Muhawara Hausa
 



Azumin Ranar Ashura
 
Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai Daga Nibras Muhammad Auwal
Azumin Ranar Ashura

Wannan ranar ita ce ranar goma da watan muharram na ko wace shekara. Watau asalin wannan azumi tun kafin zuwan musulunci ne Kuraishawan Jahiliya su ke yinsa. An ce da shi ne azumin da aka wajabta har sai da aka rubuta wa alumma azumin Ramadan sai shi ya zama na nafila.



Yahudawa sun kasance suna azumin goma da watan tevet watau watan goma na shekaransu domin godiya. Amma an samu sabani tsakaninsu a dalilin da yasa aka wajabtachi akan su. Da musulunci ya zo sai ya bayyana dalilin cewa wannan ranar farin cikice da kuma godiya ga Allah domin ranar da Allah Ya tsirar da Annabi Musa da mutanensa da ga Firauna. Saboda haka manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agareshi- y ace, mu musulmi mun fi chanchanta da Annabi Musa saboda haka yayi umurni da muyi azumin.

To ya yanuwa maza da mata, a lokacin da muke yin wannan azumi wanda ya dace da ranar assabar 24th na wannan wata na nubemba, mu roki Allah Madaukaki da ya kubutar da mu daga wadannan kananan firaunoni wadanda suke watsa barna acikin kasar mu da soran kasacen musulmi. Kuma ya kamata mu yalwata wa iyalenmu da abinci mai yawa da inganci kamar yadda yazu a wanni hadisi ko da yake mai rauni ne. wannan ranar farin ciki ne da kuma ibada da yin dadi. Babu wurin bakin ciki ko bacin rai a wannan ranar. Kuma mu sani fa Allah Mafi karfi yana sane da abunda ashararun mutane da azzalumai suke yi. Yana musu jinkirine domin su kara zurmawa cikin zunubi.

Ana so mutum ya kara da ranar 9 ko kuma 11 ya hada da ta ashura, ko ko kuma ya yi azumin kwana ukun wandan yafi hakanan. Amma ga wanda akwai azumin ramkuwa na Ramadan akansa, Imam Malik yafi rinjayar da gabatar ramuwar akan ashura domin Allah yafi son a cika farilla da yin nafila.

Allah ya shiryar damu gaba daya.

Amin.


 Posted By Aka Sanya A Thursday, December 20 @ 21:09:24 PST Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai



"Azumin Ranar Ashura" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com