Muhawara Hausa
 



Hanyar Neman Tsari Daga Sharruka
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen Hanyar Neman Tsari Daga Sharruka

Assalamu Alaikum 'yan'uwa, a takaice zamu dubi wasu hanyoyi na neman tsari daga sharruka ta duniya da lahira, wanda addinin musulunci ya koyar damu. kaman yanda kowa ya sani ne da yawa daga cikin mutane suna cikin tsoro, da rashin kwanciyar hankali, musamman a wannan zamani da fitintinu sukayi yawa, wasu mata zaka samu sukuma suna fama da matsaloli na bugun Aljannu. Duka wannan insha'Allah ana iya yin riga kafinsa Da yardar Allah,

Da farko abinda musulmi ya kamata ya gane shine komai ya sameshi daga Allah ne, babu mai iya cutar dashi ko amfanar dashi sai da yardar Allah, sabida haka in matsala ta sami musulmi abinda zai fara yi shine komawa zuwa ga Allah, kada yaje wurin boka, ko malamin tsubbu koma wace tarkace, domin ba abinda wannan zai iya masa.

Hanyoyin neman tsari:

1.Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace wa sahabinsa uqbah(Radiyallahu anhu) kulhuwallahu, falaq, da nasi, babu wani abinda mutum zai nemi tsari dasu fiye da wannan. Musulmi ya kamata ya lazimci karanta wa'innan surori uku safe da yamma da kuma in zaiyi bacci

2. Lazimtar yin Zikirori dabam dabam wanda annabi ya koyar, zikirin kafin bacci, da na tashiwa daga bacci, shiga bayan gida, fita daga bayan gida, shiga gida da fita dag gida..

Ya kamta mutum in ya fita daga gidansa ya karanta أعوذ بكلمات الله التامات من شر ما خلق، اللهم إني أعوذ بك أن أضل أو أضل،أو أزل أو أزل أو أظلم أو أظلم أو أجهل أو يجهل علي.

Sannan mutum ya karanta Kulhuwallahu da falaq da nasi kafa uku Uku, sannan In ya isa inda zai isa, yace أعوذ بكلمات الله التامات من شر ما خلق.

Ma'ana: ina neman tsarin Allah daga sharrin duk abinda ya halitta.

Manzon Allah(sallallahu alaihi wasalam) yace: ''Duk wanda ya fadi haka babu wani abinda zai cutar dashi har yabar wurin, Sannan Yana daga cikin Hanyan kariya Bin dokokin Allah da kauce wa tsaba masa, Domin duk wanda yaji tsoron Allah yabi dokokinsa Allah zai kareshi kuma zai sashi yayi rayuwa mai kyau da nastuwa, Allah yace :

ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﺻﺎﻟﺤﺎ ﻣﻦ ﺫﻛﺮ ﺃﻭ ﺃﻧﺜﻰ ﻭﻫﻮ ﻣﺆﻣﻦ ﻓﻠﻨﺤﻴﻴﻨﻪ ﺣﻴﺎﺓ ﻃﻴﺒﺔ ﻭﻟﻨﺠﺰﻳﻨﻬﻢ ﺃﺟﺮﻫﻢ ﺑﺄﺣﺴﻦ ﻣﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﻤلون.


Wanda yayi aiki na gari daga cikin maza ko mata yana mumini zamu rayar dashi rayuwa mai kyau kuma muyi masa sakamako da mafi kyawun abinda suke aikatawa.

Ayoyi masu irin wannan ma'ana suna da dimbin yawa a alQur'ani. Ya zama tilas mutum maison sa'ada da tsira ranan tashin Qiyama ya rika kiyaye dokokin Allah ako wani lokaci iyakan iyawansa, Sannan yawan karanta Alqur'ani shima yana bada kariya musamman karanta suratul baqara acikin gida, yana kare Gidan daga sharruka dabam dabam, da shaidanu, kaman yanda Annabi(sallalahu alaihi wasallam) ya bada labari, Sannan mata masu fama da aljanu, Yana da kyau su lazimci karatun AlQur'ani, da zikirin safe da yamma, sannan su guji barin gashin kansu a waje, da shiga marar kyau koda ko acikin gida ne, sannan inhar mace tana fama da aljanu yi mata aure yana taimakawa ta rabu dasu.

Allah yasa mudace, ya rabamu da duk wata musiba, duniya da lahira.......

 Posted By Aka Sanya A Wednesday, October 04 @ 09:37:09 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 5
Kurioi: 1


Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen



"Hanyar Neman Tsari Daga Sharruka" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com