Muhawara Hausa
 

 
Mugunyar Addu'a A Kan Wadanda Ke Mulkar Jama'a A Kan Zalunci Da Saba W
 
Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin Ibrahim Jalo Jalingo

Mugunyar Addu'a A Kan Wadanda Ke Mulkar Jama'a A Kan Zalunci Da Saba Wa Ka'idar Da Aka Shimfida Abu Ne Da Ya Dance Shari'a

Al'ummar Kasa su ci gaba da yin mugunyar addu'a cikin kunutin Salla ko waninsa a kan wadanda ke son mulkar kasarsu da al'ummarsu a kan zalunci da saba wa ka'idar da aka shimfida lalle wannan wani abu ne da Sahri'ar Musulunci ta amince da shi, babu kuma mai kushe masa sai wanda ya jahilci nassoshin Shari'ah. Saboda abubuwa kamar haka:-

1. Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 804, da Imam Muslim hadithi na 675 daga Sahabi Abu Hurairah Allah Ya kara masa yarda cewa:-

((ان رسول الله صلى الله عليه وسلم كان اذا أراد ان يدعو على احد او يدعو لأحد قنت بعد الركوع فربما قال اذا قال سمع الله لمن حمده اللهم ربنا لك الحمد: اللهم انج الوليد بن الوليد، وسلمة بن هشام، وعياش بن ابي ربيعة، والمستضعفين من المؤمنين، اللهم اشدد وطاتك على مضر، واجعلها عليهم سنين كسني يوسف، اللهم العن لحيان ورعلا وذكوان وعصية عصت الله ورسوله)).

Ma'ana: ((Lalle Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kasance Idan ya yi nufin yi wa wani mugunyar addu'a, ko yi wa wani kyakkyawar addu'a, ya kan yi kunuti bayan rukuu'i, yana ma yiwuwa ya ce bayan ya ce: Sami'al Lahu liman hamidahu Allahumma Rabbana lakal Hamd: Ya Allah! Ka tsirar da Waliid Bin Waliid, da Salamah Bin Hisham, da Ayyash Bin Abii Rabii'ah, da Raunana cikin Muminai. Ya Allah! Ka tsananta kamunka a kan Kabilar Mudhar, Ka sanya wannan kamu a kansu a matsayin shekarun fari kamar shekarun farin zamanin Yusuf. Ya Allah! Ka la'anci (kabilun) Lihyan da Ri'il da Zakwan da Usayyah, sun saba wa Allah da ManzonSa)).

2. Sannan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 22/270:-

((فيشرع ان يقنت عند النوازل يدعو للمومنين ويدعو على الكفار في الفجر وفي غيرها من الصلوات، وهكذا كان عمر يقنت لما حارب النصارى بدعاءه الذي فيه: اللهم العن كفرة أهل الكتاب'' الى اخره. وكذلك علي رضي الله عنه لما حارب قوما قنت يدعو عليهم. وينبغي للقانت ان يدعو عند كل نازلة بالدعاء المناسب لتلك النازلة، وإذا سمى من يدعو لهم من المؤمنين ومن يدعو عليهم من الكافرين كان ذلك حسنا)).

Ma'ana: ((An shar'anta ya yi Kunuti a lokacin da wasu musibu suka sauko, ya yi wa Muminai addu'ar alheri, ya yi wa kafurai mugunyar addu'a a cikin sallar Asuba da waninta daga cikin Salloli. Haka Umar ya kasance yake yin Kunuti a lokacin da yake yin yaki da Nasara, da addu'arsan nan da a cikinta yake cewa: Ya Allah Ka la'anci Kafuran Ahlul Kitab'' har zuwa karshe. Haka nan Alyyu Allah Ya kara masa yarda a lokacin da ya yaki wasu mutane ya yi kunuti yana musu mugunyar addu'a. Yana da kyau mai yin kunuti ya yi addu'a a duk lokacin da wata musiba ta sauko da irin addu'ar da ta dace da irin wannan musibar. Idan ya ambaci sunan Muminan da yake musu addu'a, ko sunan Kafuran da yake musu mugunyar addu'a yin hakan abu ne mai kyau)).

3. Imamun Nawawii ya yi babi cikin Littafin Azkar shafi na 489 ya ce:-

((باب جواز دعاء الانسان على من ظلم المسلمين او ظلمه وحده)).

Ma'ana: ((Babin halaccin mutum ya yi mugunyar addu'a a kan wanda ya zalunci Musulmi ko a kan wanda ya zalunce shi shi kadai)).

**

ABIN NUFI A TAKAICE:

Abin nufi a takaice a nan shi ne: Idan mai mulki ya kasance mutum ne mai adalci, mai bin gaskiya, mai tausayin talakawa, to yi wa wannan mugunyar addu'a zalunci ne kuma ketare iyakar da Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ta shata ne. To amma in mai mulki ya kasance mutum ne azzalumai, mai kuntata wa talakawa, to shi wannan yi masa mugunyar addu'a abu ne da yake halal a Shari'ance. A bisa wannan ka'idar ne za a fahimci hadithi na 1855 da Imam Muslim ya ruwaito daga Sahabi Auf Bin Malik cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:-

((خيار أئمتكم الذين تحبونهم ويحبونكم، ويصلون عليكم وتصلون عليهم، وشرار أئمتكم الذين تبغضونهم ويبغضونكم وتلعنونهم ويلعنونكم)).

Ma'ana: ((Shugabanninku na kirki su ne wadanda kuke son su, su ma suke son Ku, kuke musu addu'ar alheri su ma suke muku addu'ar alheri. Shugabanninku na banza kuwa su ne wadanda kuke kin su su ma suke kin ku, kuke tsine musu su ma suke tsine muku)).

A dai bisa wannan ka'idar ce har yanzu za a saukar da dukkan maganganun da aka ruwaito su daga Maluman Musulunci game da yi wa mai mulki kyakkyawar addu'a ko yi masa mugunyar addu'a, wannan shi ya sa ma hadithi ya inganta a kan cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi gamammiyar mugunyar addu'a a kan mai mulkin da yake kuntata wa talkawansa, ya kuma yi gamammiyar addu'ar alheri ga dukkan wani mai mulki da yake nuna tausayi da jinkai ga talkawansa. Imamu Muslim ya ruwaito hadithi na 1828 cewa Annabi Mai tsira da amincin Allah ya ce:-

((اللهم من ولي من امر امتي شيءا فشق عليهم فاشقق عليه، ومن ولي من امر شيءا فرفق بهم فارفق به)).

Ma'ana: ((Ya Allah! Duk wanda ya jibinci wani abu na lamarin al'ummata sannan ya tsananta musu, to Ka tsananta masa. Wanda kuma ya jibinci wani abu na lamarin al'ummata ya nuna musu tausayi, to Ka tausaya masa)).

Saboda wannan hadithi da Imamu Muslim ya ruwaito cikin Sahihinsa, duk wani wanda ya ce ba a yi wa shugaba mugunyar addu'a duk zalunci da sakarci da zai rika yi wa kasarsa da kuma Al'ummar kasarsa, sai dai kawai a rika cewa: Allah Ya shiryar da shi kawai! To lalle wannan ya yi kure matuka, saboda lazimin wannan magana tasa da kuma wannan akida tasa shi ne: ganin tamkar Annabi mai tsira da amincin Allah da ya yi wannan addu'a cikin wannan Hadithi Sahihi ba daidai ya yi ba, a'a kure ne ya yi!

ALLAH YA YI WA NIGERIA DA AL'UMMARTA ALBARKA, ALLAH YA LA'ANCI GUNGUN AZZALUMAN DA KE WASA DA MASLAHAR NIGERIA DA AL'UMMARTA:

Allah wadaran wauta da karkataccen tunani da wasu shugabannin Africa ke da shi, inda suke har kullum tunaninsu shi ne yadda za su yi su dawwama a kan karagar Mulki, babu kishin Kasa da jama'arta cikin tunaninsu.

**

TARIHI:

A 2010 gwamnatin Kasar Côte d'Ivoire (Ivory Coast) karkashin shugabancin Laurent Gbagbo ta shirya zaben Kasa a ranar 31/10/2010, sannan aka yi second round a ran 28/11/2010, inda Alhaji Alassane Outtara ya yi nasara a cikinsa, amma shi Shugaba Gbagbo saboda karkataccen tunani irin nasa, da kuma mugun nufi ga talakawan Ivory Coast sai ya ki ya mika ragamar mulki ga Outtara, wanda wannan mataki na kauyanci da zalunci da ya dauka ya jefa Kasar cikin yamutsi da tashin hankali inda aka kashe dubban 'Yan Cote d'Ivoire, ya kuma sa sojojin Majalisar dinkin Duniya suka shiga cikin lamarin suka kama shi Gbagbo kamu na wulakanci da kaskaskanci a ran 11/4/2011, suka mika shi ga Kotun Duniya a inda yake tsare har zuwa yanzun nan. Lalle har idan akwai dan abin da ya rage na hankali to kuwa ya kamata gunguAllahn azzalumai na Nigeria su dauki darasi.

**

HALAL NE MU RIKA YI WA GUNGUN AZZALUMAN NAN DA SUKE CUTAR DA NIGERIA DA KUMA JAMA'AR NIGERIA DOMIN NEMAN BIYAN BUKATUN KANSU:

Imamun Nawawii ya yi babi cikin Littafin Azkar shafi na 489 ya ce:-

((باب جواز دعاء الانسان على من ظلم المسلمين او ظلمه وحده)).

Ma'ana: ((Babin halaccin mutum ya yi mugunyar addu'a a kan wanda ya zalunci Musulmi ko a kan wanda ya zalunce shi shi kadai)).

Imam Muslim ya ruwaito hadithi na 1855 daga Sahabi Auf Bin Malik cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:-

((خيار أئمتكم الذين تحبونهم ويحبونكم، ويصلون عليكم وتصلون عليهم، وشرار أئمتكم الذين تبغضونهم ويبغضونكم وتلعنونهم ويلعنونكم)).

Ma'ana: ((Shugabanninku na kirki su ne wadanda kuke son su, su ma suke son Ku, kuke musu addu'ar alheri su ma suke muku addu'ar alheri. Shugabanninku na banza kuwa su ne wadanda kuke kin su su ma suke kin ku, kuke tsine musu su ma suke tsine muku)).

Imamul Bukhari Ya ruwaito Hadithi na 4259, da Imamu Muslim hadith na 626 daga Sahabi Ibnu Umar cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah Ya ce a ranar Khandaq:-

((حبسونا عن الصلاة الوسطى حتى غابت الشمس ملا الله قبورهم وبيوتهم نارا))

Ma'ana: ((Sun hana mu yin Sallar Tsakiya Allah Ya cika kaburansu da gidajensu da wuta)).

Imamul Bukhari da Imam Muslim sun ruwaito cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi mugunyar addu'a a kan wadanda suka kashe Makaranta Alqur'ani har na tsawon wata guda yana cewa:-

((اللهم العن رعلا وذكوان وعصية)).

Ma'ana: ((Ya Allah! Ka la'anci Ri'il da Zakwan, da Usayyah)).

**

Muna ba da shawara daga yanzu har zuwa makonni shida masu zuwa mu yawaita kyakkyawar addu'a ga Nigeria da kuma jama'ar Nigeria, sannan mu yawaita mugunyar addu'a a kan gungun jama'ar nan da suke yi wa Nigeria da kuma jama'ar Nigeria zagon Kasa, suke neman tilasta wa mafi yawan jama'ar Nigeria sabanin abin da yake shi ne zabinsu.

Ya Allah Ka taimaka wa Nigeria da jama'arta, Ka sanya albarka cikin Nigeria da jama'arta, Ka kubutar da su daga sharrin masharrantar da suke son dora kawunansu a kanta da kuma jama'arta ba a bisa Ka'ida ba.

Ya Allah Ka la'anci gungun azzaluman nan farar-hularsu, da bakar-hularsu, gungun nan da suka nace kan tilasta wa Mafi yawan Al'ummar Nigeria Abin da ba shi ne zabinsu ba. Ya Allah Ka la'ance su, Ka la'ance su fa Ka kuma halakar da su gabadayansu kafin su kai ga cimma wannan mugun nufi nasu. Ameen.

DR IBRAHIM JALO JALINGO

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 02:47:55 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

"Mugunyar Addu'a A Kan Wadanda Ke Mulkar Jama'a A Kan Zalunci Da Saba W" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com