بَرَاءَةٌ مِّنَ اللهِ وَرَسُولِهِ إِلَى الَّذِينَ عَاهَدتُّم مِّنَ
الْمُشْرِكِينَ
Baraatun mina Allahiwarasoolihi ila allatheena AAahadtum minaalmushrikeen
Hausa
Barranta daga Allah da ManzonSa zuwa ga waɗanda kuka yi wa alkawari daga mãsu
shirki
|
Ayah 9:2 الأية
فَسِيحُوا فِي الْأَرْضِ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَاعْلَمُوا أَنَّكُمْ غَيْرُ
مُعْجِزِي اللهِ ۙ وَأَنَّ اللهَ مُخْزِي الْكَافِرِينَ
Faseehoo fee al-ardi arbaAAataashhurin waAAlamoo annakum ghayru muAAjizee
Allahiwaanna Allaha mukhzee alkafireen
Hausa
Sabõda haka ku yi tafiya a cikin ƙasa watã huɗu, kuma ku sani lalle kũ, bã mãsu
buwãyar Allah ba ne, kuma lalle Allah ne Mai kunyatar da kãfirai.
|
Ayah 9:3 الأية
وَأَذَانٌ مِّنَ اللهِ وَرَسُولِهِ إِلَى النَّاسِ يَوْمَ الْحَجِّ الْأَكْبَرِ
أَنَّ اللهَ بَرِيءٌ مِّنَ الْمُشْرِكِينَ ۙ وَرَسُولُهُ ۚ فَإِن تُبْتُمْ فَهُوَ
خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ وَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَاعْلَمُوا أَنَّكُمْ غَيْرُ مُعْجِزِي
اللهِ ۗ وَبَشِّرِ الَّذِينَ كَفَرُوا بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
Waathanun mina Allahiwarasoolihi ila annasi yawma alhajjial-akbari anna Allaha
baree-on mina almushrikeenawarasooluhu fa-in tubtum fahuwa khayrun lakum wa-in
tawallaytumfaAAlamoo annakum ghayru muAAjizee Allahiwabashshiri allatheena
kafaroo biAAathabin aleem
Hausa
Kuma da yẽkuwa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutãne, a Rãnar Haji Babba cẽwa
lallene Allah Barrantacce ne daga mãsu shirki, kuma ManzonSa (haka). To, idan
kun tũba to shi ne mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun jũya, to, ku sani lalle
ne kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka
kãfirta, da azãba mai raɗaɗi.
|
Ayah 9:4 الأية
إِلَّا الَّذِينَ عَاهَدتُّم مِّنَ الْمُشْرِكِينَ ثُمَّ لَمْ يَنقُصُوكُمْ شَيْئًا
وَلَمْ يُظَاهِرُوا عَلَيْكُمْ أَحَدًا فَأَتِمُّوا إِلَيْهِمْ عَهْدَهُمْ إِلَىٰ
مُدَّتِهِمْ ۚ إِنَّ اللهَ يُحِبُّ الْمُتَّقِينَ
Illa allatheena AAahadtummina almushrikeena thumma lam yanqusookum shay-an walam
yuthahirooAAalaykum ahadan faatimmoo ilayhim AAahdahum ilamuddatihim inna Allaha
yuhibbu almuttaqeen
Hausa
Sai waɗanda kuka yi wani alkawari daga mãsu shirki, sa'an nan kuma ba su rage ku
da kõme ba, kuma ba su taimaki kõwa a kanku ba, to, ku cika alkawarin, zuwa gare
su, har ga iyakar yarjẽjẽyarsu. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa.
|
Ayah 9:5 الأية
فَإِذَا انسَلَخَ الْأَشْهُرُ الْحُرُمُ فَاقْتُلُوا الْمُشْرِكِينَ حَيْثُ
وَجَدتُّمُوهُمْ وَخُذُوهُمْ وَاحْصُرُوهُمْ وَاقْعُدُوا لَهُمْ كُلَّ مَرْصَدٍ ۚ
فَإِن تَابُوا وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ فَخَلُّوا سَبِيلَهُمْ ۚ
إِنَّ اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Fa-itha insalakha al-ashhuru alhurumufaqtuloo almushrikeena haythu wajadtumoohum
wakhuthoohumwahsuroohum waqAAudoo lahum kulla marsadinfa-in taboo waaqamoo
assalatawaatawoo azzakata fakhalloo sabeelahum innaAllaha ghafoorun raheem
Hausa
Kuma idan watanni, mãsu alfarma suka shige, to, ku yãki mushirikai inda kuka
sãmẽ su, kuma ku kãmã su, kuma ku tsare su, kuma ku zaune musu dukkan madãkata.
To, idan sun tũba, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka to ku
sakar musu da hanyarsu. Lalle Allah ne Mai gãfara,Mai jin ƙai.
|
Ayah 9:6 الأية
وَإِنْ أَحَدٌ مِّنَ الْمُشْرِكِينَ اسْتَجَارَكَ فَأَجِرْهُ حَتَّىٰ يَسْمَعَ
كَلَامَ اللهِ ثُمَّ أَبْلِغْهُ مَأْمَنَهُ ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لَّا
يَعْلَمُونَ
Wa-in ahadun mina almushrikeena istajarakafaajirhu hatta yasmaAAa kalama
Allahithumma ablighhu ma/manahu thalika bi-annahum qawmun layaAAlamoon
Hausa
Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya
ji, maganar Allah, sa'an nan ka isar da shi ga wurin amincewarsa. Wancan fa
domin lalle ne su, mutãne ne waɗanda ba su sani ba.
|
Ayah 9:7 الأية
كَيْفَ يَكُونُ لِلْمُشْرِكِينَ عَهْدٌ عِندَ اللهِ وَعِندَ رَسُولِهِ إِلَّا
الَّذِينَ عَاهَدتُّمْ عِندَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ ۖ فَمَا اسْتَقَامُوا لَكُمْ
فَاسْتَقِيمُوا لَهُمْ ۚ إِنَّ اللهَ يُحِبُّ الْمُتَّقِينَ
Kayfa yakoonu lilmushrikeena AAahdun AAindaAllahi waAAinda rasoolihi illa
allatheena AAahadtumAAinda almasjidi alharami fama istaqamoolakum fastaqeemoo
lahum inna Allaha yuhibbualmuttaqeen
Hausa
Yãya wani alkawari a wurin Allah a wurin ManzonSa yake kasancẽwa ga mushirikai,
fãce ga waɗanda kuka yi wa alkawari wurin Masallaci Mai alfarma? To matuƙar sun
tsaya sõsai gare ku, sai ku tsayu sõsai gare su. Lalle ne Allah Yanã son mãsu
taƙawa.
|
Ayah 9:8 الأية
كَيْفَ وَإِن يَظْهَرُوا عَلَيْكُمْ لَا يَرْقُبُوا فِيكُمْ إِلًّا وَلَا ذِمَّةً ۚ
يُرْضُونَكُم بِأَفْوَاهِهِمْ وَتَأْبَىٰ قُلُوبُهُمْ وَأَكْثَرُهُمْ فَاسِقُونَ
Kayfa wa-in yathharoo AAalaykumla yarquboo feekum illan wala thimmatan
yurdoonakumbi-afwahihim wata/ba quloobuhum waaktharuhum fasiqoon
Hausa
Yãya, alhãli idan sun ci nasara a kanku, bã zã su tsare wata zumun ta ba a
cikinku, kuma haka wata amãna, sunã yardar da ku da bãkunansu kuma zukãtansu
sunã ƙi? Kuma mafi yawansu fãsiƙai ne.
|
Ayah 9:9 الأية
اشْتَرَوْا بِآيَاتِ اللهِ ثَمَنًا قَلِيلًا فَصَدُّوا عَن سَبِيلِهِ ۚ إِنَّهُمْ
سَاءَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Ishtaraw bi-ayati Allahithamanan qaleelan fasaddoo AAan sabeelihi innahum saama
kanoo yaAAmaloon
Hausa
Sun saya da ãyõyin Allah, 'yan kuɗi kaɗan, sa'an nan suka kange daga hanyar
Allah. Lalle ne sũ, abin da suka kasance sunã aikatãwa yã mũnana.
|
Ayah 9:10 الأية
لَا يَرْقُبُونَ فِي مُؤْمِنٍ إِلًّا وَلَا ذِمَّةً ۚ وَأُولَٰئِكَ هُمُ
الْمُعْتَدُونَ
La yarquboona fee mu/minin illan walathimmatan waola-ika humu almuAAtadoon
Hausa
Bã su tsaron wata zumunta a cikin mũminai, kuma haka bãsu tsaron wata amãna.
Kuma waɗannan ne mãsu ta'adi.
|
Ayah 9:11 الأية
فَإِن تَابُوا وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ فَإِخْوَانُكُمْ فِي
الدِّينِ ۗ وَنُفَصِّلُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ
Fa-in taboo waaqamoo assalatawaatawoo azzakata fa-ikhwanukum feeaddeeni
wanufassilu al-ayatiliqawmin yaAAlamoon
Hausa
Sa'an nan idan sun tũba kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, to,
'yan'uwanku ne a cikin addini, kuma Munã rarrabe ãyõyi daki-daki, ga mutãne
waɗanda suke sani.
|
Ayah 9:12 الأية
وَإِن نَّكَثُوا أَيْمَانَهُم مِّن بَعْدِ عَهْدِهِمْ وَطَعَنُوا فِي دِينِكُمْ
فَقَاتِلُوا أَئِمَّةَ الْكُفْرِ ۙ إِنَّهُمْ لَا أَيْمَانَ لَهُمْ لَعَلَّهُمْ
يَنتَهُونَ
Wa-in nakathoo aymanahum min baAAdiAAahdihim wataAAanoo fee deenikum
faqatilooa-immata alkufri innahum la aymana lahumlaAAallahum yantahoon
Hausa
Kuma idan suka warware rantsuwõyin amãna daga bãyan alkawarinsu, kuma suka yi
sũka a cikin addininku, to, ku yaki shũgabannin kãfirci. Lalle ne sũ, bãbu
rantsuwõyin amãna a gare su. Tsammãninsu sunã hanuwa.
|
Ayah 9:13 الأية
أَلَا تُقَاتِلُونَ قَوْمًا نَّكَثُوا أَيْمَانَهُمْ وَهَمُّوا بِإِخْرَاجِ
الرَّسُولِ وَهُم بَدَءُوكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ ۚ أَتَخْشَوْنَهُمْ ۚ فَاللهُ
أَحَقُّ أَن تَخْشَوْهُ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Ala tuqatiloona qawmannakathoo aymanahum wahammoo bi-ikhraji arrasooliwahum
badaookum awwala marratin atakhshawnahum fallahuahaqqu an takhshawhu in kuntum
mu/mineen
Hausa
Shin, bã ku yaƙin mutãne, waɗanda suka warware rantsuwõyinsu, kuma suka yi niyya
ga fitar da Manzo, kuma sũ ne suka fãra muku, tun a farkon lõkaci? Shin kunã
tsõron su ne? To, Allah ne marfi cancantar ku ji tsõronSa, idan kun kasance
mũminai!
|
Ayah 9:14 الأية
قَاتِلُوهُمْ يُعَذِّبْهُمُ اللهُ بِأَيْدِيكُمْ وَيُخْزِهِمْ وَيَنصُرْكُمْ
عَلَيْهِمْ وَيَشْفِ صُدُورَ قَوْمٍ مُّؤْمِنِينَ
Qatiloohum yuAAaththibhumu Allahubi-aydeekum wayukhzihim wayansurkum AAalayhim
wayashfi sudooraqawmin mu/mineen
Hausa
Ku yãƙe su, Allah Ya yi musu azabã da hannãyenku, kuma Ya kunyatar da su, kuma
Ya taimake ku, kuma Ya warkar da ƙirãzan mutãne mũminai.
|
Ayah 9:15 الأية
وَيُذْهِبْ غَيْظَ قُلُوبِهِمْ ۗ وَيَتُوبُ اللهُ عَلَىٰ مَن يَشَاءُ ۗ وَاللهُ
عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Wayuthhib ghaythaquloobihim wayatoobu Allahu AAala man yashaowallahu AAaleemun
hakeem
Hausa
Kuma Ya tafĩ da fushin zukãtansu, kuma Ya karɓi tũba a kan wanda Ya so. Kuma
Allah ne Masani, Mai hikima.
|
Ayah 9:16 الأية
أَمْ حَسِبْتُمْ أَن تُتْرَكُوا وَلَمَّا يَعْلَمِ اللهُ الَّذِينَ جَاهَدُوا
مِنكُمْ وَلَمْ يَتَّخِذُوا مِن دُونِ اللهِ وَلَا رَسُولِهِ وَلَا
الْمُؤْمِنِينَ وَلِيجَةً ۚ وَاللهُ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ
Am hasibtum an tutrakoo walammayaAAlami Allahu allatheena jahadoo minkumwalam
yattakhithoo min dooni Allahi walarasoolihi wala almu/mineena waleejatan
wallahukhabeerun bima taAAmaloon
Hausa
Kõ kunã zaton a bar ku, tun Allah bai bayyana waɗanda suka yi jihãdi ba daga
gare ku, kuma sũ ba su riƙi wani shigeba, baicin Allah da ManzonSa da mũminai?
Kuma Allah ne Mai jarrabãwa ga abin da kuke aikatãwa.
|
Ayah 9:17 الأية
مَا كَانَ لِلْمُشْرِكِينَ أَن يَعْمُرُوا مَسَاجِدَ اللهِ شَاهِدِينَ عَلَىٰ
أَنفُسِهِم بِالْكُفْرِ ۚ أُولَٰئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ وَفِي النَّارِ هُمْ
خَالِدُونَ
Ma kana lilmushrikeena anyaAAmuroo masajida Allahi shahideena AAalaanfusihim
bilkufri ola-ika habitataAAmaluhum wafee annari hum khalidoon
Hausa
Bã ya kasancewa ga mãsu shirki su rãya masallatan Allah, alhãli kuwa sunã mãsu
bãyar da shaida a kan rãyukansu da kafirci, waɗannan ayyukansu sun ɓãci, kuma a
cikin wutã sũ madawwama
|
Ayah 9:18 الأية
إِنَّمَا يَعْمُرُ مَسَاجِدَ اللهِ مَنْ آمَنَ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ
وَأَقَامَ الصَّلَاةَ وَآتَى الزَّكَاةَ وَلَمْ يَخْشَ إِلَّا اللهَ ۖ فَعَسَىٰ
أُولَٰئِكَ أَن يَكُونُوا مِنَ الْمُهْتَدِينَ
Innama yaAAmuru masajida Allahiman amana billahi walyawmi al-akhiriwaaqama
assalata waataazzakata walam yakhsha illa AllahafaAAasa ola-ika an yakoonoo mina
almuhtadeen
Hausa
Abin sani kawai, mai rãya masallãtan Allah, shĩ ne wanda ya yi ĩmãni da Allah da
Rãnar Lãhira, kuma ya tsayar da salla kuma ya bãyar da zakka, kuma bai ji tsõron
kõwa ba fãce Allah. To, akwai tsammãnin waɗannan su kasance daga shiryayyu.
|
Ayah 9:19 الأية
أَجَعَلْتُمْ سِقَايَةَ الْحَاجِّ وَعِمَارَةَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ كَمَنْ آمَنَ
بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَجَاهَدَ فِي سَبِيلِ اللهِ ۚ لَا يَسْتَوُونَ
عِندَ اللهِ ۗ وَاللهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
AjaAAaltum siqayata alhajjiwaAAimarata almasjidi alharami kaman amanabillahi
walyawmi al-akhiri wajahadafee sabeeli Allahi la yastawoona AAinda Allahiwallahu
la yahdee alqawma aththalimeen
Hausa
Shin, kun sanya shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar
wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar
Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne
azzãlumai.
|
Ayah 9:20 الأية
الَّذِينَ آمَنُوا وَهَاجَرُوا وَجَاهَدُوا فِي سَبِيلِ اللهِ بِأَمْوَالِهِمْ
وَأَنفُسِهِمْ أَعْظَمُ دَرَجَةً عِندَ اللهِ ۚ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْفَائِزُونَ
Allatheena amanoo wahajaroowajahadoo fee sabeeli Allahi bi-amwalihimwaanfusihim
aAAthamu darajatan AAinda Allahiwaola-ika humu alfa-izoon
Hausa
Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi, a cikin hanyar
Allah, da dũkiyõyinsu, da rãyukansu, sũ ne mafi girma ga daraja, a wurin Allah,
kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
|
Ayah 9:21 الأية
يُبَشِّرُهُمْ رَبُّهُم بِرَحْمَةٍ مِّنْهُ وَرِضْوَانٍ وَجَنَّاتٍ لَّهُمْ فِيهَا
نَعِيمٌ مُّقِيمٌ
Yubashshiruhum rabbuhum birahmatinminhu waridwanin wajannatin lahum
feehanaAAeemun muqeem
Hausa
Ubangijinsu Yanã yi musu bishãra da wata rahama daga gare shi, da yarda, da
gidãjen Aljanna. sunã da, a cikinsu, ni'ima zaunanniya.
|
Ayah 9:22 الأية
خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۚ إِنَّ اللهَ عِندَهُ أَجْرٌ عَظِيمٌ
Khalideena feeha abadan innaAllaha AAindahu ajrun AAatheem
Hausa
Sunã madawwamã a cikinsu, har abada. Lalle ne Allah a wurinSa akwai lãda mai
girma.
|
Ayah 9:23 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا آبَاءَكُمْ وَإِخْوَانَكُمْ
أَوْلِيَاءَ إِنِ اسْتَحَبُّوا الْكُفْرَ عَلَى الْإِيمَانِ ۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم
مِّنكُمْ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ
Ya ayyuha allatheena amanoola tattakhithoo abaakum wa-ikhwanakumawliyaa ini
istahabboo alkufra AAala al-eemaniwaman yatawallahum minkum faola-ika humu
aththalimoon
Hausa
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi ubanninku da 'yan'uwanku masõya, idan
sun nũna son kãfirci a kan ĩmãni. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to,
waɗannan sũ ne azzãlumai.
|
Ayah 9:24 الأية
قُلْ إِن كَانَ آبَاؤُكُمْ وَأَبْنَاؤُكُمْ وَإِخْوَانُكُمْ وَأَزْوَاجُكُمْ
وَعَشِيرَتُكُمْ وَأَمْوَالٌ اقْتَرَفْتُمُوهَا وَتِجَارَةٌ تَخْشَوْنَ كَسَادَهَا
وَمَسَاكِنُ تَرْضَوْنَهَا أَحَبَّ إِلَيْكُم مِّنَ اللهِ وَرَسُولِهِ وَجِهَادٍ
فِي سَبِيلِهِ فَتَرَبَّصُوا حَتَّىٰ يَأْتِيَ اللهُ بِأَمْرِهِ ۗ وَاللهُ لَا
يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ
Qul in kana abaokumwaabnaokum wa-ikhwanukum waazwajukumwaAAasheeratukum
waamwalun iqtaraftumooha watijaratuntakhshawna kasadaha wamasakinu
tardawnahaahabba ilaykum mina Allahi warasoolihi wajihadinfee sabeelihi
fatarabbasoo hatta ya/tiya Allahubi-amrihi wallahu la yahdee alqawma alfasiqeen
Hausa
Ka ce: "Idan ubanninku da ɗiyanku da 'yan'uwanku da mãtanku da danginku da
dũkiyõyi, waɗanda kuka yi tsiwirwirinsu, da fatauci wanda kuke tsõron
tasgaronsa, da gidaje waɗanda kuke yarda da su, sun kasance mafiya sõyuwa a gare
ku daga Allah da ManzonSa, da yin jihãdi ga hanyarSa, to, ku yi jira har Allah
Ya zo da umurninSa! Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai."
|
Ayah 9:25 الأية
لَقَدْ نَصَرَكُمُ اللهُ فِي مَوَاطِنَ كَثِيرَةٍ ۙ وَيَوْمَ حُنَيْنٍ ۙ إِذْ
أَعْجَبَتْكُمْ كَثْرَتُكُمْ فَلَمْ تُغْنِ عَنكُمْ شَيْئًا وَضَاقَتْ عَلَيْكُمُ
الْأَرْضُ بِمَا رَحُبَتْ ثُمَّ وَلَّيْتُم مُّدْبِرِينَ
Laqad nasarakumu Allahu feemawatina katheeratin wayawma hunaynin ithaAAjabatkum
kathratukum falam tughni AAankum shay-an wadaqatAAalaykumu al-ardu bima rahubat
thummawallaytum mudbireen
Hausa
Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a cikin wurãre mãsu yawa, da Rãnar
Hunainu, a lõkacin da yawanku ya bã ku sha'awa, sai bai amfãnar da ku da kõme
ba, kuma ƙasa ta yi ƙunci a kanku da yalwarta, sa'an nan kuma kuka jũya kunã
mãsu bãyar da bãya.
|
Ayah 9:26 الأية
ثُمَّ أَنزَلَ اللهُ سَكِينَتَهُ عَلَىٰ رَسُولِهِ وَعَلَى الْمُؤْمِنِينَ
وَأَنزَلَ جُنُودًا لَّمْ تَرَوْهَا وَعَذَّبَ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ وَذَٰلِكَ
جَزَاءُ الْكَافِرِينَ
Thumma anzala Allahu sakeenatahu AAalarasoolihi waAAala almu/mineena waanzala
junoodan lamtarawha waAAaththaba allatheena kafaroo wathalikajazao alkafireen
Hausa
Sa'an nan kuma Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa kuma a kan mũminai,
kuma Ya saukar da rundunõni waɗanda ba ku gan su ba, kuma Ya azabtar da waɗanda
suka kãfirta: Wancan ne sakamakon kãfirai.
|
Ayah 9:27 الأية
ثُمَّ يَتُوبُ اللهُ مِن بَعْدِ ذَٰلِكَ عَلَىٰ مَن يَشَاءُ ۗ وَاللهُ غَفُورٌ
رَّحِيمٌ
Thumma yatoobu Allahu min baAAdi thalikaAAala man yashao wallahu ghafoorunraheem
Hausa
Sa'an nan kuma Allah Ya karɓi tũba daga bãyan wancana kan wanda Ya so. Kuma
Allah ne Mai gãfara, Mai rahama.
|
Ayah 9:28 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّمَا الْمُشْرِكُونَ نَجَسٌ فَلَا يَقْرَبُوا
الْمَسْجِدَ الْحَرَامَ بَعْدَ عَامِهِمْ هَٰذَا ۚ وَإِنْ خِفْتُمْ عَيْلَةً
فَسَوْفَ يُغْنِيكُمُ اللهُ مِن فَضْلِهِ إِن شَاءَ ۚ إِنَّ اللهَ عَلِيمٌ
حَكِيمٌ
Ya ayyuha allatheena amanooinnama almushrikoona najasun fala yaqrabooalmasjida
alharama baAAda AAamihim hathawa-in khiftum AAaylatan fasawfa yughneekumu Allahu
min fadlihiin shaa inna Allaha AAaleemun hakeem
Hausa
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, sabõda haka
kada su kusanci Masallaci Mai alfarma a bãyan shẽkararsu wannan. Kuma idan kun
ji tsõron talauci to, da sannu Allah zai wadãta ku daga falalarSa, idan Ya so.
Lalle Allah ne Masani, mai hikima.
|
Ayah 9:29 الأية
قَاتِلُوا الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِاللهِ وَلَا بِالْيَوْمِ الْآخِرِ وَلَا
يُحَرِّمُونَ مَا حَرَّمَ اللهُ وَرَسُولُهُ وَلَا يَدِينُونَ دِينَ الْحَقِّ
مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ حَتَّىٰ يُعْطُوا الْجِزْيَةَ عَن يَدٍ وَهُمْ
صَاغِرُونَ
Qatiloo allatheena layu/minoona billahi wala bilyawmial-akhiri wala yuharrimoona
ma harramaAllahu warasooluhu wala yadeenoona deena alhaqqimina allatheena ootoo
alkitaba hattayuAAtoo aljizyata AAan yadin wahum saghiroon
Hausa
Ku yãƙi waɗanda bã su yin ĩmãni da Allah kuma bã su ĩmãni da Rãnar Lãhira kumabã
su haramta abin da Allah da ManzonSa suka haramta, kuma bã su yin addini,
addinin gaskiya, daga waɗanda aka bai wa Littãfi, har sai sun bãyar da jizya
daga, hannu, kuma sunã ƙasƙantattu.
|
Ayah 9:30 الأية
وَقَالَتِ الْيَهُودُ عُزَيْرٌ ابْنُ اللهِ وَقَالَتِ النَّصَارَى الْمَسِيحُ
ابْنُ اللهِ ۖ ذَٰلِكَ قَوْلُهُم بِأَفْوَاهِهِمْ ۖ يُضَاهِئُونَ قَوْلَ
الَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَبْلُ ۚ قَاتَلَهُمُ اللهُ ۚ أَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ
Waqalati alyahoodu AAuzayrun ibnu Allahiwaqalati annasara almaseehuibnu Allahi
thalika qawluhum bi-afwahihim yudahi-oonaqawla allatheena kafaroo min qablu
qatalahumu Allahuanna yu/fakoon
Hausa
Kuma Yahũdãwa suka ce: "Uzairu ɗan Allah ne."Kuma Nasãra suka ce: "Masĩhu ɗan
Allah ne." Wancan zancensu ne da bãkunansu. Sunã kamã da maganar waɗanda suka
kãfirta daga gabãni. Allah Yã la'ance su! Yãya aka karkatar da su?
|
Ayah 9:31 الأية
اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِّن دُونِ اللهِ
وَالْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا إِلَٰهًا وَاحِدًا
ۖ لَّا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ سُبْحَانَهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Ittakhathoo ahbarahumwaruhbanahum arbaban min dooni Allahi walmaseehaibna
maryama wama omiroo illa liyaAAbudoo ilahanwahidan la ilaha illa huwa
subhanahuAAamma yushrikoon
Hausa
Sun riƙi mãlamansu (Yahũdu) da ruhubãnãwansu (Nasãra) Ubannangiji, baicin Allah,
kuma sun riƙi Masĩhu ɗan Maryama ( haka). Kuma ba a umurce su ba fãce da su
bautã wa Ubangiji Guda. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. TsarkinSa ya tabbata daga
barin abin da suke yin shirki da shi.
|
Ayah 9:32 الأية
يُرِيدُونَ أَن يُطْفِئُوا نُورَ اللهِ بِأَفْوَاهِهِمْ وَيَأْبَى اللهُ إِلَّا
أَن يُتِمَّ نُورَهُ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ
Yureedoona an yutfi-oo noora Allahibi-afwahihim waya/ba Allahu illa anyutimma
noorahu walaw kariha alkafiroon
Hausa
Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunãnsu. Kuma Allah Yanã ki, fãce dai Ya
cika haskenSa, kuma kõ da kãfirai sun ƙi.
|
Ayah 9:33 الأية
هُوَ الَّذِي أَرْسَلَ رَسُولَهُ بِالْهُدَىٰ وَدِينِ الْحَقِّ لِيُظْهِرَهُ عَلَى
الدِّينِ كُلِّهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُشْرِكُونَ
Huwa allathee arsala rasoolahu bilhudawadeeni alhaqqi liyuthhirahu AAala
addeenikullihi walaw kariha almushrikoon
Hausa
Shi ne wanda Ya aiko manzonSa da shiriya da addinin gaskiya, dõmin ya bayyanl
shi a kan addini dukansa, kuma kõ dã mushirikai sun ƙi.
|
Ayah 9:34 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ كَثِيرًا مِّنَ الْأَحْبَارِ وَالرُّهْبَانِ
لَيَأْكُلُونَ أَمْوَالَ النَّاسِ بِالْبَاطِلِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللهِ ۗ
وَالَّذِينَ يَكْنِزُونَ الذَّهَبَ وَالْفِضَّةَ وَلَا يُنفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ
اللهِ فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
Ya ayyuha allatheena amanooinna katheeran mina al-ahbari warruhbanilaya/kuloona
amwala annasi bilbatiliwayasuddoona AAan sabeeli Allahi wallatheenayaknizoona
aththahaba walfiddatawala yunfiqoonaha fee sabeeli Allahifabashshirhum
biAAathabin aleem
Hausa
Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã
cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda
suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar
Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
|
Ayah 9:35 الأية
يَوْمَ يُحْمَىٰ عَلَيْهَا فِي نَارِ جَهَنَّمَ فَتُكْوَىٰ بِهَا جِبَاهُهُمْ
وَجُنُوبُهُمْ وَظُهُورُهُمْ ۖ هَٰذَا مَا كَنَزْتُمْ لِأَنفُسِكُمْ فَذُوقُوا مَا
كُنتُمْ تَكْنِزُونَ
Yawma yuhma AAalayhafee nari jahannama fatukwa biha jibahuhumwajunoobuhum
wathuhooruhum hatha makanaztum li-anfusikum fathooqoo ma kuntum taknizoon
Hausa
A Rãnar da ake ƙõna shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita
ga gõshinansu da sãshinansu da bãyayyakinsu, (a ce musu): "Wannan ne abin da
kuka taskace dõmin rãyukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã sanyãwa a
taska."
|
Ayah 9:36 الأية
إِنَّ عِدَّةَ الشُّهُورِ عِندَ اللهِ اثْنَا عَشَرَ شَهْرًا فِي كِتَابِ اللهِ
يَوْمَ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ مِنْهَا أَرْبَعَةٌ حُرُمٌ ۚ ذَٰلِكَ
الدِّينُ الْقَيِّمُ ۚ فَلَا تَظْلِمُوا فِيهِنَّ أَنفُسَكُمْ ۚ وَقَاتِلُوا
الْمُشْرِكِينَ كَافَّةً كَمَا يُقَاتِلُونَكُمْ كَافَّةً ۚ وَاعْلَمُوا أَنَّ
اللهَ مَعَ الْمُتَّقِينَ
Inna AAiddata ashshuhoori AAinda Allahiithna AAashara shahran fee kitabi
Allahiyawma khalaqa assamawati wal-ardaminha arbaAAatun hurumun thalika
addeenualqayyimu fala tathlimoo feehinna anfusakumwaqatiloo almushrikeena
kaffatan kama yuqatiloonakumkaffatan waAAlamoo anna Allaha maAAaalmuttaqeen
Hausa
Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin
Littãfin Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu
mãsu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a
cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya.
Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.
|
Ayah 9:37 الأية
إِنَّمَا النَّسِيءُ زِيَادَةٌ فِي الْكُفْرِ ۖ يُضَلُّ بِهِ الَّذِينَ كَفَرُوا
يُحِلُّونَهُ عَامًا وَيُحَرِّمُونَهُ عَامًا لِّيُوَاطِئُوا عِدَّةَ مَا حَرَّمَ
اللهُ فَيُحِلُّوا مَا حَرَّمَ اللهُ ۚ زُيِّنَ لَهُمْ سُوءُ أَعْمَالِهِمْ ۗ
وَاللهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْكَافِرِينَ
Innama annasee-o ziyadatunfee alkufri yudallu bihi allatheena kafaroo
yuhilloonahuAAaman wayuharrimoonahu AAaman liyuwati-ooAAiddata ma harrama Allahu
fayuhillooma harrama Allahu zuyyina lahum soo-o aAAmalihimwallahu la yahdee
alqawma alkafireen
Hausa
Abin sani kawai, "Jinkirtãwa" ƙãri ne a cikin kãfirci, anã ɓatar da waɗanda suka
kãfirta game da shi. Sunã halattar da watã a wata shẽkara kuma su haramtar da
shi a wata shẽkara dõmin su dãce da adadin abin da Allah Ya haramta. Sabõda haka
sunã halattar da abin da Allah Ya haramtar. An ƙawãce musu mũnanan ayyukansu.
Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai.
|
Ayah 9:38 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا مَا لَكُمْ إِذَا قِيلَ لَكُمُ انفِرُوا فِي
سَبِيلِ اللهِ اثَّاقَلْتُمْ إِلَى الْأَرْضِ ۚ أَرَضِيتُم بِالْحَيَاةِ
الدُّنْيَا مِنَ الْآخِرَةِ ۚ فَمَا مَتَاعُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا فِي الْآخِرَةِ
إِلَّا قَلِيلٌ
Ya ayyuha allatheena amanooma lakum itha qeela lakumu infiroo fee sabeeli
Allahiiththaqaltum ila al-ardi aradeetum bilhayatiaddunya mina al-akhirati fama
mataAAualhayati addunya fee al-akhiratiilla qaleel
Hausa
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Mẽne ne a gare ku, idan ance muku, "Ku fita da yãƙi
a cikin hanyar Allah," sai ku yi nauyi zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rãyuwar
dũniya ne daga ta Lãhira? To jin dãɗin rãyuwar dũniya bai zama ba a cikin
Lãhira, fãce kaɗan.
|
Ayah 9:39 الأية
إِلَّا تَنفِرُوا يُعَذِّبْكُمْ عَذَابًا أَلِيمًا وَيَسْتَبْدِلْ قَوْمًا
غَيْرَكُمْ وَلَا تَضُرُّوهُ شَيْئًا ۗ وَاللهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Illa tanfiroo yuAAaththibkumAAathaban aleeman wayastabdil qawman ghayrakum
walatadurroohu shay-an wallahu AAalakulli shay-in qadeer
Hausa
Idan ba ku fita da yãƙi ba, Allah zai azabta ku da azãba mai raɗaɗi, kuma Ya
musanya wasu mutãne, wasunku (a maimakonku). Kuma bã zã ku cũtar da Shida kõme
ba. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.
|
Ayah 9:40 الأية
إِلَّا تَنصُرُوهُ فَقَدْ نَصَرَهُ اللهُ إِذْ أَخْرَجَهُ الَّذِينَ كَفَرُوا
ثَانِيَ اثْنَيْنِ إِذْ هُمَا فِي الْغَارِ إِذْ يَقُولُ لِصَاحِبِهِ لَا تَحْزَنْ
إِنَّ اللهَ مَعَنَا ۖ فَأَنزَلَ اللهُ سَكِينَتَهُ عَلَيْهِ وَأَيَّدَهُ
بِجُنُودٍ لَّمْ تَرَوْهَا وَجَعَلَ كَلِمَةَ الَّذِينَ كَفَرُوا السُّفْلَىٰ ۗ
وَكَلِمَةُ اللهِ هِيَ الْعُلْيَا ۗ وَاللهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Illa tansuroohu faqad nasarahuAllahu ith akhrajahu allatheena kafaroo
thaniyaithnayni ith huma fee alghari ithyaqoolu lisahibihi la tahzan inna
AllahamaAAana faanzala Allahu sakeenatahu AAalayhiwaayyadahu bijunoodin lam
tarawha wajaAAala kalimata allatheenakafaroo assufla wakalimatu Allahi
hiyaalAAulya wallahu AAazeezun hakeem
Hausa
Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Yã taimake shi, a lõkacin da
waɗanda suka kãfirta suka fitar da shi, Yanã na biyun biyu, a lõkacin da suke
cikin kõgon dũtse, a lõkacin da yake cẽwa da sãhibinsa: "Kada ka yi baƙin ciki,
lalle ne Allah Yanã tãre da mu." Sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kansa, kuma
Ya taimake shi da waɗansu rundunõni, ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar
waɗanda suka kãfirta maƙasƙanciya, kuma kalmar Allah ita ce maɗaukakiya. Kuma
Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
|
Ayah 9:41 الأية
انفِرُوا خِفَافًا وَثِقَالًا وَجَاهِدُوا بِأَمْوَالِكُمْ وَأَنفُسِكُمْ فِي
سَبِيلِ اللهِ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Infiroo khifafan wathiqalanwajahidoo bi-amwalikum waanfusikum fee sabeeli
Allahithalikum khayrun lakum in kuntum taAAlamoon
Hausa
Ku fita da yãƙi kunã mãsu sauƙãƙan kãyã da mãsu nauyi, kuma ku yi jihãdi da
dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare
ku, idan kun kasance kunã sani.
|
Ayah 9:42 الأية
لَوْ كَانَ عَرَضًا قَرِيبًا وَسَفَرًا قَاصِدًا لَّاتَّبَعُوكَ وَلَٰكِن بَعُدَتْ
عَلَيْهِمُ الشُّقَّةُ ۚ وَسَيَحْلِفُونَ بِاللهِ لَوِ اسْتَطَعْنَا لَخَرَجْنَا
مَعَكُمْ يُهْلِكُونَ أَنفُسَهُمْ وَاللهُ يَعْلَمُ إِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ
Law kana AAaradan qareebanwasafaran qasidan lattabaAAooka walakinbaAAudat
AAalayhimu ashshuqqatu wasayahlifoona billahilawi istataAAna lakharajna
maAAakumyuhlikoona anfusahum wallahu yaAAlamu innahum lakathiboon
Hausa
Dã yã kasance wata siffar dũniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, dã sun
bĩ ka, kuma amma fagen yã yi musu nĩsa.Kuma zã su yi ta yin rantsuwa da Allah,
"Dã mun sãmi dãma, dã mun tafi tare da ku." Sunã halakar da kansu (da rantsuwar
ƙarya) ne, kuma Allah Yanã sanin lalle, haƙĩƙa, sumaƙaryata ne.'
|
Ayah 9:43 الأية
عَفَا اللهُ عَنكَ لِمَ أَذِنتَ لَهُمْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكَ الَّذِينَ
صَدَقُوا وَتَعْلَمَ الْكَاذِبِينَ
AAafa Allahu AAanka lima athintalahum hatta yatabayyana laka allatheena
sadaqoowataAAlama alkathibeen
Hausa
Allah Ya yãfe maka laifi. Dõmin me ka yi musu izinin zama? Sai waɗanda suka yi
gaskiya ssun bayyana a gare ka, kuma ka san maƙaryata.
|
Ayah 9:44 الأية
لَا يَسْتَأْذِنُكَ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ أَن
يُجَاهِدُوا بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ بِالْمُتَّقِينَ
La yasta/thinuka allatheenayu/minoona billahi walyawmi al-akhirian yujahidoo
bi-amwalihim waanfusihim wallahuAAaleemun bilmuttaqeen
Hausa
Waɗanda suke yin ĩmãnida Allah da Rãnar Lãhira, bã zã su nẽmi izininka ga yin,
jihãdida dũkiyõyinsu da rãyukansu ba. Kuma Allah ne Masani ga mãsu taƙawa.
|
Ayah 9:45 الأية
إِنَّمَا يَسْتَأْذِنُكَ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ
وَارْتَابَتْ قُلُوبُهُمْ فَهُمْ فِي رَيْبِهِمْ يَتَرَدَّدُونَ
Innama yasta/thinuka allatheenala yu/minoona billahi walyawmi al-akhiriwartabat
quloobuhum fahum fee raybihimyataraddadoon
Hausa
Abin sani kawai, waɗanda bã sa ĩmãni da Allah, da Rãnar Lãhira, kuma zukãtansu
suka yi shakka, sũ ne ke nẽman izininka, sa'an nan a cikin shakkarsu sunã ta yin
kai kãwo.
|
Ayah 9:46 الأية
وَلَوْ أَرَادُوا الْخُرُوجَ لَأَعَدُّوا لَهُ عُدَّةً وَلَٰكِن كَرِهَ اللهُ
انبِعَاثَهُمْ فَثَبَّطَهُمْ وَقِيلَ اقْعُدُوا مَعَ الْقَاعِدِينَ
Walaw aradoo alkhurooja laaAAaddoolahu AAuddatan walakin kariha Allahu
inbiAAathahumfathabbatahum waqeela oqAAudoo maAAa alqaAAideen
Hausa
Kuma dã sun yi nufin fita, dã sun yi wani tattali sabõda shi, kuma amma Allah Ya
ƙi zãburarsu, sai Ya nauyayar da zamansu. Kuma aka ce ku zauna tãre da mãsu
zama.
|
Ayah 9:47 الأية
لَوْ خَرَجُوا فِيكُم مَّا زَادُوكُمْ إِلَّا خَبَالًا وَلَأَوْضَعُوا خِلَالَكُمْ
يَبْغُونَكُمُ الْفِتْنَةَ وَفِيكُمْ سَمَّاعُونَ لَهُمْ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ
بِالظَّالِمِينَ
Law kharajoo feekum ma zadookumilla khabalan walaawdaAAoo
khilalakumyabghoonakumu alfitnata wafeekum sammaAAoona lahum wallahuAAaleemun
biththalimeen
Hausa
Dã sun fita a cikinku bã zã su ƙãre ku da kõme ba fãce da ɓarna, kuma lalle dã
sun yi gaggãwar sanya annamĩmanci a tsakãninku, sunã nẽma muku fitina. Kuma a
cikinku akwai 'yan rahõto sabõda su. Kuma Allah ne Masani ga azzãlumai,
|
Ayah 9:48 الأية
لَقَدِ ابْتَغَوُا الْفِتْنَةَ مِن قَبْلُ وَقَلَّبُوا لَكَ الْأُمُورَ حَتَّىٰ
جَاءَ الْحَقُّ وَظَهَرَ أَمْرُ اللهِ وَهُمْ كَارِهُونَ
Laqadi ibtaghawoo alfitnata min qabluwaqallaboo laka al-omoora hatta jaa
alhaqquwathahara amru Allahi wahum karihoon
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa sun nẽmi fitina daga gabãni, kuma, suka jũya maka
al'amari, har gaskiya ta zo, kuma umurnin Allah Ya bayyana, alhãli sunã mãsu
ƙyãma,
|
Ayah 9:49 الأية
وَمِنْهُم مَّن يَقُولُ ائْذَن لِّي وَلَا تَفْتِنِّي ۚ أَلَا فِي الْفِتْنَةِ
سَقَطُوا ۗ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةٌ بِالْكَافِرِينَ
Waminhum man yaqoolu i/than lee walataftinnee ala fee alfitnati saqatoo
wa-innajahannama lamuheetatun bilkafireen
Hausa
Kuma daga cikinsu akwai mai cẽwa, "Ka yi mini izinin zama, kuma kada ka fitine
ni." To, a cikin fitinar suka fãɗa. Kuma lalle ne Jahannama, haƙĩƙa, mai
ƙẽwayẽwa ce ga kãfirai.
|
Ayah 9:50 الأية
إِن تُصِبْكَ حَسَنَةٌ تَسُؤْهُمْ ۖ وَإِن تُصِبْكَ مُصِيبَةٌ يَقُولُوا قَدْ
أَخَذْنَا أَمْرَنَا مِن قَبْلُ وَيَتَوَلَّوا وَّهُمْ فَرِحُونَ
In tusibka hasanatun tasu/humwa-in tusibka museebatun yaqooloo qad
akhathnaamrana min qablu wayatawallaw wahum farihoon
Hausa
Idan wani alhẽri ya sãme ka, zai ɓãta musu rai, kuma idan wata masifa ta sãme ka
sai su ce: "Haƙĩƙa, mun riƙe al'amarinmu daga gabãni."Kuma sujũya, alhãli kuwa
sunã mãsu farin ciki.
|
Ayah 9:51 الأية
قُل لَّن يُصِيبَنَا إِلَّا مَا كَتَبَ اللهُ لَنَا هُوَ مَوْلَانَا ۚ وَعَلَى
اللهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ
Qul lan yuseebana illama kataba Allahu lana huwa mawlanawaAAala Allahi
falyatawakkali almu/minoon
Hausa
Ka ce: "Bãbu abin da yake sãmun mu fãce abin da Allah Ya rubũta sahõda mu. Shĩ
ne Majiɓincinmu. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara."
|
Ayah 9:52 الأية
قُلْ هَلْ تَرَبَّصُونَ بِنَا إِلَّا إِحْدَى الْحُسْنَيَيْنِ ۖ وَنَحْنُ
نَتَرَبَّصُ بِكُمْ أَن يُصِيبَكُمُ اللهُ بِعَذَابٍ مِّنْ عِندِهِ أَوْ
بِأَيْدِينَا ۖ فَتَرَبَّصُوا إِنَّا مَعَكُم مُّتَرَبِّصُونَ
Qul hal tarabbasoona bina illaihda alhusnayayni wanahnu natarabbasubikum an
yuseebakumu Allahu biAAathabin minAAindihi aw bi-aydeena fatarabbasoo
innamaAAakum mutarabbisoon
Hausa
Ka ce: "Shin, kunã dãko ne da mu? Fãce dai da ɗayan abũbuwan biyu mãsu kyau,
alhãli kuwa mũ, munã dãko da ku, AllahYa sãme ku da wata azãba daga gare Shi, kõ
kuwa da hannayenmu. To, ku yi dãko. Lalle ne mũ, tãre da ku mãsu dãkon ne."
|
Ayah 9:53 الأية
قُلْ أَنفِقُوا طَوْعًا أَوْ كَرْهًا لَّن يُتَقَبَّلَ مِنكُمْ ۖ إِنَّكُمْ كُنتُمْ
قَوْمًا فَاسِقِينَ
Qul anfiqoo tawAAan aw karhan lanyutaqabbala minkum innakum kuntum qawman
fasiqeen
Hausa
Ka ce: "Ku ciyar a kan yarda kõ kuwa a kan tĩlas. Bã zã a karɓa daga gare ku ba.
Lalle ne kũ, kun kasance mutãne fãsiƙai."
|
Ayah 9:54 الأية
وَمَا مَنَعَهُمْ أَن تُقْبَلَ مِنْهُمْ نَفَقَاتُهُمْ إِلَّا أَنَّهُمْ كَفَرُوا
بِاللهِ وَبِرَسُولِهِ وَلَا يَأْتُونَ الصَّلَاةَ إِلَّا وَهُمْ كُسَالَىٰ وَلَا
يُنفِقُونَ إِلَّا وَهُمْ كَارِهُونَ
Wama manaAAahum an tuqbala minhumnafaqatuhum illa annahum kafaroo
billahiwabirasoolihi wala ya/toona assalatailla wahum kusala wala yunfiqoona
illawahum karihoon
Hausa
Kuma bãbu abin da ya hana a karɓi ciyarwarsu daga gare su fãce dõmin sũ, sun
kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma bã su zuwa ga salla fãce Luma sunã mãsu
kasãla, kuma bã su ciyarwa fãce sunã mãsu ƙyãma.
|
Ayah 9:55 الأية
فَلَا تُعْجِبْكَ أَمْوَالُهُمْ وَلَا أَوْلَادُهُمْ ۚ إِنَّمَا يُرِيدُ اللهُ
لِيُعَذِّبَهُم بِهَا فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَتَزْهَقَ أَنفُسُهُمْ وَهُمْ
كَافِرُونَ
Fala tuAAjibka amwaluhum walaawladuhum innama yureedu Allahu
liyuAAaththibahumbiha fee alhayati addunyawatazhaqa anfusuhum wahum kafiroon
Hausa
Sabõda haka, kada dũkiyõyinsu su bã ka sha'awa, kuma haka 'ya'yansu. Abin sani
kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba, da su a cikin rãyuwar dũniya, kuma
rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai.
|
Ayah 9:56 الأية
وَيَحْلِفُونَ بِاللهِ إِنَّهُمْ لَمِنكُمْ وَمَا هُم مِّنكُمْ وَلَٰكِنَّهُمْ
قَوْمٌ يَفْرَقُونَ
Wayahlifoona billahiinnahum laminkum wama hum minkum walakinnahumqawmun
yafraqoon
Hausa
Kuma sunã rantsuwa da Allah cẽwa, lalle ne sũ, haƙĩƙa, daga gare ku suke, alhãli
kuwa ba su zamo daga gare ku ba. Kuma amma sũ mutãne ne mãsu tsõro.
|
Ayah 9:57 الأية
لَوْ يَجِدُونَ مَلْجَأً أَوْ مَغَارَاتٍ أَوْ مُدَّخَلًا لَّوَلَّوْا إِلَيْهِ
وَهُمْ يَجْمَحُونَ
Law yajidoona maljaan aw magharatinaw muddakhalan lawallaw ilayhi wahum
yajmahoon
Hausa
Dã sunã sãmun mafaka kõ kuwa waɗansu ɓulõli, kõ kuwa wani mashigi, da sun, jũya
zuwa gare shi, kuma suna gaggawar shiga.
|
Ayah 9:58 الأية
وَمِنْهُم مَّن يَلْمِزُكَ فِي الصَّدَقَاتِ فَإِنْ أُعْطُوا مِنْهَا رَضُوا وَإِن
لَّمْ يُعْطَوْا مِنْهَا إِذَا هُمْ يَسْخَطُونَ
Waminhum man yalmizuka fee assadaqatifa-in oAAtoo minha radoo wa-in lam
yuAAtawminha itha hum yaskhatoon
Hausa
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake zunɗen ka a kan sha'anin dũkiyõyin sadaka,
sai idan an bã su daga cikinta, su yarda, kuma idan ba a bã su ba daga cikinta
sai su zamo sunã mãsu fushi.
|
Ayah 9:59 الأية
وَلَوْ أَنَّهُمْ رَضُوا مَا آتَاهُمُ اللهُ وَرَسُولُهُ وَقَالُوا حَسْبُنَا
اللهُ سَيُؤْتِينَا اللهُ مِن فَضْلِهِ وَرَسُولُهُ إِنَّا إِلَى اللهِ
رَاغِبُونَ
Walaw annahum radoo ma atahumuAllahu warasooluhu waqaloo hasbunaAllahu
sayu/teena Allahu min fadlihiwarasooluhu inna ila Allahi raghiboon
Hausa
Kuma dã dai su lalle sun yarda da abin da Allah Ya bã su, da ManzonSa kuma suka
ce: "Ma'ishinmu Allah ne, zai kãwo mana daga falalarSa kuma ManzõnSa (zai bã
mu). Lalle ne mũ, zuwa ga Allah mãsu kwaɗayi ne."
|
Ayah 9:60 الأية
إِنَّمَا الصَّدَقَاتُ لِلْفُقَرَاءِ وَالْمَسَاكِينِ وَالْعَامِلِينَ عَلَيْهَا
وَالْمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمْ وَفِي الرِّقَابِ وَالْغَارِمِينَ وَفِي سَبِيلِ
اللهِ وَابْنِ السَّبِيلِ ۖ فَرِيضَةً مِّنَ اللهِ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Innama assadaqatulilfuqara-i walmasakeeni walAAamileenaAAalayha walmu-allafati
quloobuhum wafee arriqabiwalgharimeena wafee sabeeli Allahi wabniassabeeli
fareedatan mina Allahi wallahuAAaleemun hakeemun
Hausa
Abin sani kawai, dũkiyõyin sadaka na faƙĩrai ne da miskinai da mãsu aiki a
kansu, da waɗanda ake lallãshin zukãtansu, kuma a cikin fansar wuyõyi, da
mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah.
Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
|
Ayah 9:61 الأية
وَمِنْهُمُ الَّذِينَ يُؤْذُونَ النَّبِيَّ وَيَقُولُونَ هُوَ أُذُنٌ ۚ قُلْ أُذُنُ
خَيْرٍ لَّكُمْ يُؤْمِنُ بِاللهِ وَيُؤْمِنُ لِلْمُؤْمِنِينَ وَرَحْمَةٌ
لِّلَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ ۚ وَالَّذِينَ يُؤْذُونَ رَسُولَ اللهِ لَهُمْ
عَذَابٌ أَلِيمٌ
Waminhumu allatheena yu/thoonaannabiyya wayaqooloona huwa othunun qul
othunukhayrin lakum yu/minu billahi wayu/minulilmu/mineena warahmatun
lillatheena amanoominkum wallatheena yu/thoona rasoola Allahilahum AAathabun
aleem
Hausa
Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke cũtar Annabi, kuma sunã cẽwa "Shi kunne
ne." Ka ce: "Kunnen alhẽri gare ku,Yanã ĩmãni da Allah, kuma Yanã yarda da
mũminai, kuma rahama ne ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare ku."Kuma waɗanda suke
cũtar Manzon Allah sunã da azãba mai raɗaɗi.
|
Ayah 9:62 الأية
يَحْلِفُونَ بِاللهِ لَكُمْ لِيُرْضُوكُمْ وَاللهُ وَرَسُولُهُ أَحَقُّ أَن
يُرْضُوهُ إِن كَانُوا مُؤْمِنِينَ
Yahlifoona billahilakum liyurdookum wallahu warasooluhu ahaqquan yurdoohu in
kanoo mu/mineen
Hausa
Sunã rantsuwa da Allah sabõda ku, dõmin su yardar da ku. Kuma Allah da ManzonSa
ne mafi cancantar su yardar da Shi, idan sun kasance mũminai.
|
Ayah 9:63 الأية
أَلَمْ يَعْلَمُوا أَنَّهُ مَن يُحَادِدِ اللهَ وَرَسُولَهُ فَأَنَّ لَهُ نَارَ
جَهَنَّمَ خَالِدًا فِيهَا ۚ ذَٰلِكَ الْخِزْيُ الْعَظِيمُ
Alam yaAAlamoo annahu man yuhadidiAllaha warasoolahu faanna lahu nara jahannama
khalidanfeeha thalika alkhizyu alAAatheem
Hausa
Shin, ba su sani ba cẽwa "Lalle ne wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, haƙĩƙa
Yanã da wutar Jahannama, Yanã madawwami a cikinta? Waccan ita ce wulãkantãwa
babba!"
|
Ayah 9:64 الأية
يَحْذَرُ الْمُنَافِقُونَ أَن تُنَزَّلَ عَلَيْهِمْ سُورَةٌ تُنَبِّئُهُم بِمَا فِي
قُلُوبِهِمْ ۚ قُلِ اسْتَهْزِئُوا إِنَّ اللهَ مُخْرِجٌ مَّا تَحْذَرُونَ
Yahtharu almunafiqoona antunazzala AAalayhim sooratun tunabbi-ohum bima
feequloobihim quli istahzi-oo inna Allaha mukhrijun matahtharoon
Hausa
Munãfukai sunã tsõron a saukar da wata sũra a kansu,wadda take bã su lãbãri ga
abin da yake cikin zukãtansu. Ka ce: "Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai
da abin da kuke tsõro."
|
Ayah 9:65 الأية
وَلَئِن سَأَلْتَهُمْ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلْعَبُ ۚ قُلْ
أَبِاللهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ
Wala-in saaltahum layaqoolunna innamakunna nakhoodu wanalAAabu qul
abillahiwaayatihi warasoolihi kuntum tastahzi-oon
Hausa
Kuma lalle ne, idan ka tambaye , su haƙĩƙa, sunã cẽwa, "Abin sani kawai, mun
kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da
ManzonSa kuka kasance kunã izgili?"
|
Ayah 9:66 الأية
لَا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُم بَعْدَ إِيمَانِكُمْ ۚ إِن نَّعْفُ عَن طَائِفَةٍ
مِّنكُمْ نُعَذِّبْ طَائِفَةً بِأَنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ
La taAAtathiroo qad kafartumbaAAda eemanikum in naAAfu AAan ta-ifatin
minkumnuAAaththib ta-ifatan bi-annahum kanoomujrimeen
Hausa
"Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyanĩmãninku. Idan Mun yãfe
laifi ga wata ƙungiya daga gare ku, zã Mu azabta wata ƙungiya sabõda, lalle, sun
kasance mãsu laifi."
|
Ayah 9:67 الأية
الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ بَعْضُهُم مِّن بَعْضٍ ۚ يَأْمُرُونَ
بِالْمُنكَرِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمَعْرُوفِ وَيَقْبِضُونَ أَيْدِيَهُمْ ۚ نَسُوا
اللهَ فَنَسِيَهُمْ ۗ إِنَّ الْمُنَافِقِينَ هُمُ الْفَاسِقُونَ
Almunafiqoona walmunafiqatubaAAduhum min baAAdin ya/muroona bilmunkariwayanhawna
AAani almaAAroofi wayaqbidoona aydiyahum nasooAllaha fanasiyahum inna
almunafiqeena humu alfasiqoon
Hausa
Munãfukai maza da munãfukai mãtã, sãshensu daga sãshe, sunã umurni da abin ƙi
kuma sunã hani daga alhẽri.Kuma sunã damƙẽwar hannayensu.Sun mance Allah, sai Ya
mantã da su. Lalle ne munãfukai sũ ne fãsiƙai.
|
Ayah 9:68 الأية
وَعَدَ اللهُ الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْكُفَّارَ نَارَ جَهَنَّمَ
خَالِدِينَ فِيهَا ۚ هِيَ حَسْبُهُمْ ۚ وَلَعَنَهُمُ اللهُ ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ
مُّقِيمٌ
WaAAada Allahu almunafiqeenawalmunafiqati walkuffara narajahannama khalideena
feeha hiya hasbuhumwalaAAanahumu Allahu walahum AAathabun muqeem
Hausa
Allah yã yi wa'adi ga munãfukai maza da munãfukai mãtã da kãfirai da wutar
Jahannama, sunã madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu. Kuma Allah Yã la'ance
su, kuma sunã da azãba zaunanniya.
|
Ayah 9:69 الأية
كَالَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ كَانُوا أَشَدَّ مِنكُمْ قُوَّةً وَأَكْثَرَ أَمْوَالًا
وَأَوْلَادًا فَاسْتَمْتَعُوا بِخَلَاقِهِمْ فَاسْتَمْتَعْتُم بِخَلَاقِكُمْ كَمَا
اسْتَمْتَعَ الَّذِينَ مِن قَبْلِكُم بِخَلَاقِهِمْ وَخُضْتُمْ كَالَّذِي خَاضُوا ۚ
أُولَٰئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ ۖ وَأُولَٰئِكَ
هُمُ الْخَاسِرُونَ
Kallatheena min qablikum kanooashadda minkum quwwatan waakthara amwalan
waawladanfastamtaAAoo bikhalaqihim fastamtaAAtumbikhalaqikum kama istamtaAAa
allatheena minqablikum bikhalaqihim wakhudtum kallatheekhadoo ola-ika habitat
aAAmaluhumfee addunya wal-akhirati waola-ikahumu alkhasiroon
Hausa
Kamar waɗanda suke a gabãninku, sun kasance mafi tsananin ƙarfi daga gare ku,
kuma mafi yawan dũkiyõyi da ɗiya. Sai suka ji daɗi da rabonsu, sai kuka ji daɗi
da rabonku kamar yadda waɗanda suke a gabãninku suka ji dãɗi, da rabonsu, kuma
kuka kũtsa kamar kũtsãwarsu. Waɗancan ayyukansu sun ɓãci a dũniya da Lãhira,
kuma waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
|
Ayah 9:70 الأية
أَلَمْ يَأْتِهِمْ نَبَأُ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ قَوْمِ نُوحٍ وَعَادٍ وَثَمُودَ
وَقَوْمِ إِبْرَاهِيمَ وَأَصْحَابِ مَدْيَنَ وَالْمُؤْتَفِكَاتِ ۚ أَتَتْهُمْ
رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ ۖ فَمَا كَانَ اللهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَٰكِن كَانُوا
أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Alam ya/tihim nabao allatheena minqablihim qawmi noohin waAAadin wathamooda
waqawmiibraheema waas-habi madyana walmu/tafikatiatat-hum rusuluhum bilbayyinati
fama kanaAllahu liyathlimahum walakin kanooanfusahum yathlimoon
Hausa
Shin lãbarin waɗanda suke a gabãninsu bai je musu ba, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da
Samũdãwa da mutãnen Ibrãhĩm da Ma'abũta Madyana da waɗanda aka birkice?
Manzanninsu sun jẽ musu da ãyõyayi bayanannu. To, Allah bai kasance Yanã
zãluntar su ba, amma sun kasance rãyukansu suke zãlunta.
|
Ayah 9:71 الأية
وَالْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۚ يَأْمُرُونَ
بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنكَرِ وَيُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَيُؤْتُونَ
الزَّكَاةَ وَيُطِيعُونَ اللهَ وَرَسُولَهُ ۚ أُولَٰئِكَ سَيَرْحَمُهُمُ اللهُ
ۗ إِنَّ اللهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Walmu/minoona walmu/minatubaAAduhum awliyao baAAdin ya/muroona
bilmaAAroofiwayanhawna AAani almunkari wayuqeemoona assalatawayu/toona azzakata
wayuteeAAoona Allahawarasoolahu ola-ika sayarhamuhumu Allahuinna Allaha
AAazeezun hakeem
Hausa
Kuma mummunai maza da mummunai mãtã sãshensu majiɓincin sãshe ne, sunã umurni da
alhẽri kuma sunã hani daga abin da bã a so, kuma sunã tsayar da salla, kuma sunã
bãyar da zakka, kuma sunãɗã'a ga Allah da ManzonSa. Waɗannan Allah zai yi musu
rahama. Lalle Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
|
Ayah 9:72 الأية
وَعَدَ اللهُ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا
الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا وَمَسَاكِنَ طَيِّبَةً فِي جَنَّاتِ عَدْنٍ ۚ
وَرِضْوَانٌ مِّنَ اللهِ أَكْبَرُ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
WaAAada Allahu almu/mineena walmu/minatijannatin tajree min tahtiha
al-anharukhalideena feeha wamasakina tayyibatanfee jannati AAadnin waridwanun
mina Allahiakbaru thalika huwa alfawzu alAAatheem
Hausa
Kuma Allah Yã yi wa'adi ga mummunai maza da mummunai mãtã da gidãjen Aljanna
ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu, da wurãren zama
mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar. Kuma yarda daga Allah ce mafi girma. Wancan
shi ne babban rabo, mai girma.
|
Ayah 9:73 الأية
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ جَاهِدِ الْكُفَّارَ وَالْمُنَافِقِينَ وَاغْلُظْ
عَلَيْهِمْ ۚ وَمَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ
Ya ayyuha annabiyyu jahidialkuffara walmunafiqeena waghluthAAalayhim wama/wahum
jahannamu wabi/sa almaseer
Hausa
Ya kai Annabi! Ka yãƙi kãfirai da munãfukai kuma ka tsaurara a kansu. Kuma
matattararsu Jahannama ce. Tir da ta zama makõmar!
|
Ayah 9:74 الأية
يَحْلِفُونَ بِاللهِ مَا قَالُوا وَلَقَدْ قَالُوا كَلِمَةَ الْكُفْرِ وَكَفَرُوا
بَعْدَ إِسْلَامِهِمْ وَهَمُّوا بِمَا لَمْ يَنَالُوا ۚ وَمَا نَقَمُوا إِلَّا أَنْ
أَغْنَاهُمُ اللهُ وَرَسُولُهُ مِن فَضْلِهِ ۚ فَإِن يَتُوبُوا يَكُ خَيْرًا
لَّهُمْ ۖ وَإِن يَتَوَلَّوْا يُعَذِّبْهُمُ اللهُ عَذَابًا أَلِيمًا فِي
الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ ۚ وَمَا لَهُمْ فِي الْأَرْضِ مِن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ
Yahlifoona billahi maqaloo walaqad qaloo kalimata alkufri wakafaroobaAAda
islamihim wahammoo bima lam yanaloowama naqamoo illa an aghnahumu
Allahuwarasooluhu min fadlihi fa-in yatooboo yaku khayran lahumwa-in yatawallaw
yuAAaththibhumu Allahu AAathabanaleeman fee addunya wal-akhiratiwama lahum fee
al-ardi min waliyyin wala naseer
Hausa
Sunã rantsuwa da Allah, ba su faɗa ba, alhãli kuwa lalle ne, haƙĩƙa, sun faɗi
kalmar kãfirci, kuma; sun kãfirta a bãyan musuluntarsu, kuma sun yi himma ga
abin da ba su sãmu ba. Kuma ba su zargi kõme ba fãce dõmin Allah da ManzonSa Ya
wadãtar da su daga falalarSa. To, idan sun tũba zai kasance mafi alhẽri gare
su,kuma idan sun jũya bãya, Allah zaiazabtã su da azãba mai raɗaɗi a cikin
dũniya da Lãhira, kuma bã su da wani masõyi kõ wani mataimaki a cikin kasa.
|
Ayah 9:75 الأية
وَمِنْهُم مَّنْ عَاهَدَ اللهَ لَئِنْ آتَانَا مِن فَضْلِهِ لَنَصَّدَّقَنَّ
وَلَنَكُونَنَّ مِنَ الصَّالِحِينَ
Waminhum man AAahada Allahala-in atana min fadlihi lanassaddaqannawalanakoonanna
mina assaliheen
Hausa
Kuma daga cikinsu akwai wadɗanda suka yi wa Allah alkawari, "Lalle ne idan ya
kãwo mana daga falalarSa, haƙĩƙa, munãbãyar da sadaka, kuma lalle ne munã
kasancẽwa, daga sãlihai."
|
Ayah 9:76 الأية
فَلَمَّا آتَاهُم مِّن فَضْلِهِ بَخِلُوا بِهِ وَتَوَلَّوا وَّهُم مُّعْرِضُونَ
Falamma atahum min fadlihibakhiloo bihi watawallaw wahum muAAridoon
Hausa
To, a lõkacin da Ya bã su daga falalarSa, sai suka yi rõwa da shi, kuma suka
jũya bãya sunã mãsu bijirẽwa,
|
Ayah 9:77 الأية
فَأَعْقَبَهُمْ نِفَاقًا فِي قُلُوبِهِمْ إِلَىٰ يَوْمِ يَلْقَوْنَهُ بِمَا
أَخْلَفُوا اللهَ مَا وَعَدُوهُ وَبِمَا كَانُوا يَكْذِبُونَ
FaaAAqabahum nifaqan fee quloobihimila yawmi yalqawnahu bima akhlafoo Allaha
mawaAAadoohu wabima kanoo yakthiboon
Hausa
Sai Ya biyar musu da munãfunci a cikin zukatansu har zuwa ga Rãnar da suke
haɗuwa da Shi sabõda sãɓã wa Allah a abin da suka yi Masa alkawari, kuma sabõda
abin da suka kasance sunã yi na ƙarya.
|
Ayah 9:78 الأية
أَلَمْ يَعْلَمُوا أَنَّ اللهَ يَعْلَمُ سِرَّهُمْ وَنَجْوَاهُمْ وَأَنَّ اللهَ
عَلَّامُ الْغُيُوبِ
Alam yaAAlamoo anna Allaha yaAAlamusirrahum wanajwahum waanna Allaha
AAallamualghuyoob
Hausa
Shin, ba su sani ba cẽwa lalle ne Allah Yanã sanin asĩrinsuda gãnawarsu, kuma
lalle Allah ne Masanin abũbuwan fake?
|
Ayah 9:79 الأية
الَّذِينَ يَلْمِزُونَ الْمُطَّوِّعِينَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ فِي الصَّدَقَاتِ
وَالَّذِينَ لَا يَجِدُونَ إِلَّا جُهْدَهُمْ فَيَسْخَرُونَ مِنْهُمْ ۙ سَخِرَ
اللهُ مِنْهُمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Allatheena yalmizoona almuttawwiAAeenamina almu/mineena fee assadaqati
wallatheenala yajidoona illa juhdahum fayaskharoona minhumsakhira Allahu minhum
walahum AAathabun aleem
Hausa
Waɗanda suke aibanta mãsu yin alhẽri daga mummunaia cikin dũkiyõyin sadaka, da
waɗanda ba su sãmu fãce iyãkar ƙõƙarinsu, sai sanã yi musu izgili. Allah Yanã
yin izgili gare su. Kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.
|
Ayah 9:80 الأية
اسْتَغْفِرْ لَهُمْ أَوْ لَا تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ إِن تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ
سَبْعِينَ مَرَّةً فَلَن يَغْفِرَ اللهُ لَهُمْ ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَفَرُوا
بِاللهِ وَرَسُولِهِ ۗ وَاللهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ
Istaghfir lahum aw la tastaghfirlahum in tastaghfir lahum sabAAeena marratan
falan yaghfira Allahulahum thalika bi-annahum kafaroo billahiwarasoolihi wallahu
la yahdee alqawma alfasiqeen
Hausa
Kõ kã nẽma musu gãfara ko ba ka nẽma musu ba, idan ka nẽma musu gãfara sau
saba'in, to, Allah bã zai gãfarta musu ba. Sabõda sũ, sun kãfirta da Allah da
ManzonSa. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne fãsiƙai.
|
Ayah 9:81 الأية
فَرِحَ الْمُخَلَّفُونَ بِمَقْعَدِهِمْ خِلَافَ رَسُولِ اللهِ وَكَرِهُوا أَن
يُجَاهِدُوا بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ فِي سَبِيلِ اللهِ وَقَالُوا لَا
تَنفِرُوا فِي الْحَرِّ ۗ قُلْ نَارُ جَهَنَّمَ أَشَدُّ حَرًّا ۚ لَّوْ كَانُوا
يَفْقَهُونَ
Fariha almukhallafoona bimaqAAadihimkhilafa rasooli Allahi wakarihoo an
yujahidoobi-amwalihim waanfusihim fee sabeeli Allahi waqaloola tanfiroo fee
alharri qul naru jahannamaashaddu harran law kanoo yafqahoon
Hausa
Waɗanda aka bari sun yi farin ciki da zamansu a bãyan Manzon Allah, kuma suka ƙi
su yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu a cikin hanyar Allah, kuma suka ce:
"Kada ku fita zuwa yãƙi a cikin zãfi."Ka ce: "Wutar Jahannama ce mafi tsanlnin
zãfi." Dã sun kasance sunã fahimta!
|
Ayah 9:82 الأية
فَلْيَضْحَكُوا قَلِيلًا وَلْيَبْكُوا كَثِيرًا جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Falyadhakoo qaleelan walyabkookatheeran jazaan bima kanoo yaksiboon
Hausa
Sabõda haka su yi dãriya kaɗan, kuma su yi kũkada yawa a kan sãkamako ga abin da
suka kasance sunã tsirfatãwa.
|
Ayah 9:83 الأية
فَإِن رَّجَعَكَ اللهُ إِلَىٰ طَائِفَةٍ مِّنْهُمْ فَاسْتَأْذَنُوكَ لِلْخُرُوجِ
فَقُل لَّن تَخْرُجُوا مَعِيَ أَبَدًا وَلَن تُقَاتِلُوا مَعِيَ عَدُوًّا ۖ
إِنَّكُمْ رَضِيتُم بِالْقُعُودِ أَوَّلَ مَرَّةٍ فَاقْعُدُوا مَعَ الْخَالِفِينَ
Fa-in rajaAAaka Allahu ila ta-ifatinminhum fasta/thanooka lilkhurooji faqul
lantakhrujoo maAAiya abadan walan tuqatiloo maAAiya AAaduwwaninnakum radeetum
bilquAAoodi awwala marratin faqAAudoomaAAa alkhalifeen
Hausa
To, idan Allah Ya mayar da kai zuwa ga wata ƙungiyã daga gare su sa'an nan suka
nẽme ka izni dõmin su fita, to, ka ce: "Bã zã ku fita tãre da nĩ ba har
abada,kuma bã zã ku yi yãƙi tãre da nĩ ba a kan wani maƙiyi. Lalle ne kũ, kun
yarda da zama a farkon lõkaci, sai ku zauna tãre da mãtã mãsu zaman gida."
|
Ayah 9:84 الأية
وَلَا تُصَلِّ عَلَىٰ أَحَدٍ مِّنْهُم مَّاتَ أَبَدًا وَلَا تَقُمْ عَلَىٰ قَبْرِهِ
ۖ إِنَّهُمْ كَفَرُوا بِاللهِ وَرَسُولِهِ وَمَاتُوا وَهُمْ فَاسِقُونَ
Wala tusalli AAala ahadinminhum mata abadan wala taqum AAala qabrihiinnahum
kafaroo billahi warasoolihi wamatoowahum fasiqoon
Hausa
Kuma kada ka yi salla a kan kõwa daga cikinsu wanda ya mutu, har abada, kuma
kada ka tsaya a kan kabarinsa. Lalle ne sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa,
kuma sun mutu alhãli kuwa sunã fãsiƙai.
|
Ayah 9:85 الأية
وَلَا تُعْجِبْكَ أَمْوَالُهُمْ وَأَوْلَادُهُمْ ۚ إِنَّمَا يُرِيدُ اللهُ أَن
يُعَذِّبَهُم بِهَا فِي الدُّنْيَا وَتَزْهَقَ أَنفُسُهُمْ وَهُمْ كَافِرُونَ
Wala tuAAjibka amwaluhum waawladuhuminnama yureedu Allahu an yuAAaththibahum
bihafee addunya watazhaqa anfusuhum wahum kafiroon
Hausa
Kuma kada dũkiyõyinsu da ɗiyansu su bã ka sha'awa. Abin sani kawai, Allah Yanã
nufin Ya yi musu azãba da su a cikin dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa
sunã kãfirai.
|
Ayah 9:86 الأية
وَإِذَا أُنزِلَتْ سُورَةٌ أَنْ آمِنُوا بِاللهِ وَجَاهِدُوا مَعَ رَسُولِهِ
اسْتَأْذَنَكَ أُولُو الطَّوْلِ مِنْهُمْ وَقَالُوا ذَرْنَا نَكُن مَّعَ
الْقَاعِدِينَ
Wa-itha onzilat sooratun an aminoobillahi wajahidoo maAAa rasoolihi
ista/thanakaoloo attawli minhum waqaloo tharnanakun maAAa alqaAAideen
Hausa
Kuma idan aka saukar da wata sũra cẽwa; Ku yi ĩmãni da Allah kuma ku yi jihãdi
tãre da ManzionSa. Sai mawadãta daga gare su su nẽmi izninka, kuma su ce: Ka bar
mu mu kasance tãre da mazauna.
|
Ayah 9:87 الأية
رَضُوا بِأَن يَكُونُوا مَعَ الْخَوَالِفِ وَطُبِعَ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا
يَفْقَهُونَ
Radoo bi-an yakoonoo maAAa alkhawalifiwatubiAAa AAala quloobihim fahum
layafqahoon
Hausa
Sun yarda da su kasance tãre da mãtã mãsu zama (a cikin gidãje). Kuma aka rufe a
kan zukãtansu, sabõda haka, sũ, bã su fahimta.
|
Ayah 9:88 الأية
لَٰكِنِ الرَّسُولُ وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ جَاهَدُوا بِأَمْوَالِهِمْ
وَأَنفُسِهِمْ ۚ وَأُولَٰئِكَ لَهُمُ الْخَيْرَاتُ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمُ
الْمُفْلِحُونَ
Lakini arrasoolu wallatheenaamanoo maAAahu jahadoo bi-amwalihimwaanfusihim
waola-ika lahumu alkhayratu waola-ikahumu almuflihoon
Hausa
Amma Manzon Allah da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sun yi jihãdi da
dũkiyõyinsu da rãyukansu. Kuma waɗannan sunã da ayyukan alhẽri, kuma waɗannan sũ
ne mãsu cin nasara.
|
Ayah 9:89 الأية
أَعَدَّ اللهُ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ
فِيهَا ۚ ذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
aAAadda Allahu lahum jannatintajree min tahtiha al-anharu khalideenafeeha
thalika alfawzu alAAatheem
Hausa
Allah yã yi musu tattalin gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu,
sunã madawwamã a cikinsu. Wancan ne babban rabo mai girma.
|
Ayah 9:90 الأية
وَجَاءَ الْمُعَذِّرُونَ مِنَ الْأَعْرَابِ لِيُؤْذَنَ لَهُمْ وَقَعَدَ الَّذِينَ
كَذَبُوا اللهَ وَرَسُولَهُ ۚ سَيُصِيبُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْهُمْ عَذَابٌ
أَلِيمٌ
Wajaa almuAAaththiroona minaal-aAArabi liyu/thana lahum waqaAAada
allatheenakathaboo Allaha warasoolahu sayuseebu allatheenakafaroo minhum
AAathabun aleem
Hausa
Kuma mãsu uzuri daga ƙauyãwa zuka zo dõmin a yi musu izini, kuma waɗanda suka yi
wa Allah da ManzonSa ƙarya, suka yi zamansu. wata azãba mai raɗaɗi zã ta sãmi
waɗanda suka kãfirta daga gare su.
|
Ayah 9:91 الأية
لَّيْسَ عَلَى الضُّعَفَاءِ وَلَا عَلَى الْمَرْضَىٰ وَلَا عَلَى الَّذِينَ لَا
يَجِدُونَ مَا يُنفِقُونَ حَرَجٌ إِذَا نَصَحُوا لِلَّهِ وَرَسُولِهِ ۚ مَا عَلَى
الْمُحْسِنِينَ مِن سَبِيلٍ ۚ وَاللهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Laysa AAala adduAAafa-iwala AAala almarda wala AAalaallatheena la yajidoona ma
yunfiqoona harajunitha nasahoo lillahi warasoolihi maAAala almuhsineena min
sabeelin wallahughafoorun raheem
Hausa
Bãbu laifi a kan maraunana kuma haka majinyata, kuma bãbu laifi a kan waɗanda bã
su sãmun abin da suke ciyarwa idan sun yi nasĩha ga Allah da ManzonSa. Kuma bãbu
wani laifi a kan mãsu kyautatãwa. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai tausayi.
|
Ayah 9:92 الأية
وَلَا عَلَى الَّذِينَ إِذَا مَا أَتَوْكَ لِتَحْمِلَهُمْ قُلْتَ لَا أَجِدُ مَا
أَحْمِلُكُمْ عَلَيْهِ تَوَلَّوا وَّأَعْيُنُهُمْ تَفِيضُ مِنَ الدَّمْعِ حَزَنًا
أَلَّا يَجِدُوا مَا يُنفِقُونَ
Wala AAala allatheena ithama atawka litahmilahum qulta la ajidu maahmilukum
AAalayhi tawallaw waaAAyunuhum tafeedumina addamAAi hazanan alla yajidoo
mayunfiqoon
Hausa
Kuma bãbu (laifi) a kan waɗanda idan sun je maka dõmin ka ɗauke su ka ce: "Bã ni
da abin da nake ɗaukar ku a kansa," suka jũya alhãli kuwa idãnunsu sunã zubar da
hawãye dõmin baƙin ciki cẽwa ba su sãmi abin da suke ciyarwa ba.
|
Ayah 9:93 الأية
إِنَّمَا السَّبِيلُ عَلَى الَّذِينَ يَسْتَأْذِنُونَكَ وَهُمْ أَغْنِيَاءُ ۚ
رَضُوا بِأَن يَكُونُوا مَعَ الْخَوَالِفِ وَطَبَعَ اللهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ
فَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Innama assabeelu AAalaallatheena yasta/thinoonaka wahum aghniyaoradoo bi-an
yakoonoo maAAa alkhawalifi watabaAAaAllahu AAala quloobihim fahum la yaAAlamoon
Hausa
Abin sani kawai, laifi Yanã a kan waɗanda suke nẽman izininka alhãli kuwa sũ
mawadãta ne.Sun yarda su kasance tãre da mãtã mamaya (gidãje), kuma Allah Yã
danne a kan zukãtansu, dõmin haka sũ, bã su gãnẽwa.
|
Ayah 9:94 الأية
يَعْتَذِرُونَ إِلَيْكُمْ إِذَا رَجَعْتُمْ إِلَيْهِمْ ۚ قُل لَّا تَعْتَذِرُوا لَن
نُّؤْمِنَ لَكُمْ قَدْ نَبَّأَنَا اللهُ مِنْ أَخْبَارِكُمْ ۚ وَسَيَرَى اللهُ
عَمَلَكُمْ وَرَسُولُهُ ثُمَّ تُرَدُّونَ إِلَىٰ عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ
فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
YaAAtathiroona ilaykum itharajaAAtum ilayhim qul la taAAtathiroo lan
nu/minalakum qad nabbaana Allahu min akhbarikumwasayara Allahu AAamalakum
warasooluhu thummaturaddoona ila AAalimi alghaybi washshahadatifayunabbi-okum
bima kuntum taAAmaloon
Hausa
Sunã kãwo uzurinsu zuwa gare ku idan kun kõma zuwa gare su Ka ce: "Kada ku kãwo
wani uzuri, bã zã mu amince muku ba. Haƙĩƙa, Allah Yã bã mu lãbãri daga
lãbãrunku, Allah zai ga aikinku kuma ManzonSa (zai gani). Sa'an nan kuma a mayar
da ku zuwa ga Masanin gaibi da bayyane, sai Ya bã ku lãbarin abin da kuka
kasance kunã aikatãwa."
|
Ayah 9:95 الأية
سَيَحْلِفُونَ بِاللهِ لَكُمْ إِذَا انقَلَبْتُمْ إِلَيْهِمْ لِتُعْرِضُوا
عَنْهُمْ ۖ فَأَعْرِضُوا عَنْهُمْ ۖ إِنَّهُمْ رِجْسٌ ۖ وَمَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ
جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Sayahlifoona billahilakum itha inqalabtum ilayhim lituAAridoo AAanhumfaaAAridoo
AAanhum innahum rijsun wama/wahumjahannamu jazaan bima kanoo yaksiboon
Hausa
Zã su yi rantsuwa da Allah a gare ku idan kun jũya zuwa gare su, dõmin ku kau da
kai daga gare su. To, ku kau da kai daga gare su don kõ sũ ƙarantã ne, kuma
Jahannama ce matattararsu bisa ga sãkamakon abin da suka kasance sunã
tsirfatãwa.
|
Ayah 9:96 الأية
يَحْلِفُونَ لَكُمْ لِتَرْضَوْا عَنْهُمْ ۖ فَإِن تَرْضَوْا عَنْهُمْ فَإِنَّ
اللهَ لَا يَرْضَىٰ عَنِ الْقَوْمِ الْفَاسِقِينَ
Yahlifoona lakum litardawAAanhum fa-in tardaw AAanhum fa-inna Allaha layarda
AAani alqawmi alfasiqeen
Hausa
Sunã rantsuwã gare ku dõmin ku yarda da su. To, idan kun yarda da su, to, lalle
ne Allah bã shi yarda da mutãne fãsiƙai.
|
Ayah 9:97 الأية
الْأَعْرَابُ أَشَدُّ كُفْرًا وَنِفَاقًا وَأَجْدَرُ أَلَّا يَعْلَمُوا حُدُودَ مَا
أَنزَلَ اللهُ عَلَىٰ رَسُولِهِ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Al-aAArabu ashaddu kufran wanifaqanwaajdaru alla yaAAlamoo hudooda ma
anzalaAllahu AAala rasoolihi wallahuAAaleemun hakeem
Hausa
¡auyãwã ne mafi tsananin kãfirci da munãfinci, kuma sũne mafi kamanta ga, rashin
sanin haddõjin abin da Allah Ya saukar a kan ManzonSa. Kuma Allah ne Masani, Mai
hikima.
|
Ayah 9:98 الأية
وَمِنَ الْأَعْرَابِ مَن يَتَّخِذُ مَا يُنفِقُ مَغْرَمًا وَيَتَرَبَّصُ بِكُمُ
الدَّوَائِرَ ۚ عَلَيْهِمْ دَائِرَةُ السَّوْءِ ۗ وَاللهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Wamina al-aAArabi man yattakhithuma yunfiqu maghraman wayatarabbasu bikumu
addawa-iraAAalayhim da-iratu assaw-i wallahusameeAAun AAaleem
Hausa
Kuma daga ƙauyãwã akwai waɗanda suke riƙon abin da suke ciyarwa a kan tãra ce,
kuma sunã saurãron aukuwar masĩfa a gare ku, aukuwar mummunar masĩfa ta tabbata
a kansu. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.
|
Ayah 9:99 الأية
وَمِنَ الْأَعْرَابِ مَن يُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَيَتَّخِذُ مَا
يُنفِقُ قُرُبَاتٍ عِندَ اللهِ وَصَلَوَاتِ الرَّسُولِ ۚ أَلَا إِنَّهَا قُرْبَةٌ
لَّهُمْ ۚ سَيُدْخِلُهُمُ اللهُ فِي رَحْمَتِهِ ۗ إِنَّ اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Wamina al-aAArabi man yu/minu billahiwalyawmi al-akhiri wayattakhithu mayunfiqu
qurubatin AAinda Allahi wasalawatiarrasooli ala innaha qurbatun
lahumsayudkhiluhumu Allahu fee rahmatihi inna Allahaghafoorun raheem
Hausa
Kuma daga ƙauyãwã akawi waɗanda suke yin ĩmanida Allah da Rãnar Lãhira, kuma
sunã riƙon abin da suke ciyarwa (tamkar) waɗansu ibãdõdin nẽman kusanta ne a
wurin Allah da addu'õ'in ManzonSa. To, lalle ne ita (ciyarwar nan) ibãdar nẽman
kusanta ce a gare su. Allah zai shigar da su a cikin RahamarSa. Lalle Allah ne
Mai gãfara, Mai jin ƙai.
|
Ayah 9:100 الأية
وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنصَارِ وَالَّذِينَ
اتَّبَعُوهُم بِإِحْسَانٍ رَّضِيَ اللهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ وَأَعَدَّ
لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۚ
ذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Wassabiqoona al-awwaloonamina almuhajireena wal-ansari wallatheenaittabaAAoohum
bi-ihsanin radiya AllahuAAanhum waradoo AAanhu waaAAadda lahum jannatintajree
tahtaha al-anharu khalideenafeeha abadan thalika alfawzu alAAatheem
Hausa
Kuma mãsu tsẽrẽwa na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da
kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya
yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; ¡õramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna
madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma.
|
Ayah 9:101 الأية
وَمِمَّنْ حَوْلَكُم مِّنَ الْأَعْرَابِ مُنَافِقُونَ ۖ وَمِنْ أَهْلِ الْمَدِينَةِ
ۖ مَرَدُوا عَلَى النِّفَاقِ لَا تَعْلَمُهُمْ ۖ نَحْنُ نَعْلَمُهُمْ ۚ
سَنُعَذِّبُهُم مَّرَّتَيْنِ ثُمَّ يُرَدُّونَ إِلَىٰ عَذَابٍ عَظِيمٍ
Wamimman hawlakum mina al-aAArabimunafiqoona wamin ahli almadeenati maradoo
AAala annifaqila taAAlamuhum nahnu naAAlamuhum sanuAAaththibuhummarratayni
thumma yuraddoona ila AAathabin AAatheem
Hausa
Kuma daga waɗanda suke a gẽfenku daga ƙauyãwa akwai munãfukai, haka kuma daga
mutãnen Madnĩa. Sun gõge a kan munãfunci, bã ka sanin su, Mũ ne Muke sanin su.
zã Mu yi musu azãba sau biyu, sa'an nan a mayar da su zuwa ga azãba mai girma.
|
Ayah 9:102 الأية
وَآخَرُونَ اعْتَرَفُوا بِذُنُوبِهِمْ خَلَطُوا عَمَلًا صَالِحًا وَآخَرَ سَيِّئًا
عَسَى اللهُ أَن يَتُوبَ عَلَيْهِمْ ۚ إِنَّ اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Waakharoona iAAtarafoo bithunoobihimkhalatoo AAamalan salihan waakharasayyi-an
AAasa Allahu an yatooba AAalayhim inna Allahaghafoorun raheem
Hausa
Kuma da waɗansu, sun yi furuci da laifinsu, sun haɗa aiki na ƙwarai da wani
mummuna. Akwai tsammãnin Allah Ya karɓi tũba a kansu. Lallai Allah ne Mai
gãfara, Mai jin ƙai.
|
Ayah 9:103 الأية
خُذْ مِنْ أَمْوَالِهِمْ صَدَقَةً تُطَهِّرُهُمْ وَتُزَكِّيهِم بِهَا وَصَلِّ
عَلَيْهِمْ ۖ إِنَّ صَلَاتَكَ سَكَنٌ لَّهُمْ ۗ وَاللهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Khuth min amwalihim sadaqatantutahhiruhum watuzakkeehim biha wasalliAAalayhim
inna salataka sakanun lahum wallahusameeAAun AAaleem
Hausa
Ka karɓi sadaka daga dũkiyõyinsu kana tsarkake su, kuma kana tabbatar da
kirkinsu da ita. Kuma ka yi musu addu'a. Lallai addu'õ'inKa natsuwã ne a gare
su. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.
|
Ayah 9:104 الأية
أَلَمْ يَعْلَمُوا أَنَّ اللهَ هُوَ يَقْبَلُ التَّوْبَةَ عَنْ عِبَادِهِ
وَيَأْخُذُ الصَّدَقَاتِ وَأَنَّ اللهَ هُوَ التَّوَّابُ الرَّحِيمُ
Alam yaAAlamoo anna Allaha huwayaqbalu attawbata AAan AAibadihi
waya/khuthuassadaqati waanna Allaha huwa attawwabuarraheem
Hausa
Shin, ba su sani ba cẽwa lallai Allah, ne Yake karɓar tũbã daga bãyinSa, kuma
Yanã karɓar sadakõkinsu, kuma lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai?
|
Ayah 9:105 الأية
وَقُلِ اعْمَلُوا فَسَيَرَى اللهُ عَمَلَكُمْ وَرَسُولُهُ وَالْمُؤْمِنُونَ ۖ
وَسَتُرَدُّونَ إِلَىٰ عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا
كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Waquli iAAmaloo fasayara AllahuAAamalakum warasooluhu walmu/minoona
wasaturaddoona ilaAAalimi alghaybi washshahadatifayunabbi-okum bima kuntum
taAAmaloon
Hausa
Kuma ka ce: "Ku yi aiki, sa'an nan Allah zai ga aikinku, da ManzonSa da Muminai
kuma zã a mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, sa'an nan Ya bã ku lãbãri
ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
|
Ayah 9:106 الأية
وَآخَرُونَ مُرْجَوْنَ لِأَمْرِ اللهِ إِمَّا يُعَذِّبُهُمْ وَإِمَّا يَتُوبُ
عَلَيْهِمْ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Waakharoona murjawna li-amri Allahiimma yuAAaththibuhum wa-imma yatoobuAAalayhim
wallahu AAaleemun hakeem
Hausa
Kuma da waɗansu waɗanda aka jinkirtar ga umurnin Allah, kõ dai Ya yi musu azãba
kõ kuma Ya karɓi tũba a kansu.Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
|
Ayah 9:107 الأية
وَالَّذِينَ اتَّخَذُوا مَسْجِدًا ضِرَارًا وَكُفْرًا وَتَفْرِيقًا بَيْنَ
الْمُؤْمِنِينَ وَإِرْصَادًا لِّمَنْ حَارَبَ اللهَ وَرَسُولَهُ مِن قَبْلُ ۚ
وَلَيَحْلِفُنَّ إِنْ أَرَدْنَا إِلَّا الْحُسْنَىٰ ۖ وَاللهُ يَشْهَدُ إِنَّهُمْ
لَكَاذِبُونَ
Wallatheena ittakhathoomasjidan diraran wakufran watafreeqan baynaalmu/mineena
wa-irsadan liman haraba Allahawarasoolahu min qablu walayahlifunna in aradna
illaalhusna wallahu yashhadu innahum lakathiboon
Hausa
Kuma waɗanda suka riƙi wani masallãci dõmin cũta da kãfirci da nẽman rarrabẽwa a
tsakãnin muminai da fakẽwã ga taimakon wanda ya yãƙi Allah da ManzonSa daga
gabãni, kuma haƙĩƙa sunã yin rantsuwa cẽwa, "Ba mu yi nufin kõmai ba fãce
alhẽri", alhãli kuwa Allah Yanã yin shaida cẽwa,su, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
|
Ayah 9:108 الأية
لَا تَقُمْ فِيهِ أَبَدًا ۚ لَّمَسْجِدٌ أُسِّسَ عَلَى التَّقْوَىٰ مِنْ أَوَّلِ
يَوْمٍ أَحَقُّ أَن تَقُومَ فِيهِ ۚ فِيهِ رِجَالٌ يُحِبُّونَ أَن يَتَطَهَّرُوا ۚ
وَاللهُ يُحِبُّ الْمُطَّهِّرِينَ
La taqum feehi abadan lamasjidunossisa AAala attaqwa min awwali yawmin ahaqquan
taqooma feehi feehi rijalun yuhibboona an yatatahharoowallahu yuhibbu
almuttahhireen
Hausa
Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne, Masallaci wanda aka yi harsãshinsa
a kan taƙawa tun farkon yini, shĩ ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A
cikinsa akwai waɗansu maza sunã son su tsarkaka. Kuma Allah Yanã son mãsu nẽman
tsarkakuwa.
|
Ayah 9:109 الأية
أَفَمَنْ أَسَّسَ بُنْيَانَهُ عَلَىٰ تَقْوَىٰ مِنَ اللهِ وَرِضْوَانٍ خَيْرٌ أَم
مَّنْ أَسَّسَ بُنْيَانَهُ عَلَىٰ شَفَا جُرُفٍ هَارٍ فَانْهَارَ بِهِ فِي نَارِ
جَهَنَّمَ ۗ وَاللهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
Afaman assasa bunyanahu AAalataqwa mina Allahi waridwanin khayrunam man assasa
bunyanahu AAala shafa jurufinharin fanhara bihi fee narijahannama wallahu la
yahdee alqawma aththalimeen
Hausa
Shin, wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan taƙawa daga Allah da yarda, shi ne
mafi alhẽri kõ kuwa wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan gãɓar rãmi mai
tusgãwa? Sai ya rũsa da shi a cikin wutar Jahannama. Kuma Allah bã Ya shiryar da
mutãne azzãlumai.
|
Ayah 9:110 الأية
لَا يَزَالُ بُنْيَانُهُمُ الَّذِي بَنَوْا رِيبَةً فِي قُلُوبِهِمْ إِلَّا أَن
تَقَطَّعَ قُلُوبُهُمْ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
La yazalu bunyanuhumuallathee banaw reebatan fee quloobihim illa an
taqattaAAaquloobuhum wallahu AAaleemun hakeem
Hausa
Gininsu, wanda suka gina, bã zai gushe ba Yanã abin shakka a cikin zukãtansu
fãce idan zukãtansu sun yanyanke. Kuma Allah ne Masani, Mai Hikima.
|
Ayah 9:111 الأية
إِنَّ اللهَ اشْتَرَىٰ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ أَنفُسَهُمْ وَأَمْوَالَهُم بِأَنَّ
لَهُمُ الْجَنَّةَ ۚ يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللهِ فَيَقْتُلُونَ وَيُقْتَلُونَ
ۖ وَعْدًا عَلَيْهِ حَقًّا فِي التَّوْرَاةِ وَالْإِنجِيلِ وَالْقُرْآنِ ۚ وَمَنْ
أَوْفَىٰ بِعَهْدِهِ مِنَ اللهِ ۚ فَاسْتَبْشِرُوا بِبَيْعِكُمُ الَّذِي
بَايَعْتُم بِهِ ۚ وَذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Inna Allaha ishtara minaalmu/mineena anfusahum waamwalahum bi-anna
lahumualjannata yuqatiloona fee sabeeli Allahifayaqtuloona wayuqtaloona waAAdan
AAalayhi haqqan fee attawratiwal-injeeli walqur-ani waman awfabiAAahdihi mina
Allahi fastabshiroo bibayAAikumuallathee bayaAAtum bihi wathalika huwaalfawzu
alAAatheem
Hausa
Lalle ne, Allah Ya saya daga mummunai, rãyukansu da dũkiyõyinsu, da cẽwa sunã da
Aljanna, sunã yin yãƙi a cikin hanyar Allah, sabõda haka sunã kashẽwa anã kashẽ
su. (Allah Yã yi)wa'adi a kanSa, tabbace a cikin Attaura da Linjĩla da
Alƙur'ãni. Kuma wãne ne mafi cikãwa da alkawarinsa daga Allah? Sabõda haka ku yi
bushãra da cinikinku wanda kuka ƙulla da Shi. Kuma wancan shi ne babban rabo,
mai girma.
|
Ayah 9:112 الأية
التَّائِبُونَ الْعَابِدُونَ الْحَامِدُونَ السَّائِحُونَ الرَّاكِعُونَ
السَّاجِدُونَ الْآمِرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَالنَّاهُونَ عَنِ الْمُنكَرِ
وَالْحَافِظُونَ لِحُدُودِ اللهِ ۗ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ
Atta-iboona alAAabidoonaalhamidoona assa-ihoona arrakiAAoonaassajidoona
al-amiroona bilmaAAroofiwannahoona AAani almunkari walhafithoonalihudoodi Allahi
wabashshiri almu/mineen
Hausa
Mãsu tũba, mãsu bautãwa, mãsu gõdẽwa, mãsu tafiya, mãsu ruku'i, mãsu sujada mãsu
umurni da alhẽri da mãsu hani daga abin da aka ƙi da mãsu tsarẽwaã ga iyãkõkin
Allah. Kuma ka bãyar da bushãra ga muminai.
|
Ayah 9:113 الأية
مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَن يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ
وَلَوْ كَانُوا أُولِي قُرْبَىٰ مِن بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ
أَصْحَابُ الْجَحِيمِ
Ma kana linnabiyyi wallatheenaamanoo an yastaghfiroo lilmushrikeena walaw
kanooolee qurba min baAAdi ma tabayyana lahum annahum as-habualjaheem
Hausa
Bã ya kasancẽwa ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga
mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a
gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne.
|
Ayah 9:114 الأية
وَمَا كَانَ اسْتِغْفَارُ إِبْرَاهِيمَ لِأَبِيهِ إِلَّا عَن مَّوْعِدَةٍ وَعَدَهَا
إِيَّاهُ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُ أَنَّهُ عَدُوٌّ لِّلَّهِ تَبَرَّأَ مِنْهُ ۚ
إِنَّ إِبْرَاهِيمَ لَأَوَّاهٌ حَلِيمٌ
Wama kana istighfaruibraheema li-abeehi illa AAan mawAAidatin waAAadahaiyyahu
falamma tabayyana lahu annahu AAaduwwun lillahitabarraa minhu inna ibraheema
laawwahun haleem
Hausa
Kuma istigifãrin Ibrãhĩm ga ubansa bai kasance ba fãce sabõda wani wa'adi ne da
ya ƙulla alƙawarinsa da shi, sa'an nan a lõkacin da ya bayyana a gare shi
(Ibrãhĩm) cẽwa lalle ne shĩ (ubansa) maƙiyi ne ga Allah, sai ya barranta daga
gare shi. Lalle ne Ibrahim, haƙĩƙa, mai yawan addu'a ne, mai haƙuri.
|
Ayah 9:115 الأية
وَمَا كَانَ اللهُ لِيُضِلَّ قَوْمًا بَعْدَ إِذْ هَدَاهُمْ حَتَّىٰ يُبَيِّنَ
لَهُم مَّا يَتَّقُونَ ۚ إِنَّ اللهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
Wama kana Allahu liyudillaqawman baAAda ith hadahum hattayubayyina lahum ma
yattaqoona inna Allaha bikullishay-in AAaleem
Hausa
Kuma Allah bai kasance mai ɓatar da mutãne a bãyan Yã shiryar da su ba, sai Ya
bayyanã musu abin da zã su yi taƙawa da shi. Lalle ne Alllh, ga kõme, Masani ne.
|
Ayah 9:116 الأية
إِنَّ اللهَ لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۚ وَمَا
لَكُم مِّن دُونِ اللهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ
Inna Allaha lahu mulku assamawatiwal-ardi yuhyee wayumeetu wama lakummin dooni
Allahi min waliyyin wala naseer
Hausa
Lalle ne Allah Yanã da mulkin sammai da ƙasa, Yanã rãyarwa kuma Yanã matarwa.
Kuma bã ku da wani masõyi, kuma bã ku da mataimaki, baicin Allah.
|
Ayah 9:117 الأية
لَّقَد تَّابَ اللهُ عَلَى النَّبِيِّ وَالْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنصَارِ الَّذِينَ
اتَّبَعُوهُ فِي سَاعَةِ الْعُسْرَةِ مِن بَعْدِ مَا كَادَ يَزِيغُ قُلُوبُ فَرِيقٍ
مِّنْهُمْ ثُمَّ تَابَ عَلَيْهِمْ ۚ إِنَّهُ بِهِمْ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ
Laqad taba Allahu AAalaannabiyyi walmuhajireena wal-ansariallatheena
ittabaAAoohu fee saAAati alAAusrati minbaAAdi ma kada yazeeghu quloobu fareeqin
minhumthumma taba AAalayhim innahu bihim raoofun raheem
Hausa
Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Ya karɓi tũbar Anbabi da Muhãjirĩna da Ansãr waɗanda
suka bĩ shi, a cikin sã'ar tsanani, daga bãya zukãtan wani ɓangare daga gare su
sun yi kusa su karkata, sa'an nan ( Allah) Ya karɓi tũbarsu. Lalle, Shĩ ne Mai
tausayi, Mai jin ƙai gare su.
|
|