MUTANE DA DABBOBI SUN YI KAMA ( 1 )
 
Wannan Labari Ya fito Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
URL na Wannan Labari Shine:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=800

 
Dr. Mansur Sokoto

Mutane Da Dabbobi Sun yi Kama ( 1 )
'Yan uwana Assalamu Alaikum.

Da yawa daga cikinmu sun taba karanta wannan ayar – koma in ce, sun sha karanta ta – inda Allah yake cewa:

"Babu wata dabba mai tafiya a doron kasa, ko wani tsuntsu da yake tashi da fukafukansa face suma al'ummomi ne masu kama da ku.

Ba mu rage kome daga wannan littafi ba.

Sannan zuwa ga Ubangijinku ake tattaraku" [Al- an'am:38].

Amma kadan ne daga cikin masu karanta wannan ayar suka tsaya cikin nutsuwa suka yi tunani game da sirrin da yake cikin wannan ayar. Ka dubi ayar sarai, ka kula da abin da Allah ya nuna a cikinta, na cewa dabbobin da suke tafiya a kan doron kasa da masu tashi a sararin sama'u, duk al'ummomi ne masu kama da mu, mu mutane. Ta ina ne dabobi da tsintsaye suka yi kama da mu?
Malamai a baya sun yi kokarin fito da fiskokin kamanceceniya tsakanin mutum dan Adam da wasu dabbobi.

Daga cikin abin da wasu malamai suka fada ya hada da cewa; 1) Dabbobi da tsintsaye suma suna da sunayen a tsakaninsu kamar yadda kowane mutum yake da suna.

2) Wasu kuma malamai suka ce, Suma suna tasbihi kamar yadda mutane ke yin tasbihi ga Allah. Ta nan ne suka yi kama da mutane.

3) Wasu kuma suka ce, ai suma za a ta she su ne ranar kiyama a yi musu hisabi kamar yadda za a yi wa mutane.

4) Wasu suka ce, suma suna fita neman abinci kamar irin yadda mutum yake fita neman abinci.

To haka dai kowane malami yi yi ta kokarin kawo bayaninsa don fito da yanayin da dabbobi da tsintsaye suka yi kama da mutane.

To ana cikin ruguntsumin gano hakikanin abin da wannan sirri na al'kur'ani ya kunsa, sai kwatsam ga Mal.

Sufyanu bn Uyainah ya bayyana ta shi fassarar da Allah ya yi masa budi da ita. Lokacin da ya ji wannan aya sai ya kada baki ya ce, "Ai babu wani mutum dan adam face yana da takwaransa a cikin dabbobi. Akwai wanda shi kamar zaki yake, ba ya barin ko-ta-kwana.

Idan aka ce da shi kule, to kuwa zai ce, cas!

Akwai kuma wanda yake tamkar Kyarkeci yake, nan da nan ya kai sura da farmaki na ta'addanci. Sannan ga wani shi kuma kamar Kare yake, ban da haushi ba abin da ya iya.

Wani shi kuma sai karairaya da takama kamar Dawisu".

Kai a nan nima bakina ya zo daya da na malam Al-Khattabi, yayin da yake jinjinawa Mal. Ibn Uyainah akan wannan nasara da fatahi da ya samu wajen kara gano asirin wannan aya. Ya kara da cewa, "wannan bayani da sufyanu ya yi game da wannan aya ya yi matukar kyau. Domin kuwa ita magana idan aka lura zahirinta ba zai yi ma'ana ba, to wajibi ne abinciki sirrinta, domin kuwa dukkanmu mun kwana da sanin cewa, zahirin halittar bil-adama ba ta yi kama da ta tsutsu ko dabba ba. To ka ga akwai wani sirri ke nan a karkashin wannan aya".

– Shaykh Dr. Muhd Sani Umar



 

Batu: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai


Comments 💬 التعليقات