Muhawara Hausa
 



FARKON SHIGA ALJANNAH (SAWW)
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen FARKON SHIGA ALJANNAH (SAWW)

Farkon wanda zai shiga Aljannah aranar Alqiyamah shine Annabinmu Muhammadu (saww)
kamar yadda Imamu Muslim ya ruwaito daga Sayyiduna Anas bn Malik (rta) yace Manzon Allah (saww) yace:

"ZAN ZO KOFAR ALJANNAH ARANAR ALQIYAMAH, SAI IN KWANKWASA, SAI MAI TSARONTA (WATO MALA'IKA RIDHWAN)
YACE : "KAI WANENE?".

ZAN CE MASA "MUHAMMADU NE". SAI YACE : "SABODA KAI AKA UMURCENI KAR IN BUDE MA WANI KAFIN KA".

Acikin wata ruwayar kuma yace: "NINE NAFI DUKKAN ANNABAWA YAWAN MABIYA, KUMA NINE FARKON WANDA ZAI KWANKWASA (KOFAR ALJANNAH)." (Muslim ne ya ruwaitoshi).

Acikin ruwayar Abu Hurairah kuma Annabi (saww) yace: "MUNE NA KARSHE KUMA MUNE NA FARKO ARANAR ALKIYAMAH. KUMA MUNE FARKON WADANDA ZASU SHIGA ALJANNAH".

(Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi).

Akwai kuma hadisan da suka nuna cewar Talakawan wannan al'ummar sai sun riga mawadata (Masu kudi)
shiga Aljannah, kamar yadda Imamu Ahmad da Tirmidhiy suka ruwaito Daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace Manzon Allah (saww)
yace:

"TALAKAWAN MUSULMAI ZASU RIGA SHIGA ALJANNAH KAFIN MAWADATANSU DA TSAWON RABIN WUNI GUDA, WATO SHEKARU DARI BIYAR KENAN (500 years).

Imamu Muslim kuma ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Amru bn Al-Aas (ra) yace Manzon Allah (saww)
yace:

"TALAKAWA DAGA CIKIN SAHABBAN DA SUKAYI HIJIRA, ZASU RIGA MAWADATANSU SHIGA ALJANNAH ARANAR ALKIYAMAH DA TSAWON SHEKARU ARBA'IN".

(Muslim ne ya ruwaitoshi).

Don haka ya kai 'dan uwa, Kada wadata tasa ka rika yin Girman kai ko Alfahari. Domin girman kai babu inda zai kaika sai wuta. Kuma koda ka tsaya ka bi Allah, sai Talakawa sun rigaka shiga Aljannah kamar yadda Sahihan hadisan nan suka tabbatar.

Ba wani abu ne zai kawo maka wannan jinkirin shiga Aljannar ba, illa hisabin dukiyarka da za'ayi ma. Domin ba zaka gushe daga gaban Zatin Allah ba, sai an tambayeka akan kowanne kwabo da Sisi da Naira da dollars : Ta ina ka sameta? Kuma ta ina ka 'batar da ita?.

Acikin bin Allah, ko kuma bin sha'awar son zuciyarka?

Shi kuwa Talaka bashi da komai sai ransa. Don haka babu abin tambaya sosai akansa.

Amma duk da haka ina jan hankalin 'Yan uwana Talakawa cewa mu Zage damtse wajen neman ilimi da bauta ma Allah ta hanyoyin da suka dace domin samun babban rabo awajen Allah. Kar mu sake wasu sun fimu jin dadi aduniya, kuma alahirar ma su sha gabanmu.

Hakika mun gode ma Allah da ya sanyamu acikin wannan al'ummar ta Annabi Muhammad (saww). Allah yasa muna daga cikin sahun farkon wadanda zasu shiga Aljannah aranar Alqiyamah. Acikin Makobtaka da Masoyinmu (saww).

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (15-09-1437)
20-06-2016.

 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 06:04:11 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen



"FARKON SHIGA ALJANNAH (SAWW)" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com