Muhawara Hausa
004 AURE KO MAKARANTA?
Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy* Rubutu na 4004 AURE KO MAKARANTA? Daga: *zauren majlisin sunnah* *MU YI TUNANI* 39. Menene amfanin ƙoƙarin yarinya a irin wannan makarantar? 40. Menene fa'idar kammala karatun yarinya a irin wannan makarantar? 41. Wace irin babbar mutum ce irin wannan makarantar take yayewa? 42. Menene ya fi rayuwa a cikin irin wannan makarantar cutar da ilimi? 43. Menene ya fi rayuwa a cikin irin wannan makarantar cutar da lafiya? 44. Anya yarinyar kirki za ta iya natsuwa a cikin irin wannan makarantar? 45. Saboda irin wannan makarantar ce za a hana yarinya yi aure? 46. Ba sa'o'in masu shekaru sha-uku ne suka cika irin waɗannan makarantun ba? 47. Yanzu rayuwa a cikin irin wannan makarantar ba aure zai fi rayuwa tare da aure? *YA JIRA HAR YAUSHE?* 48. Kuna tsammanin shi ne kaɗai tasirin jiran zai shafa? 49. Wanene tsawon jiran zai fi cutarwa: Ita ce ko shi? 50. Kun tabbatar za ta tabbata a kan halinta na-gari a bayan tsawon jiran? 51. Kun amince za ta zama a cikin kyakkyawar surarta na-asali a bayan jiran? 52. Kun amince ba za ta sauya ra'ayinta game da shi ba, a bayan jiran? 53. Kun amince ba za ta karya alƙawarin da kuka yi masa ba, a bayan jiran? 54. Kun tabbata za ta iya haƙurin kame kanta har zuwa ta kammala karatun? 55. Kun amince wani ba zai riga 'saninta' kafin lokacin auren ba? 56. Kun riga kun ɗauki waɗansu matakai ne domin tabbatar da haka? 57. Kuna jin za ta iya haƙurin bin mijin bayan kammala karatun? 58. Kuna jin shi saurayin zai iya yin haƙuri na tsawon jiran da kuke so? 59. Kun amince sai in ya jira ta ne, ya nuna yana sonta da gaske? 60. Kuna jin zai riƙe ta da mutunci a bayan tsawon jiran da kuka sa ya yi? 61. Kuna jin zai ga girmanku da mutuncinku bayan tsawon jiran? Dan uwanku: *Muneer Yusuf Assalafy* Ku kasance da majlisin sunnahWhatsApp 08164363661 Facebook Www.facebook.com/majlisinsunnah Ko zauren admin muneer a Facebook www.facebook.com/Muneer-Yusuf-Assalafy-502666713417261/?re
Posted By
Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 01:29:16 PDT Da MediaHausaTeam
Comments 💬 التعليقات
<
Matsalar Magana
Matsakaicin Maki: 0 Kurioi: 0
Ya Danganta Kanun Labarai
"004 AURE KO MAKARANTA?" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata
Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama
Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com