Muhawara Hausa
 



Sha'aban Da kintsa Wa Ramadan (4)
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Daga hudubar Yaseen Bi-Asbi'i
Masallaci: Ba a fada ba
Fassara Salihu Makera

Sha'aban Da kintsa Wa Ramadan (4)

Huduba ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah a bisa kyautatawarSa, muna yi maSa shukura a bisa dacewa da ni'imarSa. Na shaida ba wanda za a bauta maSa da gaskiya sai Allah Shi kadai, girmamawa ga sha'aninSa. Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, mai kira zuwa ga yardarSa. Ya Allah Ka kara tsira da aminci a gare shi da alayensa da sahabbansa da 'yan uwansa.

Bayan haka, ku sani-ya bayin Allah! Lallai akwai shiriya da haske a cikin Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa (SAW). bata da rudu suna cikin abin da yake sabaninsu; ''To wanda ya bi shiryarwaTa, to, ba ya bacewa, kuma ba ya wahala. Kuma wanda ya bijire daga ambatoNa (Alkur'ani), to, lallai ne rayuwa mai kunci ta tabbata a gare shi, kuma Muna tayar da shi a Ranar kiyama yana makaho.'' (k: 20: 23-24).

Bayin Allah! Daga cikin manyan abubuwan da mutum zai tarbi Ramadan da su a watan Sha'aban akwai abin da dabarani da Ibnu Hibban suka ruwaito daga Mu'azu bin Jabal (RA) daga Annabi (SAW) inda ya ce: ''Allah Yana duban daukacin bayinSa a daren rabin Sha'aban, sai ya gafarta wa dukkan bayinsa, face mushiriki da muhashin.''

Don haka ku tsare tauhidinku, ya ku bayi Allah! Kada ku yarda babba ko karamar shirka su warware shi. Ku tsarkake kawunanku daga rowa da keta da bakin rai da kuncin zuciya. Domin Allah Madaukaki Yana gafartawa a daren rabin Sha'aban ga dukkan bayinsa face mushiriki da muhashin. Kashedinku da yi wa Allah shirki, mu binciki kawunanmu, domin ta yiwu dayanmu an jarrabe shi da wani abu daga shirka amma bai sani ba. Mushiriki shi ne wanda ya bauta wa wanin Allah da kowane nau'i na ibada. Wanda ya kirayi wanin Allah ko ya yi bakace da shi, ko ya yi yanka dominsa ko makamancin haka na daga ayyukan ibada, hakika ya yi shirka, kuma ya cancanci ukuba, ita ce rashin samun gafara da tabbata a wuta. Allah Ya ce: ''Lallai shi, wanda ya yi wa Allah shirki, hakika Allah Ya haramta masa Aljanna kuma makomarsa wuta ce, kuma azzalumai ba su da wani mataimaki.'' (k5:72). Kuma Allah Ya ce: ''Lallai Allah ba Ya gafartawa a yi shirki da Shi, amma Yana gafarta abin da bai kai haka ba, ga wanda Ya so. Wanda ya yi shirki da Allah, hakika ya bace bacewa mai nisa.'' (k:4:116).

Muhashin shi ne mai gaba ko mai husuma ko mai yanke zumunta ko mai juya baya a fagen jihadi ko mai hassada ko mai kullatar mutane a zucci. Dukkan wadannan siffofi ne na muhashin. Kuma suna jawo rashin samun gafara.

An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda) -marfu'i- cewa: ''Ana bude kofofin Aljanna a ranakun Litinin da Alhamis, sai a gafarta wa kowane bawa da ba ya shirki da Allah, face wanda ya kullaci dan uwansa. Sai Ya ce: ''Ku dubi wadannan biyu har sai sun sulhunta.'' Muslim ya ruwaito. Kuma daga Abu Sa'alabata Al-Khushni daga Annabi (SAW) ya ce: ''Lallai Allah Yakan duba bayinSa a daren rabin Sha'aban, sai Ya gafarta wa muminai, Ya yi wa kafirai talala, sannan Ya kyale masu hassada da kullatar juna da hassadarsu ko kullatarsu, har sai sun bari.'' dabarani ya ruwaito, kuma shi ne Hadisi na 1144 a Silsilatus Ahadisis Sahiha. kullin da ake nufi shi ne yanke zumunta da bata tsakanin mutane.

Kuma Annabi (Sallahu Alaihi Wasallam) ya ce: ''Wata cuta ta al'ummar da ta gabace ku, za ta shigo cikinku wato: Hassada da gaba. Ita mai askewa ce. Ban ce tana aske gashi ba, a'a tana aske addini. Na rantse da wanda raina ke hannunSa, ba za ku shiga Aljanna ba, har sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba, har sai kun so juna. Ko kuna son in nuna muku abin da zai sa ku so juna? Ku yawaita yin sallama a tsakaninku.''

Don haka hada shirka da kullata na nuni da cewa dukkansu suna aske addini su bata shi. Bambanci kawai shi ne shirka na bata addini ba ta barin komai daga gare shi, yayin da gaba da hassada da yanke zumunta da sauransu suke fatattaka shi su bar shi ba ya da ruhi, koda ba su tuttuge shi daga tushe ba. kullatar juna da hassada suna bata addini suna aske shi. Hassada da keta da kullata ba su shiga zukata face sun zama sababi na raunin imani, kuma suna iya raba mutum da imanin baki daya, kamar yadda ya faru da Iblis lokacin da ya yi hassada ya kullaci Annabi Adam (Alaihis Salam). Don haka Allah Ya yi gargadi mai karfi a kansu, Ya ambace su tare da zunubi mafi girma wato shirka. Domin shirka tana bata alakar mutum da Ubangijinsa, yayin da kullata da hassada ke bata alakar mutum da 'yan uwansa muminai. Idan alakar mutum ta baci a tsakaninsa da Ubangijinsa da kuma muminai, shi ke nan babu abin da ya saura a addininsa. Ta yaya Allah zai gafarta masa?! Don haka ne aka haramta masa falalar wancan dare mal albarka.

Ku saurara! Wadansu mutane sukan kebance ranar daren rabin Sha'aban da azumi da tsayuwar dare da wadansu nau'o'in addu'o'i da zikirori da rera wakoki. To dukkan wadannan ba su tabbata ba daga Annabi (SAW). Iyaka an samu hakan ne ko a Hadisi mai rauni ko kirkirarre da aka yi wa Annabi (SAW) karya, kamar yadda Ibnu Rajab da wadansu suka ce. Duk wadannan (hadisai) ba a kafa hujja da su, kuma ba a aiki da su a hukunce-hukunce. Amma duk mutumin da ya saba tsayuwar dare, to, ba zai bar tsayuwar daren a wannan ranar ba. Kuma duk wanda ya saba yin azumin nafila, idan ya dace da daren rabin Sha'aban, sai ya yi azuminsa ba zai bari ba. Haka ma wanda ya saba azumi a Sha'aban ya azumce shi (ranar rabin Sha'aban) yana mai koyi da Annabi (SAW). Kebewa ne a ce sai ranar za a yi ya zama bidi'a abar kyama. Don haka ku tafi a kan shiriyar Annabinku (SAW) wadda take sadarwa zuwa ga Aljanna. Ku kiyayi hanyoyin bata da bidi'a, masu sadarwa zuwa ga gidan hallaka.

Ya ku masu biyayya da zababbu! Ku fuskanci wannan wata da tuba na gaskiya daga shirki da bidi'a, ku fuskance shi da istigfari. Ramadan ya darkako, saura kadan ya kankama, don haka ya kai Musulmi! Me ka tanada ga Ramadan? Da me ka kintsa kanka don zuwansa?

Hakika wadansu mutane da yawa sun mutu. Wadansu mutane sun rabauta, wadansu kuma sun tabe. Wadansu sun shiryu, wadansu sun bace. Don haka ka auna ni'imar Allah a kanka, ka roke Shi Ya kai ka Ramadan, ka kara himma a al'amuranka.

Ya kai mai zunubi! Ka koma ga Ubangijinka! Ya kai mai gujewa da kauracewa da wulakanta iyaye! Ka koma ga kyautata musu! Ya kai mai yanke zumunta da rashin kyautata wa makwabta ka koma ga sadar da zumunta da kyautata wa makwabta!

Sha'aban yana kiranka, yana nemanka, ka zo ka tsarkake kanka, ka sabunta zuciyarka, ka wanke kurar rarrabar kai da bin son zuciya da rike wasi-wasin Shaidan, ka yi kwadayin abin da zai amfane ka, ka yi kusan barin duniya, kuma ka yi kusan isa Lahira!

Lallai Allah Ya yi muku umarni da wani al'amari da Ya fara da kanSa, Ya yabi Mala'iku masu tasbihi game da tsarkake Shi a kansa, Ya fadi magana wadda take mai girma cewa: ''Lallai Allah da Mala'ikunSa suna salati ga Annabi, ya ku wadada suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi taslimi tare da sallamawa.'' (k:33:56)
Don haka ku yi salati da taslimi a bisa mafi tsarkin mutane. Allahumma salli wa sallim ala abdika wa rasulika Muhammad. Wa'ardi Allahumma an khulafa'ihil abrar wa sahabatihil adhar, almuhajirina minhum wal'ansar, wa'anna ma'ahum bi-judika wa-afwika Ya Azizu Ya Gaffar!

Allahumma a'izzal Islama wa Musulimin, wa dammir dugghata wal mu'utadin, wan shiril amni wa istikrari war rakha'i fi jami'i biladil Muslimin Ya Rabbil alamin.

 Posted By Aka Sanya A Sunday, June 12 @ 05:49:19 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc



"Sha'aban Da kintsa Wa Ramadan (4)" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com