Muhawara Hausa
 




EsinIslam Media: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Bincike Akan Wannan Batun:   
[ Jeka Gidan Dandalin Watsa Labarai | Zaɓi Sabon Taken ]

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

It's Haram To Aid, Promote Or Participate In The Oodua Nation Agitation
(Labarin Cikakkun... | 2035 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)




(Labarin Cikakkun... | 2035 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tauhidi ginshikin Musulunci (5)
(Labarin Cikakkun... | 6053 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tauhidi ginshikin Musulunci (5)

Ba zan iya amfana muku komai a wajen Allah ba". Sai ya kira Abbas (xan baffansa) ya ce, "Ba zan iya amfana maka komai a wajen Allah ba". Sai ya kira Safiyya (‘yar uwar mahaifiyarsa) ya ce, "Ba zan iya amfanar maki komai wajen Allah ba". karshe kuma sai ya kira 'yarsa ya ce, "Ya Fatima, idan kina da bukata ta dukiya, ki tambaye ni abin da kike so. Idan ina da shi zan ba ki, amma ba zan iya amfana miki komai wajen Allah ba."

BABI NA GOMA SHA SHIDA

Abin da ke faruwa ga Mala'iku Idan Allah ya yi magana Idan Allah (S.W.T) Ya yi magana Mala'iku sukan tsorata har ma su suma. Domin haka ne Allah Ya ba da labari a cikin Suratul-Saba, "Idan aka zare wannan tsoron daga zukatansu (Mala'iku) sai su ce wa Jibrilu, ‘me Ubangji Ya faxa?" Sai Jibrilu ya ce ‘Allah Ya faxi gaskiya, domin Shi Maxaukaki ne, Mai Girma".

An samu Hadisi daga Abu Huraira, Annabi (S.A.W) ya ce, "Idan Allah Ya hukunta wani al'amari a sama, Mala'iku sai su faxi da fukafukansu don kaskantar da kai ga zancen Allah domin suna jin maganar kamar wata sarka ce aka ja a kan falalen dutse. Wannan karar tana sanya su suma har idan suka farka daga wannan sumar sai su ce ‘me ubangijinmu Ya faxa?" Sai Jibrilu ya ce, ‘Allah Ya faxi gaskiya domin Shi ne Maxaukaki, Mai Girma'. To a wannan lokaci ne aljannu masu satar ji suke satar ji, kuma su faxa wa na kusa da su. Har ma lokacin da Sufwan yake siffantawa sai ya buxe tsakanin yatsunsa, wani a kan wani ya ce haka suke yi. Watau na sama ya faxawa na kasa da shi har su faxa wa boka ko xan duba. Shi kuma idan ya tashi zai faxa sai ya kara karya xari.


(Labarin Cikakkun... | 6053 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tauhidi ginshikin Musulunci (4)
(Labarin Cikakkun... | 11932 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tauhidi ginshikin Musulunci (4)

Babi na Goma Sha daya

Ba a yanka domin Allah a wurin da ake yanka domin wanin Allah

Allah Ya ce, "kar ka je ka yi sallah a wannan masallacin har abada, domin masallacin da aka gina shi a kan tsoron Allah tun ranar gininsa shi ya fi dacewa ka yi sallah a ciki domin akwai mazaje muminai a cikinsa wadanda ke kaunar su tsarkaka. Allah kuma Yana son masu son tsarkakuwa." (Taubah, 108) 8

Babi na Goma Sha Biyu

Shirka ne yin alwashi domin wanin Allah

Allah Ya ce, dagane da sha'anin muminai, "Su ne wadanda suke cika alwashinsu, kuma suna tsoron wata rana wacce take sharrinta mai fantsama ne". (Al-Insan, 7). Amma awata aya sai Allah Ya ce, "Duk abin da kuke ciyarwa ko kuka yi alwashin bakance, hakika Allah masani ne a kansa." (Bakara, 270).

An samu Hadisi daga A'isha (R.A) cewa Annabi (S.A.W) ya ce, "Wanda ya yi alwashin zai bi Allah to ya yi kok arin daurewa domin biyayaya ga Allah. Amma wanda yayi alkawarin zai sabawa Allah, to ya bari kar ya sabawa Allah din".


(Labarin Cikakkun... | 11932 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tauhidi ginshikin Musulunci (2) - (3)
(Labarin Cikakkun... | 6784 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tauhidi ginshikin Musulunci (3)

Sanya kambu da guru da laya da makamantansu don dauke wata cuta ko tunkudeta, shirka ne Allah Ya ce, "Ku b ani labarin abin da kuke kira ba Allah ba, yanzu idan Allah Ya nufe ni da wani ciwo za su iya warkar da ni, ko Allah Ya nufe ni da wata rahama da za ta same ni, shin za su tare wannan rahamar ba za ta same ni ba? To ka ce, ni dai Allah ne madogara na kuma gareShi duk masu dogara suke dogara." (Zumar, 38).

An ruwaito daga Imrana dan Husaini (R.A) ya ce, Annabi (S.A.W) ya ga wani mutum sanye da kambu na farin karfe sai Annabi ya ce, "mene ne wannan?" Sai ya ce ai maganin shawara ne. Sai Annabi ya ce, "To cire ta, ba za ta kara maka komai ba sai rauni. Kuma wallahi da ka mutu da wannan kambun a jikinka da ba ka da rabo har abada." (Imam Ahmad ya ruwaito).

An samu wani Hadisi daga Ukbata dan Amru shi kuma ya karbo daga Annabi (S.A.W). Annabi ya ce, "Wanda ya rataya laya, to kar Allah ya biya masa bukatarsa. Wanda kuma ya rataya wuri, kar Allah Ya yi masa maganin abin da ya rataya dominsa". A wata ruwaya Annabi cewa ya yi, "Duk wanda ya rataya laya to ya yi shirka da Allah" kamar yadda aka samu daga Abi Hatim shi kuma daga Huzaifa; wata rana ya ga wani mutum yana sanye da zare wanda aka yi guru da shi wai maganin zazzabi, sai ya tsinke wannan zaren, sai ya karanta masa ayar Al-kur'ani inda Allah Yake cewa, "Yawancin wadanda suka yi imani da Allah sai a same su kuma suna shirka da Allah." (Yusuf, 106).


(Labarin Cikakkun... | 6784 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tauhidi ginshikin Musulunci (1)
(Labarin Cikakkun... | 6368 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tauhidi ginshikin Musulunci (1)

DSP Imam Ahmad Adam Kutubi

Yau cikin yardar Allah za mu fara tsakuro wani abu ne daga littafin Kitabut Tauhid da DSP Imam Ahmad Adam Kutubi ya fassara kuma ya aiko mana muna fata za a karu da abin da littafin yake karantarwa; Bismillah:

Babi na daya

Dalilin halittar mutum da aljan:

Allah Ya ce a cikin Alkur'ani Mai girma, "Ban halicci mutum da aljan ba, sai don su bauta Min. Ba Na bukatar wani arziki daga gare su, kuma ba Na neman su ciyar da Ni. Lallai ne Allah, Shi ne Mai azurtawa kuma Ma'abucin karfi." (Zariyati, 56-58). A wata aya kuma Allah Yana cewa, "Hakika kowace al'umma Mun aika mata da wani Manzo a kan su bauta wa Allah su nisanci dagutu." (Nahli, 36). Ma'anar dagutu, duk wani abin da ake bautawa ba Allah ba, kamar Mala'iku ko Annabawa ko aljanu ko waliyai ko salihai da sauransu.

A wata aya kuma Allah Yana cewa, "Hakika Allah Ya yi horo a kan a bauta maSa Shi kadai, kuma a kyautata wa iyaye biyu. Koda dayansu ya tsufa ko dukansu biyu, idan magana ta tashi tsakaninka da su, kada ka ce musu tir, kada kuma ka yi musu tsawa. Ka yi musu magana kyakkyawa ka tausasa musu, kuma ka nuna kai ba komai ba ne a gabansu. Idan kuma za ka yi musu addu'a, sai ka ce, ‘Allah Ka jikan mahaifana kamar yadda suka raine ni tun ina karami har na girma." (Isra'i, 23). Kuma a wata ayar, sai Allah Ya ce, "Ku bauta wa Allah Shi kadai, kada ku hada Shi da kowa." (Nisa'i, 36).


(Labarin Cikakkun... | 6368 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)
(Labarin Cikakkun... | 5942 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)

Tambaya: Mene ne hukuncin wuce Mikati ba tare da Harama ba,?

Amsa: Hakan ya halatta, matukar cewa ba ka zo ne da niyyar yanka ba, ya halatta ka shiga Makka ba tare da Harama ba, idan ka zo ne ba da niyyar Umara ko Hajji ba, kawai dai ka zo ne don wani dalili naka kamar neman ilimi ko duba mara lafiya, ko kasuwanci, kai ko ma a ce hanya ce ta biyo da kai, wannan babu komai a kanka. Wanda dole sai ya shiga da Harama shi ne wanda ya zo don aikin Hajji ko Umara, idan ya wuce ba tare da ya yi Harama ba, to sai ya zubar da jini, ma'ana sai ya yi yanka.

Tambaya: Ni mutumin kasar Sa'udiyya ne ina aiki a wajen kasar, a watan azumi na zo, iyalaina suna Jiddah, na fara sauka a wajensu na yi kwana uku, daga baya na yi Haramar yin Umara, shin ina da laifi?

Amsa: Wannan zuwa ka zo ne don iyalanka, sai bayan ka je gida sannan ka yi niyyar yin Umara, yin haka babu laifi, sai ka yi Harama a Jiddah kamar yadda mutanen Jiddah za su yi.

Tambaya: Ni ma'aikaci ne ina aiki a Riyad, sai na zo Jiddah don yin fasfo, bayan na gama abin da nake sai na yi niyyar yin Umara, na yi Harama daga Jiddah, bayan kwana uku na sake yin wata Haramar don yi wa mahaifiyata Umara, na yi Harama daga Mikatin Nana A'isha, sai kuma na yi niyyar yi wa mahaifina da ma wadansu mutane daban Umara, tare da cewa mahaifina da mahaifiyata sun rasu, shin abin da na yi niyya ya halatta?


(Labarin Cikakkun... | 5942 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)
(Labarin Cikakkun... | 6565 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)

Tambaya: Mene ne hukuncin mutumin Makka wanda yake so ya yi Umara, zai yi harama daga gidansa ne ko sai ya je Tan'im ko Ja'aran zai daura harami?

Amsa: Bai halatta ya yi harama daga gida ba, idan ya yi haka sai ya yi yanka (fidiya), sai dai ya yi harama daga Hillu, domin ko a ina bangaren gidansa yake abin da ake so shi ne ya fita wajen gari ya yiwo harama daga can.

Tambaya: Mu mutanen Makka ne, mun saba kowane watan Ramadan muna yin Umara amma daga gidajenmu muke daukar Harama, sai kuma mu tafi Tan'im mu dauki niyya, shin hakan da muka yi ya yi ko dole sai a Tan'im za mu daura Harami ?

Amsa: Abin da kuka yi ya yi babu laifi, matukar cewa ba ku yi niyyar Umara ba sai a Hallu, to hakan ya halatta, insha Allah babu laifi.

Tambaya: Matata ta zo daga Gabas da dadewa ba ta yi Umara ba, sai yanzu take so ta yi, shin sai na mayar da ita inda Mikatinsu yake ta yi Harama, ko ta yi Haramarta a Makka tunda a nan muke a zaune ?


(Labarin Cikakkun... | 6565 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (1)
(Labarin Cikakkun... | 4755 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (1)

Tambaya: Shin wajibi ne ga mai iko duk shekara sai ya yi aikin Hajji, ko kuwa sau daya ne yake wajibi?

Amsa: Ba dole ba ne sai an yi duk shekara, na wajibi sau daya ne a rayuwa. Koda kuwa mutum yana da iko, ba ya zama dole a kansa, kamar yadda ya zo a cikin Hadisai da dama cewa Manzon Allah (SAW) ya tara mutane ya yi musu Huduba ya kwadaitar da su kan aikin Hajji. Sai wani Sahabi mai suna Akara'u dan Habis ya mike ya ce: "Ya Ma'aikin Allah shin duk shekara sai an yi? Sai ya ce: "A'a, da na ce eh da sai ya zama wajibi, sau daya ake aikin Hajji).

Tambaya: Wanda ya zo don yin Umara shin dole ne sai ya yi Hajjin wannan shekara? Saboda muna jin mutane suna fadar hakan shin gaske ne?

Amsa: Wannan kuskure ne, babu wanda ya fadi hakan cikin Malaman Musluunci.

Tambaya: Shin ya Halatta ga yaran da ba su kai shekara bakwai ba su yi dawafi tare da mahaifansu?

Amsa: Ya Halatta su yi haramar Hajji ko ta Umara, ko da ba su kai shekaru bakwai ba, kamar yadda ya zo a kissar matar nan Khas'imiyah wacce ta dauko karamin yaro da ke cikin shimfidar goyo (shawul) ta ce: ya Ma'iakin Allah (SAW)! Shin wannan zai iya yin Hajji? Ya ce: "kwarai kuwa amma ladan naki ne." Ta nan aka gane cewa Umarar yaron da bai kai shekaru bakwai ba ta halatta, kuma yana iya yin Hajji da dawafi amma a matsayin nafila.


(Labarin Cikakkun... | 4755 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
(Labarin Cikakkun... | 6416 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Darussa daga Hadisin Matafiya Uku

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika Kuma madalla da Shi da Ya sanya mana ni'imarSa, cikin gane al'amurran rayuwa a misalai daga karantarwar Alkur'ani da Hadisan ManzonSa. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni gare su wajen samun abubuwan more rayuwar duniya da Lahira. Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, yau makalarmu za ta yi tsokaci ne don samun darussa daga wani Hadisi da ya yi bayanin wadansu waliyan Allah guda uku da suka yi tafiya, har ta kai su ga (shiga) wani kogo, inda suka samu mafaka don su kwana su huta, sannan su wuce su ci gaba da tafiyarsu. Suna cikin kogon ne kuwa wani katon dutse ya gangaro ya toshe musu kofar kogon, ta yadda ba su da wata hanya ta fita. Sai suka rasa yadda za su yi, saboda haka suka ce, babu yadda za a yi su fita, sai dai su roki Allah ta hanyar tawassuli (jingina) da ayyukan alherin da kowanensu ya aikata a rayuwarsa, don su samu Allah din Ya taimaka musu su fita! Za mu ga yadda ta kaya, insha Allah!


(Labarin Cikakkun... | 6416 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Mugunyar Addu'a A Kan Wadanda Ke Mulkar Jama'a A Kan Zalunci Da Saba W
(Labarin Cikakkun... | 15325 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Ibrahim Jalo Jalingo

Mugunyar Addu'a A Kan Wadanda Ke Mulkar Jama'a A Kan Zalunci Da Saba Wa Ka'idar Da Aka Shimfida Abu Ne Da Ya Dance Shari'a

Al'ummar Kasa su ci gaba da yin mugunyar addu'a cikin kunutin Salla ko waninsa a kan wadanda ke son mulkar kasarsu da al'ummarsu a kan zalunci da saba wa ka'idar da aka shimfida lalle wannan wani abu ne da Sahri'ar Musulunci ta amince da shi, babu kuma mai kushe masa sai wanda ya jahilci nassoshin Shari'ah. Saboda abubuwa kamar haka:-

1. Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 804, da Imam Muslim hadithi na 675 daga Sahabi Abu Hurairah Allah Ya kara masa yarda cewa:-

((ان رسول الله صلى الله عليه وسلم كان اذا أراد ان يدعو على احد او يدعو لأحد قنت بعد الركوع فربما قال اذا قال سمع الله لمن حمده اللهم ربنا لك الحمد: اللهم انج الوليد بن الوليد، وسلمة بن هشام، وعياش بن ابي ربيعة، والمستضعفين من المؤمنين، اللهم اشدد وطاتك على مضر، واجعلها عليهم سنين كسني يوسف، اللهم العن لحيان ورعلا وذكوان وعصية عصت الله ورسوله)).

Ma'ana: ((Lalle Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kasance Idan ya yi nufin yi wa wani mugunyar addu'a, ko yi wa wani kyakkyawar addu'a, ya kan yi kunuti bayan rukuu'i, yana ma yiwuwa ya ce bayan ya ce: Sami'al Lahu liman hamidahu Allahumma Rabbana lakal Hamd: Ya Allah! Ka tsirar da Waliid Bin Waliid, da Salamah Bin Hisham, da Ayyash Bin Abii Rabii'ah, da Raunana cikin Muminai. Ya Allah! Ka tsananta kamunka a kan Kabilar Mudhar, Ka sanya wannan kamu a kansu a matsayin shekarun fari kamar shekarun farin zamanin Yusuf. Ya Allah! Ka la'anci (kabilun) Lihyan da Ri'il da Zakwan da Usayyah, sun saba wa Allah da ManzonSa)).


(Labarin Cikakkun... | 15325 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

017 Hunkunce-Hunkunce Da Suka Kebanci Mata Muminai Fitowa Ta 17
(Labarin Cikakkun... | 2209 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

017 Hunkunce-Hunkunce Da Suka Kebanci Mata Muminai Fitowa Ta 17

Malam ya cigaba da kawo mana bayanai a game da abunda ya shafi: HUKUNCE-HUKUNCEN TUFAFI DAGA CIKIN FASALI NA HUDU.
.
● Sheikhul islam Ibn Taimiyya (Rahimahullah) cikin Majmu'ul Fatawa (22/148-155) yace:
.
Abunda yake bambance tufar maza data mata yana komawa ne ga abunda yake dacewa da maza da kuma abunda yake dacewa da mata. Wannan kuwa shine abunda ya dace aka umurci maza dashi kuma aka umurci mata dashi, mata dai an umurce su da suturce jiki da yin lullu6i da Barin bayyana ado ga maza da barin bayyana Kai.
.
Don haka ne a shari'a ba a sanyawa mace daukaka murya domin qiran sallah ba ko yin talbiya (wato Labbaika) ko hawa kan dutsen safa da marwa, ko cire tufafi domin yin ihrami kamar yadda namiji yake yi, saboda shi namiji an umurce shi da ya bude kansa kuma kada ya saka tufafi na al'ada wato tufafin da ake dinka su gorgodon ga6ar jiki bazai saka taguwa ko wando ba ko irin rigar nan mai hade da hula ba, har inda sheikhul Islam yace:


(Labarin Cikakkun... | 2209 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Azumin Tsofaffi
(Labarin Cikakkun... | 2802 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Azumin Tsofaffi

Sau da dama 'yan uwa sukan rikice da batun Azumin watan Rajab, zatonsu ana yaqar yin azumi ne,wanda abin ba haka yake ba. Yadda lamarin yake a taqaice shine:-

© Azumi ibada ce mai girma da Allah(swa) yake bayar da amincinsa ga masu yinsa a cikin watan Rajab da waninsa cikin watanni,amma bisa qa'idar da mai RISALA ya fada a muqaddimar littafinsa

''ولا قول ولا عمل ولا نية إلا بموافقة السنة''

''BABU INGANCIN ZANCE KO AIKI KO NIYYA SAI IDAN YA DACE DA SUNNAH''

Irin wadannan batutuwa lalubesu a littafin DAN-FODIO (rt) mai suna:

وثيقة الإخوان.

© Idan mutum ya quduri yin azumi a watan rajab kamar

* AZUMIN LITININ DA AL-HAMIS

*AZUMIN AYYAMUL BHYYD( 13,14,15)

*KAYI YAU GOBE KA HUTA (AZUMIN DAWUD)


(Labarin Cikakkun... | 2802 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Azumin Watan Rajab
(Labarin Cikakkun... | 4169 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Azumin Watan Rajab

Watan RAJAB, daya ne daga cikin watanni masu alfarma guda 4, wadanda tun a jahiliyya Ana girmama su, sauran sune: Zul Qa'ada, Zul Hajj, da kuma Muharram. Abinda ake nufi da rajab shine mai girma ko abin Qimantawa. Kuma ana ambatar shi da wannan sunan ne saboda yadda tun wancan lokacin larabawa suke girmama shi cikin watanni.

Zamu kara gane haka idan muka lura da sunan watan da ke biye da shi wato Sha'aban, daga kalmar

شعب يتشعب بمعنى يتفرّق، أي يتفرّقون لإغارة بعد عقودهم في رحب. Wato suna fita su warwatsu cikin garuruwa Don Maida gari bayan dogon Hutu da akayi na kin yin yaki.

Shin RAJAB yana da wata falala akan sauran watanni?
Amsa shine : Eh! Amma falalar bata wuce abinda Ubangiji Ya ambata cikin littafinSa ba, na cewa yana daga cikin watanni masu alfarma, Don haka wani Magabaci cikin manyan malaman tafsiri mai suna Qatada bni Da'aama assadusiy yake cewa: '' Allah kan zabi Wasu cikin mutane Ya fifita su, kamr yadda yake fifita Wasu daga cikin Mala'iku, haka Ya ke fifita Wasu wurare kan Wasu, Don haka duk abinda Allah Ya fifita yakan girmama laifinsa, kamar yin laifi a haramin Makkah Ya dara yin sa a sauran wurare, haka yin laifi cikin wata Mai alfarma Ya data yin sa cikin wani wata da ba shi ba. Shin Me Ya kamata ayi a wannan watan?


(Labarin Cikakkun... | 4169 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

046 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 46
(Labarin Cikakkun... | 10359 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

RUBUTU NA QARSHE !!!

046 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI

★ A Qarshen littafin Malam Yayi mana nasiha kamar haka:
.
Ya ku 'Yan uwa muminai maza da mata, ina tunatar daku wasiyyar ALLAH gare ku a inda yake cewa:
.
قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَٰلِكَ أَزْكَىٰ لَهُمْ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ ٭ وَقُل لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آبَائِهِنَّ أَوْ آبَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ أَوْ أَبْنَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ أَوْ نِسَائِهِنَّ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ أَوِ التَّابِعِينَ غَيْرِ أُولِي الْإِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ أَوِ الطِّفْلِ الَّذِينَ لَمْ يَظْهَرُوا عَلَىٰ عَوْرَاتِ النِّسَاءِ وَلَا يَضْرِبْنَ بِأَرْجُلِهِنَّ لِيُعْلَمَ مَا يُخْفِينَ مِن زِينَتِهِنَّ وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
.
Ma'ana: ''Kace da muminai maza su kame ganin su, kuma su kiyaye farjinsu, wannan shi yafi tsarki agare su, haqiqa ALLAH masanin abunda suke aikatawa ne. * Kace da Muminai mata su kame ganinsu, kuma su kiyaye farjinsu. Kada kuma su fito da adonsu, sai dai abunda ya bayyana daga gare shi, kuma suyi lullu6i da mayafansu akan wuyan rigunan su, kuma kada su bayyana adon su sai ga mazajensu, ko iyayensu, ko iyayen mazajensu ko 'ya'yayensu ko 'ya'yayen Mazajensu ko 'Yan uwansu maza ko 'Ya'yan 'Yan uwansu maza ko 'Ya'Yan 'Yan uwansu mata ko mata (musulmai) 'Yan uwansu Ko kuma Abunda hannayensu suka mallaka (wato bayi) ko kuma mabiya ba masu buqatar mata ba daga maza ko kuma qananan yara wad'anda basu san sha'awar al'aurar mata ba. kada kuma su buga qafafuwansu don agane abunda suka 6oye na adon qafafun su (wato mundaye) kuma ku tuba ga ALLAH gaba d'ayanku yaku wad'annan muminai don ku rabauta.''
.
[Suratul Noor aya ta 30-31]


(Labarin Cikakkun... | 10359 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

045 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 45
(Labarin Cikakkun... | 5978 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

045 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 45

✺✺FASALI NA GOMA (10)✺✺
.
Malam Ya cigaba da Bayani akan Hukunce-Hukuncen da suke kiyayewa Mace Martabarta, kuma suke tsare mutuncinta.
.
[C]→Wasu mata da waliyansu suna yin sassauci wajen shigar mace wajen Likita ita kad'ai da hujjar wai cewa magani take nema. Wannan munkari maigirma kuma had'ari ne babba Wanda bai kamata a qyale shi ba, ayi shiru akansa.
.
→ Sheikh Muhammad Ibn Ibrahim (Rahimahullah) Yace acikin [Majmu'ul Fatawa nasa 10/13]:
.
Kad'aituwa da mace Ajnabiya haramun ne acikin shari'ah, koda kuwa da likita ne, saboda hadisin da yake cewa: ''Wani namiji bai ta6a kad'aituwa da mace ba face shaid'an ya zama na ukunsu.'' Don haka dole ne asamu wani tare da ita, kodai mijinta ko wani namiji daga cikin muharramanta. Idan ba a samu haka ba, to ko dai wata mace daga cikin 'yan uwanta, idan kuma ba a samu hakan ba a samu wani daga cikin wad'anda ba a ambata ba, kuma idan rashin lafiyar mai had'ari ne, bazai yuwu a jinqirta shi ba, to sai a samu ko da wata daga cikin ma'aikatan jinya na asibitin don a tsaru daga kad'aituwar da aka hana.


(Labarin Cikakkun... | 5978 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

006 AURE KO MAKARANTA?
(Labarin Cikakkun... | 3085 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Rubutu na 6

006 AURE KO MAKARANTA?

Daga: *zauren majlisin sunnah*

*MU KOMA GA NASSI*

90. Shin ba Allaah Maɗaukakin Sarki ba ne ya ce:
وَأَنكِحُوا الْأيَامَى مَنكُمْ
Kuma ku aurar da marasa aure daga cikinku?

91. Shin lafazin 'marasa aure' bai haɗa tsofaffi da sababbin balaga ba?

92. Kuma wannan lafazin na 'marasa aure' bai haɗa maza da mata ba?

93. Shin yin gaggawa wurin bin umurnin Allaah (Subhaanahuu wa Ta'aalaa) ba wajibi ba ne a kan dukkan musulmi?

94. Ko akwai wani nassin da ya nuna halaccin dakatar da yin aure domin kawai rashin kammala wani karatu ba ma na-boko ba?


(Labarin Cikakkun... | 3085 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

BIDI'OIN DA AKEYI AWAJAN WANKE MAMACI
(Labarin Cikakkun... | 3628 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

BIDI'OIN DA AKEYI AWAJAN WANKE MAMACI

1-Ajeye abinci da ruwa awajan da aka wanke mamacin tsawan kwana uku.
2-Sanya fitila awajan Taiwan kwana uku ko bakwai daga faduwar rana zuwa fitowar sa.
3-Yin zikiri da addua idan ana wanke mamaci akowace gaba.
4-Saukar da gashin mamaci akan kirjinsa.

BIDO O IN LIKKAFANI DA FITA DA GAWA

1-Daukar gawa zuwa waje mai nisa dan abunne shi dare da nagartattu kamar ahlul baiti.
2-Ciwar wasu wai mamata suna alfari da likkafanin da aka sa musu saboda kyansa.
3-Rubuta sunan mamaci tare da sunan ahlul baiti da kasar husaini asanyashi acikin likkafani.
4-Rubuta adduo I ajikin likkafani.
5-Yiwa gawa kwalliya.
6-Sanya tutoci agaban gawa.
7-Sanya rawani akan makara.
8-Daukar fulawoyi da hotun mamacin agaban gawa.
9-Yanka raguna lokacin dazaa fita da gawa da daukar abincin da zaa ci bayan an gama bunne gawa.
10-Cewa wai idan gawa ta garice bata nauyi.


(Labarin Cikakkun... | 3628 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

BIDI'O IN DA AKEYIWA MARA LAFIYA KAFIN YA RASU DA BAYAN YA RASU
(Labarin Cikakkun... | 3499 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

BIDI'O IN DA AKEYIWA MARA LAFIYA KAFIN YA RASU DA BAYAN YA RASU

1-Fadin wasu cewa shedanu suna zuwa a siffar iyayan mara lafiya dan su batar dashi.
2-Sanya alqur'ani awajan kan wanda zai mutu.
3-Laqqanawa fadin sunan Annabi da alayansa.
4-karanta YASIN .
5-Sanya wanda zai mutu ya kalli gabas.

BIDI O INDA AKEYI BAYAN MUTUWA

1-Fadin yan shi'a dan adam idan ya mutu najasa ne.
2-Futarda masu haila da haihuwa da janaba daga gidan.
3-Daina aiki ga wanda agabansa akai mutuwa.
4-Fadin wai ruhin yana yawo awajan.
5-Sanya turare tun dare har safe.
6-Sanya koran mayafi adakinda akai mutuwa.
7-Karatun alqura'ni har sai anyi masa wanka.
8-Yanke farcen mamaci da aske gashin hammatarsa.
9-Shigar da auduga cikin dubura ko hanci ko huyansa.
9-Sanya kasa a idan mamaci.


(Labarin Cikakkun... | 3499 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

YIWA MAMACI SALLAH (SALLAR GAWA)
(Labarin Cikakkun... | 2654 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

YIWA MAMACI SALLAH (SALLAR GAWA)

Bayan an gama yiwa gawa likkafani sai kuma ayi mata sallah.Yin sallah gawa wajine akan duk alummah amma idan wasu suka yi ya saraya akan sauran.

MUTUM BIYU BA AYI MUSU SALLAH

1-Karamin yaran da bai balaga ba.
2-Wanda yayi shahada.

YA HALATTA AYIWA WADANNAN MUTANAN SALLAH

1-Yaro karami ko wanda akai farinsa.
2-shahidi.
3-Wanda aka kashe ta hanyar yanke mai haddi.
4-Fasiqi mai sabo kamar mai barin sallah ko zakkah.
5-Wanda ake bi bashi bai biya ba harya mutu kuma bai bar kudunda zaa biya masa ba.
6-Wanda akai masa sallah sai wani yazo zai iya yi masa amqabar.
7-Wanda ya mutu agarinda babu wanda zai masa sallah.


(Labarin Cikakkun... | 2654 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

BIDI'OIN DA AKEYI AWAJAN WANKE MAMACI
(Labarin Cikakkun... | 2637 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

BIDI'OIN DA AKEYI AWAJAN WANKE MAMACI

1-Ajeye abinci da ruwa awajan da aka wanke mamacin tsawan kwana uku.

2-Sanya fitila awajan Taiwan kwana uku ko bakwai daga faduwar rana zuwa fitowar sa.

3-Yin zikiri da addua idan ana wanke mamaci akowace gaba.

4-Saukar da gashin mamaci akan kirjinsa.

BIDO O IN LIKKAFANI DA FITA DA GAWA

1-Daukar gawa zuwa waje mai nisa dan abunne shi dare da nagartattu kamar ahlul baiti.

2-Ciwar wasu wai mamata suna alfari da likkafanin da aka sa musu saboda kyansa.

3-Rubuta sunan mamaci tare da sunan ahlul baiti da kasar husaini asanyashi acikin likkafani.

4-Rubuta adduo I ajikin likkafani.


(Labarin Cikakkun... | 2637 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

BIDI'O IN DA AKEYIWA MARA LAFIYA KAFIN YA RASU DA BAYAN YA RASU
(Labarin Cikakkun... | 3425 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

BIDI'O IN DA AKEYIWA MARA LAFIYA KAFIN YA RASU DA BAYAN YA RASU

1-Fadin wasu cewa shedanu suna zuwa a siffar iyayan mara lafiya dan su batar dashi.

2-Sanya alqur'ani awajan kan wanda zai mutu.

3-Laqqanawa fadin sunan Annabi da alayansa.

4-karanta YASIN .

5-Sanya wanda zai mutu ya kalli gabas.

BIDI O INDA AKEYI BAYAN MUTUWA

1-Fadin yan shi'a dan adam idan ya mutu najasa ne.

2-Futarda masu haila da haihuwa da janaba daga gidan.

3-Daina aiki ga wanda agabansa akai mutuwa.


(Labarin Cikakkun... | 3425 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

005 AURE KO MAKARANTA?
(Labarin Cikakkun... | 2959 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Rubutu na 5

005 AURE KO MAKARANTA?

Daga: *zauren majlisin sunnah*

*GYARA TUNANI*

62. Ko kuna tsammanin muna ƙyamar ilimin bokon mace ne?

63. Ba ku san mun san cewa: Mata su ne kashin bayan rayuwa ba?

64. Ba ku san mun san cewa: Mata da 'ya'ya su ne mafiya soyuwan mutane a wurin Annabin Rahama (SAAS) ba?

65. Amma kuma ba ku san duk da haka, ya nuna cewa: Mata sun fi yawa a cikin Wutar Lahira ba?

66. Ba ku san mun fi kowa son ganin gyaruwa da daidaituwar al'amuran mata ba?

67. Ba ku san cewa mu ma mun yi karatun bokon, kuma mun san irin alfanu ko rashin alfanunsa ba?


(Labarin Cikakkun... | 2959 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

004 AURE KO MAKARANTA?
(Labarin Cikakkun... | 2305 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Rubutu na 4

004 AURE KO MAKARANTA?

Daga: *zauren majlisin sunnah*

*MU YI TUNANI*

39. Menene amfanin ƙoƙarin yarinya a irin wannan makarantar?

40. Menene fa'idar kammala karatun yarinya a irin wannan makarantar?

41. Wace irin babbar mutum ce irin wannan makarantar take yayewa?

42. Menene ya fi rayuwa a cikin irin wannan makarantar cutar da ilimi?

43. Menene ya fi rayuwa a cikin irin wannan makarantar cutar da lafiya?

44. Anya yarinyar kirki za ta iya natsuwa a cikin irin wannan makarantar?


(Labarin Cikakkun... | 2305 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

HUKUNCIN MASU CIKI KO MASU SHAYARWA IDAN SUKA KASA YIN AZUMIN RAMADAN
(Labarin Cikakkun... | 3596 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

HUKUNCIN MASU CIKI KO MASU SHAYARWA IDAN SUKA KASA YIN AZUMIN RAMADAN

1. Farko dai: Maluman Musulunci sun yi Ittifaqi a kan cewa mace mai ciki da wacce take shayarwa idan suka ji tsoron cutuwar kansu, ko cutuwar kansu tare da cutuwar 'yan'yansu, to, suna da daman su bar yin azumin Ramadan, sannan daga baya su biya, babu kuma wata ciyarwa a kansu bayan biyan.

2. Abu na biyu: Su Malaman sun yi sabani game da: Idan ita Mai cikin, da Mai shayarwar suka ajiye azumi saboda tsoron kada 'yan'yansu su cutu, ba wai kada su su cutu ba. Sun yi sabani cikin wannan Mas'alah har zuwa kauli shida:

– Kaulin farko: Mai ciki da Mai shayarwa idan suka sha ruwa saboda tsoron kada 'ya'yansu su cutu, ba wai saboda su kansu su cutu ba, babu ciyarwa a kansu sai dai biya kawai. Wannan shi ne mazhabar Hanafiyyah. Da wasu Taabi'ai da Taabi'ut Taabi'in.

– Kauli ba biyu: Ita mai ciki za ta biya ba tare da ciyarwa ba, amma mai shayarwa za ta biya, sannan kuma za ta ciyar. Wannan shi ne mazhabar Malikiyyah. Kuma wannan shi ne mazhabar Laith Bin Sa'ad.


(Labarin Cikakkun... | 3596 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Bambanci tsakanin Maniyyi Da maziyyi wa wadiy da hukuncinsu
(Labarin Cikakkun... | 1973 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

Bambanci tsakanin Maniyyi Da maziyyi wa wadiy da hukuncinsu

Assalamu Alaikum warahmatullah wabarkatuh, yau a fagen Fiqhu zamu dubi abubuwa guda uku wanda suke da alaka da tsarki, abubuwan sune Maniyyi, da maziyyi da wadiy,

1.maniyyi: Shi wannan wani ruwa ne da yake fitowa lokacin Yin jima'i ko mafarki ko makamantansu, yana da kauri in na namiji ne, inkuma ta macece yana nan tsiriri kuma yana fita da karfi, yana bibiyar juna.

Hukuncin maniyyi: Akwai tsabani tsakanin maluma kan kasancewar maniyyi najasa ne ko ba najasa ba, abinda ya dace mutum dai yayi in maniyyi ta shafi tufafinsa ko jikinsa shine in maniyyin bai bushe ba sai ya wanke wurin da ruwa, inkuma ya bushe sai ya kankareshi.

sannan hukuncin wanda maniyyin ta fito daga jikinsa, shine zaiyi wankan janaba, In maniyyin ya fito ta jima'i ne ko mafarki, hakanan mutumin daya farka daga bacci yaga maniyyi ajikinsa Shima zaiyi wanka. amma in mutum yayi mafarki ya tashi baiga wani maniyyi ajikinsa ba toh babu wani wanka akansa. hakanan mutumin da yake farke maniyyi ta fito ba tare da wata sha'awah ba, haka kawai ta fito kodun ciwo ko wahala, shima wannan babu wanka akansa.


(Labarin Cikakkun... | 1973 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

NURUN ALA NUR FITOWA TA 7
(Labarin Cikakkun... | 3836 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

NURUN ALA NUR FITOWA TA 7

Dr. Dr. Mansur Sokoto

''BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI''

''Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad Al-Kadhibi – Wani malami dan kasar Bahrain da Allah ya ganar da shi gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi'a.''

BABBAN GINSHIKIN SHI'A YA GANTALE (2)

Akwai kuma wasu riwayoyi masu yawa daga Zuraratu dan A'ayan da Ya'qubu dan Shu'aib da Abdul A'ala duk sun tambayi Imam As-Sadiq cewa, idan wani abu ya faru ga imami ya mutane za su yi? Sai ya ce, su yi kamar yadda Allah ya ce:

''Ina ma da wata qungiya daga cikin kowannen su ta fita don ta karanci addini..'' zuwa qarshen ayar. Sai na ce, to mene ne halinsu? Sai ya ce, suna da uzuri. Sai na ce, Allah ya sanya ni fansar ka. Masu jira ya za su yi kafin masu yin karatu su dawo? Sai ya ce, Allah ya jiqan ka, kai ba ka san cewa a tsakanin annabi Isa da annabi Muhammad akwai shekaru dari biyu da hamsin ba? Ai wasu sun mutu a kan addinin annabi Isa suna jiran annabi Muhammad, don haka Allah ya ba su lada ninki biyu. Na ce, to idan mun tafi sai wasu suka mutu a hanya fa? Sai ya karanta min ayar: ''Wanda duk ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da manzonsa sannan mutuwa ta riske shi to, ladarsa ta tabbata a wurin Allah''. Na ce, to idan mun isa a garin mun tarar Imam ya kulle gidansa ya shige ya zamu yi? Ya ce, wannan lamari fa ba ya kasancewa sai da lamari bayyananne. Shi ne wanda idan ka shiga a gari ka ce ina wanda wane ya yi ma wasici? Za a ce ma ka ga shi nan.


(Labarin Cikakkun... | 3836 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

SANYA TUFAFI YAWUCE IDON 'KAFA HARAMUNNE KUMA ALLAAH YAYIWA MA'ABOCINS
(Labarin Cikakkun... | 7518 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

SANYA TUFAFI YAWUCE IDON 'KAFA HARAMUNNE KUMA ALLAAH YAYIWA MA'ABOCINSA TANADIN AZABA MAI RA'DA'DI

Yana daga abunda yazama ruwan dare gama-duniya har yazama an maidashi kamar ba laifi ba; shine sanya tufafin da yawuce idon sawu('kafa)
ga maza.

A inda zakaga babba da yaro, mahaifa da 'ya'ya, malamai da dalibai, masu kudi da talakawa, suna sanya tufafi(riga ko wando ko malum-malum) 'kasa da idon sawu.

Bayan kuma yin hakan haramunne qa'd'an, kamar yadda hakan ya tabbata daga fiyayyen halitta (s.a.w) kuma hadisan sun bayyana narkon azaba mai ra'da'di da 'kuna ga duk mai aikata hakan.

Ga wadannan hadisan kamar haka:

– ﺭﻭﻯ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ :

) ﻣﺎ ﺃﺳﻔﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻹﺯﺍﺭ ﻓﻔﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ ( ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﺭﻗﻢ 5787.

Ma'ana: Duk tufafin da yawuce idon 'kafa ma'abocinsa dan wutane.


(Labarin Cikakkun... | 7518 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

HAKKOKIN MUSULMAI A KAN JUNANSU
(Labarin Cikakkun... | 3050 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

DR. MANSUR SOKOTO

HAKKOKIN MUSULMAI A KAN JUNANSU

Hakika Allah ya umurci Musulmai da hadin kai wajen tsayar da Addini, Allah ya ce:

13] "Ku tsayar da Addini kada ku rarraba a cikinsa".

Sai Allah ya hanesu ga rarrabuwa. Kuma wannan shi ne abin da ya shar'anta mana, kuma ya yi wasiyyansa ga Shugabannin Manzanni; Muhammad (saw), Ibrahim (saw), Musa (saw), Isa (saw), Nuhu (saw).

– Kuma Allah ya hanesu a kan sabani, inda ya ce:

46] "Kada ku yi jayayya a tsakaninku sai ku karaya, karfinku ya kare".

– Kuma ya umurcesu da taimakekeniya, inda ya ce:


(Labarin Cikakkun... | 3050 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

TAMBAYOYI DA AMSA RANCEN AIRTIME (MTN, GLO DSS) DAGA SERVICE PROVIDERS HALAS NE
(Labarin Cikakkun... | 4054 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

SHEIKH DR. MANSUR IBRAHIM SOKOTO

RANCEN AIRTIME (MTN, GLO DSS) DAGA SERVICE PROVIDERS HALAS NE KO HARAM?

 Sheikh Dr. Mansur Ibrahim Sokoto

 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Na karanta rubutun da dan uwa Shehun Malami Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi akan wannan lamari kuma har na yi sharing tare da dan ta'aliki a kai. Na so na wadatu da wannan, amma sai na ga a wasu shafukan yan uwa ana ta tafka muhawara da sa bakin masu masaniya a Fikihu da wadanda ma ba su da ita sam.

 Akwai masu ra'ayin cewa, an dulmuyar da Dr. Sani ne har ya canja fatawa. Ina son in fada ma wadannan cewa, sun jahilci wane ne Dr. Sani a kaifin basirarsa da bincikensa na ilimi. Ba na maganar wani dan bokon da bai san kimar ilimin annabawa ba don ya ce masa "Dan Arabiyya zalla" ko "Mai ido daya" . Domin ko ya sani ko bai sani ba da annabin Allah yake. Shi ne mai Arabiyya zalla. Kuma idonsa mai tsarki da tarin albarka bai taba kallon wani bokon da shi wannan jahilin yake takama da shi ba. Littafin Allah da ya zo da shi Arabiyya ce zalla, haka ma hadisansa Arabiyya ne zalla. Ashe wanda ya sha su ya koshi shi ke zama dan Arabiyya zalla. Mai sukar sa ta wannan fuska kuma ya san ko waye yake suka. Allah ya shirye mu.

 A nan dai ina son ne in dan kara haske a kan matsalar don masu neman bayani tsakani da Allah ko za su gane:


(Labarin Cikakkun... | 4054 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

SALLAH MAFIFICIYAR IBADAH !!! FITOWA TA 8
(Labarin Cikakkun... | 2263 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

SALLAH MAFIFICIYAR IBADAH !!! FITOWA TA 8

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

CIGABA GAME DA WASA DA SALLAH !!!

Kamar yadda muka fara haqalto abunda ya tabbata daga Qur'ani da hadisi da maganganun magabata dan gane da wasa da sallah, haqiqa addinin musulunci yayi bayani sosai ga matsayin sallah da hukuncin wasa da shi.

•Imam Ahmad Ya ruwaito cikin "isnadi" daga hadithin Abdullahi dan Amr (ALLAH Ya qara masa yarda) daga Annabi (sallallahu alaihi wasallam) Yace: "Wanda baya kiyaye sallah, bayi da wani haske bayi da hujja bayi da ku6uta, kuma zai kasance a ranar alqiyama tare da Qaruna da Fir'auna da Hamaana da ubayyu bin khalaf" .

"Sahih ne Ahmad ya fitar dashi 6576 da Daarimy 2/301-302] .


(Labarin Cikakkun... | 2263 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com