Muhawara Hausa
 

 
046 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 46
 
Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin RUBUTU NA QARSHE !!!

046 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI

★ A Qarshen littafin Malam Yayi mana nasiha kamar haka:
.
Ya ku 'Yan uwa muminai maza da mata, ina tunatar daku wasiyyar ALLAH gare ku a inda yake cewa:
.
قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَٰلِكَ أَزْكَىٰ لَهُمْ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ ٭ وَقُل لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آبَائِهِنَّ أَوْ آبَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ أَوْ أَبْنَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ أَوْ نِسَائِهِنَّ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ أَوِ التَّابِعِينَ غَيْرِ أُولِي الْإِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ أَوِ الطِّفْلِ الَّذِينَ لَمْ يَظْهَرُوا عَلَىٰ عَوْرَاتِ النِّسَاءِ وَلَا يَضْرِبْنَ بِأَرْجُلِهِنَّ لِيُعْلَمَ مَا يُخْفِينَ مِن زِينَتِهِنَّ وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
.
Ma'ana: ''Kace da muminai maza su kame ganin su, kuma su kiyaye farjinsu, wannan shi yafi tsarki agare su, haqiqa ALLAH masanin abunda suke aikatawa ne. * Kace da Muminai mata su kame ganinsu, kuma su kiyaye farjinsu. Kada kuma su fito da adonsu, sai dai abunda ya bayyana daga gare shi, kuma suyi lullu6i da mayafansu akan wuyan rigunan su, kuma kada su bayyana adon su sai ga mazajensu, ko iyayensu, ko iyayen mazajensu ko 'ya'yayensu ko 'ya'yayen Mazajensu ko 'Yan uwansu maza ko 'Ya'yan 'Yan uwansu maza ko 'Ya'Yan 'Yan uwansu mata ko mata (musulmai) 'Yan uwansu Ko kuma Abunda hannayensu suka mallaka (wato bayi) ko kuma mabiya ba masu buqatar mata ba daga maza ko kuma qananan yara wad'anda basu san sha'awar al'aurar mata ba. kada kuma su buga qafafuwansu don agane abunda suka 6oye na adon qafafun su (wato mundaye) kuma ku tuba ga ALLAH gaba d'ayanku yaku wad'annan muminai don ku rabauta.''
.
[Suratul Noor aya ta 30-31]

Dukkan Yabo ya tabbata ga ALLAH Ubangijin taliqai, kuma ALLAH Yayi dad'in tsira ga Annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa kuma da aminci.
.
Qarshen littafin kenan !!!
.
____________________­__________
ALHAMDULILLAH, Farin cikina da godiyata ga ALLAH bazai misaltu ba, ina qara yiwa ALLAH godiya da ya bani iko da dama sannu a hankali har na gabatar da wannan littafi a wannan dandali ta social media.
.
Wannan littafi ne mai matuqar muhimmanci yana d'auke da Hukunce-Hukunce da suka ke6anci mata Wanda hujjojinsa da dalilansa suka kasance daga ayoyi da hadisai da Maganganun magabata na qwarai, Littafin Yana da Fasaloli guda 10 akowani fasali yana d'auke da gundarai da suka dace da wannan fasalin. Cikin qudurar ALLAH ya bani damar gabatar dashi sannu a hankali inda na ringa kawo shi kad'an-kad'an har sau 46.
.
A iya sani na nasan an rubuta wannan littafin da harsuna guda 3 wato Larabci, Hausa, Turanci.
.
Babban Malamin da Ya wallafa shi da harshen Larabci shine: Sheikh Salih Bin Fauzan AlFauzan (Hafizahullah) Ya sanya mishi suna:
.
تنبيهات على أحكام تختص بالمؤمنات.
.
Sannan Babban Malaminmu anan Nigeria Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar (Hafizahullah) Shugaban cibiyar yad'a addinin musulunci ta Al-Furqan, Sannan kuma babban Malami a sashen nazarin addinin musulunci na Jami'ar Bayero ta Kano, Haka kuma shine babban limamin masallacin Jumma'a na Al-Furqan dake Alu Avenue Nassarawa, Kano, Har ila yau kuma shugaban cibiyar tattaunawa a tsakanin addinai ta Jami'ar Bayero,Kano. Shi yayi nasarar Fassara wannan littafin zuwa Harshen Hausa domin al'umma su samu sauqin karanta shi musamman mutanen mu na nan arewa da suka fi fahimtar Harshen Hausa sama da ko wani harshe, an ambaci wannan littafi da suna kamar haka:
.
Fad'akarwa kan HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KE'BANCI MATA MUMINAI.
.
Hakanan kuma nace akwai na Turanci lallai nasan akwai na turanci amma bansan sunan da aka sanya mishi ba kuma bansan sunan mafassarin ba.
.
Ina qira ga 'Yan uwana mata da suyi qoqari su mallaki wannan littafin domin warware matsalolinsu na addini dana rayuwa, haqiqa wannan littafin ya ta6a 6angarori da yawa, kuma haqiqa zai taimaka miki sosai wajen warware matsaloli da wayewa. Suma maza ba a barsu a baya ba suna iya mallakar wannan littafin domin warware matsalolin iyalansu.
.
Malamanmu da suke fad'akar damu ta hanyar qoqarinsu da jajircewarsu wajen yad'a addinin musulunci ALLAH Ya saka musu da alkhayri tare da iyayen mu. (Ameen)
.
ALLAH Yasa mu amfana da abunda muka karanta (Ameen)

WALLAFAR: SHEIKH SALIH FAUZAN AL-FAUZAN.
.
FASSARAR: DR. BASHIR ALIYU UMAR.
.
GABATARWA: FARIDAH BINTU SALIS (Bintus~sunnah)
.
نسأل الله العلي القدير أن يوفق جميع المسلمين والمسلمات إلى ما يحب ويرضى، وآخر دعوانا أن الحمد لله رب العالمين.

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 02:19:06 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

"046 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 46" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com