Muhawara Hausa
 

 
006 AURE KO MAKARANTA?
 
Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Rubutu na 6

006 AURE KO MAKARANTA?

Daga: *zauren majlisin sunnah*

*MU KOMA GA NASSI*

90. Shin ba Allaah Maɗaukakin Sarki ba ne ya ce:
وَأَنكِحُوا الْأيَامَى مَنكُمْ
Kuma ku aurar da marasa aure daga cikinku?

91. Shin lafazin 'marasa aure' bai haɗa tsofaffi da sababbin balaga ba?

92. Kuma wannan lafazin na 'marasa aure' bai haɗa maza da mata ba?

93. Shin yin gaggawa wurin bin umurnin Allaah (Subhaanahuu wa Ta'aalaa) ba wajibi ba ne a kan dukkan musulmi?

94. Ko akwai wani nassin da ya nuna halaccin dakatar da yin aure domin kawai rashin kammala wani karatu ba ma na-boko ba?

95. Kuma shin ba Annabi (Sallal Laahu Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ba ne ya ce:
إِذَا أَتَاكُمْ مَنْ تَرْضَوْنَ دِينَهُ وَخُلُقَهُ فَزَوِّجُوهُ، إِلَّا تَفْعَلُوا تَكُنْ فِتْنَةٌ فِي الْأَرْضِ وَفَسَادٌ كَبِيرٌ
Idan wanda kuka yarda da addininsa da ɗabi'unsa ya zo muku, to ku aura masa. Idan kuma ba ku yi haka ba, to wata mummunar fitina za ta auku a duniya da ɓarna mai girma'?

96. Shin wannan bai zama babban dalili a kan a gaggauta yi wa duk wanda ya isa aure ba?

97. Kuma shin aukuwan bala'o'i da masifu a yau ba su zama masu tabbatar da gaskiyar wannan Hadisin ba?

98. Jinkirta aure da ƙin gaggauta yinsa bayan haɗuwar rukunnansa bai zama babbar hanyar saɓa wa wannan Hadisin ba?

99. Cewa: 'Ban da garaje! A bar ta, ta kammala karatunta tukuna' bai zama saɓa wa wannan Hadisin a fili ƙarara ba?

100. Wannan maganar ba ta zama musifar da ta fi komai cutar da ilimi da lafiya da rayuwar al'umma gaba ɗaya ba?

*A ƘARSHE*

Muna roƙon Allaah Maɗaukakin Sarki ya ƙara tsare mu, ya shiryar da mu baki ɗaya, kuma ya ba mu ƙarfin gwiwar kafewa a kan bin Sunnah har zuwa ƙarshenmu.
Kuma godiya ta tabbata ga Allaah a farko da ƙarshe. Tsira da amincin Allaah su tabbata ga shugaban na-farko da na-ƙarshe, shi da iyalai da sahabbansa da sauran Salihai.
Daga:
Muhammad Abdullaah Assalafiy,
Masjidut Tajwiid,
Zango.
26/Nuwamba/1992.

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 02:14:36 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

"006 AURE KO MAKARANTA?" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com