Hakika Allah ya umurci Musulmai da hadin kai wajen tsayar da Addini, Allah ya ce:
13] "Ku tsayar da Addini kada ku rarraba a cikinsa".
Sai Allah ya hanesu ga rarrabuwa. Kuma wannan shi ne abin da ya shar'anta mana, kuma ya yi wasiyyansa ga Shugabannin Manzanni; Muhammad (saw), Ibrahim (saw), Musa (saw), Isa (saw), Nuhu (saw).
– Kuma Allah ya hanesu a kan sabani, inda ya ce:
46] "Kada ku yi jayayya a tsakaninku sai ku karaya, karfinku ya kare".
– Kuma ya umurcesu da taimakekeniya, inda ya ce:
"Ku taimaki juna a kan aiyukan alheri, da jin tsoron Allah".
Wannan ya sa Shari'a ta ba mu labarin cewa; musulmai suna da hakkoki a kan junansu, kuma ta yi kira ga a kula da su, kuma a kiyayesu, don al'ummar musulmi ta zama al'umma mai karfi da hadin kai, mai tausayin juna, wacce tsaro da zaman lafiya zai jagoranceta.
* Daga cikin hakkokin musulmi a kan dan uwansa musulmi akwai:
1. Kada ya ZAGE shi, ko ya TSINE masa, kuma kada ya FASIKANTAR da shi, ko ya KAFIRTA shi.
« ﻻ ﻳﺮﻣﻲ ﺭﺟﻞ ﺭﺟﻼ ﺑﺎﻟﻔﺴﻮﻕ، ﻭﻻ ﻳﺮﻣﻴﻪ ﺑﺎﻟﻜﻔﺮ، ﺇﻻ ﺍﺭﺗﺪﺕ ﻋﻠﻴﻪ، ﺇﻥ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﺻﺎﺣﺒﻪ ﻛﺬﻟﻚ » "Babu mutumin da zai jefi wani mutum da fasikanci, ko ya jefe shi da kafirci face kalmar ta dawo kansa, in wancan mutumin nasa bai kasance hakan ba".
– Kuma du ya ce:
« ﻭﻟﻌﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﻛﻘﺘﻠﻪ، ﻭﻣﻦ ﺭﻣﻰ ﻣﺆﻣﻨﺎ ﺑﻜﻔﺮ ﻓﻬﻮ ﻛﻘﺘﻠﻪ » "Tsine wa mumini kamar kashe shi ne, duk wanda ya jefi mumini da kafirci kamar ya kashe shi ne".
Ma'ana; tsine masa haramun ne kamar yadda kisansa haramun ne, kuma dadai suke a zunubi.
Saboda haka wajibi ne a kan kowane musulmi ya san wannan hakki da yake kansa, kuma ya kiyaye shi a kan dan uwansa musulmi, don a zama al'umma guda daya, kamar yadda Allah yake so, kuma ya yi umurni.
– Aliyu Sani
Posted By
Aka Sanya A Wednesday, October 04 @ 08:18:45 PDT Da MediaHausaTeam
Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama
Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista