Matsara Wasu Yan Bidi'ah Da Wasu Kafurai Ta Yi Matukar Kama Game Da Khawaar
 
Wannan Labari Ya fito Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
URL na Wannan Labari Shine:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=900

 
Ibrahim Jalo Jalingo

Matsara Wasu Yan Bidi'ah Da Wasu Kafurai Ta Yi Matukar Kama Game Da Khawaarijan Boko-Haram

Matsayar wasu daga cikin 'yan bidi'ar kasan nan, da wasu daga cikin kafuran kasan nan ta yi matukar kama game da abin da ya shafi Khawarijawan Bokoharam.

Dalili kuwa shi ne:-
1. Wasu daga cikin kafuran wannan Kasa tamu suna nan suna ta cewa: Dukkan wani musulmi dan bokoharam ne! Dalilinsu na nazari a kan wannan ikirari shi ne: 'Yan bokoharam da sauran musulmai Annabinsu daya ne, Alkur'aninsu daya ne, matsayarsu game da rukunai biyar din nan na Musulunci daya ne, matsayarsu game da dukkan wani mutumin da bai yi imani da Alkur'ani da Annabi ba daya ne! A dai nazarce su kan iya lissafa abubuwa da yawa bayan wadannan da aka ji yanzu kuma su ce 'Yan bokoharam da sauran Musulmin Kasar nan ba su da wani sabani ko banbanci a cikinsu!!

Wasu daga cikin 'yan bidi'ar wannan Kasa tamu suna nan suna ta cewa: Dukkan wani Ahlus Sunnah a wannan Kasa tamu dan bokoharam ne! Dalilinsu na nazari a kan wannan likirari nasu shi ne: 'Yan bokoharam da sauran Ahlus Sunnah sun yarda da Kitaabut Tauheed na Sheikh Muhammad Bin Abdil Wahhab, kuma dukkansu sun yarda da littattafan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah, kuma dukkansu suna kiran kansu Ahlus Sunnah Wal Jama'ah! A dai nazarcen su kan iya lissafa wasu abubwa da yawa bayan wadannan da kuka ji, sannan su ce 'yan bokoharam da sauran Ahlus Sunnan Kasar nan ba su da wani sabani a cikinsu!!
Lalle idan kafirci, ko bidi'ah suka yi tsatsa a cikin zuciyar mutum to kuwa babu irin wata wauta sakarci da ba zai iya furtawa da bakinsa ba, ko ba zai iya kudurtawa a cikin zuciyarsa ba, ko ba zai iya rubutawa da alkalaminsa ba!!

Allah muna rokon Ka da Ka tausaya wa wannan Al'ummah tamu Ka dora ta a kan sunnar AnnabinKa mai tsira da amincin Allah, a cikin Aqeedah, da Ibadah, da kuma Mu'amalah. Ameen.

KULLUM TURAWA KOKARINSU SHI NE SU WAUTAR DA HANKULAN MUSULMI

1. Har kullum Turawa ta kafofin yada labaransu kokari suke yi su wautar da hankulan al'ummar Musulmi. Babban misali a kan wannan mugun manufa tasu shi ne abin nan da suke yayatawa cikin kafofin yada labaransu cikin kwanakin nan bayan 'yan ta'addan kasar Masar sun kai hari a wani masallacin juma'a a yankin Sinai a inda suka kashe masallata kusan 300. A inda suka yi ta yada cewa: 'Yan ta'addan sun kai wa Masallatan harin ne saboda su Masallatan Sufaye ne su!!
2. Gaskiyan al'amari cikin wannan mas'ala shi ne: Su wadannan 'Yan ta'adda suna kashe dukkan mutanen da ba su yarda da manufofinsu ba ne sawaa'un Sufaye ne su ko kuwa wasun Sufaye ne su, tabbas wannan shi ne hakikanin abin da kowa yake iya gani cikin dukkan wata kasa da su wadannan 'Yan ta'adda suke yin ta'addanci a cikinta.
3. Allah Ka tsare wannan Al'ummah Muhammadiyyah daga fadawa cikin tarkon da Turawa ke ta nada mata har kullum domin ta fada cikinsa ta halaka. Ameen.

WAYE DR IBRAHIM JALO JALINGO?

Dr Ibrahim Muhammad Jalo Jalingo an Haife shi a garin Muri dake Jahar Taraba, yayi karatun sa na allo da na Addini a gun Mahaifinsa da Mahaifiyarsa, yayi Primary da Secondary a Garin Sung, yayi diploma a Jami'ar Bayaro kano, ya wuce Jami'ar Musulunci ta Madina yayi Karatu a Fannin Fikhu.
''
Kuma kafin ya tafi Jami'a ya sauke littafin Ahlari, Ishmawi, Iziya, Risala, Askari, Muktasar.
''
A bangaran wakoki ya sauke littafin Daliya, Shariya, muktaril shi'iri jahili, Mukamatul hariri.
''
A bangaran Nahau ya sauke Addurusin Nahawiya, Nahaul wadhi, Alfiyatu bin Malik.
''
Duk takamar ka da ka karanta Nahau ba ka wuce Alfiyatu bin malik ba. To tun Dr be je Jami'a ba ya karanta.
''
Duk takamarka ka karanta Fikhu baka wuce Muktasar Khlili ba. Dr ya karanta tun be je Jami'a ba.
''
Duk takamarka ka karanta lugga baka wuce Mukamatul hariri ba. Dr ya karanta tun be je Jami'a ba.
''
Dr Ibrahim Jalo Jalingo yayi degree din sa na 1 a Fannin Fikhu, Yayi Degree na 2 a Fannin Fikhu, Yayi Degree na 3 wato P.H.D a Fannin Fikhu.
''
A tsarin karatun Jami'ar Musulunci ta Madina ba a daukar mutum yayi masters sai yana da Mumtazi ma'ana sai yanada 4.75 a madadin 4.5 a Jami'oin kasar mu nigeria, kuma a cikin wayanda suke da 4.75 ma sai an sake musu jarabawa don a kara tace a reraye kafin mutum ya samu daman yin degree 2, shi ma ba za a bawa mutum daman yayi degree 3 ba wato P.H.D sai an tabbatar yanada Inmtiyadi zuwa sama.
''
Wannan shine Dr Ibrahim Muhammad Jalo Jalingo.
''
Ka gaya min ta yaya Jahili zai tsallake wannan Matsayin har ya kai Dr ba a gane Jahili ba ne sai kai dan tashi zaka gane?
Wannan bayanin ya fito ne daga marigayi Sheik Dr. Alhassan Sa'id Adam Jos.


 

Batu: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai


Comments 💬 التعليقات