Muhawara Hausa
 



MARIGAYI SHAIKH JA'AFAR MAHMOUD ADAM – ALLAH YA YI MA SA RAHAMA JAAFARMAHMU
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc MARIGAYI SHAIKH JA'AFAR MAHMOUD ADAM – ALLAH YA YI MA SA RAHAMA JAAFARMAHMUDADAM.ORG

Marigayi Shaikh Ja'afar Mahmoud Adam – Allah Ya yi ma sa rahama

jaafarmahmudadam.org/

ya na daya ne daga cikin mafiya shahara da kuma fitattun Malaman Musulunci kuma Jagorori a kan shiriya da miliyoyin al'ummar Musulmin Najeriya – Musamman Arewacinta – da kuma yammacin Afirika su ka gani a farkon karni na 15 bayan Hijrar Manzon Allah (sallallahu 'alaihi wa alihi wa sallam) daga Makkah zuwa Madina.

Shehin Malamin ya yi rayuwa cike da kokari da sadaukar da kai domin addininsa wadanda ke bayyana karara daga irin kishinsa na ganin an samara da Al'ummar Musulmi ta gari wadda ke girmama tare da riko da koyarwar addinin Musulunci kamar yanda Annabi Muhammad (sallallahu 'alaihi wa alihi wa sallam) ya koyar kuma bisa fahimtar magabata na kwarai.

Don haka ne ya tafiyar da 'yar takaitacciyar rayuwarsa a yada karantarwar addinin Islama ta hanyar bayar da darussa, laccoci da kuma tarrurrukan karawa juna sani, yin fatawowi da kuma shirye-shirye daban- dabam a kan batutuwa masu yawa, a wurare da dama. Dadin dadawa kuma, ya kasance mai matukar damuwa da kulawa da dalibai ma su karatu a fagagen Addinin Musulunci da fannonin rayuwa.

A zahiri, kyakkyyawar niyyarsa da kuma ayyukansa na kwarai, sune su ka sa Allah Madaukaki Ya sanya ya riski mafi girman manufofinsa a rayuwa wadanda kuma ya ke ta fadi-tashi domin su, wato tabbatar da cewa Sunnar Manzon Allah (sallallahu alaihi wa alihi wa sallam) a dukkanin harkokin rayuwa, ta daina zama bakon abu a kowanne lungu da sako a cikin Al'ummar Musulmin Najeriya da kewaye.

Ranar Juma'a 25 ga watan Rabi'ul Awwal, 1428 A.H.

(13 April 2007, C.E.), wasu 'yan ta'adda da kuma bindiga dadin da har yanzu ba a san ko su waye ba, sun yiwa Malam Ja'afar Kisan gilla lokacin da ya ke jagorantar jama'a a sallar Asuba a masallacin Juma'arsa da ke unguwar dorayi a birnin Kano, Najeriya.

Hakikanin gaskiya, Malam Ja'afar zai dade a zukatan dukkanin Musulmi a matsayin wata alama ta masu riko da madarar karantarwar addinin Musulunci bisa madaidaicin ra'ayi adalci da kuma basira.

Don haka, bukatar samar da website da sunansa ba za ta misaltu ba. Wannan website zai tattara tare da yada gagaruman ayyukan Shaikh Ja'afar ta dukkanin hanyoyi, abun da mutane da yawa a ko'ina cikin kasa ke yunwar samu, musamman saboda Shehin malamin wata alama ce ta malaman da su ke kira zuwa ga akidar Ahlus Sunnah wal Jama'ah.

Wannan website zai taimaka wajen yada ayyukan Shaikh Ja'afar na alkhairi da taimakon al'umma tare da bayar da hadin kai don yada kyawawan ayyuka da ciyar da su gaba ta hanyar tallafawa ilimi da harkokin zamantakewa.

Wannan shi ne ya sa wasu daga cikin dalibai da masoyan Malam Ja'afar su ka bude wannan website.

jaafarmahmudadam.org/

Da fatan Allah Ya bamu dacewa. Mu na rokon Allah Ta'ala Ya lullube shi da rahama, kuma ya saka ma sa da Aljannar Firdausi.

 Posted By Aka Sanya A Wednesday, October 04 @ 08:49:12 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 5
Kurioi: 1


Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc



"MARIGAYI SHAIKH JA'AFAR MAHMOUD ADAM – ALLAH YA YI MA SA RAHAMA JAAFARMAHMU" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com