Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
 
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, mun kwana a karshen bayanin manuniya kan cewa kofar tuba a bude take, yau, saboda mu samu armashin kawo karashen mukalar, za mu gabatar da ita ne daga farkon maganar tuba, kamar haka:
kofar Tuba A Bude Take

Wani ko wata zai ko za ta iya tunanin cewa, "Yanzu na ji wa'azi, to yaya zan yi in tuba in daina, kuma shin ma Allah zai karbi tuban nawa, bayan dukkan wadannan abubuwa da na aikata?" Sai mu ce:

Babu wani zunubi a bayan kasa da Allah ba Ya gafarta shi, matukar dai mai yin sa ya tuba, tuba ingantacciya, saboda Allah Yana cewa, "Ka ce, ya ku bayiNa wadanda suka yi wa kansu barna kada ku debe kauna ga rahamar Allah, hakika Allah Yana gafarta zunubai gaba daya, lallai shi Allah, Mai gafara ne, Mai jinkai". (Surar Azzumar, aya ta 53). Sannan Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Allah Ya sanya wata kofa a wajen mafadar rana, fadinta tafiyar shekara saba'in ce, saboda tuba, ba kuma za a rufe wannan kofar ba, matukar dai rana ba ta bullo daga inda kofar take ba". Tirmizi ne ya rawaito wannan hadisi.

A wannan aya da hadisi, za mu ga yadda Allah Madaukakin Sarki, saboda rahamarSa da falalarSa, Ya bude tangamemiyar kofar karbar tuba, har zuwa lokacin tashin alkiyama. Don haka babu wani zunubi da mutum zai yi a fadin duniyar nan, face in ya tuba, Allah zai karbi tubansa. Abin da dai ya wajaba a kiyaye yayin tuban shi ne:

• Yin nadama a kan abin da ya gabata, ya zama yana tunawa kuma yana damuwa, yana nadama, yana jin yaya ma aka yi ya aikata wannan laifin!

• kudurcewa a zuciya yayin tuba, cewa ba zai kara koma wa wannan laifi ba, har karshen rayuwarsa.

• Barin wannan sabon, in yana cikin yi ne yayin da zai tuba, kada ya ce bari in karasa, sannan sai in tuba.

• Yin tuban a lokacin da Allah Yake karba, shi ne kafin tashin alkiyama, kuma ba lokacin da yake gargarar mutuwa ba. Hakika Allah ba Ya karbar tuba a wadannan lokatai guda biyu, kamar yadda Alkur'ani da hadisi suka nuna.

• Ya zama ya sauke nauyin wani da ya hau kansa, idan kudi ne ya biya shi, in cin mutunci ne ya nemi ya yafe masa.

Wadannan su ne abubuwan da mai tuba zai kiyaye da su yayin tubarsa. Allah Madaukakin Sarki Ya sa mu dace.
Ina So In Tuba Sai Dai…

Da yawa daga cikin mutane suna son su tuba su bar zunubin da suke yi, sai wasu abubuwa sukan zo su sha gabansu, su kange su ga barin tuba din, har kuma su halaka suna kan wannan sabon, to amma mutum musulmi, wanda ya san abin da yake, ya san babu wani abin da yake k2are mutum daga tuba.

A nan za mu kawo kadan daga cikin irin wadannan abubuwan da suke kange wasu daga tuba, mu yi bayanin yadda mutum zai yi:

• Wata ta ce, ina so in tuba in bar yin zina, sai dai abokin barnata yana tsorata ni da cewa idan na ki yarda da shi, zai fallasa ni ya tona min asiri, domin kuwa yana da ‘recording' din wasu daga cikin abubuwan da muka yi tare da shi, to yaya zan yi?

• Amsa: Ki sani cewa kunyar lahira ta fi ta duniya, kuma Allah Madaukakin Sarki kike saba wa ba wani dan Adam ba, Allah kuma Ya fi iko a kanki fiye da yadda wancan abokin badalarki yake da iko a kanki, Allah zai iya tona miki asiri ke da shi a nan duniya, kuma Ya ki rufa muku asiri a lahira. Don haka ki zabi kunyar duniya a kan ta lahira, ki dogara ga Allah, babu abin da zai cutar da ke nawa ne cikin mutane da suka shahara da barna da fasadi a bayan kasa, amma Allah Ya rufa musu asiri ya karbi tubansu, ya zamana ko da abokan badalarsu a baya, sun fadi wani abu a kansu, ba ya wani ta'asiri, domin dukkan zukatan bayi suna a hannun Allah ne, Yana jujjuya su yadda Ya ga dama. Don haka ki dogara ga Allah ki tuba, Allah Mai ji ne, Mai gani. Shi kuma (mai yi miki waccan barazana) ki bar shi da Allah, Zai ishar miki sharrinsa.

• Wani kuma ya ce, na yi lalata da yawa, na shigar da mutane masu dimbin yawa cikin wannan hanya, yanzu idan na tuba yaya zan yi da wadanda na rena, anya kuwa Allah Zai gafarta min?

• Amsa: Ka sani sanya zuciyarka ta yi wannan tunani na tuba alama ce daga cikin alamomin Allah Yana nufinka da alheri, kuma babu abin da ya wajaba a kanka face ka gaggauta tuba da barin wannan sabo, wadanda kuwa ka sanya a wannan harka ka kirawo su zuwa ga tuba, kamar yadda ka kirawo su – a baya – zuwa ga halaka, wanda duk ya amsa kana da lada, wanda kuwa ya bijere maka, to Allah Yana ji, Yana gani, kai dai ka tsarkake niyyarka ka tuba, ka yawaita istigfari da neman tsari daga wurin Allah, ka yawaita alheri, Allah Mai gafarta zunubai ne gaba daya.

• Wata kuwa cewa ta yi: Yo in ma na tuba komawa nake, sau nawa ina tuba ina komawa, don haka gara kurum in ci gaba, nan gaba na tuba!

• Amsa: A'a ya 'yar uwa, wannan ba dalili ba ne na kin tuba, wala'alla a baya ba ki tsarkake niyyarki ba, kina tuban ne a baki, amma zuciyarki tana tattare da abin. Kuma ki sani yawan tuba matukar da niyya mai kyau kike yi, to ko da kin koma wa laifin daga baya, wannan ba zai hana ki sake tuba ba. Don haka ki gaggauta ki sake tuba, ki kuma tsarkake niyyarki, Allah Zai taimake ki.

Wadannan kadan ke nan daga cikin irin tunanin wasu dangane da tuba. A karshe dai abin ya wajaba mu sani shi ne Allah Yana karbar tuban bayinsa gaba daya. Mai son karin bayani ya duba littafin Uridu An Atuba Walakin Na Sheikh Saleh Al-munajid, zai samu karin bayani.

A karshe, ina rokon Allah da kyawawan sunayenSa da siffofinSa madaukaka Ya kare mu daga fadawa cikin wannan bala'i da sauran abubuwan da Ya hana, wadanda kuma aka jarraba da yi, to Allah Ya shirye su, Ya sanya su tuba su koma kan hanya madaidaiciya.

Wassalamu alaikum warahmatullaahi wabarakaatuh!
 
 
 Posted By Aka Sanya A Monday, September 09 @ 00:53:43 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

"Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: