Muhawara Hausa
Azumin Tsofaffi
Azumin Tsofaffi Sau da dama 'yan uwa sukan rikice da batun Azumin watan Rajab, zatonsu ana yaqar yin azumi ne,wanda abin ba haka yake ba. Yadda lamarin yake a taqaice shine:- © Azumi ibada ce mai girma da Allah(swa) yake bayar da amincinsa ga masu yinsa a cikin watan Rajab da waninsa cikin watanni,amma bisa qa'idar da mai RISALA ya fada a muqaddimar littafinsa ''ولا قول ولا عمل ولا نية إلا بموافقة السنة'' ''BABU INGANCIN ZANCE KO AIKI KO NIYYA SAI IDAN YA DACE DA SUNNAH'' Irin wadannan batutuwa lalubesu a littafin DAN-FODIO (rt) mai suna: وثيقة الإخوان. © Idan mutum ya quduri yin azumi a watan rajab kamar * AZUMIN LITININ DA AL-HAMIS *AZUMIN AYYAMUL BHYYD( 13,14,15) *KAYI YAU GOBE KA HUTA (AZUMIN DAWUD) *AZUMI RANAR JUMA'A TARE DA RANAR DAKE BINTA KO BAYANTA ( ALHAMIS/ASABAR) Wadannan duk ba laifi a cikinsu,saboda suna da asali daga Hadisan Annabi(s.a.w) ingantattu. © Amma kebantar watan Rajab dayin AZUMI NA MUSAMMAN! Kamar AZUMIN TSOFAFFI…. Sunan Azumin kadai ya isheka shaidar cewa ba shari'a bane!! Saboda Tsofaffi hatta azumin farilla ya saraya a kansu idan zai wahalar dasu. Kamar yadda Ibn Abbas(r.a) ya fada qarqashin fadin Allah s.w.a ''و علي الذين يطيقونه فدية طعام مسكين'' Sai ibn Abbas r.a yake cewa:- ليست بمنسوخة،إنه الشيخ كبير والمرأة الكبيرة لا يستطيعان أن يصوما،فليطعمان مكان كل يوم مسكينا. Wane kuma ya ware wata guda cur yace su azumta..?? © SANNAN DUK HADISAN DA SUKE BAYANI DANGANE DA FALALAR AZUMTAR WATAN RAJAB ,BABU 1 TAK DAYA INGANTA TA FUSKAR ISNADI!! Da wannan nake shawartarmu da muke taqaituwa a bisa iyakar da addininmu ya zana mana,ba tare da munyi masa qarin komai ba. والله أعلم.
Posted By
Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 02:27:21 PDT Da MediaHausaTeam
Comments 💬 التعليقات
<
Matsalar Magana
Matsakaicin Maki: 0 Kurioi: 0
Ya Danganta Kanun Labarai
"Azumin Tsofaffi" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata
Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama
Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com