Muhawara Hausa
 

 
045 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 45
 
Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin 045 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 45

✺✺FASALI NA GOMA (10)✺✺
.
Malam Ya cigaba da Bayani akan Hukunce-Hukuncen da suke kiyayewa Mace Martabarta, kuma suke tsare mutuncinta.
.
[C]→Wasu mata da waliyansu suna yin sassauci wajen shigar mace wajen Likita ita kad'ai da hujjar wai cewa magani take nema. Wannan munkari maigirma kuma had'ari ne babba Wanda bai kamata a qyale shi ba, ayi shiru akansa.
.
→ Sheikh Muhammad Ibn Ibrahim (Rahimahullah) Yace acikin [Majmu'ul Fatawa nasa 10/13]:
.
Kad'aituwa da mace Ajnabiya haramun ne acikin shari'ah, koda kuwa da likita ne, saboda hadisin da yake cewa: ''Wani namiji bai ta6a kad'aituwa da mace ba face shaid'an ya zama na ukunsu.'' Don haka dole ne asamu wani tare da ita, kodai mijinta ko wani namiji daga cikin muharramanta. Idan ba a samu haka ba, to ko dai wata mace daga cikin 'yan uwanta, idan kuma ba a samu hakan ba a samu wani daga cikin wad'anda ba a ambata ba, kuma idan rashin lafiyar mai had'ari ne, bazai yuwu a jinqirta shi ba, to sai a samu ko da wata daga cikin ma'aikatan jinya na asibitin don a tsaru daga kad'aituwar da aka hana.

Hakanan bai halatta ga likita namiji ya kad'aita da mace Ajnabiya, ko da likita ce mace abokiyar aikinsa, ko mai aikin jinya. Haka ma bai halatta Malami mai koyarwa koda makaho ne ya kad'aita da d'aliba. Haka ma mace ma'aikaciya acikin jirgin sama bai halatta ta kad'aita da ajnabi gareta ba.
.
Wad'annan al'amura mutane suna sake dasu da sunan cigaba da wayewa ta qarya, da kuma koyi da kafirai, da kuma saboda yiwa hukunce-hukuncen shari'ah riqon sakainar kashi. Babu qarfi babu dabara sai da ALLAH Mad'aukaki Mai girma.
.
Kuma bai halatta namiji ya kad'aita da 'Yar aiki agidansa ba, haka ma mace Uwar-gida bai halatta ta kad'aita da namiji d'an aiki agidan ba. Wannan mushkila ta masu aikin gida mushkila ce mai had'ari da ya gallabi mutane da yawa a wannan zamani. Wannan kuwa saboda mata sun shagaltu da karatu da aiki awaje. To wannan yana nuna cewa lallai ne Muminai Maza da Mata suyi hattara sosai, su kuma d'auki dukkan matakai na tsentsani, kada su miqa wuya ga miyagun al'adu.
.
★ BAYANI NA QARSHE !!!
.
● Haramun Ne Ga Mace Tayi Hannu Da Namijin Da Ba Muharraminta Ba.
.
→ Sheikh Abdul'aziz Bin Abdullah Bin Baaz, babban shugaban Ma'aikatar Fatawa da Da'awa da kuma Shiryarwa (Rahimahullah) Yace: ''Bai halatta ba ayi hannu da mata wad'anda ba muharramai ba akowane hali ko yara ne su ko tsofaffi, haka kuma mai yin hannu dasu ko yaro ne ko tsoho. Wannan kuwa hatsarin fitina ga kowanne daga cikin su. ''Hadisi ya inganta daga Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) bai ta6a, ta6a hannun wata mace (wadda ba ta halatta gareshi ba). Idan zai yi musu mubaya'a magana kawai yake yi musu.''
.
Kuma duk d'aya ne babu bambanci wai tayi hannu dashi alhali hannun nata yana lullu6e da wani abu , ko baya lullu6e da komai duk d'aya ne saboda dalilai masu dama na shari'ah, kuma saboda toshe hanyar 6arna mai kaiwa ga fitina.
.
→ Sheikh Muhammad Al-Ameen Al-Shanqid'i (Rahimahullah) Yace: '' Ka sani cewa bai halatta ba ga namiji ajnabi yayi hannu da mace ajnabiya gare shi, kuma bai halatta gare shi ba ya shafi jikinta da wani 6angare na jikinsa. Dalili akan wannan kuwa sune:
.
◉ AL'AMARI NA FARKO: Hadisi ya tabbata daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa Yace: ''Ni bana yin hannu da mata'' har zuwa qarshen hadisin. Kuma ALLAH Ta'ala Yace: ''Haqiqa abun koyi kyakykyawa ya kasance agare ku daga wajen Manzon ALLAH''.Don haka dole ne a kanmu kada muyi hannu da mata domin koyi da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), Hadisin da muka kawo munyi magana akansa a bayyane acikin suratul Hajji, wajen magana kan hana sa kaya jajaye ga maza, acikin halin ihrami da wajensa, da kuma acikin suratul Ahzab wajen ayoyin hijabi. Kuma kasancewarsa (Sallallahu Alaihi Wasallam) baya yin hannu da mata lokacin mubaya'a dalili ne mabayyani akan cewa namiji baya hannu da mace, kuma wani abu na jikinsa bazai shafi wani abu na jikinta ba, domin yin hannu shine mafi qarancin shafa. To idan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya hanu daga yin haka alokacin da aka samu dalilin yin haka, wato lokacin yin mubaya'a wannan ya nuna cewa yin haka bai halatta ba.
.
Kuma babu wanda yake da damar sa6awa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) domin shine mai kafa shari'ah ga al'ummarsa da maganganunsa da ayyukansa, da kuma abubuwan da akayi a gabansa ya tabbatar dasu.
.
◉ AL'AMARI NA BIYU: Shine abunda ya gabata cewa Mace dukkanta Al'aura ce, Wajibi ne akanta ta killace kanta, kuma ba wani abu ne yasa akayi umurni da kame idanu ba sai don jin tsoron afkawa cikin fitina. Kuma babu shakka shafar jiki da jiki shine mafi qarfi wajen motsa sha'awa, da kaiwa ga fitina fiye da kallon ido; kuma dukkan mai adalcin ra'ayi yasan gaskiyar wannan magana.
.
◉ AL'AMARI NA UKU: Shine cewa wannan tafarki ne na jindad'i da mace ajnabiya, saboda qarancin tsoron ALLAH a wannan zamanin, da tozartar da amana da rashin kame kai daga zargi.
.
Munji labaru da suke cewa sau da yawa ana samun namiji daga gama garin mutane yana sumbantar 'yar-uwar matarsa, baki akan baki; suna qiran wannan Sumba wacce take haramun bisa ijma'in malamai, suna qiranta gaisuwa, sai kaji sunce: ka gaisa da ita, wai suna nufin ka sumbace ta (Wa'iyazubillahi)
.
To gaskiya wacce babu qoqonto acikinta, itace lallai a nisanci dukkan fitinu da zargi da hanyoyin da ke kaiwa gare su. Daga cikin mafi girman wad'annan hanyoyi shafar namiji ga wani 6angare na jikin mace ajnabiya gare shi. Kuma dukkan hanya dake kaiwa ga haramun wajibi ne a toshe ta.''
.
[Tafsirin Adawa'ul Bayan 6/602-603]
.
Mu had'u a FITOWA TA 46 Inshaa ALLAH..
WALLAFAR: SHEIKH SALIH FAUZAN AL-FAUZAN.
.
FASSARAR: DR. BASHIR ALIYU UMAR.
.
GABATARWA: FARIDAH BINTU SALIS (Bintus~sunnah)

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 02:17:28 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

"045 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 45" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com