A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa "Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo
muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi,
tsammãninku, ku ji ɗimi."
To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa, "An tsarkake wanda yake
cikin (wurin) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah
Ubangijin halittu."
"Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita
ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba, "Yã
Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuriNa."
"Kuma ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, bãbu wata cũta,
a cikinwasu ãyõyi tara zuwa ga Fir'auna da mutãnensa. Lalle ne sũ, sun kasance
mutãne ne fãsiƙai."
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce: "Gõdiya
ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyinSa mũminai."
Kuma sulaimãn ya gãji Dãwũda ya ce: "Yã ku mutãne! An sanar da mu maganar
tsuntsãye, kuma an bã mu daga kõwane abu. Lalle ne wannan haƙĩƙa shi ne falalar
(Allah) bayyananna."
Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, "Yã kũ
jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya
ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba."
Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, "Yã Ubangijĩna!
Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga
mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka
shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai."
"Na sãme ta ita da mutãnenta, sunã yin sujada ga rãnã, baicin Allah, kuma
Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka ya karkatar da su daga hanya,
sa'an nan sũ, ba su shiryuwa."
Suka ce: "Mũ ma'abũta ƙarfi ne, kuma ma'abbũta yãƙi mai tsanani ne, kuma
al'amari yã kõma zuwa gare ki, sabõda haka ki dũbamẽne ne zã ki yi umurui (da
shi)?"
Ta ce: "Lalle sarakuna idan sun shiga wata alƙarya, sai su ɓãta ta, kuma su
sanya mãsu darajar mutãnenta ƙasƙantattu. Kuma kamar wancan ne suke likatãwa."
To, a lõkacin da ya jẽ wa Sulaiman ya ce: "Shin, za ku ƙãra ni da dũkiya ne? To,
abin daAllah Ya bã ni, shi ne mafi alhẽridaga abin da Ya bã ku. A'a, kũ nekuke
yin farin ciki da kyautarku."
"Ka kõma zuwa gare su. Sa'an nan lalle munã je musu da rundunõni, bãbu wata
tãɓukawa gare su game da su, kuma lalle munã fitar da su daga gare ta, sunã mafi
wulãkantuwa, kuma sunã ƙasƙantattu."
Wani mai ƙarfi daga aljannu ya ce: "Nĩ inã zo maka da shi a gabãnin ka tãshi
daga matsayinka. Kuma llale nĩ a gare shi, haƙĩƙa, mai ƙarfi ne amintacce."
Wanda yake a wurinsa akwai wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni inã zo maka da shi
a gabãnin ƙyaftãwar ganinka ta kõma gare ka." To, a lõkacin da ya gan shi
matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijĩna yake, dõmin Ya
jarraba ni: Shin, zan gõde ne, kõ kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gõde, to, yanã
gõdẽwa ne dõmin kansa, kuma wanda ya kãfirta, to, lalle Ubangijina Wadãtacce ne,
Karĩmi."
To a lõkacin da ta jẽ aka ce "Shin, kamar wannan gadon sarautarki yake?" Ta ce:
"Kamar dai shĩne. Kuma an bã mu ilmi daga gabãninta kuma mun kasance mãsu
sallamãwar (al'amari ga Allah)."
Aka ce mata, "Ki shiga a gidan sarauta." To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi
zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye daga ƙwaurinta. Ya ce: "Lalle ne shi, gidan
sarauta ne mai santsi daga madũbai." Ta ce: "Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai
da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, "Inã
rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba." Lalle nĩ, na
zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin
halittu."
Ya ce: "Yã mutãnẽna! Don me kuke nẽman gaggãwa game da mũnanãwa, a gabãnin
kyautatãwa. Don me bã ku nẽman Allah gãfara, tsammãninku, zã a yi muku rahama?"
Kuma waɗansu jama'a tara sun kasance a cikin birnin, sunã yin ɓarna, kuma bã su
kyautatãwa. Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa, shi da
mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba
kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'."
Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa, shi da mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'.". (49..)
Bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa fãce suka ce "Ku fitar da mutãnen Lũɗu
daga alƙaryarku, lalle sũ, wasu irin mutãne ne mãsu da'awar sunã da tsarki."
Ka ce: "Godiya ta tabbata ga A1lah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyinSa,
waɗanda Ya zãɓa." Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi?
Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa,
Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku
tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne
suna daidaitãwa (Allah da wani).
Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta
kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a
tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi
yawansu ba su sanĩ ba.
Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku,kuma wãne ne Yake aikõwar
iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamarSa? Ashe akwai wani abin bautãwa
tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi.
Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita,kuma Wãne ne Ya
azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce:
"Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya."
Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce
wanda yake yin ĩmãni da ãyõyinMu. To, sũ ne mãsu sallamãwa (al'amari zuwa ga
Allah).
Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba daga ƙasa, tanã
yi musu magana, cẽwa "Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin
ĩmãnin yaƙĩni."
Shin, ba su gani ba, cẽwa, lalle Mũ, Mun sanya dare dõmin su natsu a cikinsa,
kuma da yini mai sanya gani? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi! Dõmin mutãne
waɗanda suka yi ĩmãni.
Kuma da rãnar da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda
suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa
sunã ƙasƙantattu.
Kuma kanã ganin duwãtsu, kanã zaton su sandararru, alhãli kuwa sũ sunã shũɗẽwa
shũɗewar girgije, bisa sanã'ar Allah wanda Ya kyautata kõwane abu. Lalle Shi,
Mai lãbartãwa ne game da abin da kuke aikatãwa.
(Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari, Wanda Ya mayar da shi
Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu
sallamãwa."
Kuma ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu."
Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba.