Muhawara Hausa
 

 
YIWA MAMACI SALLAH (SALLAR GAWA)
 
Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin YIWA MAMACI SALLAH (SALLAR GAWA)

Bayan an gama yiwa gawa likkafani sai kuma ayi mata sallah.Yin sallah gawa wajine akan duk alummah amma idan wasu suka yi ya saraya akan sauran.

MUTUM BIYU BA AYI MUSU SALLAH

1-Karamin yaran da bai balaga ba.
2-Wanda yayi shahada.

YA HALATTA AYIWA WADANNAN MUTANAN SALLAH

1-Yaro karami ko wanda akai farinsa.
2-shahidi.
3-Wanda aka kashe ta hanyar yanke mai haddi.
4-Fasiqi mai sabo kamar mai barin sallah ko zakkah.
5-Wanda ake bi bashi bai biya ba harya mutu kuma bai bar kudunda zaa biya masa ba.
6-Wanda akai masa sallah sai wani yazo zai iya yi masa amqabar.
7-Wanda ya mutu agarinda babu wanda zai masa sallah.

★Haramune yiwa kafiri ko munafiki sallah ko nema masa gafara.
★Wajibine ayi jam'I a sallar jana'iza.
★Mafi karancin ja'in ya kasance mutum uku amma idan suka wuce yafi falala.
★Mustahabbine mutane suyi sahu uku abayan liman.
★Idan babu kowa sai mutum daya to ya tsaya bayan liman.
★Shugaba shi yafi dacewa da yin sallah ko mataimakinsa.
★Idan babu shugaba da mataimaki to agabatar sa wanda yafi alqurani.
★Idan gawawwaki sunasa yawa maza da mata ya halatta ayi sallah daya ko kuma kowa ayi masa nasa.
★Ya halatta yin sallar gawa a masallaci amma awaje yafi.
★bai halattaba yin sallar gawa a maqabarta ba.
★liman ya tsaya dai dai kan namiji idan macace ya tsaya adai dai tsakiyarta.
★Ya halatta liman yayi kabbara sau hudu 4 ko biyar 5 ko tara 9 duk ya tabbata daga manzan Allah (saw).
★liman ya daga hannunsa akabbar farko sannan ya daura hannun sa akan kirjin sa.
★Ana karanta fahiha da surah akabbar farki aboye.
★Akabbara ta biyu anayiwa manzan Allah (saw) salati.
★akabbar ta uku data hudu har zuwa tara idan haka zaayi addua akeyiwa mamacin misali.

(ALLAHUMMA IGFIR LAHU WAR HAMHU WA AFIHI WAAFU ANHU WA AKRIM NUZLAHU WA WASIA MUDKALAHU WAGSILHU BIL MA'I WASSALJI WALBARAD WANAKKIHI MINAL KHADAYA KAMA UNAKKI SAUBUL ABYADU MINAL DANAS WAABDILHU DARAN KHAIRA MIN DARIHI WA AHLAN KHAIRA MIN AHLIHI WAZAUJAN KHAIRA MIN ZAIJIHI WA ADKHILHUL JANNATA WAAIZHU MIN AZABIL QABARI WAMIM AZABINNARI).

★Sannan ayi sallama kamar irin ta sallah.

BA AYIN SALLAR GAWA ALOKUTA UKU

1-Fitowar rana.
2-kwallewar rana.
3Faduwar rana.

★★manzan Allah saw yace:duk mamacinda musulmi dari sukai masa sallah suna naima masa gafara face Allah sai ya gafarta masa.
Allah kai mana rahama da gafara.

Dan uwanku Bashir Hassan Bashir kurawa

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 01:50:56 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

"YIWA MAMACI SALLAH (SALLAR GAWA)" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com