Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
EsinIslam Media: Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Search on This Topic:   
[ Go to Home | Select a New Topic ]

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Musulmi da farfagandar makiya
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Musulmi da farfagandar makiya

Masallacin Haramin Ka'aba da ke Makka

Godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da aminci su tabbata ga Annabi (SAW).

Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku bi Allah Madaukaki da takawa ku sani bin Allah da takawa shi ne zai kare mu daga dukan bala'o'i.

'Yan uwa a imani! Tun lokacin da Allah Ya halicci duniya ake fafata yaki a tsakanin sassa daban-daban domin a mallake zukata da tunanin mutane; kamar yadda ake neman mallakar dan Adam a jikinsa. A yau ana yakar dan Adam ta wajen tunani da fikirarsa fiye da kowane lokaci; ana yakar tunaninsa ta dukan hanyoyi fiye da yaki irin na soja. Wannan yaki, shi ne yakin farfaganda.

Farfaganda wata muguwar hanya ce, kuma makami mafi hadari da ya fi ruguza dan Adam. Hadarinta babba ne kuma ba za a iya misalta barnarta ga dan Adam ba, saboda mugun illarta. Don haka wajibi ne a samu yunkuri don nazartarta ta yadda za a gano tushenta a tuttuge ta, kafin ta jawo mummunar illar da ba za a iya magance ta ba ga dan Adam.

'Yan uwa a Musulunci! Idan dayanmu zai yi dubi na basira ga tarihin dan Adam, zai ga cewa farfaganda da jita-jita sun taka rawa da tasiri a dukan zamunna; bilhasali ma sun samu gurbi babba wajen ci gaban masu da'awar wayewa, kuma su suke jawo rudu da bala'o'i ga kasashe da dama. An bi dukan matakan shigar da wannan muguwar dabi'a, domin juya akalar duniya kafin bayyanar Musulunci. Musulunci a matsayinsa na addinin da ginshikinsa shi ne tabbatar da rahama da adalci da zaman lafiya ga dan Adam, ya dauki kwararan matakai don yaki da wannan muguwar dabi'a, ta hanyar bin matakan haramta ta a cikin Alkur'ani da Sunnah.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Abin da za mu yi Allah Ya so mu (2)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Abin da za mu yi Allah Ya so mu (2)

Mu sake tambayar kanmu, "Shin Allah Yana sonmu?" Idan har muna ji a jikinmu cewa Allah ba Ya son mu saboda ba mu aikata abin da ya dace, to 'yan uwa mu yi wa kanmu kiyamul laili, mu tuna da karashen wannan Hadisi da muka fara kawowa, mu guje wa abin da zai fusata Allah. Mu guji mutanen da suke aikata ayyukan da suke fusata Allah.

Domin Manzon Allah (SAW) ya fadi a karshen Hadisin cewa: "Idan kuma Allah Ya ki mutum (saboda saba maSa), zai kira Mala'ika Jibril (AS) Ya ce masa: "Ya Jibrilu! BawaNa wane dan wane yana ci gaba da fusata Ni, don haka fushiNa ya tabbata a gare shi."

Ke nan samun so daga Allah yana ta'allaka ne da bin abin da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi na daga ayyukan da'a.

Kuma Allah Yana daukar duk wanda ya yi maSa biyayya a matsayin masoyinSa. Shi ya sa za mu ga Alkur'ani da Sunnah cike suke da darussan da suke nuni kan yadda za mu samu soyayya daga Allah Subhanahu Wa Ta'ala.

Babban ginshikin samun soyayya a tsakanin bawa da Ubangijinsa, shi ne yin imani da yin aiki nagari. "Lallai wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na kwarai (nagari), wadannan su ne mafifita alherin halitta. Sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shi ne gidajen Aljanna koramu na gudana a karkashinsu, suna madauwama a cikinsu har abada. Allah Ya yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa." (k:98:8).


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Abin da za mu yiAllah Ya so mu (1)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Abin da za mu yiAllah Ya so mu (1)

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai. Mai nuna mulki Ranar Sakamako. Kai kadai muke bautawa kuma gare Ka kadai muke neman taimako. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da sauran masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Bayan haka ganin halin da mu Musulmi muka samu kanmu a ciki a wannan lokaci, ya kamata mu rika wa kanmu wannan tambaya ta sama. "Shin Allah Yana sonmu kuwa?"

Yin Tambayar zai sa mu yi kokarin gano amsa kuma ta haka ne za mu iya gane ko muna tafiya a kan hanyar da Allah Yake so ko a'a. Na fadi haka ne saboda yadda muka iske kanmu a cikin wani yanayi na rana kuna inuwa zafi a kusan duk duniyar Musulmi.

Domin amsa wannan tambaya za mu leka tarihi mu ga yadda magabatan kwarai (Salafus Salih) da mamayan kwarai (Khalfus Salih) suka gudanar da rayuwarsu har suka samu daukakar da yanzu muke ta karantawa a littattafan tarihi da na addini, kuma suka zama su ne suke juya duniya a zamaninsu.

Bayan wafatin Annabi (SAW) ba da dogon lokaci ba, Abu Idris Alkhaulani (wanda ya rasu a shekara ta 80 Bayan Hijira daidai da shekara ta 699-700 Miladiyya) a Damaskus ta kasar Syriya ya tafi Masallacin Al-Kabir. A cikin masallacin ya iske rukunin mutane sun kewaye wani mutum. Ya bayyana siffar mutumin da mutum mai yawan murmushi kuma mutanen sun kewaye shi suna yi masa tambayoyi. Sai Abu Idris Al-Khaulani ya tambaya: "Wane ne wannan mutum?" Sai suka amsa: "Mu'azu bin Jabal ne (RA), sahabin Manzon Allah (SAW)."


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Giba da illolinta (1)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Giba da illolinta (1)

Masallacin Harami na Ka'aba, Makka

Fassarar Salihu Makera

Huduba ta farko

Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman gafararSa muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma Ya batar babu mai shiryar da shi. Mun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya, kuma mun shaida Shugabanmu Annabi Muahmmad bawanSa ne kuma ManzonSa. Allah Ya kara tsira da amince a gare shi da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa.

Bayan haka, ina yi mana wasiyya da bin Allah da takawa, wanda ya yi maSa takawa Ya isar masa, wanda ya ji tsoron mutane ba su isar masa. Ina yi mana wasiyya da takawa, wadda ba Ya karbar waninta, kuma ba Ya jinkan kowa sai ma'abutanta, ba Ya bayar da lada sai a kanta, masu wa'aztuwa da ita suna da yawa, amma masu aiki da ita kalilan ne, Allah Ya sanya mu cikin masu takawa.

Ya ku Musulmi! Addinin Allah ya cika ya kammala, ya kunshi akida da shari'a da tauhidi da ibada da mu'amala da dabi'u, yana zance da hankali da zuciya da jiki da rai a cikin al'amuran da suka shafi shari'a da halaye da tarbiyya, addini daga Ubangijinmu yana tsara dokoki da rayuwa ga Musulmi mai mutunci da tsarki na zahiri da badini. Ya zamo Musulmi mai kubutacciyar zuciya, mai kame harshe, mai da'a ga Ubangijinsa mai halin kirki ga jama'a. Mai kokarin tsare mutuncinsa da kin bin son rai. "Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lallai sashen zato zunubi ne. Kuma kada ku yi rahoto, (bincikar laifin mutane)." (K: 49:12).


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Yadda Musulunci ya 'yanta mace (5)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Yadda Musulunci ya 'yanta mace (5)

Mutumin da ba ya da kishi shi ake kira da Larabci da Duyus, wato mai tabbatar da kazanta a cikin iyalinsa, wato mutum ya zamo gaso-rogo ko mijin Hajiya, babu ruwansa da masu shiga kan iyalinsa ko masu hulda da su. Malamai sun ce: "Duyus shi ne wanda ba ya kishin iyalin gidansa, kuma an samu gargadi mai tsanani tare da yi masa tattalin azaba a kan haka. An karbo daga Abdullahi dan Umar (RA) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Mutum uku Allah Madaukaki ba zai dube su (da idon rahama) ba a Ranar Alkiyama: Mai guje (saba) wa iyayensa da mace mai shigar maza da kuma Duyus (namiji marar kishin matarsa)" (Ahmad da Nisa'i suka ruwaito).

Nuna kishi ga hurumin kamewa rukuni ne sananne da ke kare martaba da dabi'un mutane a zamanin Jahiliyya da kuma bayan zuwan Musulunci. Domin shi, wata dabi'a ce da dan Adam ya ginu a kanta, dabi'a ce mai kyau da tsabta. Duk mutumin da ba ya da kishin iyalinsa, ba ya da bambanci da dabba. Domin dabba ce kawai ba ta kishin muharraminta.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Yadda Musulunci ya 'yanta mace (4)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Yadda Musulunci ya 'yanta mace (4)

4 – 10. Runtse ido da tsare farji da sauransu:

Manufar shari'ar Musulunci ita ce kare martabar mace wadda ita ce ginshikin iyali. Kuma kare martabarta zai tabbata ne kawai idan aka hana abin da zai kai ga yaduwar zinace-zinace. Zinace-zinace kuwa masominsu shi ne gwamutsuwar maza da mata da bayyana kawa da kallo a karshe kuma a auka wa keta martabar mace. Musulunci ya umarci maza da mata su runtse daga ganinsu kuma su tsare farjojinsu daga aikata zina. (k:24:30-31)

Musulunci ya hana mata bayyana ado ko kawarsu face ga mazansu da wadansu da shari'a ta ambata. (k:24:31). duk wadda ta yi tawaye ga wannan doka sai mu ajiye ta a sahun mushirikai da kafiran Yamma.

Musulunci ya hana mata sassautar da magana ga mazan da ba na su ba don kada su ba masu muguwar zuciyar damar su yi tsammanin wani abu daga gare su. "Ya matan Annabi! Ba ku zama kamar kowa daga (sauran) mata ba in kuka yi takawa, saboda haka kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cuta a zuciyarsa ya yi tsammani…" (k:33:32). Musulunci ya haramta kebanta da ajaniba ko yin tafiya ga mace ba tare da muharraminta ba. An karbo daga Ibn Abbas (RA) ya ce: "Na ji Annabi (SAW) yana huduba yana cewa: "Kada namiji ya kebanta da mace face tare da ita akwai muharraminta, kuma kada mace ta yi tafiya sai tare da muharrami." Sai wani mutum ya tashi ya ce: "Ya Manzon Allah! Lallai matata ta tafi aikin Hajji, ni kuma an rubuta ni cikin masu tafiya yaki kaza da kaza." Sai (SAW) ya ce: "Tashi ka tafi aikin Hajji tare da matarka." (Buhari da Muslim). Ibn Hajrin ya ce, "A cikinsa (Hadisin) akwai hanin kebanta da ba'ajanabiya kuma shi ne ijma'in malamai." (Fathul Bari: 4/92). Alkali Iyal ya ce, "Mace fitina ce kuma an hana kadaita da ita ce, saboda abin da aka halicci zukatan maza na sha'awa a kansu (mata), kuma aka sallada Shaidan a tsakaninsu…." (Ikmalul Mu'allim: 4/448). Haka Musulunci ya hana shiga gidan da mace take ba tare da muharraminta ba. Ukbatu bin Amir (RA) ya ruwaito cewa: "Manzon Allah ya ce: "Kashedinku da shiga gidajen mata!" Sai wani mutum daga Ansar ya ce: "Ya Manzon Allah koda matan dan uwa ne (wa ko kane)?" Sai (SAW) ya ce: "Matan dan uwa mutuwa ce!" Khurdabi ya ce: "Fadinsa matar dan uwa mutuwa ce" na nufin shigarsa gidan matar dan uwansa yana kama da mutuwa wajen ki da barna. Wato abin haramtawa ne. An kai iyaka ne wajen gargadi aka kwatanta da mutuwa…. (Almufham:4/501).


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Tukuici ga mai azumi (4)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Tukuici ga mai azumi (4)

Nafilfilin dararen goma na karshen watan Ramadan:

Daga A'isha (Allah Ya yarda da ita),ta ce: "Annabi (SAW), ya kasance idan goman karshe na watan Ramadan ya zo, to ba ya barci, sai ya tada mutanen gidansa maza da mata ya dukufa da nafilfili har karshen watan Ramadan." Buhari ya ruwaito.

I'itikafi:

Shi I'itikafi shi ne mutum ya zauna a masallaci don nafilfili da karatun AIkur'ani da zikiri da addu'o'i don neman dacewa daga Allah a duniya da Lahira. Shi kuma Sunnah ne da ake so, amma abin da aka fi so daga goman karshe na watan Ramadan. Kuma an ce karancinsa kwana daya da wuni, amma akasarinsa kwana uku. Awata ruwaya kuma an ce karancinsa kwana uku, amma mafi yawansa kwana goma har zuwa wata guda. Kowanne ka zaba daga cikin wadannan maganganu ya yi daidai. An karbo daga A'isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: Annabi (SAW) ya kasance yana I'ittikafi a kwana goma na karshen Ramadan har ya bar duniya.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Tukuici ga mai azumi (3)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Tukuici ga mai azumi (3)

Wadanda azumi bai wajaba a kansu ba, amma dole su biya:

1. Matafiyi idan ya sha azumi a cikin tafiya dole ne ya biya.

2. Mara lafiya yana iya shan azumi duk lokacin da ya warke sai ya biya abin da ya sha.

3. Mai haila ba azumi a kanta, amma in ta yi tsarki za ta biya abin da ta sha, kuma idan mai haila ta dauki azumi sai jini ya zo mata kafin rana ta fadi, to, azuminta ya baci, haka nan kuma idan haila ya dauke mata da rana a Ramadan ba azumi a kanta a sauran wannan yinin sai dai za ta rama azumin ranar da sauran kwanakin da ta sha. Bugu da kari idan jinin ya dauke kafin fitowar alfijir ko da mintuna kadan ne kafin fitowar alfijir, to, azumi ya wajaba a kanta.
karin bayani: Shi ma jinin haihuwa (biki) kamar jinin haila ne cikin dukkan hukunce-hukuncensa.

4. Mace mai shayarwa idan ta ji tsoron danta ba zai samu nonon da za ta shayar da shi ba, sai ta ci abinci, to, tana iya cin abincin bayan azumi ya wuce sai ta rama gwargwadon abin da ta sha. Haka hukuncin yake ga mace mai ciki idan ta ji tsoron abin da ke cikinta, ita ma tana iya shan azumi kuma wajibi ne a kanta ta biya gwargwadon azumin da ta sha bayan ta haife cikin nata.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu

Masallacin Annabi (SAW) da ke birnin MadinaHuduba ta daya:

Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah, Wanda muke neman taimakonSa, kuma muke neman gafararSa, kuma muke neman shiriyarSa. Kuma muna neman tsarin Allah daga sharrance-sharrancen kawunanmu da na miyagun ayukkanmu. Wanda duk Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi; Wanda kuma Ya batar, babu mai shiryar da shi. Na shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake, ba Ya da abokin tarayya a gare shi; kuma na shaida cewa lallai Annabi Muhammadu (Sallahu Alaihi Wasallam), bawanSa ne kuma ManzonSa ne, (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi da jama'ar gidansa da sahabbansa baki daya).

Bayan haka, ya ku bayin Allah! Babu shakka, shirya al'amurra da gudanar da su a hannun Allah yake! Shi Allah Yana aikata abin da Yake son aikatawa a cikin bayinSa, kuma ba a isa a tambaye Shi dalili ba, amma mu bayinSa ana tambayarmu, kuma Allah Shi ne Mai cikakken sani!

Daga cikin sunnoninSa Madaukakin Sarki, akwai jarrabar mutane da abubuwa masu kyau ko marasa kyau domin su (gane Allah su) koma maSa. A dalilin jarrabawar ne ake gane mumini da munafuki, kamar yadda ake gane na kwarai da mugu. Allah Madaukakin Sarki Ya ce; "Ashe, mutane sun yi zaton a kyale su, su ce:"Mun yi imani" alhali kuwa ba a fitine su (jarrabe su) ba? Kuma hakika Mun fitini (jarrabi) wadanda ke a gabaninsu, domin lallai Allah Ya san wadanda suka yi gaskiya, kuma lallai Ya san makaryata (Wato Ya bambanta a tsakanin masu da'awar imanin gaskiya da makaryata)." (Ankabuti: 2-3.).


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallaahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira kuwa bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, mun kwana bayan mun gabatar da ladubban addu'a guda biyar daga cikin goman da Imamu Abu Hamid Alghazaliy ya jera a cikin littafinsa Al'ihyaa'u. Yau za mu fara ne daga ladabi na:

(6) Shi ne mutum ya kasance yana nuna tawali'u (marairaita) da bayyana khushu'i (kankan da kai) da nuna kauna da tsoro da bege da nacewar kwadayin bukatuwa don kaiwa ga cin nasarar samun abin da ake nema wajen Mai abin (Allah).


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, sallallaahu alaihi wasallam, wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa ranar karshe.

Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alkhairin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, sallallahu alaihi wasallam. Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira kuwa data ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, mun kwana a karkashin wannan mukala, a daidai inda muka gabatar da bayani kan abin da shaihin malami Al'imamu Abiy Alkasim Alkushairiy, Allah Ya jikan shi, ya yi nuni a kansa, inda ya ce, "Yana daga sharuddan (samun karduwar) addu'a, ya kasance abincin mutum halal ne." Sannan aka kawo dalili a kan haka na daga hadisin da Imam Muslim ya ruwaito a cikin Sahihinsa, hadisi na 1,015, cikin zakkah, babin kardarta daga abin da aka samu mai tsarki (na halal). Sai kuma manuniyar da wani daga cikin magabata, Yahya bn Mu'az Arraaziy, Allah Ya jikan shi, ya yi, inda yake ce wa Allah, "Yaya za a yi in rokeKa, alhali ni mai sado ne? Kuma yaya za a yi ba zan rokeKa ba, alhali Kai, Mai karimci (Kariimi) ne?"


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Manuniya kan ladubban yin addu'a
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Manuniya kan ladubban yin addu'a

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, sallallaahu alaihi wasallam, wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa ranar karshe.

Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alkhairin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, sallallahu alaihi wasallam. Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira kuwa bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, yau mukalarmu za ta gudana ne, kamar yadda muka fada a makon da ya gabata, kan ladubban yin addu'a, kuma za mu takaita ne a kan abin da yake cikin littafin Al'azkaar na Imam Abu Zakariyya Yahya bn Sharf Annawawiy, sai dai inda bukatar wani abu ta taso. Muna fata Allah Ya ba mu dacewa, amin. Malam ya ce:


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, sallallaahu alaihi wasallam, wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa ranar karshe.

Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alkhairin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, sallallahu alaihi wasallam. Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira kuwa bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, yau mukalarmu za ta gudana ne, kamar yadda muka fada a makon da ya gabata, kan muhimmanci da matsayin addu'a (rokon Allah). Yadda kanun mukalar ya nuna, a matsayin addu'a na babban makami, yana iya isa a ce lallai tana da muhimmanci, kuma kamar yadda mukalar da ta gabata ta nuna na cewa Allah na fushi da wanda ba ya rokonSa, yana iya isa a ce lallai tana da matsayi. In Allah Ya so, bayanin da zai zo, zai kara fito mana da wannan manufa sosai don mu fahimce ta. Allah Ya sa abin da za a karanta ya zama mai amfani gare mu duniyarmu da lahirarmu, amin.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi sawunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Bayan haka, yau, 27 ga Zul-kida shekara ta 1436 Bayan Hijira, insha Allah a takaice, za mu dubi rantsuwar da Allah Ya yi da kwanaki goma na watan Zul-Hajji, sannan sai bayani kan sha'anin Layya da Sallar Idi da fatan Allah Ya sa bayanin ya amfane mu duniya da Lahira.

Wadannan kwanuka goma na watan Zul-Hajji, su ne wadanda Allah Ya yi rantsuwa da su, kamar yadda malamai (kamar su ++Abdullahi Ibn Abbas da Ibn Zubayr da Mujahid da wasunsu cikin Salaf da wadanda suka maye gurabunsu) suka bayyana, yayin da Allah Ya ce, "Ina rantsuwa… da Darare Goma… Ko a cikin wadannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?" Surar Fajr, aya ta 1- 5.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Idan za ku fadi magana ku yi adalci
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Idan za ku fadi magana ku yi adalci

Daga hudubar Imam Salah bin Muhammad Al-Budair

Masallacin Annabi, Madina

Godiya ta tabbata ga Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Ina shaidawa Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma ManzonSa ne. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku ji tsoron Allah, hakika wanda ya ji tsoron Allah ya tsira, wanda kuma ya bi son zuciya ya bata. "Ya ku wadanda suka yi imani ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa da takawa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa (Musulmi)." (k:3:102).

Ya ku Musulmi! Ku sani ana fassara maganar mutum bisa jahilci kuma a kafa masa hujja a kai. Kuma harshe yana da kaifi biyu kodai jahilci ya fi munanta shi, ko hankali ya rinjayar da shi. Kuma laifin magana barin yin adalci yayin furuci.

Wani mawaki ya ce: "Yin shiru ya fi yin furuci da zunubi. Ka kasance mai shiru ka kubuta, idan kuma za ka yi magana, to, ka yi adalci."


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

FASSARAR AQIDAR DAHAWIY
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Littafan Aqidah

FASSARAR AQIDAR DAHAWIY

Malaman Hadisi sun yi rubuce-rubuce masu yawa akan aqidah. Akwai taqaitattu, akwai masu tsayi. Sannan akwai wadanda ke ruwaitowa da isnadi. Akwai kuma wadanda malaman baya suka rubuta ta hanyar naqaltowa daga littafan magabata. An kuma sami wadanda suka zayyana aqidar salaf a waqe.
Daga cikin liffafan aqida masu isnadi akwai:
– Assunnah Na Abdullahi Dan gidan Imamu Ahmad
– Assunnah na Ibn Abi Asim
– Khalq Af'alil Ibad Na Al-Imamul Bukhariy
– Usulus Sunnah Na Ibn Abi Zamanin
– Sharh Usuli I'itiqadi Ahlis Sunnah Na HibatulLaahi Al-Laalaka'iy
– Kitabut Tauhid Na Ibn Khuzaimah
– Kitabul Arsh da Kuma Al'ulu dukkansu na Al-Imamuz Zahabi
– Kitabut Tauhid Na Ibn Mandah
– Zammul Kalam Na Abu Ismail Al-Harawiy
Da sauransu da yawa kwarai. Kamar littafan Al-Imamul Baihaqi da na Daraqudni da na Darimiy da Ibn Dattah da makamantansu.
Akwai kuma littafai taqaittatu wadanda ke dunkule bayani ba tare da dogon sharhi ba.
Alal misali


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

YADDA AKE DAUKAR RAN KAFIRI KO FASUQI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
YADDA AKE DAUKAR RAN KAFIRI KO FASUQI

Manzan Allah (saw )yaci gaba ba fadin cewa:hakika bawa kafiri ko fasiqi idan zai bar duniya malaiku zasu sakko wajansa masu bakin fuska da tsanani tare dasu akwai likkafani na wuta su zagayeshi tsawan ganinsa sannan malaikan mutuwa yazu saiyace yake wanan rai mummuna ki fito zuwaga fushin Allah.saita fito daga jikinsa ana fusgarta ana janta kamar wanda aka sawa sarkoki awuya da hannaye da kafafuwa ana jansa duk jijiyoyinsa su tsinke gabobin su balle. duk malaiku su tsine masa duk saman da akaje saisuce waya wannan ?

Sai ace wanene dan wane.har sai anje sama da bakwai sai Allah yace:asanya littafinsa asijjin inda ake sa littattafan kafirai sai Allah yace:adawo da bawana kasa dayi alkawarin daga cikin ta suka fito kuma daga cikin ta zasu koma. Sai a wurgo ruhinsa tun daga sama duk ya fatattake manzan Allah (saw) yace:idan har kafiri zai shiga aljannah to sai dai idan rakumi zai iya shiga ta kofar tsinin allora.saiamayar masa da ransa acikin qabarinsa alokacin yana jin takun takalman yan uwansa.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

YADDA AKE DAUKAR RAN MUMINI DA YADDA AKE DAUKAR RAN KAFIRI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
YADDA AKE DAUKAR RAN MUMINI DA YADDA AKE DAUKAR RAN KAFIRI

An rawaito hadisi daga barrau ibn azib yace :(mun fita tare da manzan Allah (saw)a janaizar wani mutum daga madina bayan munje maqabarta sai muka tarar baa gama hakan qabarin ba sai manzan Allah (saw) ya zauna ya kalli alqibla muma sai muka zauna agefansa mukai nutsuwar da tsuntsu zai iya hawakanmu.sai ma aiki ya kalli sama ya kalli kasa sau uku sai yace:kunaimi naimi tsarin Allah daga azabar qabari sau uku sannan yace:allah ina naiman tsarinka daga azabar qabari sau uku sai yace:hakika idan mumini zai rabu da duniya malaiku zasu zo masu farin fuska kamar rana tare da likkafani na aljannah da turare su zauna ajefansa tsawan ganinsa sai malaikan mutuwa yazu ya zauna akansa yace:yake Wannan rai nai tsarki da nutsuwa ki fito zuwa rahamar Allah da yardarsa saita ran ya fito kamar ana zubarda ruwa abuta sai malaiku suyi masa salati ayi sama dashi duk kofar da aka zo sai malaiku suce wannan wana raine mai kamshi haka sai ace wane ne dan gidan wane irin sunanda ake kiransa aduniya har sai anje sama ta bakwai sai


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

003 JININ DABI'A GA MATA RUBUTU NA 3
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
003 JININ DABI'A GA MATA RUBUTU NA 3

Amma MATSAYI NA BIYU: Shine gwargodon Haila wato gwargodon zamaninta, haqiqa malamai sunyi sa6ani mai yawa a kusan zantuka guda 6 koma 7.
.
Ibnul Munzir Yace: ''wata jama'a tace: babu wata iyaka ta kwanaki ga mafi qarancin Haila ko mafi yawanta''sai nace: wannan magana kamar maganar Darimiy ce wacce ta gabata, haka kuma shine za6in Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah kuma shine dai dai domin qur'ani da sunnah da kuma abunda ake gani yau da gobe, sun nuna hakan.
.
DALILI NA FARKO: Fadinsa Madaikakin sarki: ''kuma suna tambayarka game da jinin haila kace shi qazantane saboda haka lu nisanci mataye a yayin da suke haila.kada ku kuaancesu har sai sunyi tsarki'' [suratul Baqara aya 222]
.
Sai ALLAH ya sanya matuqar hana kusantar itace samun tsarki bai sanya matuqar ta zama tsayin wuni ko dare ko kwana 3 ko kwana 15 ba.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

002 JININ DABI'A GA MATA RUBUTU NA 2
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
002 JININ DABI'A GA MATA RUBUTU NA 2

FASALI NA BIYU: CIKIN ZAMANIN HAILA DA GWARGODONSA.
.
Zance acikin wannan fasalin yana da matsayi guda 2.
.
MATSAYI NA FARKO: A cikin shekarun da haila take zuwa acikin su.
.
MATSAYI NA BIYU: A cikin lokacin Haila.
.
Amma MATSAYI NA FARKO shekarun da haila tafi rinjaye acikinsu shine: tsakanin shekara 12 Zuwa shekara 50, amma ana samu sau da yawa mace tana yin haila a kafin haka ko bayan haka gwargodon halinta da tasowarta da kuma tsufanta. Lallai malamai sunyi sa6ani akan shin shekarun da haila take zuwa aciki suna da iyaka da aka ayyana ta yadda mace ba zatayi haila gabanninsu ba ko bayansu. Kuma shin jinin da yake zuwa ga mace a gabanninsu ko bayansu jinin haila ne ko na cuta? Malamai sunyi sa6ani acikin wannan.
.
Darimiy yace: Bayan ya kawo sa6anin: dukkan wadannan kuskure ne awajena domai a baki dayan wannan yana komawa ne izuwa samuwar jinin, duk jinin da ya samu a kowani hali da shekaru, ya wajaba a sanya shi a matsayin haila. Wallahu a'alamu. (Al-majmu'u sharhil Muhazzab 1/336)


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

001 JININ DABI'A GA MATA RUBUTU NA 1 -- ^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
001 JININ DABI'A GA MATA RUBUTU NA 1

001 JININ DABI'A GA MATA RUBUTU NA 1

FASALI NA FARKO
ACIKIN MA'ANAR JININ HAILA DA HIKIMARSA !!!
.
HAILA A LUGGA: shine kwararar abu da kuma gudanarsa.
.
A SHARI'A: shine jini da yake faruwa ga mace na dabi'a ba tare da wani sababi ba acikin wasu sanannun lokuta. Shine jini na dabi'a ( mai zubowa) ba tare da wani sababi na rashin lafiya ba ko rauni ko zubewar ciki ko haihuwa ba.
.
Saboda cewa shi jinine na dabi'a don haka yana sa6awa gwargodon halin mace da yanayin tasowarta da tsufanta, saboda haka mata suna sassa6awa a cikinsa sassa6awa mabanbanta na zahiri.
.
HIKIMA A CIKINSA: yayin da dan tayi ya kasance acikin mahaifiyarsa bazai yuwu ya ringa yin kalaci da irin abunda mutum na wajen ciki yake yin kalaci dashi ba. Kuma bazai yuwu ga wanda yafi kowa tausayinsa ba ya iya sadar da kalaci gare shi (ta kowace hanya ba) saboda haka sai ALLAH (SWT) ya sanya jijiyoyin jini acikin mace wanda ta hanyar sune dan tayin da yake cikin mahaifiyarsa zai dinga yin kalaci acikin mahaifiyarsa ta hanyar cibiya jinin zai dinga shiga ta jijiyoyin d'an cikin yayi kalaci dashi. Tsarki ya tabbata ga ALLAH mafi kyawun masu halitta.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

BAYANIN IBNU TAIMIYYAH GAME DA CIN YANKAN DA AHLUL KITABI SUKA YI SABODA IDINSU
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
By: Dr. Ibrahim Jalo

BAYANIN IBNU TAIMIYYAH GAME DA CIN YANKAN DA AHLUL KITABI SUKA YI SABODA IDINSU

Kwanakin baya mun yi bayani gameda hukuncin karban kyautukan idi na dukkan nau'ukan kafurai, mun kuma yi bayani game da hukuncin cin yankan da Ahlul Kitabi; watau Yahudawa da Kiristoci suka yi saboda idodinsu, to amma muna jin akwai mutanen da suka karanta wancan rubutun namu amma kuma suka kasa fahimtar wani bangare nasa, watakila saboda yawan rubutun. Dalilin da ya sa kuwa muka ce akwai wadanda ba su fahimci abin da aka rubuta sosai ba shi ne: irin yadda aka cigaba da aiko mana da tambayoyi game da mas'alar cin yankan da Ahlul Kitabi suka yi domin bukuwan idodinsu.

A wannan rubutu namu za mu kawo bayanan Salaf ne da Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya kawo dangane da hukuncin cin yankan da Yahudawa da Kiristoci suka yi domin bukukuwan idodinsu. Ibnu Taimiyyah ya ce a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqim 2/555,558 :-


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

ISBALIN TUFAFI YANGA CE A MAHANGAR MUSULUNCI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Dr. Ibrahim Jalo

ISBALIN TUFAFI YANGA CE A MAHANGAR MUSULUNCI

Tabbas yin aiki da ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah cikin Aqidah, da Ibadah, da Mu'amalah shi ne alheri ga mutane duniyarsu da lahirarsu.

Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce Isbalin tufafi yanga ce. Imamu Abu Dawuda ya ruwaito hadithi na 4086 da isnadi sahihi daga Sahabi Jabir Bin Sulaim Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-

(( ﻭﺍﺭﻓﻊ ﺍﺯﺍﺭﻙ ﺍﻟﻰ ﻧﺼﻒ ﺍﻟﺴﺎﻕ ﻓﺎﻥ ﺍﺑﻴﺖ ﻓﺎﻟﻰ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ ﻭﺍﻳﺎﻙ ﻭﺍﺳﺒﺎﻝ ﺍﻻﺯﺍﺭ ﻓﺎﻧﻬﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺨﻴﻠﺔ ﻭﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﺤﺐ ﺍﻟﻤﺨﻴﻠﺔ)).

Ma'ana: ((Ka dage zaninka zuwa tsakiyar kwabrinka, in ka ki to zuwa idon sawunka, ka nisanci isbalin tufa lalle shi daga yanga yake, kuma lalle Allah ba ya son yanga)). Babu Musulmin kirki da zai san wannan hadithi ingantacce sannan ya ci gaba da kiran mutane cewa su rika yin isbali matukar dai isbalin da suke yi ba saboda yanga ba ce suke yin sa! Saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ya riga ya gama magana cewa zatin isbalin kansa yanga ce.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

MARIGAYI SHAIKH JA'AFAR MAHMOUD ADAM ALLAH YA YI MA SA RAHAMA JAAFARMAHMU
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
MARIGAYI SHAIKH JA'AFAR MAHMOUD ADAM – ALLAH YA YI MA SA RAHAMA JAAFARMAHMUDADAM.ORG

Marigayi Shaikh Ja'afar Mahmoud Adam – Allah Ya yi ma sa rahama

jaafarmahmudadam.org/

ya na daya ne daga cikin mafiya shahara da kuma fitattun Malaman Musulunci kuma Jagorori a kan shiriya da miliyoyin al'ummar Musulmin Najeriya – Musamman Arewacinta – da kuma yammacin Afirika su ka gani a farkon karni na 15 bayan Hijrar Manzon Allah (sallallahu 'alaihi wa alihi wa sallam) daga Makkah zuwa Madina.

Shehin Malamin ya yi rayuwa cike da kokari da sadaukar da kai domin addininsa wadanda ke bayyana karara daga irin kishinsa na ganin an samara da Al'ummar Musulmi ta gari wadda ke girmama tare da riko da koyarwar addinin Musulunci kamar yanda Annabi Muhammad (sallallahu 'alaihi wa alihi wa sallam) ya koyar kuma bisa fahimtar magabata na kwarai.

Don haka ne ya tafiyar da 'yar takaitacciyar rayuwarsa a yada karantarwar addinin Islama ta hanyar bayar da darussa, laccoci da kuma tarrurrukan karawa juna sani, yin fatawowi da kuma shirye-shirye daban- dabam a kan batutuwa masu yawa, a wurare da dama. Dadin dadawa kuma, ya kasance mai matukar damuwa da kulawa da dalibai ma su karatu a fagagen Addinin Musulunci da fannonin rayuwa.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

MUSABAKAR HADDAR ALQUR'ANI KO HADITHI KO WANI NAU'IN ILMI A MAHANGAR M
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
MUSABAKAR HADDAR ALQUR'ANI KO HADITHI KO WANI NAU'IN ILMI A MAHANGAR MUSULUNCI

Da yawa daga cikin wadanda suka zaba wa kansu sabanin shiriyar Manzon Allah cikin gudanar da addininsu suna ganin cewa: In har Idin Maulidi bidi'ah ne, to kuwa lalle Musabaka a kan haddar Alqur'ani Mai girma, ko haddar Hadithan Annabi masu daraja ko haddar wani ilmi na Musulunci su ma yin su bidi'ah ce!!!

A nan muna ganin cewa yawan nisantar wadannan mutane ga littattafan Shari'ah na maluman Musulunci ne ya sa ba su ma san cewa: Dukkan abin da halaccinsa ya tabbata ta yanyar Ijma'in Musulmi cikin wani zamani daga cikin zamuna, to dole ne ya zamanto daya daga cikin abubuwa uku:-

1- ko dai ya zamanto Mubaahi, watau abin da yin sa da rashin yin sa duk daya a idanun Shari'ah.

2- ko kuwa ya zamanto Mustahabbi, watau abin da in har ba a yi shi ba to ba a yi wani laifi ba, in kuma aka yi shi to ana da wani lada na musamman.

3- ko kuwa ya zamanto Waajibi, watau abin da in har ba a yi shi ba za a sami zunubi, in kuma an yi shi to an yi abin da Shari'ah ta tilasta yin shi.

shi kuwa Musabaka domin haddar Alqur'ani Mai girma abu ne da Maluman Sunnah, da su kansu masu bidi'ah na Duniya suka hadu a kan halaccinsa a bisa hujjar kiyasin shi a kan Musaabakokin da Nassi ya zo da halaccinsu.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

GARKUWAR MUSULMI TA ADDU'O'I DAGA ALKUR'ANI DA SUNNAH (Hisnul Mus
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
GARKUWAR MUSULMI TA ADDU'O'I DAGA ALKUR'ANI DA SUNNAH (Hisnul Muslim)

Rubutu Na Farko 0001

TA'ALIFIN Shaikh Sa'id Ibn Ali Ibn Wahb Alkandahi

FASSARAR Dr. Bashir Aliyu Umar Hafizahullah

RUBUTAWA Abubakar Nuhu Koso (Abu Abdullah Assunni)

GABATARWAR MAWALLAFI.

Dukkan yabo da godiya ta tabbata ga Allah muna godiya gareShi, mana neman taimakonsa, kuma muna neman gafararsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrance-sharrencen rayukanmu da miyagun aiyukanmu. Wanda Allah Ya shiryeshi babu mai batar dashi, wanda kuma Ya batar babu mai shiryar dashi. Ina mai shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, babu abokin tarayya gare Shi, kuma ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne, Allah Yayi tsira a gare Shi da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyakkyawan kwaikwayi har zuwa ranar kiyama kuma ya yi musu aminci, aminci mai yawa.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

SHAWARWARI 60 GA MATAN AURE
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

SHAWARWARI 60 GA MATAN AURE

Shawarwari 60 ga matan aure domin samun zamantakewa mai inganci, da aure mai albarka, kamar yadda muka Bawa maza suma shawara 60.

1.Ta rike masa amana, 2. Tayi masa biyayya akan duk abinda ba sabon Allah bane.

3. Ta kula da dukiyarsa 4. Ta kula da Sallah akan lokaci. Da addua zaman lafiya 5. TA girmama shi a gaban idansa 6. TA kare girmansa a bayan idansa 7. Ta so abinda yake so, koda ba abin so bane a wajenta 8. Ta ki abinda yake ki, koda ba abin ki bane awajenta 9. Ta damu da duk abin da ya damu dashi.

10. Ta kau da kai daga abinda ya kauda kai, daga gareshi 11.Tayi fushi , da dukkan abinda yayi fushi da shi .

12.Ta yarda da duk abinda ya yarda da shi 13.Idan ya bata kadan taga yawansa 14.Idan ya bata da yawa tayi godiya 15.Ta farka daga bacci kafin ya farka 16.Sai yayi bacci kafin tayi 17.Tayi hakuri idan yayi fushi 18 Tayi taushi idan yayi tsauri 19.Ta lallashe shi idan ya hasala 20.kada ta nuna raki a gabansa 21.kada tayi kuka alhali yana dariya 22.kada tayi dariya alhali yana kuka 23.kada ta tsaya kai da fata sai yayi mata wani abu 24.kada ta matsa masa da bukatu 25.kada ta dinka ganinsa kamar yaran gida 26.kada ta dinka yi masa gyara barkatai 27.kada ta dinka kushe tsarinsa 28.Ki dinka zuga shi a gaban danginta 29.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA, TSARABAN RAMADAN
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA, TSARABAN RAMADAN

(1) Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawa 6/505:-

(( ﻭﺍﻟﺨﻴﺮ ﻛﻞ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻓﻲ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ ﻭﺍﻻﺳﺘﻜﺜﺎﺭ ﻣﻦ ﻣﻌﺮﻓﺔ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ ﻓﻴﻪ ﻭﺍﻻﻋﺘﺼﺎﻡ ﺑﺤﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﻼﺯﻣﺔ ﻣﺎ ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﻭﺍﻷﻟﻔﺔ ﻭﻣﺠﺎﻧﺒﺔ ﻣﺎ ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻼﻑ ﻭﺍﻟﻔﺮﻗﺔ ﺍﻻ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﺃﻣﺮﺍ ﺑﻴﻨﺎ ﻗﺪ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻓﻴﻪ ﺑﺄﻣﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺠﺎﻧﺒﺔ، ﻓﻌﻠﻰ ﺍﻟﺮﺃﺱ ﻭﺍﻟﻌﻴﻦ )).

Ma'ana: ((Sannan alheri kuma dukkan alheri yana cikin bin magabata na gari, da kuma yawaita ilmin hadithin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, da kyakkyawar fahimta cikinsa, da yin riko da igiyar Allah, da lazimtar abin da ke kira zuwa ga jama'a da hadin kai, da nisantar abin da ke kira zuwa ga sabani da rarraba, sai fa abin da ya kasance al'amari ne bayyananne da tabbas Allah da manzonSa ne suka yi umurni cikinsa da wani umurni na a nisanta, to wannan kam biyayya sau da kafa)).

(2) Alhaafiz Ibnu Rajab ya ce cikin littafinsa Alhikamul Jadiiratu Bil Izaa'ah shafi na 12:-


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

GUZURI GA MANIYYATA AIKIN HAJJI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
GUZURI GA MANIYYATA AIKIN HAJJI

Ra'ayoyin Jama'a Published on Friday, 12 September 2014 00:00 Written by Sheikh Abdullahi Bala Lau Hits: 355 Ya kai dan'uwana Alhaji, wanda Allah Ya zabe shi a tsakanin miliyoyin Musulmi, domin ziyarar dakinSa mai alfarma, ina rokon Allah da ya jibinci al'amuranka a Duniya da Lahira, kuma ya sanya ka mai albarka duk inda kake. Ya kai dan'uwa mai girma, ya kai wanda ka gamu da wahalhalun tafiya, kuma kayi hakuri da su, kuma ka fitar da dukiyarka, kuma ka bar gidanka, ka yi bankwana da iyalinka da 'ya'yanka, ba don komai ba sai domin sauke faralin da Allah ya dora maka, na ziyarar dakinSa mai alfarma, Allah ya sanya hajjinka karbabbe ne, kuma ya gafarta maka zunubanka, ya rufa maka asiri tare da mu gaba daya.

Ya dan'uwana Alhaji, saboda son da nake maka da sha'awar da kake ba ni, tare da farin cikina da zuwanka, da jin dadina da kubutarka, ya sa na fuskance ka da wasu sakonni, saboda in sauke wani wajibi da ya hau kaina, game da kai, kuma in kasance na bi umurnin Allah da ya ce: ''Kuma suka yi wa juna wasiyya da gaskiya, kuma suka yi wasiyya da hakuri''.

(asr 3)
Kuma in bi umurnin masoyinmu, shugabanmu, abin koyinmu, Annabinmu Muhammad (SAW) da yake cewa:


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

KANASON ALJANNAH CIKIN SAUKI?? TO GA MAFITA
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Abdullahi Muhammad Auwal KANASON

ALJANNAH CIKIN SAUKI??

TO GA MAFITA..........

Manzon Allaah sallallaahu alaihi wasallam yana cewa:

( ﻣﻦ ﺳﻠﻚ ﻃﺮﻳﻘﺎً ﻳﻠﺘﻤﺲ ﻓﻴﻪ ﻋﻠﻤﺎً؛ ﺳﻬّﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻪ ﺑﻪ ﻃﺮﻳﻘﺎً ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨّﺔ ) ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .

A wani hadisin kuma yana cewa:

( ﻣﻦ ﺳﻠﻚ ﻃﺮﻳﻘﺎً ﻳﻄﻠﺐ ﻓﻴﻪ ﻋﻠﻤﺎً؛ ﺳﻠﻚ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻪ ﻃﺮﻳﻘﺎً ﻣﻦ ﻃﺮﻕ ﺍﻟﺠﻨﺔ ). ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺻﺤّﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .

Ma'ana: (Duk wanda yabi wata hanya ko ya ri'ki wata hanya wanda yike neman ilmi a cikinta; to Allaah zai sau'ka'ke yakuma yassare mishi da wannan ilmin hanya zuwa Aljannah).


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: