Muhawara Hausa
 



ARBA'UNA HAADITH (29) HADISI NA ASHIRIN DA TARA
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji ARBA'UNA HAADITH (29) HADISI NA ASHIRIN DA TARA

An karbo daga Mu'azu dan Jabal R.A yace nace ya Manzon Allah bain labarin wani aiki da zai shigar dani aljanna ya kuma nisantar dani sdaga wuta sai yace hakika kayi tambaya game da abin da yake mai girma si dai abu ne mai sauki ga wanda Allah ya saukake shi a gershi ka bauta wa Allah ba tare da ka hada shi da wani ba, kuma ka tsayar da Sallah, kuma ka bada zakka kuma ka azimci Ramadan sanan ka ziyarci dakin Allah sannan sai Annabi yace shin b azan shiryar da kai kofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne sadaka kuma tana shafe kurakurai kamar yadda ruwa yake kasha wuta haka sallar mutum a cikin yankn dare.

Sannan ya karanta (fadin Allah) gefen jikinsa yana nisantar gurin kwanciyar su har ya kai inda allah yake cewa 'ya 'amaluun (sannan sai Annabi s.a.w yace b azan ba ka labarin kan Al'amarin ba, da ginshikansa da kololuwar samansa ? sai nace eh. Sai yace, kan al'amarin shien musulunci ginshikinsa kuwa sallah kololuwar samansa kuwa jihadi sai Annabi s.a.w yace ba zna baka labairn abin da yake mallakar kusan gaba daya ba sai nace bani labari sai ya akam harshensa yace ka rike wannan sai na ce shin yanzu za akama mud a Maganar da muka yi sai Annabi yace da ma mahaifiyarka ta rasa ka akwai abin da yake jefa mutane a wuta kan fuskokinsu (ko yace) kan hancinsu sai sakamakon abin da harshensu ya fada Tirmizi (# 2616) ya ce hadisi ne mai kyau ingantacce.

SHARHI Wannan hadisi daga Mu'azu dan Jabal RA yace bani labarin wni aiki da zai shigar da ni Aljanna ya kuma nisantar dani daga wua wannan ne ya sa ake cewa fatawar sahabbai ta sha bambam da tamu, saboda su kullum nema suke ina inda za'a shiga aljanna ina inda za' sami tsira da tsari daga wuta. Haka za kaji kullum suna tambaya Annabi s.a.w sai Annabi s.w.a ya zana musu dangogi masu yawa, don idan ka kasa yin wancan kayi wannan . dangane da fadain Annabi s.a.w hakika kayi tambaya game da abinda yake mai girma sia dai abu ne mai sauki ga wanda Allah ya saukake shi a gareshi, wannan shi yasa ake son kullum ka roki Allah tabbatuwar shiriya a akan tafarki madaidaici duk yadda ka kai son gaskiya da begenta in ba Allah ne yayi ma gam da katar ba baz aka dace da itaba.

Fadin Annabi s.a.w cewa Azumi garkuwa ne yana nufin na nafila don Azumin wajibi ya riga ya gabata a can a wani hadisin yace a zum garkuwa ne zai kare mutum daga wuta duba tirmizi 764) saboda haka Annabi ke kwadaitar damu da yawaita azumin nafila bayan mun sauke na farilla azumin nafila kuwa yana da yawa litinin da Alhamis anayi shida a cikin shawwal bayan karamar sallah kenan, wand ayake kankare zunubin shekara dya gaba daya, azumin tasu'a da Ashura tara da kuma goma ga watan muharram shi ne farko azumin da ak wajabta a musulunci, daga baya aka wajabtar da Ramadan shi wancan aka maid a shi ya zama mustahhabi, azumi uku a kowanne wata musamman ma sha uku da sha hudu da sha biyar ga wta. A takaice duk wannan dangogin azumi azumi ne nafila da zai taimaka wa mutum. Azumin nafila idan zaka yi sama da haka ka ga kanada karfin da zaka yi sama da abin da muka ambta to sai kayi azumi yau gobe ka ki jibikayi gata ka huta citta kayi wannan shine siyamu dawud da annabio s.a.ws yace, Azumin da Allah yafiso shine azumin Annabi dawud yayi yau ya huta gobe jibi yayi gata ya huta.

(duba sahhi al'bukhari 1131 da sahih Muslim 1159 saboda haka ba sunna bane ka je ka jeranta azumi kwanaki masu yawa na nafila sai dai kayi yau gobe ka huta jibi kayi gata ka huta haka Annabiya koya wa sahabbai jarumta ba, ne don kayi wta biyu a jeer ko wata uku a jeer ka saba sunnar Annabi s.a.w baka sani ba, shi addini musulunci ba wai jarumta ko gwaninta yake so ba 'a'a abin da ake so akayi asai kayi shike nan Magana ta kare, komai kankantarsa kada ka raina shi sadaka ma ana ana nufin ta nafila domin maganar zakka ta riga ta gabata a baya.

Sallar mutum a cikin wani yanki na dare wato kiyamulllallai kenan zak ayi cikin jam'I zaka yi kai kadai zak yi kai da matarka duk wanda ya sami dama kayi sai dai kiyamul lallaili a cikin jam'I yafi falala sama da kayi kai kadai wannan itace fatawar muka tafi a akaki don akwai hadisi akai inda Annab s.a.w yace, duk wanda yayi sallama sanann kai ma kayi sallama za a'a rubuta maka kamar ka sallaci daren gaba daya (tirmizi d anasa'I 1605 da Ibnu majah 1327 suka rawaito shi ) amma idan kai kadai ne, to sai kayi adadin da ake bukata sannan zaka ace kayi kiyamulllail amma matukar a abayan liman ne ko raka'a hudu ya yi yta tafi gida ko shafa'I da wutiri kadai kuka yi da liman ya tafi gida za'a rubuta maka ka sallaci dare gaba daya kaga ba zaka hada wnda yayi shi kadai ba.

Fadin manzon Allah s.a.w mu'azu cewa sakilatka ummuka jumloli ne dab a a nufin zahiri ma'anarsa larabawasun saba suna amfani sai ya kasance ka fassara su da abin da bai dace ba. Fassara ta kai kai tsaya, sakilatka ummuka yana nufin dama dai mahaifiyarka bat a haife ka ba, kaga ba zai yiwu Annabi s.a.w ya fada masa haka ba !

amma su Larabawa suka fadi haka ga mutumin da bai fahimci wani abin day a kama ya fahimta ba, su ce wane wana irin tunani ne gareka? Ina hankalina ya tafi har ka kasa fahimtar abin da muke nufi ? kamar haka ne Annabi yake nufi.

Fadin Manzon Allah s.a.w cewa shin akwai abin da yake jefa mutane wuta akan fuskokinsu ko yace kan hancinsu face girbe-girben harsunansu ? wannan yana nuna illar munanan maganganun da mutane kamar gori ko kazafi ko fadin abin da bai dace da shari'a ba a wannan galibi shi ke jawo a jefa mutum a wuta, fuska ta fara zuwa ko haram hancinsa ya ara zuwa shi harshe da shi ne wdancan zasu gyaru ta iya yiwuwa kayi sallah wanda ana zaton tana nisantar da mutum daga wuta,ta kai shi aljanna kayi azumi kayi zakka kayi dukkan abinb da ake bukata amma harshenka ba ka kula da yi ba, ka zagi wannan ka cuci wancan kayi da wannan da makamancin wannan sai a tashi ranar kiyama ba ka da komai na ladan wadannan abubuwan duk an dauka an ba wadannan kamar yadda hadisin abu Huraira yake nunawa yace Annabi s.a.w yace kun san waye matalauci ? sai suka ce wanda bashi da kudi bashi da haja sai Annabi s.a.w yace wannan bashi ne matalauci ba ba matalauci a lahira shine wanda zai zo ranar lahira ga sallah, ga azumi ga hajji ga zakka amma ya zagi wancan ya zubar da mutncin wane, ya zubar da jinin wannan sai a dinga daukar ladansa a abda wadannan mutane, har ayyukan alheri na ladansa su kare mutane, basu gama zuwa ba, suna neman bashi a wurinsa sai a debi ayyukansa na zunubi a dora masa, daga karshe sai a kaishi wuta (Duba sahih Muslim [#2581]).

 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 04:45:58 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji



"ARBA'UNA HAADITH (29) HADISI NA ASHIRIN DA TARA" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com