Muhawara Hausa
 

 
005 AURE KO MAKARANTA?
 
Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Rubutu na 5

005 AURE KO MAKARANTA?

Daga: *zauren majlisin sunnah*

*GYARA TUNANI*

62. Ko kuna tsammanin muna ƙyamar ilimin bokon mace ne?

63. Ba ku san mun san cewa: Mata su ne kashin bayan rayuwa ba?

64. Ba ku san mun san cewa: Mata da 'ya'ya su ne mafiya soyuwan mutane a wurin Annabin Rahama (SAAS) ba?

65. Amma kuma ba ku san duk da haka, ya nuna cewa: Mata sun fi yawa a cikin Wutar Lahira ba?

66. Ba ku san mun fi kowa son ganin gyaruwa da daidaituwar al'amuran mata ba?

67. Ba ku san cewa mu ma mun yi karatun bokon, kuma mun san irin alfanu ko rashin alfanunsa ba?

68. Ba ku san mun san cewa: Ilmantar da mace kamar ilmantar da duniya ce ba?

69. Amma ina amfanin ilimi in babu tarbiyya da kyawawan ɗabi'u da halaye?

70. Ko kuwa ina amfanin ilimin da zai kai mace ga karewa a cikin Wuta a Lahira?

71. Yaushe za a iya samun nagartaccen ilimi ba tare da natsuwar zuciya da kwanciyar hankali ba?

72. Ashe aure ba shi ne cikakkiyar hanyar samun wannan natsuwar da kwanciyar hankalin ga matasa ba?

73. Yanzu daliba ba za ta iya yin karatun boko tare da aurenta ba?

74. Samun juna-biyu a yau a wurin ma'aurata, ba sai da yarda kuma da ganin-damarsu ba?

75. Ko kuwa kun yarda ne da zancen masu cewa: Aure da wuri yana da hatsari?!

76. Kun amince ne da tatsuniyar masu son rage al'ummar musulmi?

77. Kun yi watsi ne da koyarwar addininku da kyawawan al'adunku?

78. Wannan watsin ba shi ne ummul habaa'isin aukuwan wahalhalu da masifu a cikinmu ba?

*MAFITA GUDA*

79. Shin menene amfanin yawan jama'ar musulmi a ƙasar nan?

80. Shin menene amfanin tarin dukiyoyin jama'ar musulmi a ƙasar nan?

81. Shin menene amfanin ƙarfin mulkin jama'ar musulmi a ƙasar nan?

82. Yanzu musulmi ba za ku iya gyara tsarin koyarwa a makarantun bokon maza da mata ba?

83. Yanzu ba za ku iya gyara makarantun bokon su dace da yadda addininku da kyawawan al'adunku su ke ba?

84. Yanzu musulmi ba za ku iya gyara tsarin karatun bokon ya dace da ƙa'idojin addininku da kyawawan al'adunku ba?

85. Yanzu musulmi ba za ku iya samar da makarantun bokon da suka dace da mata ma'aurata ba?

86. In kuwa haka ne, to ina amfanin iliminku, ya ku musulmi!?

87. In kuma haka ne, ina amfanin albarkar yawanku, ya ku musulmi!?

88. Sannan kuma in haka ne, menene amfanin rayuwarku, ya ku jama'ar musulmi!?

89. Menene amfanin rayuwa a cikin wulaƙanci da ƙaskanci da rashin 'yancin yin addini?

Dan uwanku: *Muneer Yusuf Assalafy*

Ku kasance da majlisin sunnah a
www.facebook.com/­majlisinsunnah


08164363661

Ko zauren admin muneer dake fb a

www.facebook.com/­Muneer-Yusuf-Assalafy­-502666713417261/?re

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 01:32:18 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

"005 AURE KO MAKARANTA?" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com