Muhawara Hausa
 

 
BIDI'OIN DA AKEYI AWAJAN WANKE MAMACI
 
Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin BIDI'OIN DA AKEYI AWAJAN WANKE MAMACI

1-Ajeye abinci da ruwa awajan da aka wanke mamacin tsawan kwana uku.

2-Sanya fitila awajan Taiwan kwana uku ko bakwai daga faduwar rana zuwa fitowar sa.

3-Yin zikiri da addua idan ana wanke mamaci akowace gaba.

4-Saukar da gashin mamaci akan kirjinsa.

BIDO O IN LIKKAFANI DA FITA DA GAWA

1-Daukar gawa zuwa waje mai nisa dan abunne shi dare da nagartattu kamar ahlul baiti.

2-Ciwar wasu wai mamata suna alfari da likkafanin da aka sa musu saboda kyansa.

3-Rubuta sunan mamaci tare da sunan ahlul baiti da kasar husaini asanyashi acikin likkafani.

4-Rubuta adduo I ajikin likkafani.

5-Yiwa gawa kwalliya.

6-Sanya tutoci agaban gawa.

7-Sanya rawani akan makara.

8-Daukar fulawoyi da hotun mamacin agaban gawa.

9-Yanka raguna lokacin dazaa fita da gawa da daukar abincin da zaa ci bayan an gama bunne gawa.

10-Cewa wai idan gawa ta garice bata nauyi.

11-Lazimtar cewa saida dama zaa fara daukar gawa.

12-Yin sadaqa da tafiya a hankali da kin kusan tar gawa.

13-Daga sauti da zikiri da rashin yin magana da karanta Quran da dalalilu dss.

14-Yin zikiri da fadin lailaha illallahu idan an takko gawa.

15-Bin gawa da turaren wuta da zagayawa da ita.

16-Lazimtar taukar gawa a mota.

Allah yasa mu daci.

Dan uwanku Bashir Hassan Bashir kurawa

YIWA IYALAN MAMACI GAISUWA (TA-AZIYYA)

Ya halatta ayiwa iyalan wanda akaiwa rasuwa gaisuwa amma akula da abubuwa kamar haka:-

1-Yin gaisuwa da abinda zai sanyaya musu rai ya rage musu zafin rabuwa ya sanyasu cikin yadda da kaddara da hakuri da duk abinda ya kamata in bai sabawa sharia ba.

2-Yin addua kamar haka:(INNA LILLAHI MA AKHAZA WA LILLAHI MA A ADA WA KULLU SHAI IN INDAHU ILA AJALIN MUSAMMA FALTASBIR ALTAHTASIB).

3-Ta aziyya bata wuce kwan uku duk lokacin da aka hadu sai ayita.

4-Akauracewa abubuwa biyu:
1-Taruwa awaje keban tacce kamar gida ko masallaci ko maqabarta.
2-Yin abici da yan uwan mamacim sukeyi dan walima ga wanda suka zo ta aziyya.

5-Sunnah shine yan uwa da makota su hadawa iyalan mamacin abinci.

6-Mustahabbine ashafi kan maraya da girmamashi.

ABINDA ZAI ANFANAR DA MAMACI.

1-Adduar musulmi na gari.

2-Ramuwar azumin bakance da waliyin mamaci zaiyi masa.

3-Biya masa bashi daga dan uwansa ko wani daban.

4-Duk abinda ya bari na alkhairi ko sadaqa jariya.

Allah yasa mubar abinda zai amfa nemu kafin mu mutu.

Dan uwanku Bashir Hassan Bashir kurawa

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 01:40:43 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

"BIDI'OIN DA AKEYI AWAJAN WANKE MAMACI" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com