Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya ce duk wanda ya gode wa ni'imarSa, zai samu kari. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni gare su wajen samun abubuwan more rayuwar duniya da Lahira. Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, mun kwana bayan kawo misali da yabon da Allah Ya yi wa ManzonSa na farko Annabi Nuhu (Alaihis Salam), wanda aka ce bawa ne mai godiya. Sai kuma Hadisin da aka samo daga Anas bin Malik (Allah Ya yarda da shi), inda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, "Allah Yana murna da bawanSa, wanda idan ya ci ko ya sha wani abu, sai ya gode wa Allah saboda haka."

Yau ga ci gaba:

Haka nan Allah Ya umarci bawanSa, Annabi Musa (Alaihis Salam) ya riskar da abin da Ya ba shi na annabta da zancen da aka yi da shi, ya yi godiya a kan haka. Sai Ya ce, "Ya kai Musa! Lallai Ni na zabe ka a kan mutane da sakoNa da kuma zanceNa, don haka ka karbi abin da Na ba ka, kuma ka kasance cikin masu godiya." (Suratul A'raf, aya ta 144).

Ma'ana, Ubangiji Ya ce da Annabi Musa, ya kai Musa, lallai Na zabe ka a kan mutane da wahayin da Na aiko maka da kuma zancen da Na yi da kai, "….don haka ka karbi abin da Na ba ka…." na wannan wahayi, kuma ka kasance cikin bayi masu godiya. Bayi masu godiya kuwa su ne masu bautar Allah Shi kadai, ba tare da sun hada Shi da wani ba. (Tarjama da Sharhin Ma'anonin Alkur'ani Mai girma na Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, shafi na 529).

Haka nan dai Allah Ya yabi abokinsa na-gidi, na kut-da-kut (Khalil), Annabi Ibrahim (Alaihis Salam), saboda godiyar da ya yi a kan ni'imarSa, inda Allah Ya ce, "(Shi Ibrahim) Mai godiya (ne) ga ni'imominSa (Allah), Ya zabe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici." (Suratun Nahli, aya ta 121).

An ambaci Ibrahim saboda ya gode wa ni'imomin Allah domin Musulmi su yi koyi da shi wajen gode wa Allah ga ni'imomin da Ya yi ishara zuwa gare su a cikin wannan sura da watanta. Gode wa ni'ima (ita ma) wata ni'ima ce. (Alkur'ani Mai girma da kuma Tarjamar Ma'anoninsa Zuwa Ga Harshen Hausa na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, shafi na 412).

Sai kuma Allah Ya umarci AnnabinSa Dawud (Alaihis Salam) saboda yin godiya, a inda Ya ce, "….Ku aikata godiya, ya 'ya'yan Dawuda…." (Suratu Saba'i, aya ta 13).

A can gaban wannan aya, sai aka bayyana cewa: kissar Dawuda da ta Sulaiman (Alaihimas Salam), na nuna yadda Allah ke saukake wa bayinSa hanyar ibada da ta samun abinci da sauki, idan sun mayar da al'amuransu gare Shi. kissar Saba'awa (kuwa) tana nuna yadda Allah ke karbe wadata daga wanda ya kafirce maSa. (Tarjamar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, shafi na 649).

Haka nan Allah Ya umarci ManzonSa Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya yi godiya, sai Ya ce masa, "A'aha! Ka bauta wa Allah kadai, kuma ka kasance daga masu godiya." (Suratuz Zumar, aya ta 66). Wato manufa: Shi (Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam) da wadanda suka bi shi, suka yi imani da shi, sai su bauta wa Allah da gaskiya, Shi kadai ba tare da sun hada kowa da Shi ba a cikin bautar, kuma su kasance masu godiya ga Allah (din) a kan wannan baiwa da Ya yi musu na zama bayinSa na kwarai! (Tafsir Ibnu Kasir).

Sannan farkon wasiyyar da Allah Ya yi wa mutum ita ce ta ya yi godiya gare Shi, sannan iyayensa (shi mutum), sai Ya ce, "(Muka ce masa), "Ka gode Mini da kuma mahaifanka biyu. Makoma zuwa gare Ni kawai take." (Suratu Lukman, aya ta 14). Manufa, idan mutum ya bi wannan wasiyya, ya gode wa Allah, zai samu gwaggwabar lada da sakamako mai yawa.

Da ita wannan godiyar ce dai, Annabawa suka umaci mutanensu su yi, kamar yadda Ibrahim (Alaihis Salam), ya fada wa mutanensa cewa, "….Saboda haka ku nemi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta maSa, kuma ku yi godiya zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku." (Suratul Ankabut, aya ta 17). A tafsirin Ibnu Kasir, sai aka ce, "Wannan ya kara karfafa manufar a roki Allah Shi kadai kawai, kamar dai yadda aka nuna a surar Fatiha, aya ta 5, ‘Kai (kadai) muke bauta wa, kuma daga gare Ka (kadai) muke neman taimako.' Da kuma inda aka yi nunin addu'ar matar Fir'auna yayin da ta ce, ‘Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurinKa a cikin Aljanna…' (Suratut Tahrim, aya ta 11). Cewar da Allah Ya yi, ‘a nemi arziki…' yana nufin kada a nemi komai daga wurin kowa, sai wurinSa, domin babu wanda yake da wani karfi ko ikon yi ko hani, sai (Allah) Shi kadai. Saboda haka sai ku ci daga abin da Ya azurta ku da shi kuma ku gode maSa, don albarkar da Ya kwararo muku. Kuma ku tuna gare Shi ake mayar da ku, sai Ya saka muku da abin da kuka aikata, a Ranar Tashin kiyama."

Dukkan dangogin bauta, kamar Sallah, Zikiri, Addu'a da sauransu, hakkin Allah ne Shi kadai. Saboda haka Ya halicci mutum da aljan; kamar yadda a wurinSa kadai ake neman taimako cikin abin da babu mai yin sa sai Shi kadai, kamar azurtawa, dauke wata cuta, gafartawa da makamantansu. (Tarjama da Sharhin Ma'anonin Alkur'ani Mai girma na Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, shafi na 6).

Mafi falalar addu'a ita ce wadda aka yi wa Ubangijin taimako a kan abin da Ya yarda da shi na daga godiyar ni'imarSa da bauta gare Shi. Sheikhul Islam Ahmad Ibn Taimiyya, a cikin littafinsa Madarijus Salikin, mujalladi na 1, shafi na 78, ya ce, "Na hararo mafi amfanin addu'a, sai na gano ita ce a tambayi Mai taimako a kan abin da Ya yarda da shi, sannan sai na ga wannan abin a cikin surar Fatiha a cikin ayar, ‘Kai (kadai) muke bauta wa, kuma daga gare Ka (kadai) muke neman taimako.'

Yayin da makiyin Allah, Shaidan ya san girman matsayin godiya, wadda tana daya daga cikin mafi daukakar lamarin ibada (bauta) ga Allah kuma mafi muhimmancinta, sai ya sa matukar zirga-zirgarsa da kokarinsa wajen kange mutane daga barin ta.

Mu kwanan nan, sai mako na gaba, mu ga makircin Shaidan a wannan fanni na hana bayin Allah yin godiya. Allah Ya taimake mu, mu gode wa ni'imar da Ya yi mana. Amin.

Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!
 
 
 Posted By Aka Sanya A Monday, September 09 @ 01:22:30 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: