Muhawara Hausa
 

 

Layya da hukunce-hukuncenta
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen Layya da hukunce-hukuncenta

Abin da ake cewa Layya shi ne duk wani abu da aka yanka domin neman kusanci ga Allah. Layya na da asali a cikin Alkur'ani da Hadisin Annabi (SAW). Allah (TWT) Yana cewa: "Ka yi Sallah ga Ubangijinka kuma ka yi yanka." (Kausar: 2) A Hadisi kuwa Anas Bin Malik (RA) ya ruwaito cewa: "Manzon Allah (SAW) ya yi Layya da raguna biyu bakake, masu kahonni. Ya yanka su da hannunsa, ya yi bisimillah ya yi kabbara, ya kwantar da su ta gefensu." (Muslim).

A shekara ta biyu Bayan Hijira aka shar'anta yin Layya kuma sunnah ce mai karfi a kan:

1. Musulmi da, namiji ko mace. Tana zama sunnah a kan mutum ga kansa da iyayensa, idan talakawa ne, da 'ya'yansa maza da ba su balaga ba ko mata da ba su yi aure ba. Ba sunnah ba ce mutum ya yanka wa matarsa ko dansa da aka haifa a ranar Layyar.

2. Kada ya kasance mahajjaci, domin shi mahajjaci, hadaya ce a kansa.

3. Ya zama ba matalauci ne ba, da ke cikin tsananin bukata. Amma zai iya cin bashi ya yi Layyar, idan ya san zai iya biya, ba tare da takura ba. Wasu malamai sun ce kada mutum ya ci ba shi domin yin Layya.

Dabbobin da ake yin Layya su ne: Rago wanda ya shekara, taure sai ya shiga shekara ta biyu. Sa, wanda ya shekara uku, rakumi sai ya kai shekara biyar. A wajen Layya, rago ya fi falala, sai taure, sai sa, sai rakumi. A cikin dukkan dabbobin an fi fifita maza a kan matansu da lafiyayyunsu (wadanda suke yin barbara) a kan fidiyayyuns, sai idan fidiyayyun sun fi kitse sai a yi da su.

Sharuddan ingancin Layya

1. Dole ne a yi yankan da rana, bai inganta a yanka da dare ba.

2. Mai yin yankan dole ne ya zama Musulmi,yankan kafiri bai halatta ba.

3. Bai halatta mutane da yawa su hadu a cikin kudin dabbar Layya daya ba. In kuma suka hada kudi suka saya suka yanka, ba ta zama Layya ba. Amma idan daya daga cikinsu ya biya saura kudinsu, shi ya kadaita da dabbar, a wannan lokacin ya halatta ya yi Layya da ita. Kuma ya halatta ga mai Layya ya sanya wani ko wadansu cikin ladan Layyar, kafin ya yanka, ba bayan ya yanka ba. Koda kuwa wadanda zai sa a cikin ladan sun wuce bakwai da sharuddan:

a) Ya kasance wanda zai saka cikin ladan na kusa da shi ne. kamar da, dan uwa, dan ammi ko matarsa.

b) Ya kasance wanda zai shigar cikin ladan Layyar, wanda ciyar da shi ya wajaba a kansa ne. Ko kuma dai shi yake ciyar da shi.

c) Ya kasance suna zaune tare a gida daya.

Idan wadannan sharuda suka tabbata, Layya ta fadi daga kan wanda aka shigar cikin Layyar. Ana bukatar wadannan sharudda ne idan zai shigar da wasu mutane cikin Layyarsa ne. Amma idan su kadai zai yi Layya a ware ban da shi a ciki, ya inganta ya yi. Ba sai da cikar wadancan sharudda da aka ambata ba. Ya halatta a yi gamayya a cikin Layya idan dabbar Layyar ta zama rakumi ko saniya. Amma kada adadin masu gamayyar ya wuce bakwai. Idan suka wuce bakwai, bai halatta ba. Dalili a nan shi ne Hadisin Jabir (RA) da yake cewa: "Mun yi Layya tare da Manzon Allah (SAW) a shekarar Hudaibiyya, kowace taguwa mutum bakwai, saniya ma mutum bakwai" (Muslim).

4. Dole ne dabbar Layyar ta kasance ta kubuta daga cututtuka ko aibubbuka da suke a fili. Saboda Hadisin Bara'u (RA), daga Manzon Allah (SAW) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya mike tsaye a cikinmu ya ce: "Dabbobi hudu bai halatta a yi Layya da su ba. Mai ido daya wadda rashin idon ya fito fili. Marar lafiya, wadda rashin lafiyarta fito fili. Gurguwa, wadda gurguntakarta ta fito fili, wadda ta karye a kafa da kuma wadda ba ta da bargo" (Abu Dauda ya ruwaito), da kuma Hadisin Aliyu (RA) cewa: "Annabi (SAW) ya hana a yi Layya da dabba mai gutsurarren kunne da guntulallen kaho" (Abu Dauda). Ba zai yiwu a yi Layya da dabbar da ta zama mai ido daya, ko mara ido, koda akwai alamun idon. Haka ba za a yi da mai guntulalliyar kafar gaba ko ta baya ba, ko marar ji ko mai warin baki ko wadda ba ta yin kuka ko marar bargo ko mai gutsurarren bindi ko marar lafiyar da rashin lafiyarta ya fito fili ko mahaukaciya, madauwamin hauka, ko gurguwa ko ramammiya. Dukkan abubuwan da aka ambata a baya, idan masu sauki ne, babu laifi, sai a yi Layya da ita. Haka nan bai halatta a yi Layya da dabbar da kahonta ya karye yake yin jini ba. Ko wadda kashi daya daga cikin uku na bindinta ya gutsure. Amma idan wanda ya gutsure bai kai haka ba, babu laifi. Haka wadda ta rasa hakora biyu ko fiye domin yarinta ko tsufa. Amma idan hakori daya ne babu laifi. Haka idan fiye da kashi daya cikin uku na kunnenta ya tsage, ba a Layya da ita. Kubutar dabba daga aibubbukan da aka ambata sharadi ne na ingancin Layya. Idan mai yin Layya bai lura da wani aibi da yake jikin dabbar Layyarsa ba, sai bayan ya yanka, sai ya yi sadaka da kudin lamunin da zai amso daga wajen wanda ya saida masa da dabbar ko kuma kimar kudin lamunin. Domin ita Layya sai an yanka ta take wajaba. Ba ta wajaba da niyya ko warewa.

Lokacin yanka Layya

Lokacin yankan Layya yana farawa ne daga lokacin da Liman ko shugaba ya yanka tasa dabbar Layyar. Liman zai yanka dabbar Layyarsa ne bayan sallame Sallar Idi da gama hudubarsa. Idan kuma Liman ba ya da abin Layya, in ya gama Sallah da huduba sai ya umarci jama'a kowa ya je gida ya yanka abin Layyarsa. Lokacin yin yankan yana zarcewa har zuwa faduwar ranar kwana ta uku daga kwanakin yanka. Barra'u (RA) ya ruwaito cewa: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Wanda ya yi yanka bayan an yi Sallah ya cika yankarsa, kuma ya dace da Sunnah" (Buhari ya ruwaito), sai wanda Jundubi bin Sufyan Al-Bajli ya ruwaito cewa: "Na kasance tare da Annabi (SAW) a ranar yanka, sai yake cewa: "Wanda duk ya yanka kafin a yi Sallah, to, ya yanka wata a madadinta, wanda kuwa bai yanka ba, to, ya yanka." (Buhari ya ruwaito). Wanda lokacin yankan da aka ambata a sama ya kubuce masa, ba zai yi ramuwar yankan a wani lokaci ba. Idan Liman ba tare da wani uzuri ba, ya yi jinkirin yanka Layyarsa, sai a dan saurara gwargwadon lokacin da zai isa a yi yankan bayan gama Sallah. Idan akwai uzurin da ya sa ya jinkirta yanka Layyar, sai jama'a su saurare shi har zuwa kusa da zawali, ta yadda gwargwadon yankan ne kawai zai saura ga zawali, sai kowa ya yanka Layyarsa. Idan ba a yin Sallar Idi a gari, sai mutanen garin su kintaci idar da Sallah da hudubar gari mafi kusa da su. Kuma babu wani laifi, koda ta bayyana cewa sun riga limamin wancan gari da suka kintata wajen yanka Layyar.

Abin so ga mai yin Layya:

1. Kada ya aske duk wani gashi daga jikinsa ko yanke farce da zarar wata ya kama har sai ya yi Layya. Duk daya ne ko shi ne zai yi Layyar ko za a saka shi cikin ladanta ne. Saboda Hadisin da Ummu Salma (RA) ta ruwaito cewa Annabi (SAW) ya ce: "Idan goma (ta watan Zul-Hajji) ta fara, alhali kuma dayanku yana da niyyar yin Layya, kada ya shafi wani abu daga gashin jikinsa." (Muslim)

2. Ya yanka abin Layyarsa da kansa. Namiji ne ko mace ko yaro, saboda yin koyi da Annabi (SAW). An karbo daga Anas (RA) cewa "Manzon Allah (SAW) ya yanka taguwoyi bakwai da hannuwansa a tsaye" (Abu Dauda ya ruwaito). Abin ki ne mutum ya wakilta wani ya yanka masa, matukar dai zai iya yankawa da kansa.

3. Ya hallata mutum ya ci, ko ya yi sadaka ko ya yi kyauta da naman Layyarsa, ba tare da iyakancewa ba.

Muntasir Umar F/Kano 0803774701

 Posted By Aka Sanya A Monday, September 09 @ 02:43:36 PDT Da MediaHausaTeamComments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

"Layya da hukunce-hukuncenta" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com