1-Ajeye abinci da ruwa awajan da aka wanke mamacin tsawan kwana uku. 2-Sanya fitila awajan Taiwan kwana uku ko bakwai daga faduwar rana zuwa fitowar sa. 3-Yin zikiri da addua idan ana wanke mamaci akowace gaba. 4-Saukar da gashin mamaci akan kirjinsa.
BIDO O IN LIKKAFANI DA FITA DA GAWA
1-Daukar gawa zuwa waje mai nisa dan abunne shi dare da nagartattu kamar ahlul baiti. 2-Ciwar wasu wai mamata suna alfari da likkafanin da aka sa musu saboda kyansa. 3-Rubuta sunan mamaci tare da sunan ahlul baiti da kasar husaini asanyashi acikin likkafani. 4-Rubuta adduo I ajikin likkafani. 5-Yiwa gawa kwalliya. 6-Sanya tutoci agaban gawa. 7-Sanya rawani akan makara. 8-Daukar fulawoyi da hotun mamacin agaban gawa. 9-Yanka raguna lokacin dazaa fita da gawa da daukar abincin da zaa ci bayan an gama bunne gawa. 10-Cewa wai idan gawa ta garice bata nauyi.
11-Lazimtar cewa saida dama zaa fara daukar gawa. 12-Yin sadaqa da tafiya a hankali da kin kusan tar gawa. 13-Daga sauti da zikiri da rashin yin magana da karanta Quran da dalalilu dss. 14-Yin zikiri da fadin lailaha illallahu idan an takko gawa. 15-Bin gawa da turaren wuta da zagayawa da ita. 16-Lazimtar taukar gawa a mota. Allah yasa mu daci.
Dan uwanku Bashir Hassan Bashir kurawa
YADDA AKE DAUKAR RAN KAFIRI KO FASUQI
Manzan Allah (saw )yaci gaba ba fadin cewa:hakika bawa kafiri ko fasiqi idan zai bar duniya malaiku zasu sakko wajansa masu bakin fuska da tsanani tare dasu akwai likkafani na wuta su zagayeshi tsawan ganinsa sannan malaikan mutuwa yazu saiyace yake wanan rai mummuna ki fito zuwaga fushin Allah.saita fito daga jikinsa ana fusgarta ana janta kamar wanda aka sawa sarkoki awuya da hannaye da kafafuwa ana jansa duk jijiyoyinsa su tsinke gabobin su balle. duk malaiku su tsine masa duk saman da akaje saisuce waya wannan ?
Sai ace wanene dan wane.har sai anje sama da bakwai sai Allah yace:asanya littafinsa asijjin inda ake sa littattafan kafirai sai Allah yace:adawo da bawana kasa dayi alkawarin daga cikin ta suka fito kuma daga cikin ta zasu koma. Sai a wurgo ruhinsa tun daga sama duk ya fatattake manzan Allah (saw) yace:idan har kafiri zai shiga aljannah to sai dai idan rakumi zai iya shiga ta kofar tsinin allora.saiamayar masa da ransa acikin qabarinsa alokacin yana jin takun takalman yan uwansa.
Sai malaiku biyu suzo masa masu tsanani da hantara su hantareshi su zaunar dashi suce waye:ubangijinka? Yace:haahu haahu bansaniba.meye addininka? Saiyace haahu haahu bansaniba.wane mutun aka aiko muku? Saiyace haahu haahu bansaniba.naji mutane suna fada nima saina bada sai malaiku suce:kar Allah yasa kasani.
Sai mai kiri yayi kira ace karya yake kuyi masa shunfida da hutu ku bude masa kofar huta ya ringa jin zafinta qabarin ya matseshi kashin kirjinsa ha hade.sai wani mutum yazo mummuna baki da bakin kaya mai wari yazo yace masa kayi bushara da ada bainda akai maka alqawqari.sai yace waye kai ? Yace nine ayyukanka munana nayanka bakasan ayyukan alkhairi sai ayyukan sharri sai Allah ya saka maka dani. Sai aturo masa wani MAKAWO BEBAI KURMA ahannunsa akawai wata guduma dazaa daki dutsan uhudu da ita da saiya zama kasa. Sai a maka mai gudumar man yayi iho har yazama kasa Sai Allah yakuma dawo dashi dai dai haka zaayi tayi masa kowa yana jin ihonsan banda mutum daaljani.sai ya dunga cewa Allah karka tashi alqiyama.dan ya san balain yafi na qabari.
Allah ka tsaremu daga azabar qabari kasamu a aljannah.
Dan uwanku Bashir Hassan Bashir kurawa
Posted By
Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 01:58:44 PDT Da MediaHausaTeam
Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama
Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista