Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya ce duk wanda ya gode wa ni'imarSa, zai samu kari. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni gare su wajen samun abubuwan more rayuwar duniya da Lahira. Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, yau za mu ci gaba da mukalar tamu ne daga bayanin:

Makircin Shaidan wajen hana gode wa Allah

Yayin da makiyin Allah, Shaidan ya san girman matsayin godiya, wadda tana daya daga cikin mafi daukakar lamarin ibada (bauta) ga Allah kuma mafi muhimmancinta, sai ya sa matukar zirga-zirgarsa da kokarinsa wajen kange mutane daga barin ta.

Dubi abin da Shaidan din ya ce a lokacin da Allah Ya tsine masa (Ya nisantar da shi daga rahamarSa), bayan da ya bijire wa umarnin Allah wajen yi wa Annabi Adam (Alaihis Salam) sujada, bayan da Allah Ya kore shi daga cikin Aljanna. Farko dai ya roki a yi masa jinkirin rayuwarsa, aka yardar masa, sannan sai ya yi rantsuwa da halakarwar da aka yi masa, cewa sai ya tare wa bayin Allah hanyarSa madaidaiciya, kuma ya ce, "….Sannan kuma, hakika, ina je musu daga gaba gare su, kuma daga baya gare su, kuma daga jihohin damansu da jihohin hagunsu; Kuma ba za Ka samu mafi yawansu masu godiya ba." (Suratul A'raf, aya ta 17).

(Daga cikin malaman tafsiri da dama suka ce, cewar "…za Ka samu mafi yawansu ba za su zamo masu godiya ba," yana nufin da yawansu ba za ka samu suna da tauhidi ba, sai ka samu suna shirka, sai ka samu suna tsibbu, sai ka samu suna duba, ko sun yarda da masu duba.

Hadisi ya tabbata cikin Sunanun Nasa'i, Hadisi na 3,134, daga Sabrah Ibn Abu Fakih, ya ce, na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana cewa, "Shaidan ya zaune wa dan Adam dukkan wata hanya da zai bi, kowace hanya da dan Adam zai bi, to Shaidan yana zaune a kanta, yana neman hana shi bi, in dai hanyar alheri ce…." (Tarjama da Sharhin Ma'anonin Alkur'ani Mai girma na Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, shafi na 393-396)).

Daga nan Dokta Abdul Muhsin, ya ce:

Masu godiya (kan ni'imar da Allah Ya yi musu) 'yan kadan ne a cikin halitta, saboda haka sai ka yi kokarin kasancewa cikin wadannan 'yan kadan din, wadanda suke masu albarka, wadanda kuma su ne Allah Mai girma da daukaka Ya ce, "…kuma kadan ne mai godiya daga bayiNa." (Suratus Saba'i, aya ta 13).

Duk wata ni'imar da ba ta kusantar da wanda ya same ta zuwa ga Allah to, wannan ba ni'ima ba ce, bala'i ne. Malam Fudailu, wani daga cikin magabatan malaman Musulunci, (Allah Ya yi masa rahama), ya ce, "Na hore ku da lizimtar godiya a kan ni'imar Allah (komai kankantarta a ganinku); ku tuna abu ne mawuyaci (kadan ne kwarai), ni'imar da ta gushe daga wajen wadansu al'umma, ta komo gare su."

Saboda haka idan ka ga Ubangijinka Ya taimaka maka da ni'imarSa, kai kuma ka kama saba maSa, to lallai ka ji tsoronSa (domin idan Ya kama ka, to ba ka da wanda zai kubutar da kai). Shi bawan Allah, idan ya samu wani matsayi (ni'ima) daga wajen Allah, kuma ya tsare matsayin nan, ya doge ya mayar da hakali a kan tsarewar, sannan ya nuna godiyarsa ga Allah kan abin da Ya ba shi, babu shakka Allah Zai ba shi wani abin da ya fi wanda yake da shi. Idan ya wofinta (wulakanta ko ya raina) wannan matsayi (ni'ima) ya ki nuna godiyasa, to sai Allah Ya yi masa talala, har zuwa lokacin da Zai damke shi, ya rasa mafita! Ita ni'ima wani al'amarin ne da yake saduwa da godiya (wato yana cakude da ita), shi ya sa ma take hade da karuwa a koyaushe. Shi kuwa karin nan ba ya gushewa, har sai godiyar ta gushe, wato matukar ana godiya, to lallai ana tare da samun karuwa. Duk wanda aka azurta shi da yin godiya, lallai yana samun karuwar arziki. In dai ka gode, to babu shakka za a kara maka! Alkawarin Allah ba ya tashi, balle ya gushe!

Dubin abin da Allah, Mai girma da daukaka Ya ce, "Kuma (ka ambata) a lokacin da Ubangijinku Ya sanar, ‘Lallai ne idan kun gode, hakika, Ina kara muku, kuma lallai ne idan kun kafirta, hakika azabaTa, tabbas, mai tsanani ce." (Suratu Ibrahim, aya ta 7). Ashe godiyar nan, imani ne da kuma bin dokokin Allah da mayar da al'amari gare Shi, sai yadda Ya hukunta a bi, ta hanyar MazanninSa masu shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya, wadda Shaidan yake hawa kanta ya tsare bayin Allah kada su yi godiyar ni'imar da aka yi musu. Rashin godiya da butulci suna jawo azabar Allah!

A dalilin gode wa ni'imar Allah din nan da yi maSa biyayya, sai a yi wa bawan Allah budin duniya da Lahira. Komai sai ya zo masa cikin sauki. Allah Ta'ala Ya ce, "Kuma in da a ce mutanen da suka rayu a cikin alkaryu sun yi imani, kuma sun tsare dokokin Allah, lallai da Mun bude musu albarkatu na sama da kuma na kasa, sai dai sun karyata, Mu kuwa sai Muka kama su da irin abin da suka kasance suna aikatawa." (Suratul A'araf, aya ta 96).

Ubangiji Ya ce, in da a ce mutanen da suka rayu a cikin birane da dauloli ko alkaryu da suka shude a baya, sun yi imani kuma sun tsare dokokin Allah, yi-na-yi, bari-na-bari, "….da Mun bude musu albarkatu na sama da kuma na kasa…." Albarkatun sama ta hanyar ruwan sama; albarkatun kasa kuma ta hanyar tsairrai da amfanin gona da kayan abinci da kayan marmari da sauran ma'adinai da suke boye a karkashin kasa, duk sai Allah Ya bude musu su, Ya nuna musu inda suke, don su hako su ci moriyarsu, in da a ce sun yi imani da takawa. Allah Ya ce, sai dai mutane sun karyata Annabawa ne, sun karyata littattafan da aka saukar tare da Annabawan, "….Mu kuwa sai Muka kama su da irin abin da suka kasance suna aikatawa," na mugun aiki, na muguwar magana doriya a kan mugunyar magana irin tasu. (Tarjama da Sharhin Ma'anonin Alkur'ani Mai girma na Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, shafi na 488).

Mu kwana nan, sai mako na gaba, in Allah Ya nufe mu da kaiwa, za mu ga wani Hadisi game da matsayin godiyar nan, sai kuma mu kammala da yadda za a gode wa ni'imar Allah.

Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Monday, September 09 @ 01:27:49 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: