle, Shĩ , Shĩ ne Ya halaka Ădăwa na farko.

Ayah  53:51  الأية
وَثَمُودَ فَمَا أَبْقَىٰ
Wathamooda fama abqa

Hausa
 
Da Samũdăwa, sa'an nan bai rage su ba.

Ayah  53:52  الأية
وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا هُمْ أَظْلَمَ وَأَطْغَىٰ
Waqawma noohin min qablu innahum kanoohum athlama waatgha

Hausa
 
Da mutănen Nũhu a gabănin haka, lalle sũ sun kasance mafi zălunci kuma mafi girman kai.

Ayah  53:53  الأية
وَالْمُؤْتَفِكَةَ أَهْوَىٰ
Walmu/tafikata ahwa

Hausa
 
Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kăyar da su.

Ayah  53:54  الأية
فَغَشَّاهَا مَا غَشَّىٰ
Faghashshaha ma ghashsha

Hausa
 
Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.

Ayah  53:55  الأية
فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ
Fabi-ayyi ala-i rabbika tatamara

Hausa
 
To, da wace daga ni'imőmin Ubangijinka kake yin shakka?

Ayah  53:56  الأية
هَٰذَا نَذِيرٌ مِّنَ النُّذُرِ الْأُولَىٰ
Hatha natheerun mina annuthurial-oola

Hausa
 
wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin măsu gargaɗi na farko.

Ayah  53:57  الأية
أَزِفَتِ الْآزِفَةُ
Azifati al-azifat

Hausa
 
Makusanciya fa, tă yi kusa.

Ayah  53:58  الأية
لَيْسَ لَهَا مِن دُونِ اللهِ كَاشِفَةٌ
Laysa laha min dooni Allahi kashifat

Hausa
 
Băbu wani rai, banda Allah, mai iya băyani gare ta.

Ayah  53:59  الأية
أَفَمِنْ هَٰذَا الْحَدِيثِ تَعْجَبُونَ
Afamin hatha alhadeethitaAAjaboon

Hausa
 
Shin, kuma daga wannan lăbări kuke mămăki?

Ayah  53:60  الأية
وَتَضْحَكُونَ وَلَا تَبْكُونَ
Watadhakoona wala tabkoon

Hausa
 
Kuma kună yin dăriya, kuma bă ku yin kũka?

Ayah  53:61  الأية
وَأَنتُمْ سَامِدُونَ
Waantum samidoon

Hausa
 
Alhăli kună măsu wăsă?

Ayah  53:62  الأية
فَاسْجُدُوا لِلَّهِ وَاعْبُدُوا ۩
Fasjudoo lillahi waAAbudoo

Hausa
 
To, ku yi tawăli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa). 

© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us