Muhawara Hausa
 

 

Tukuici ga mai azumi (4)
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Tukuici ga mai azumi (4)

Nafilfilin dararen goma na karshen watan Ramadan:

Daga A'isha (Allah Ya yarda da ita),ta ce: "Annabi (SAW), ya kasance idan goman karshe na watan Ramadan ya zo, to ba ya barci, sai ya tada mutanen gidansa maza da mata ya dukufa da nafilfili har karshen watan Ramadan." Buhari ya ruwaito.

I'itikafi:

Shi I'itikafi shi ne mutum ya zauna a masallaci don nafilfili da karatun AIkur'ani da zikiri da addu'o'i don neman dacewa daga Allah a duniya da Lahira. Shi kuma Sunnah ne da ake so, amma abin da aka fi so daga goman karshe na watan Ramadan. Kuma an ce karancinsa kwana daya da wuni, amma akasarinsa kwana uku. Awata ruwaya kuma an ce karancinsa kwana uku, amma mafi yawansa kwana goma har zuwa wata guda. Kowanne ka zaba daga cikin wadannan maganganu ya yi daidai. An karbo daga A'isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: Annabi (SAW) ya kasance yana I'ittikafi a kwana goma na karshen Ramadan har ya bar duniya.

Zakkar Fid-da-Kai:

ZakkarFid-da-Kai ita ce zakkar da ake yi idan aka gama azumin Ramadan, an ce ya halatta a fitar da ita kafin a gama azumi da wuni uku ko biyu, ko daya ko a daren Sallah ko ranar Sallah kafin a je masallaci. Domin an samu daga dan Abbas (RA) ya ce: "Annabi (SAW) ya wajabta mana Zakkar Fid-da-Kai don tsarkakke mai azumi daga miyagun maganganu da kuma kura-kurai. Kuma ciyarwa ce ga talaka. Wanda ya ba da ita kafin a je masallacin Idi ya samu ladar zakka cikakke, amma wanda ya ba da ita bayan dawowa daga masallacin Idi, wannan yana da ladar sadaka ce kawai."Abu Dauda ne ya ruwaito.

Ita Zakkatul Fidiri tana kan mai gida ne da wadanda suke karkashinsa kamar matarsa da 'ya'yansa maza da mata da ma'aikatan da suke karkashinsa.

Azumin da ake so mutum ya rika yi bayan na Ramadan:

1.Guda shida a watan Shawwal, domin Annabi (SAW) ya ce: "Wanda ya yi azumin watan Ramadan ya kuma yi shida a watan Shawwal, to, za a ba shi ladar wanda ya shekara yana azumi."

2. Azumin Litinin da Alhamis: Saboda Annabi (SAW) yana yawaita azumi ranar Litinin da Alhamis, sai aka tambaye shi yaya kake yawaita azumi ranar Litinin da Alhamis sai ya ce a ranakun ne ake daukar ayyukan bayi zuwa gaAllah.

3.Yin azumi uku kowane wata, ranar 13 da 14 da 15 ga kowane wata, kuma suna da lada kamar mutum ya yi azumin shekara ce. Domin duk wani aikin alheri za a ba ka lada goma.

4. Sai azumi guda tara da ake so mutum ya yi a watan Zul-Hajji da na Ranar Arfa. Idan mutum ba aikin Hajji yake yi ba.

5. Azumin Tasu'a da Ashura wato azumin ranar tara da goma ga watan Muharram, shi ne ake cewa azumin Tasu'a da Ashura.

Imam DSP Ahmad Adam Kutubi, 08036095723
Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)

Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)

Shi kuma Salam bin Abu Mudi'u ya ce: "kattada yana sauke Alkur'ani a (kwana ko dare) bakwai, amma idan Ramadan ya zo a kowane uku. Idan goman karshe suka zo, sai ya rika saukewa a kowane dare." (Siyar A'alamin Nubla'i, 5/276).

Rabi'u bin Sulaiman ya ce: "Imam Shafi'i ya kasance yana sauke Alkur'ani sau sittin a cikin watan Ramadan." (Siyar A'alamin Nubla'i, 10/36). Akwai misalan haka da dama.

Tsayuwar Ramadan:

An karbo daga Abu Huraira (RA) cewa: "Lallai Manzon (SAW) ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar Ramadan (Sallar Tarawihi ko Asham) yana mai imani kuma domin Allah kawai, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa." Buhari da Muslim suka ruwaito.

Aliyu bin Al-Madani ya ce: "Suwaidu bin Ghafalata ya rika yi mana limanci a tsayuwar Ramadan har ya kai shekara 120 a duniya." (Siyar A'alamin Nubla'i, 4/72).

Yin azumin Ramadan bisa imani kuma domin Allah kawai da yin nafilfilin dare bisa imani kuma domin Allah kawai da raya daren Lailaul kadari bisa imani kuma domin Allah kawai, suna sa mutum ya samu gafara da 'yantuwa daga wuta. Saboda Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya yi wadannan abubuwa uku an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa. Kamar yadda Buhari da Muslim suka ruwaito daga Abu Huraira.

Kafin mu karkare dan wannan rubutu, za mu tunatar da kanmu kan wasu hadisai guda biyu: Hadisi na farko shi ne wanda Manzon Allah (SAW) ya ce: "Idan watan Ramadan ya zo akan bude kofofin Aljanna a rufe kofofin wuta kuma a daure shaidanu." Muslim ya ruwaito a Babin Falalar Watan Ramadan, a duba Hadisi na 1079. Alkali Iyal ya ce: "Ana iya daukar bude kofofin Aljanna da abin da Allah zai bude ga bayinSa na su samu damar gudanar da ayyukan da'a a wannan wata, wadanda ba a samunsu a waninsa, kamar yin azumi da tsayuwar dare. Haka kuma kulle kofofin wuta da daure shaidanu na nufin hana mutane damar aikata ayyukan sabo." (An cirato ne daga Sharhin Muslim na Annawawi, 7/188).

Hadisi na biyu shi ne wanda Manzon Allah (SAW) ya ce: "Allah Ya turbude hancin mutumin da aka ambace ni a wurinsa, amma bai yi min salati ba. Allah Ya turbude hancin mutumin da Ramadan ya shigo sannan ya fita amma bai yi abin da za a gafarta masa ba. Kuma Allah Ya turbude hancin mutumin da tsufa ya riski iyayensa suna tare da shi, amma ba su yi sanadin shigarsa Aljanna ba (saboda rashin kyautatawarsa gare su)" (Tirmizi Hadisi na 3545 da Ahmad Hadisi na 7402, kuma Ibnu Khuzaima ya ruwaito makamancinsa, Hadisi na 1888).

'Yan uwa da wannan ya kamata wadannan Hadisai biyu su tayar da tsiminmu wajen ganin mun yi tilawar Alkur'ani da tsayuwar dare da sauran ayyukan alheri a cikin wannan wata mai albarka, domin neman yardar Allah kawai, ba domin riya ko jiyarwa ba.

A karshe muna yi wa 'yan uwa masu yin tahajjud cikin lasifika suna hana sauran mutane yin barci, su yi kokari su guji hakan, domin kada garin neman lada a samu zunubi. Saboda sallar dare ana so ne mutum ya yi ta a boye, a lokacin da sauran mutane suke barci. Idan aka bude lasfika ya zamo an tashi mutane daga barci ke nan, kuma hana mutane barci ko Musulmi ko wadanda ba Musulmi ba, ya saba wa koyarwar Musulunci. Mutane suna da 'yancin yin barci Musulmi ko wadanda ba Musulmi ba a cikin dararen watan Ramadan, kada a tashe su saboda ibadar da Musulunci ya fi so a yi ta a boye.

Zakar Fidda Kai:

Zakkar Fidda Kai ko Zakkar Kono kamar yadda wadansu ke fada. Kalmar zakka a lugga tana nufin tsarki da karuwa da yabo da albarka. Wadannan kalmomi duk Alkur'ani ya yi amfani da su. Kalmar Fitr a lugga kuma tana nufin bude wani abu, kuma daga nan ne aka jinigna ta ga mai azumi saboda yana bude bakinsa domin cin abinci.

A shari'a kuma Zakkatul Fitri na nufin zakkar da ake bayarwa bayan kammala azumin Ramadan.

Zakkar Fidda Kai, Sunnah ce ta Manzon Allah (SAW), Allah Ya farlanta azumi, shi kuma Manzo (SAW) ya farlanta zakka bayan kammala azumin. Bin Manzon Allah (SAW) kuma bin Allah ne, saboda Allah Madaukaki Ya ce: "Abin da Manzon (Allah) ya zo muku da shi, ku rike shi, kuma abin da ya hane ku, to ku hanu." (Hashri:7). Kuma Allah Ya sake cewa: "Wanda ya yi da'a ga Manzon (Allah), hakika ya yi da'a ga Allah." (Nisa'i: 80).

 Posted By Aka Sanya A Monday, September 09 @ 02:20:20 PDT Da MediaHausaTeamComments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

"Tukuici ga mai azumi (4)" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com