Muhawara Hausa
 

 
017 Hunkunce-Hunkunce Da Suka Kebanci Mata Muminai Fitowa Ta 17
 
Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin 017 Hunkunce-Hunkunce Da Suka Kebanci Mata Muminai Fitowa Ta 17

Malam ya cigaba da kawo mana bayanai a game da abunda ya shafi: HUKUNCE-HUKUNCEN TUFAFI DAGA CIKIN FASALI NA HUDU.
.
● Sheikhul islam Ibn Taimiyya (Rahimahullah) cikin Majmu'ul Fatawa (22/148-155) yace:
.
Abunda yake bambance tufar maza data mata yana komawa ne ga abunda yake dacewa da maza da kuma abunda yake dacewa da mata. Wannan kuwa shine abunda ya dace aka umurci maza dashi kuma aka umurci mata dashi, mata dai an umurce su da suturce jiki da yin lullu6i da Barin bayyana ado ga maza da barin bayyana Kai.
.
Don haka ne a shari'a ba a sanyawa mace daukaka murya domin qiran sallah ba ko yin talbiya (wato Labbaika) ko hawa kan dutsen safa da marwa, ko cire tufafi domin yin ihrami kamar yadda namiji yake yi, saboda shi namiji an umurce shi da ya bude kansa kuma kada ya saka tufafi na al'ada wato tufafin da ake dinka su gorgodon ga6ar jiki bazai saka taguwa ko wando ba ko irin rigar nan mai hade da hula ba, har inda sheikhul Islam yace:

Ita kuwa mace ba hanata sa wata tufa daga cikin tufofinta ba, domin ita an umurceta ne da suturce kai da yin hijabi, don haka bazai yuwu a umurceta da abunda zai sa6awa haka ba, sai dai an haneta da sanya abun rufe fuska da safar hannu saboda wadannan tufafi ne da aka dinka su da siffar ga6ar jiki, kuma bata buqatar su. A qarshe Sheikhul islam Ibn Taymiyya Yace:
.
Idan aka gane cewa ba makawa a samu bambanci tsakanin tufafin maza dana mata yadda maza zasu bambanta dabam daga, mata tufafinsu ya kasance mai suturcewa da 6oye dukkan jiki Wanda shine abunda ake nema acikin shari'a, lokacin ne ginshiqin da aka gina wannan babin akansa zai bayyana gare ka. Kuma za'a gane cewa idan wata tufa ta zamanto a galibi maza ne suke sakawa to mace an hanata sa wannan tufar.
.
*5•* Kada tufar ta zamo tana da ado wanda take Jan hankalin mutane gareta idan ta fita daga gida, don kada ta zamanto cikin mata masu bayyana adonsu ga maza.
.
Mu hadu a FITOWA TA 18 Inshaa ALLAH.

.
WALLAFAR: SHEIKH SALIH FAUZAN AL-FAUZAN.
.
FASSARAR: DR. BASHIR ALIYU UMAR.
.
GABATARWA: FARIDAH BINTU SALIS (Bintus~sunnah)

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 02:31:16 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

"017 Hunkunce-Hunkunce Da Suka Kebanci Mata Muminai Fitowa Ta 17" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com