Muhawara Hausa
 



043 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 43
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen 043 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 43

✺✺FASALI NA GOMA (10)✺✺
.
Malam Ya cigaba da Bayani akan Hukunce-Hukuncen da suke kiyayewa Mace Martabarta, kuma suke tsare mutuncinta.
.
3● Har wa yau yana daga cikin matakan taimakawa ga tsare farji, hana mace tayi tafiya in bada muharrami ba, wanda zai tsare ta, ya kareta daga kwad'aice-kwad'aicen­ lalatattu da fasiqai, ingantattun hadisai sunzo wad'anda suke hana mace tayi tafiya ba tare da muharrami ba, daga ciki akwai:
.
● Hadisin Abdullahi Ibn Umar (RA) Yace: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: ''kada Mace tayi tafiyar kwana uku sai da muharrami tare da ita.''
.
[Bukhari da Muslim suka ruwaito]
.
● Kuma Abu Sa'idul khudriy (RA) Yace: Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya hana mace tayi tafiyar kwana biyu ba tare da mubarraminta tare da ita ba.''
.
[Bukhari da Muslim suka ruwaito shi]
.
● Daga Abu-hurairah (RA) Yace: Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: ''Bai halatta ba ga mace tayi tafiyar kwana d'aya da wuni d'aya ba, sai tare da muharrami agare ta.''
.
[Bukhari da Muslim suka ruwaito]

→ Qaddarawar da akayi da kwana uku, kwana biyu da kuma kwana d'aya da wuni d'aya, abunda ake nufi dashi shine tsawon tafiyar gwargodon irin abun hawan da ake dashi ne awancan zamanin, na tafiya a qafa ko akan taguwa. Malamai suka ce sa6anin gwargodon kwanakin da yazo acikin hadisan da kwana uku, ko biyu ko d'aya koma Abunda bai kai haka ba, ba ana nufin zahirinsa bane, abunda ake nufi dukkan abunda ake qira bulaguro, to mace an hanata tayi shi (sai da cika wannan sharad'in)
.
→ Imamun Nawawy (Rahimahullah) Yace: ''Dukkan abunda ake qiransa tafiya to an hana mace tayi ba tare da mijinta ba ko muharrami ko ta kwana uku, ko ta kwana biyu, ko ta kwana d'aya, ko ta baridi d'aya (wato mil goma sha biyu) ko wanin haka. Dalili kuwa shine ruwayar Ibn Abbas Wanda bata qayyade ba, kuma itace qarshen ruwayoyin da Muslim ya kawo wanda tace: ''kada mace tayi tafiya sai tare da muharrami.'' Wannan ya had'a dukkan abunda ake qira tafiya, kuma ALLAH shine mafi Sani.''
.
[Sharhi sahihi Muslim 9/103]
.
Malaman da suka yi fatawa da halarcin tafiyar Hajjin Mace cikin qungiyar mata, wannan sa6anin Sunnah ne.
.
→ Al-imam Alkhad'd'abi Yace: ''Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya hana mace tayi tafiya sai idan tare da ita akwai namiji wanda yake muharrami agareta. Don haka halatta mata yin tafiya domin hajji ba tare da cika sharad'in Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba sa6awa Sunnah ne. Saboda haka idan dai fitar ta ba tare da muharrami ba sa6o ne, to bai halatta a lizimta mata yin hajji ba, domin a lokacin ya zamo yin aikin biyayya ga ALLAH amma da abunda zai kai ga sa6a masa.''
.
[Ma'alimus sunan 2/276-277]
.
Qarin bayani kuma shine cewa malaman basu halattawa mace tayi tafiya ba tare da muharrami ba ako wani irin hali; sun halatta mata ne kawai acikin tafiya domin yin aikin hajji na farilla kad'ai.
.
→ Imamun Nawawy (Rahimahullah) Yace: ''Bai halatta ba tayi tafiya domin hajjin tad'awwu'i ko tafiya domin tijara ko ziyara ko makamancinsu sai da muharrami.''
.
[Majmu' 8/249]
.
Don haka wad'anda suke yin sassauci awannan zamanin wajen halattawa mace tayi ko wace irin tafiya ba tare da muharrami ba, babu Wanda yayi muwafaqa dasu acikin malaman da ake dogaro dasu acikin addini.
.
× Abunda kuma suke fad'a wai cewa: Ai muharrami nata shine Wanda zai d'aurata akan jirgin sama, sannan kuma wani muharrami ya taryeta idan ta isa garin da zata je, domin jirgin saman amintacce ne a ruwayarsu, saboda yawan wad'anda suka hau shi wad'anda suka had'a maza da mata.
.
√ Sai muce dasu: Sam ba haka bane ! Had'arin da ke cikin jirgin sama yafi na waninsa, domin matafiya acikinsa suna cakud'uwa da juna, wataqila ma ta zauna kusa da namiji, ko kuma wani abu ya faru da zai sa jirgin yaje ya sauqa wata tasha ta daban, inda babu Wanda zai taryeta, ta kasance ta shiga hali mai had'ari.
.
To idan kuwa irin haka ya faru, menene zai kasance halin mace data sauqa a qasa wadda bata santa ba, kuma babu wani muharrami nata a qasar ???
.
Mu had'u a FITOWA TA 44 Inshaa ALLAH..
WALLAFAR: SHEIKH SALIH FAUZAN AL-FAUZAN.
.
FASSARAR: DR. BASHIR ALIYU UMAR.
.
GABATARWA: FARIDAH BINTU SALIS (Bintus~sunnah)

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 02:02:44 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen



"043 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 43" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com