Muhawara Hausa
 

 
Bambanci tsakanin Maniyyi Da maziyyi wa wadiy da hukuncinsu
 
Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin Bambanci tsakanin Maniyyi Da maziyyi wa wadiy da hukuncinsu

Assalamu Alaikum warahmatullah wabarkatuh, yau a fagen Fiqhu zamu dubi abubuwa guda uku wanda suke da alaka da tsarki, abubuwan sune Maniyyi, da maziyyi da wadiy,

1.maniyyi: Shi wannan wani ruwa ne da yake fitowa lokacin Yin jima'i ko mafarki ko makamantansu, yana da kauri in na namiji ne, inkuma ta macece yana nan tsiriri kuma yana fita da karfi, yana bibiyar juna.

Hukuncin maniyyi: Akwai tsabani tsakanin maluma kan kasancewar maniyyi najasa ne ko ba najasa ba, abinda ya dace mutum dai yayi in maniyyi ta shafi tufafinsa ko jikinsa shine in maniyyin bai bushe ba sai ya wanke wurin da ruwa, inkuma ya bushe sai ya kankareshi.

sannan hukuncin wanda maniyyin ta fito daga jikinsa, shine zaiyi wankan janaba, In maniyyin ya fito ta jima'i ne ko mafarki, hakanan mutumin daya farka daga bacci yaga maniyyi ajikinsa Shima zaiyi wanka. amma in mutum yayi mafarki ya tashi baiga wani maniyyi ajikinsa ba toh babu wani wanka akansa. hakanan mutumin da yake farke maniyyi ta fito ba tare da wata sha'awah ba, haka kawai ta fito kodun ciwo ko wahala, shima wannan babu wanka akansa.

2.Maziyyi: Shi Maziyyi wani ruwane da yake fita sakamakon tashiwar sha'awah, Yafi fitsari kauri, Sannan yana fita batare da jin dadi ko sanin mutum ba sai dai mutum inyaji tufafinsa ta dan jike,

Hukuncin maziyyi: Shi maziyyi najasane amma mai Sauki, Zai isar wurin tsarki daga gareshi jike inda ya taba ajikin tufafi da ruwa, sannan hukuncin wanda maziyyi ya fita daga jikinsa shine ya wanke farjinsa Da inda ya taba sannan in yana da alwala sai ya sake wata. shi maziyyi ba'a masa wanka.

3.Wadiy: Shi wadiy wani ruwa ne da yake fita a karshen fitsari ya bambanta da fitsari, Shima najasa ne, kuma in ya taba tufafi sai an wanke inda ya taba kaman fitsari, sannan a wanke farji, da kuma sake alwala. a takaice hukuncinsa hukuncin fitsari ne.

Wassalamu Alaikum.

 Posted By Aka Sanya A Wednesday, October 04 @ 09:32:28 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 5
Kurioi: 1


Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

"Bambanci tsakanin Maniyyi Da maziyyi wa wadiy da hukuncinsu" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com