1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الْبُرُوجِ
Wassama-i thatialburooj
Hausa
Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.
|
Ayah 85:2 الأية
وَالْيَوْمِ الْمَوْعُودِ
Walyawmi almawAAood
Hausa
Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,
|
Ayah 85:3 الأية
وَشَاهِدٍ وَمَشْهُودٍ
Washahidin wamashhood
Hausa
Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa
|
Ayah 85:4 الأية
قُتِلَ أَصْحَابُ الْأُخْدُودِ
Qutila as-habu alukhdood
Hausa
An la'ani mutãnen rãmi.
|
Ayah 85:5 الأية
النَّارِ ذَاتِ الْوَقُودِ
Annari thati alwaqood
Hausa
Wato wuta wadda aka hura.
|
Ayah 85:6 الأية
إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌ
Ith hum AAalayha quAAood
Hausa
A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.
|
Ayah 85:7 الأية
وَهُمْ عَلَىٰ مَا يَفْعَلُونَ بِالْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌ
Wahum AAala ma yafAAaloona bilmu/mineenashuhood
Hausa
Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.
|
Ayah 85:8 الأية
وَمَا نَقَمُوا مِنْهُمْ إِلَّا أَن يُؤْمِنُوا بِاللهِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ
Wama naqamoo minhum illa anyu/minoo billahi alAAazeezi alhameed
Hausa
Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda
ake gõdewa.
|
Ayah 85:9 الأية
الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَاللهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ
شَهِيدٌ
Allathee lahu mulku assamawatiwal-ardi wallahu AAala kullishay-in shaheed
Hausa
Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.
|
Ayah 85:10 الأية
إِنَّ الَّذِينَ فَتَنُوا الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ لَمْ يَتُوبُوا
فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ عَذَابُ الْحَرِيقِ
Inna allatheena fatanoo almu/mineenawalmu/minati thumma lam yatooboo falahum
AAathabujahannama walahum AAathabu alhareeq
Hausa
Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba
ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.
|
Ayah 85:11 الأية
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن
تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ۚ ذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْكَبِيرُ
Inna allatheena amanoowaAAamiloo assalihati lahum jannatuntajree min tahtiha
al-anharu thalikaalfawzu alkabeer
Hausa
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen
Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo
babba.
|
Ayah 85:12 الأية
إِنَّ بَطْشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ
Inna batsha rabbika lashadeed
Hausa
Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.
|
Ayah 85:13 الأية
إِنَّهُ هُوَ يُبْدِئُ وَيُعِيدُ
Innahu huwa yubdi-o wayuAAeed
Hausa
Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).
|
Ayah 85:14 الأية
وَهُوَ الْغَفُورُ الْوَدُودُ
Wahuwa alghafooru alwadood
Hausa
Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.
|
Ayah 85:15 الأية
ذُو الْعَرْشِ الْمَجِيدُ
Thoo alAAarshi almajeed
Hausa
Mai Al'arshi mai girma
|
Ayah 85:16 الأية
فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ
FaAAAAalun lima yureed
Hausa
Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.
|
Ayah 85:17 الأية
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْجُنُودِ
Hal ataka hadeethu aljunood
Hausa
Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.
|
Ayah 85:18 الأية
فِرْعَوْنَ وَثَمُودَ
FirAAawna wathamood
Hausa
Fir'auna da samũdãwa?
|
Ayah 85:19 الأية
بَلِ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي تَكْذِيبٍ
Bali allatheena kafaroo fee taktheeb
Hausa
Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.
|
Ayah 85:20 الأية
وَاللهُ مِن وَرَائِهِم مُّحِيطٌ
Wallahu min wara-ihimmuheet
Hausa
Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa).
|
Ayah 85:21 الأية
بَلْ هُوَ قُرْآنٌ مَّجِيدٌ
Bal huwa qur-anun majeed
Hausa
Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.
|
Ayah 85:22 الأية
فِي لَوْحٍ مَّحْفُوظٍ
Fee lawhin mahfooth
Hausa
A cikin Allo tsararre.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|