Yana daga abunda yazama ruwan dare gama-duniya har yazama an maidashi kamar ba laifi ba; shine sanya tufafin da yawuce idon sawu('kafa) ga maza.
A inda zakaga babba da yaro, mahaifa da 'ya'ya, malamai da dalibai, masu kudi da talakawa, suna sanya tufafi(riga ko wando ko malum-malum) 'kasa da idon sawu.
Bayan kuma yin hakan haramunne qa'd'an, kamar yadda hakan ya tabbata daga fiyayyen halitta (s.a.w) kuma hadisan sun bayyana narkon azaba mai ra'da'di da 'kuna ga duk mai aikata hakan.
Ma'ana: Tufafin musulmi zuwa rabin 'kwaurine, amma babu laifi ga abunda ke tsakanin rabin 'kwauri da idon 'kafa, kuma duk wanda yasanya yawuce idon 'kafa to 'dan wutane.
Wadannan hadisan da makamantansu suna nuna mana sanya tufafi daidai rabin kwauri shi akafiso, amma babu laifi idan yazama tsakanin kwauri da idon 'kafa. Sannan kuma sun bayyana mana haramcin sanya tufafi kasa da idon sawu, kuma duk mai wannan dabi'ar Allaah yayi mishi tanadin azaba mai ra'da'di.
Amma a wadannan zamunnan sai shai'dan yayi galaba akan jama'a; a inda zakaga mata na 'dage tufafinsu sukuma maza suna takewa, Allaah yakaremu daga fito na fito da shari'arsa.
Sannan zakaga wasu suna kawo shubuha akan cewa su ba da girman kai suke sawa ba, wanda wannan yike nuna rashin fahimtarsu ga hadisan, domin hadisan dasukazo da 'kaidin sanya tufafi don girman kai; sun bayyana 'karin laifine da narkon azaba ga mai aikata hakan. Ma'ana bayan sa'bon Allaah dakayi na sanya tufafin da yawuce idon sawu sai kuma kahadashi dawani sa'bon wanda yafishi muni; wato girman kai da fankama da ji-dakai. Domin Tirmizhiy ya ruwiaito hadisi kuma ya ingantantashi daga sahabi Jabir yace: Manzon Allaah yace masa:
Ma'ana: Wadannan hadisan suna nuna mana cewa sanya tufafi 'kasa da idon sawu da girman kai babban kabirah ce, amma sanyawa yawuce idon sawu batare da girman kai ba shi kuma haramunne.
ALLAAH YABAMU IKON GYARAWA.
Dan'uwanku: Abdullahi Almadeeniy kagarko.
Posted By
Aka Sanya A Wednesday, October 04 @ 09:22:46 PDT Da MediaHausaTeam
Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama
Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista