Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
EsinIslam Media: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Search on This Topic:   
[ Go to Home | Select a New Topic ]

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan kammalalliyar godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa; muna neman taimakonSa; muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu; wanda duk Allah Ya shiryar, to shi ne shiryayye, wanda duk Allah Ya batar, to ba mai shiryarwa a gare shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai ba Shi da abokin tarayya; ina shaidawa, hakika, Annabi Muhammadu Bawan Allah ne kuma ManzonSa ne (SAW).

Bayan haka dan tsokaci ne nake son yi kan sharuddan da suka kamata mutum ya lura da su kafin ya kafirta wani, kuma akwai bukatar a mayar da hankali sosai don ganin an nisanci aiwatar da abin da ba a sani ba, ko ba a fahimce shi ba sosai a sha'anin addini. Allah Ya ba mu dacewa.

Wannan rubutu ne da aka tsakuro daga makalar da marigayi Gambo Bako Malumfashi, Allah Ya jikansa Ya kuma gafarta masa, ya yi, dangane da mas'alar kafirci, kodayake har yanzu ba a wallafa littafin ba:

Mas'alar kafirtawa, mas'ala ce mai girma, kuma mai hadarin gaske, wadda ta dalilinta ne rarrabuwa da kiyayya da kashe-kashe tsakanin Musulmi suka auku. Don haka ya zama wajibi mutum ya yi tsantseni wajen fahimtar shiryarwa ta Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a kan wannan mas'ala.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Wani abu kan Sallar Idi
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Wani abu kan Sallar Idi

A yayin da ranar Litinin mai zuwa ta kasance ranar Babbar Sallar bana, sakamakon cewa za a hau Arfa a jibi Lahadi, mun gabato da wata fadakarwa kan abubuwan da suka kamata mu yi da wadanda za mu guje musu a wannan rana ta farin ciki kamar haka:

Sallar Idi da ladubbanta:

Malamai sun hadu cewa ta kowane hali ko dalili a ranakun Idi biyu a hana yin azumi, koda na bakance ko kaffara ne kamar yadda Imam Annawawi ya nakalto a sharhinsa ga Sahihu Muslim. (8/15). Kuma sun ce, hikimar hanin ita ce idan aka yi azumin kamar an ki amincewa da liyafar da Allah Ya shirya ga bayinSa ne. (Nilul Audar, 4/262).

Sannan Sunnah ce, a yi wanka a sanya sababbin kaya ko a wanke wadanda suka fi kyau a sanya, kuma a fesa turare a fita masallacin Idi, maza da mata manya da yara tare da tsare ladubban fitar, wato kada mata sun caba ado ko su sanya turare kuma kada a cakuda maza da mata da sauran abubuwan da shari'a ta hana.

Ranar Sallah ranar ce ta murna da farin ciki da bukukuwa, to, sai dai kada wajen murna a wuce gona da iri. Kada murna ta sanya a koma ga sabo. Kada murna ta sa a aikata bidi'o'in da za su bata kyawawan ayyuka.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)

Na Khalid Bin Salamah

Fassarar Imam DSP Ahmad Adam Kutubi

Manufa ta Biyu: Tabbatar da girman Allah Madukaki:

Allah Ta'ala Ya ce: "Wancan ke nan. Kuma wanda ya girmama ibadojin Allah, to lallai ne (ita girmamawar) tana daga ayyukan zukata na ibada." (AI-Hajji). Su kuwa kalmomin sha'a'ir da mash'ar; su ne duk wani abu da ya sanya jin girman Allah da wadatuwarSa a cikin zuciya, da kaskancin abin halitta da bukatuwarsa, wannan kuwa yana bayyana karara a kasar Muzdalifa. To tsarkin ya tabbata ga Wanda wuyaye suka risina ga girmanSa. Hakika duk wanda ya kwatanta tsakanin yanayin alhazai a Mina da Arfa ta wani bangaren da kuma- yanayinsu a Muzdalifa a daya gefen, zai lura da bambancin mai zurfi a tsakanjn yanaye-yanayen guda biyu, wadanda su ne cewa alhazai a kasar Mina da Arfa bambancin matsayinsu yana bayyana karara ta bangaren wadata da talauci, cikin irin hemominsu da abincinsu da abin hawansu.

A dai Mina da Arfa za ka samu talakan da yakan zauna da yunwa a gefen hanya, kuma za ka samu mawadacin da yakan ja hankali da hemarsa da yanayin tufarsa da kuma kayansa.

Kai ta kai wani lokacin ma alhazai na iya shagaltuwa a nan da yanayin shiga ta ababen halitta ga barin wadatar Mahalicci Mai tsarki, kuma su shagala da girman ababen haiitta ga barin girman Mahalicci wanda tsarki ya tabbata gare Shi, har ma wadansu gafalallun zukata kan kusa su manta wane ne Mai girman ma a lokacin!


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)

Na Khalid Bin Salamah
Fassarar Imam DSP Ahmad Adam Kutubi

ambaya: Saboda me duga-dugan Manzo (SAW) masu alfarma ba su taba kasar Arafa ba a Hajjin Ban-Kwana?

Yana daga abin da aka sani yanke cewa Manzon Allah (SAW) abin so ne a wajen kowane mumini, haka nan gurabansa (abubuwan da ya bari kamar tufafi da abubuwan da ya yi amfani da su) su ma ababen so ne, kuma ma da yawa mutane na nemansu, kuma hakika Allah Ya yi nufin kada wani gurbin wani abin so ya kasance a Arafa ban da Shi Maddaukakin Sarki, koda kuwa guraben Manzon Allah (SAW) ne. Watakila hikamar haka- Allah Shi ne Mafi sani – ita ce da a ce Manzon Allah (SAW) yana da wani gurbi a Arafa da wadansu mutane sun rataya da ita su shagala da ita ga barin soyayyar Allah Ta'ala a wannan wuni mai girma, kuma da zukata sun karkata zuwa ga soyayyar bawa ga barin soyayyar Ubangiji Mai tsarki. Yaya haka kuwa ba zai auku ba, alhali mu mun sani cewa mafi yawan dalilin da mutane suka bata ta hanyarsa
shi ne wuce gona da iri cikin soyayyar salihan bayi da gurabensu.

Ashe shirka ta farko a bayan kasa a zamanin Annabi Nuhu (AS) ba ta kasance ta dalilin zurfafawa ba ne-cikin soyayyar salihai da gurabensu? Shin Nasara (Kiristoci) ba sun bata ba ne da shisshigi cikin soyayyar Annabi Isa (AS)? Hakan Rafidawa ba sun bata ba ne ta hanyar wuce gona da iri cikin soyayyar Aliyu da Husain (Allah Ya yarda da su)? Kuma wadansu daga cikin Sufaye sun bata ne saboda zurfafawarsu cikin soyayyar Jilani da waninsa. Sun so su irin son da ya yi kafada-da-kafada da sonsu ga Allah Mabuwayi, Madaukaki, sai suka halaka a cikin haka.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Sallar Idi da ladubbanta
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Sallar Idi da ladubbanta

Malamai sun hadu cewa ta kowane hali a ranakun Idi biyu a hana yin azumi, koda na bakance ko kaffara kamar yadda Annawawi ya nakalto a sharhinsa ga Sahihu Muslim. (8/15). Kuma sun ce, hikimar hanin ita ce idan aka yi azumin kamar an ki amincewa da liyafar da Allah Ya shirya ga bayinSa ne. (Nilul Audar, 4/262).

Sannan Sunnah ce, a yi wanka a sanya sababbin kaya ko a wanke wanda suka fi kyau cikin tufafin mutum, a sa turare a fita masallacin Idi, maza da mata manya da yara tare da tsare ladubban fitar, wato kada mata sun caba ado ko sun sanya turare kuma kada a cakuda maza da mata da sauran abubuwan da shari'a ta hana.

Ranar Sallah ranar ce ta murna da farin ciki da bukukuwa, to, sai dai kada wajen murna a wuce gona da iri. Kada murna ta sanya a koma ga sabo. Kada murna ta sa a aikata bidi'o'in da za su bata kyawawan ayyuka.

Daga cikin ladubban murnar Sallah akwai:

1. Taya juna murna da duk lafazin da ya sauwaka, kamar "Allah Ya karba mana da makamancin haka. An ruwaito cewa wasu daga magabatan kwarai sun aikata haka. Misali Jubairu bin Nufair ya ce, "Sahabban Annabi (SAW) idan suka hadu da juna sukan ce, "Allah Ya karba mana, Ya karba muku." Imam Ahmad ya ce Isnadinsa mai kyau ne, sannan Hafiz ya kyautata Isnadinsa a cikin Fathul Bari (2/517), kuma a duba Tamamul Minnah na Albani don karin bayani. Kuma an ruwaito Imam Ahmad yana cewa: "Ba zan fara fada wa mutum haka ba, amma idan ya fada min zan amsa." Shi kuma Shaihul Islam Ibnu Taimiyya (RH) ya ce, "Fara taya murna ba Sunnah ce da aka yi umrni da ita ba, kuma ba a hana ba, wanda ya aikata, ya yi koyi, wanda ya ki, ya yi koyi." Majmu'u Al Fatawa (24/253). Hakika irin wannan gaisuwa na yin tasiri wajen karfafa zumunta da ruhin soyayya a tsakanin Musulmi.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Kyauta da kyauta – yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi'un Musulmi. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma ya koyar da cewa kyauta da kyauta-yi ba ta rage dukiya; Amincin Allah Ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, mun yi tsokaci mai tsawo dangane da nuni kan kyauta cikin kyauta-yi tare da kawo misalai masu yawa da manuniya kan muhimmancin wannan dabi'a daga Hadisan Ma'aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya isa ga mai hankali da lura ya kama aiki. Allah Ya kara mana taimakonSa. Yau, in Allah Ya so, za mu kammala mukalar daga cewa:


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Kyauta da kyauta – yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi'un Musulmi. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma ya koyar da cewa kyauta da kyauta-yi ba ta rage dukiya; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, mun kwana bayan mun koro bayani a karkashin kanun, "Allah Yana sane kuma ana musanyawa," har muka kai daidai inda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, "Dukiyar da take taskance ita ce wadda aka bayar da ita saboda Allah." A'isha (Allah Ya yarda da ita), ta ba da labarin wata tunkiya da aka yanka, aka yi ta rabon namanta, har sai lokacin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya tambayi ko me ya rage a cikinta, sai aka ce masa, "Karfata daya." Sai ya ce, "An taskance komai na tunkiya, sai karfata daya kadai." Imamu Tirmiziy ne ya ruwaito shi kuma ya ce Hadisi ne mai kyau, ingantacce.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi'un Musulmi. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma ya koyar da cewa kyauta da kyauta-yi ba ta rage dukiya; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, yau, kamar yadda kanun mukala ya nuna, za mu duba dabi'ar kyauta da kyauta-yi ne, kamar yadda bayanin haka ya zo a cikin littafin Shakhsiyyatul Muslim Kama Yasughuhal Islam Fiy Alkitab Wassunnah na Dokta Muhammad Ali al-Hashimi, tare da wasu bayanai daban. Allah Ya ba mu dacewa wajen bi da kuma aiwatar da wannan dabi'a, wadda ba ta sa talauci, don mu samu rabauta duniyarmu da lahirarmu.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Ibrahim Jalo Jalingo

Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai

Muna tabbatar wa al'ummar Musulmin Duniya cewa babu wani nassi daga Alkur'ani da Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah, da yake haramta jefa kuri'a saboda zaben Shugaban Kasa ko waninsa, haka nan babu wani nassi daga Alkur'ani ko Sunnah da yake haramta nada Shugaba ta hanyar jama'a masu rinjaye, haka nan babu wani nassi daga Alkur'ani ko Sunnah da ya halatta kashe masu jefa kuri'unsu saboda zaben wanda zai mulke su: shugaban Kasa, ko gwamna, ko wani dan majalisa.

**

Sannan muna tabbatar wa Musulmin Duniya cewa Nassi da Ijmaa'i duk sun tabbata a kan halacci da kuma wajibcin yakar Khawaarijawa masu kashe dukkan wani da ya saba wa bidi'arsu da batarsu. Ga kadan daga cikin dalila:-

1. Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 7/481 :-

((وان قتال الخوارج مما امر به صلى الله عليه وسلم ولذلك اتفق على قتالهم الصحابة والاءمة)).

Ma'ana: ((Kalle yakar Khawaarijawa yana daga cikin abin da (Annabi) mai tsira da amincin Allah ya yi umurni da shi, wannan shi ne ma ya sa Sahabbai da sauran Shugabanni suka yi ittifaki a kan yakarsu)).


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Yanke Farce Da Aski Ga Wanda Zai Yi Layya: Me Ya Tabbata A Sunna?
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Rubutawar: Dr. Mansur Sokoto

Me Ya Sa Yan Shi'a Suke Kin Banu Umayya?! -Dr Mansur Sokoto

Yanke Farce Da Aski Ga Wanda Zai Yi Layya: Me Ya Tabbata A Sunna?

2 ga Dhul Hajji1438H (24/8/2017)

A can baya inda muka fito, albarkacin kiran Danfodiyo da tajdidin Sheikh Abubakar Mahmud Gummi *_(Allah ya jikan su da gafara gaba daya)_* ba mu bukatar sai mun fadada sharhi a kan mas'ala idan muka kawo Hadisin da ya tabbatar da ita. Musamman kuma a yan shekarun nan na baya, bayan bayyanar matasan Malamai masu kira zuwa ga Sunnah a cikin kungiyar Izala da wadanda ma ba a cikin ta ba. Amma a yan kwana kwanan nan abin ya fara sauyawa saboda bayyanar wasu wadanda babu wata Sunnah da suka bari sai sun dauki sungumi suna son rusa ta. Suna amfani da sunan Malikiyya, alhali Imam Malik da Malikawan Malamai sun yi hannun riga da wannan tafarki nasu.

Hana yanke farce da cirar gashi ga wanda yake niyyar yin layya, Sunnah ce da Nana Ummu Salma (R) ta cirato mana daga Manzon Allah (S) a hadisi ingantacce wanda Imamu Muslim ya riwaito a cikin ingantacce kuma karbabben Littafinsa (Hadisi na 1977). Wannan shi kadai ya isa a wurin Ahlus Sunnah ba sai an tafi da nisa ba. To, amma sai suka sanya shakku game da Hadisin, wai Nana A'isha ta soke shi. Allah ya tsare ta da soke abinda ya tabbata daga Manzon Allah (S).


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

A Ganin - Dr. Kabir Asgar - A Ganina
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
A Ganin - Dr. Kabir Asgar - A Ganina

Kisan kai mummunan laifi ne, ba wai a musulunci kawai ba, har a cikin daukakin dokokin al'ummonin Dan Adam.

Akwai haqqin Allah, ga kuma haqqin wanda aka kashe din ga kuma na 'yan uwa da iyalansa da danginsa.

Shi ya sa shariar musulunci ta yi hani akan kisan kai ta ko wane hali. Kuma tai tanadi na hukunce-hukunce a kan kisan kai. Tun daga ramuwa, diyya da kuma kaffara gwargwadon yanayi.

A ganina, yadda mutane suka kutsa cikin batun kisan gilla da ake zargin wata mata mai suna Maryam Sanda ta yi wa mijinta kwanakin baya a Abuja ya saba wa qaidoji da yawa na rayuwa da addini.

Musulunci ya yi horo da kamewa daga zance maras amfani da yada labarai marasa dadi da kutse cikin al'amuran da ba su shafe ka ba da muguwar addua da sakin baki da ba da labarin dukkan abin da ka ji da yada hotuna barkatai da kuma mai da komai abin zolaya da tattaunawa da ire-iren su.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

HADARIN FATAWA {6} & HADARIN FATAWA {5}
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
HADARIN FATAWA {6} & HADARIN FATAWA {5}

SIFFOFIN MAI FATAWA

TAKATSANTSAN A CIKIN ABIN DA ZAI FADA KO RUBUTA:-

Harshe wani ingarman doki ne da ke ke da gudun tsiya, dole a sa masa linzami mai qarfi ta yadda in ya sukwana za a iya yi masa burki, musamman a wurin bada fatawa da amsa tambayoyin addini, ba ya kamata ga mai fatawa ya saki harshensa yai ta surutu ba tare da takatsantsan ba cikin mai yake fada, da lura da waye yake magana da su ba ko yake amsa musu tambayoyi ba m. Ya zama tilas ya zama mai zaben kalmomi da jumloli wadanda suka dace da amsar da zai bada, da mutanen da yake ba amsar, da wurin da ya ke bada amsa a cikin, da mas'alar da yake bada amsa a kanta. Kar zafin rai yai masa tasiri ko farin ciki, ko soyayya ko qiyayya. Kar ya maida halas haram, ko haram halas, ko wajibi mandubi, ko mandubi wajibi, ko haram makruhi, ko makruhi haram.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

**DUNIYAR MUTUWA**(5)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
**DUNIYAR MUTUWA**(5)

Da muka isa sama ta 2, nanma aka bude mana har muka isa ta 7, sai naga itace mafi girman sammai, sai naga tamkar rafi agabanmu, naga Mala'iku sun sunkuyas da kawunansu, suka ce: ''Allahumma innaka antas-salaam waminkas-salaam tabaarakta ya zhal-jalaali wal ikraam'' sai naji wani firgici, na qasqantar da kaina hawaye na zubomin, sai Allah yacewa Mala'ikun: ''Ku sanya littafin bawana cikin illiyin (shine rukunin da ake sanya littafan yan Aljannah -Allah ka sanya mu cikinsu-), kuma ku maisheshi zuwa qasa, domin daga gareta na haliccesu kuma cikinta zan maishesu kuma daga gareta zan tashesu wani lokaci na daban. Sabida tsananin Firgici, tsoro, da farin ciki da Murna, ban iya cewa komai ba sai: Tsarki ya tabbata gareka, bamu bauta maka ba yanda ya kamata!.

Sai mala'ikun nan suka sauko dani zuwa qasa, duk sanda muka hadu da mala'iku sai muyi masu sallama, sai nacewa Mala'ikun: shin zai yiwu nasan abinda ya faru da gangan jikina da iyalaina?

Sai sukace: jikinka dai zaka ganshi, amma iyalanka ayyukansune kawai da zasu dinga maka kyautarsu zasu dinga riskarka, amma bazaka gansu ba! Suka dawo dani qasa, suka ajeni kusa da jiki na, sukace: ka kasance a jikinka, mu aikinmu ya qare anan, bayan an sanyaka a qabarinka, wasu Mala'ikun 2 zasu zo maka! Sai nace dasu: Allah maku Albarka, ya saka maku da Alkhairi! To amma zan sake ganinku kuma? Sai sukace: A ranar Qiyaamah zamu tsayu gaba daya, wannan shine ranar halatta (domin dukkan mutane, Aljanu da mala'iku zasu halacce ta), sai naga sanda suka ambaci qiyamah sautinsu ya chanza, sannan sukace: Amma in ka kasance cikin yan Aljannah, zamu zamo tare ku zaka gammu.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

HADARIN FATAWA {4} & HADARIN FATAWA {3}
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
HADARIN FATAWA {4} & HADARIN FATAWA {3}

SANIN HALIN MUTANE DA AL'ADUNSU:-

Wannan wata sifface mai matuqar mahimmanci ga mai fatawa, ya san halin mutanen da yake rayuwa a cikinsu da sassabawar ta'adojinsu, da yanayinsa, domin sune za su riqa yi masa tambayoyi shi kuma ya riqa basu amsa wadda ita ce ''fatawa''.
Wani lokaci ana iyama malami mai fatawa tambayoyi biyu iri daya amma amsoshinsu su banbanta domin sanin halayen mutane da su kai wadannan tambayoyi masu kama daya amma da mabanbantan amsoshi.

DOGARO DA KAI A RAYUWA

Tabbas ana buqatar mai bada fatawa ya zamo mai dogaro da kansa don kar ya zama karen farautar wani, ko makamin wani, ko mai gadin wani, domin in hannu ya amsa, baki kuma ya ci, to dole ido ya ji kunya. Shi yasa wata rana aka ga Babban Malami Sufyan al-thauriy a kasuwa yana qirga kudinsa bayan ya gama cin kasuwa, sai aka ce masa: Har da ku malam!? Sai ya ce: ai badan wadannan ba {kudi} da 'yan duniya sun maida mu {malami} tsimman share majina. Sannan. Babban Malami Ibnul – uthaimen ya kasa malamai zuwa gida uku:-

1- Malaman talakawa, masu son talakawan gari su yarda da dasu, su so su.
2- Malaman hukuma, masu son shuwagabanni su yarda da su, su riqa basu kudi.
3- Malamai na addini na Allah, wadanda suka tsayu da kansu akan gaskiya, Allah kawai suke buqatar ya yarda da su. Allah ka samu a cikinsu.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

HADARIN FATAWA {2} & 001 KADDARA TA RIGA FATA -Shimfida
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
HADARIN FATAWA {2} & 001 KADDARA TA RIGA FATA -Shimfida

Fatawa ta kasance aba mai hadari ne saboda wadannan sababai kamar haka:-
Mai fatawa yana wakiltar Allah {Ta'ala} ne ko Manzonsa {S.A.W} a wajen yin hukunci game da addini.
Fatawa akwai halastawa ko haramtawa a ciki.
Fatawa na bada amsar abin da in akwai; za a shiga aljanna ko wuta ne a ranar gobe qiyama.
Fatawa na bada amsa a game da abin da ya shafi rayuwa ne duka, kamar Aqeedah, da Ibadah, da Mu'amalah.
Fatawa na zama sanadiyyar qarewar aure, ko cigabansa.
Fatawa na zama sanadiyyar mallaka wani haqqi zuwa ga wani, kamar a rabon gado, da ciniki, da kyauta, da bashi, da sauransu.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

002 KADDARA TA RIGA FATA -Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya Samu Sauki
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
002 KADDARA TA RIGA FATA -Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya Samu Sauki

Ana haka ne sai kwatsam Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya samu sauki har ya umurci iyalinsa su kai masa ruwa ya yi wanka. Samun wannan kuzari da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi sai ya fita Masallaci har ma ya samu sukunin yin huduba wadda a cikinta ya yi addu'a ga wadanda su kayi shahada a yakin Uhudu, ya tsawaita addu'a gare su.

Sannan ya ce ma mutane,''ku sani Allah ya bai wa wani bawansa za6i a tsakanin rayuwar duniya da koma ma Allah, amma wannan bawan ya zabi abin da ke wurin Allah''. Mafi yawan Sahabbai ba su gane in da maganar ta nufa ba sai da suka ga Abubakar yana kuka, yana cewa, a'a Manzon Allah! Mun fanshe ka da iyayenmu da ubanninmu!!

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi umurni a cikin hudubarsa da a tabbatar da ganin rundunar da ya tura don ta yaki Rumawa a karkashin jagorancin Usamatu Dan Zaidu ta tafi.

Ya bayyana ma jama'a cewa, ya ji maganganun da ake yi game da kuruciyar Usamatu. Ya ce, to, ai babansa ma haka ku ka ce masa.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

**DUNIYAR MUTUWA**(4)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
**DUNIYAR MUTUWA**(4)

Dukanmu sai Hankalinmu ya karkata ga wasu Malaa'iku da mukaga sunzo sun wucemu da sauri, dauke da wata Ruhi mai tsananin Qamshi, inda na shaqi qamshin miskinda ban taba shaaqar tamkarsaba a rayuwata, nacewa Malaa'iku: Wanene wannan? Nidai banda nasan cewa Annabi Muhammad s.a.w shine qarshen Annabaawa, da nace wannan Ruhin Annabi ne! Sabida Rakiyar Malaa'iku da na gani sun mata, da Qamshinta gamida yanda suke riqe da ita cikin Girmamawa da Karramaawa!

Sai suka ce: wannan Ruhin shahidi ne da yayi shahaada a Palastine, dazunnan Yahudawa suka kasheshi, yana mai kaariya ga Addininsa da Garinsa, Haqiqa Allah ya sa yanada yawan Ibaadah gashi Mujaahidi!

Sai nace: kaicona ma ace nayi mutuwar Shahaadah ne!
Ba'a jimaba sai naga wasu Malaa'ikun dauke da wata ruhi abar qyama, wani wari mai doyi na tashi daga gareta! Sai nace waye wannan?

Sai sukace: Wannan Mutumin Handusa ne, yana daga cikin Masu bautar shaanu, ya mutu ba da jimawa ba bisa tsawa da Allah ya turo masu, sai na gode Allah bisa ni'imar Musulunci.

Sai nace masu: wlh duk yanda na karanta wadannan abubuwa, banyi zatonsu haka ba, sai malaa'ikun sukace: Bushaararka da Alkhairi, amma ka sani Al'amarindake gabanka mai tsayi ne


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

**DUNIYAR MUTUWA**(3)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
**DUNIYAR MUTUWA**(3)

Chan sai ga wani mutum ya zomin, cikin tsananin duhu da nake gani, yazo min da Gemuna fari Fat, Ya ce dani: Yaa kai Daana, wannan itace qarshen rayuwarka, kuma nazo maka ne ina mai maka nasiha kafin ka hadu da Uban-gijinka, Haqiqa na sanka, kai mutum ne mai hazaaqa, kana son Alkhairi, don haka da sannu zan maka wasiyya da wata wasiyya, domin Allah ne ya aikoni wajenka.

Sai nace: Menene kake so?

Sai yace: Kace: ''Na yi Imaani da Cross'', domin na rantse da Allah shine kubutarka, idan kai Imaani dashi zan maisheeka ga iyaalanka da yaaranka, sannan in mayas maka da ranka, ka fadi haka da sauri, bamuda lokacin tsaiko!.
Na san wannan shine Shaidan, dukda irin radadinda nake fama dashi na fitar raina, ban gushe da Yarda ga Ubangijina ba da Annabina s.a.w.
Nace masa: Maza juya kabani waje ya maqiyin Allah, haqiqa na rayuwa musulmi, kuma da izinin Allah zan mutu akan haka.

Sai Fuskarsa ta chanza yace: Ka saurareni, bazaka kubuta ba a yanzu, face ka mutu banasare ko bayahude, in kuwa kaqi, zan qaara maka radadi kuma in dauki ranka.

Nace: Rayuwa da Mutuwa duk suna hannun Allah ne, ba a hannunka ba, ni bazan mutuba sai akan Musulunci, sai fuskarsa ta yamutse, shaidaanin yace: idan ka fitineni (kaqi bin umarnina) to Daruruwanka bazasu iya ba! Kuma ya isheni tunda na iya sanyaka kana saabawa Allah da yawa, kuma kana keta iyakokinsa.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

**DUNIYAR MUTUWA**(02)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
**DUNIYAR MUTUWA**(02)

Bayan gama wayata da mataata, tunani ya tarun-min a raina, damuwata ta dinga qaruwa, na shiga zurfin tunani, ban Farka ba sai ji nayi Direba na Tambayata: Wai shin Yaranka nawa ne? Nace: 4, 2 maza 2 mata. Yace: Allah ya shiryar maka dasu! Nace: Amin, kaima haka.

Na kalli hanya, sannan na kalli sama ina kallonta, na kalli rana, sai naga kadan ya rage ta faadi, na fadi ina mai qura kallo: Ya Allah, Rahmarka nake kwadayi yaa Rahmaan yaa Raheem! Ban Aune ba naji direba na neman izinina wai yanaso ya kunna sigaari, sai nace: Ya kai dan'uwana, kai mutum ne me daraja, kuma ina tsammanin tattare dakai akwai Alkhairi mai girma, ya zaka yardarwa kanka ka qona kanka? Ka qona kudinka? Kuma ka tauye Addininka a dalilin Sigaari? Kuma a qarshe bata amfaanarka sai dai cutar dakai???
Sai yace: Yaa kai dan Halal, kamin Addu'a, wallahi nayi qoqarin barin shanta cikin Ramadan da ya gabata amma na kasa.

Sai nace dashi: kai mutum ne da Allah ya bashi iko amma ka kasa akan sigari??!! Naci gaba da masa nasiha da shiryar dashi, shi kuwa yana saurarena, yana mai nadamar shan sigaari da yakeyi, bayan kammalawata sai yace: Inshaa Allah daga yau bazan sake shan sigaari ba! Nace masa ina mai farin ciki: Allah ya Tabbatar damu akan Addini!


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

**DUNIYAR MUTUWA**(01)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
**DUNIYAR MUTUWA**(01)

A daya daga cikin tadfiye tafiye na zuwa Birnin Riyaad, nai shirin zuwa filin jirgin sama kafin lokacin tashin Jirgin da Awa 1, sai dai cunkoson hanyar, da kuma Bincike yasa na makara a tafiyata, sai na dinga sauri har na isa wajen tsayuwar motoci, sai na dauki Kaati na (Visa) da sauri, nai Parking motata a wurinda ni bansan shin wurin Parking din ma'aikata ne ko na matafiya, ni dai na sauko da sauri daga mota na dauki Jakaata a hannuna, na shiga abin tafiya (Escalator) na isa dakin bincike, na cire duk abindake aljihuna na riqe a hannu, na danna na'urar bude qofa, amma sai naji sanarwar cewa wai a jikina akwai wani abu da bazan iya wucewa dashi ba, sai na shiga damuwa, chan sai na tuna Agogona ne ai, sai na cire, na sake danna na'urar, sai ta bude na wuce lafiya.

Na isa wajen mai bada Tikitin Jirgi da sauri, nace: Ni matafiyi ne zuwa Riyaad, cikin jirgi mai lamba 1411, sai ma'aikacin yace: Ai Jirgin ya cika, sai nace dashi: Don Allah ka taimakamin, inada Alqawarine wanda ba makawa in halarceshi a wannan Dare.

Sai yace: Kada ka yawaita magana, don Jirgi ya riga ya cika, kuma babu wanda zai daga maka qafa, sai nace: Hasbiyallah!!!!


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

YIN TABLIGI BAYAN LIMAN BA TARE DA BUKATA TA SHARI'A BA BIDI'A CE:YIN
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
By Dr. Ibrahim jalo jalingo

YIN TABLIGI BAYAN LIMAN BA TARE DA BUKATA TA SHARI'A BA BIDI'A CE:YIN TABLIGI BAYAN LIMAN BA TARE DA BUKATA TA SHARI'A BA BIDI'A CE

Babu sabani a tasakanin Malamai cewa yin tabligi a bayan liman ba tare da wata bukata ta Shari'ah ba bidi'ah ce a bar kyama.

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 23/403 ((واما التبليغ خلف الامام لغير حاجة فهو بدعة غير مستحبة باتفاق الايمة، وانما يجهر بالتكبير الامام كما كان النبي صلى الله عليه وسلم وخلفاوه يفعلون، ولم يكن احد يبلغ خلف النبي صلى الله عليه وسلم لكن لما مرض النبي صلى الله عليه وسلم ضعف صوته فكان ابو بكر رضي الله عنه يسمع بالتكبير. وقد اختلف العلماء: هل تبطل صلاة المبلغ؟ على قولين في مذهب مالك واحمد وغيرهما)). 
Ma'ana: ((Amma Tabligi bayan liman ba tare da wata bukata ba hakan bidi'ah ce ba mustahabbah ba a bisa ittifakin Shugabanni. Abin da aka sani Liman ne zai rika bayyanar da kabbara kamar yadda Annabi mai tsira da amincin Allah da Khalifofinsa suka kasance suna yi. Babu koda mutum guda da ya kasance yana yin tabligi a bayan Annabi mai tsira da amincin Allah, sai dai a lokacin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi rashin lafiya sautinsa ya yi rauni Abubakar Allah Ya kara masa yarda ya kasance yana jiyar da kabbararsa. Hakika Malamai sun yi sabani game da cewa: Ko sallar mai yin tabligi tana baci? A bisa zantuka biyu cikin mazhabar Malik da Ahmad da wasunsu)).

Saboda abin da muka ji yanzu yana kyau al'ummarmu su sanya girmama sunnar Manzon Allah cikin dukkan ayyukansu na ibadah, su daure su daina yin tabligi a lokacin da mamu ke jin kabbarorin limaminsu, wannan ita ce Sunnah ta Annabi mai tsira da amincin Allah da babu sabani a cikinka adai gurin Malamai ba murakkaban jahilai ba.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB NE SHI KO KUWA WANINSA: (I)

1. Ya kamata a san cewa aqidar Ahlus Sunnah wal Jama'ah ita ce: Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib -Allah Ya kara masa yarda- Sahabi ne babba mai yawan daraja. A kuma san cewa abin da ake nufi da Sahabi shi ne: wanda ya samu haduwa da Annabi mai tsira da amincin Allah alhalin yana mumini kuma ya mutu yana mai imani. A kuma san cewa abin da ake nufi da munafuki shi ne: mutumin da ya bayyanar da Musulunci da nuna biyayya ga manzon Allah mai tsira da amincin Allah amma kuma yake boye kafurci cikin zuciyarsa.

A kuma san cewa yana daga cikin aqidar Ahlus Sunnah wal Jama'ah nuna kauna da soyayya ga dukkan sahabban manzon Allah mai tsira da amincin Allah; saboda su ne suka fi kowa cikar imani da ihsani, suka fi kowa yawan da'ah da jihadi, Allah kuma Ya zabe su da abokantakar annabinSa mai tsira da amincin Allah, babu kuma wani da zai zo daga bayansu da darajarsa za ta kai tasu. A kuma san cewa su Sahabbai dukkansu adilai ne; saboda irin yadda Allah da manzonSa suka bayyanar da adalcinsu, kuma su waliyyan Allah ne zababbu cikin halittarSa, kuma su ne suka fi kowa daraja cikin wannan Al'ummah, babu wani da ya fi su daraja in banda manzon Allah mai tsira da amincin Allah; daga cikin abin da ke tabbatar da wannan magana tamu shi ne fadar Allah Madaukaki cikin suratut Tauba aya ta 100 inda Ya ce:

((Na farko wadanda suka tsere wa kowa daga cikin Muhajirai, da Ansarawa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautayi, Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi, kuma Ya yi musu tattalin gidajen Aljannah da korumma ke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har a bada, wannan kuwa shi ne rabo mai girma))


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

MUTUMIN DA KE DA MATA 4 SANNAN YA YI WA DAYANSU YANKAKKEN SAKI KO ZAI HALATTA YA
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

MUTUMIN DA KE DA MATA 4 SANNAN YA YI WA DAYANSU YANKAKKEN SAKI KO ZAI HALATTA YA AURI WATA MATAR KAFIN IDDAR WANNAN TA CIKA?

1. Babu sabani tsakanin Malamai cewa: ba ya halatta ga namiji ya hada Ya da Kanwa karkashin aurensa a lokaci guda. Haka nan ba ya halatta gare shi ya daura wa mace ta biyar aure koda kuwa akwai wacce ya saka saki na kome matukar dai ba ta gama iddarta ba. Wannan mas'ala babu sabani a cikinta tsakanin Malaman Sunnah; saboda dalilai da yawa daga cikinsu akwai: Fadar Allah cikin surar Nisaa'i aya ta 23 ((Kuma kada ku hada tsakanin Ya da Kanwa saifa abin da ya riga ya wuce)). Da kuma wasu hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah, daga cikinsu akwai hadithi na 2243 da Imam Abu Dawud ya ruwaito, da hadithi na 1952 da Imam Ibnu Majah ya rueaito, da hadithi na 4631 da Imam Ahmad ya ruwaito, da hadithi na 4156 da Imam Ibnu Hibban ya ruwaito dukkansu da isnadi sahihi cewa Sahabi Wahb Al-Asadiy ya musulunta alhalin yana da mata 8 sai Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce da shi ya zabi 4 kawai daga cikinsu. Haka nan ya faru da sahabi Gailan Bin Salamah, haka nan ya faru da sahabi Qais Bin Al-Harith.

2. Amma su Malaman Sunnah sun yi sabani game da idan mai mata 4 ya saki guda a cikinsu saki yankakke watau: saki na 3 ko kuwa sakin Khul'i, ko yana da damar ya daura wa wata matar aure kafin iddar wannan da ya saken ta kare? Akwai mazhabobi biyu na Malamai cikin wannan mas'ala:-


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

MATAKAN SAMUN ALBARKAN ILIMI DUNIYA DA LAHIRA
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
MATAKAN SAMUN ALBARKAN ILIMI DUNIYA DA LAHIRA

Asshaykh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntun Hafizahullah a wata muhadara daya gabatar mai taken 'ILIMI DA TASIRINSA' ya baiwa daliban ilimi wadanda suke fatan iliminsu yayi albarka suci moriyarsa duniya da lahira shawara da matakan daya kamata abi domin dacewa da abinda ake fata, matakan kuwa sune abu na farko ya zama.

1-MANUFAR NEMAN ILIMIN YA ZAMA DON ALLAH:-

wannan shine abu na farko da dukkan daliban ilimi ya kamata su kudurta ya zamana cewa manufar neman ilimin tazama don neman yardan Allah ne, kada ya zamana cewa kana neman ilimine don kayi kafada da kafada da malamai ko kuma don al'umma ta yabeka da cewa kai mai ilimine, ko kuma domin samun wani abu na duniya, idan har wannan ya zama shine manufarka tabbas iliminka zai zamanto sanadiyar halakarka a ranar alkiyama koda kuwa kasamu dan jin dadi anan duniya.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

SHIN KA TABA ZUBDA HAWAYE SABODA TSORON ALLAH?
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
SHIN KA TABA ZUBDA HAWAYE SABODA TSORON ALLAH?

Zubar da hawaye saboda tsantsar tsoron Allah yana daga cikin halayen bayin ALLAH na kwarai. Musamman Annabawa, Sahabbai, da waliyyan Allah.

Acikin Mutanen da zasu shiga Inuwar al'arshi aranar da babu wata inuwa sai ita, Manzon Allah (saww) ya Qirga har da mutumin da ya tuna Allah shi kadai aboye, har idanunsa suka zubda hawaye.

Annabi Dawud (as) ya kasance mutum ne mai yawan zikirin Allah. Har ma Ubangiji ya hore masa duwatsu da Tsuntsaye suna yin Tasbeehi tare dashi.

Manzon Allah (saww) yace:

''MUTANE SUN KASANCE SUNA ZUWA SUNA GAISAR DA ANNABI DAWUD, SUNA ZATON KAMAR BASHI DA LAFIYA NE.. AMMA BABU KOMAI GARESHI IN BANDA TSORON ALLAH''.

Wato wannan ya faru ne saboda ramewa da kuma bayyanar alamomin jinya agareshi. amma ba jinya bace.. Tsoron Allah ne yayi ka-ka-gida azuciyarsa.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

NURULHUDA KUSAKURAN DA SUKA YADU A BAKUNAN MUTANE
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
FADAKARRAWA GA MUSULMAI

NURULHUDA KUSAKURAN DA SUKA YADU A BAKUNAN MUTANE 1

Cewa: AN HALICCI DUNIYANE DOMIN MANZON ALLAH ‏ Wannan kuskure ne ya sabawa nassin Alqur'ani..

Allah ya halicci duniya tun kafin ya halicci manxon ‏Allah.. kuma ya halicci manzon Allah ﷺ da duniya domin Bautarsa ne kawai.

Allah yace cikin suratul kahfi:

''Kace ni ban kasance ba face mutum kamar ku, ana wahayi gareni cewa lallai Allahnku Allah dayane, duk wanda yake burin haduwa da Ubangijinsa. Toh ya aikata aiki NA gari. Kuma kada ya hada bautar ubangijinsa da kowa ''.

Wannan ayar ta nuna mana..

Annabi mutum ne kamar kowa..

Banbancin mu dashi kawai shine shi Anai masa wahayi.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH FATAWOYIN LAYYA2
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH FATAWOYIN LAYYA2

SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

A wannan darasi za mu amsa tambayoyi kamar haka; *Tambaya:

Mene ne sharuddan layya?

AMSA:

Yana daga cikin sharuddan layya:

abin da za a yanka, lallai ya kasance daga cikin ''bahimatul anʿām'' (dabbobin ni'ima), irin su:

rakuma da shanu da awaki da tumaki). Domin haka, ba ya cikin sharuddan layya, a yi ta da namun daji, kuma ba za a yanka kaji da sauran tsuntsaye ba, kamar yadda wasu daga cikin 'yan Zahiriyyah suka tafi a kai.

Dalili kuwa fadin Ubangiji subhanahu wa ta'ala cewa:


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH MECE CE ALAMAR SON MANZON ALLAH (S.
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH MECE CE ALAMAR SON MANZON ALLAH (S.A.W)?

Amsa:

Kafin mu amsa wannan tambayar ya na da kyau muyi wa kanmu wadannan tambayoyin:

-Mece ce soyayya?

-Mene ne yake sa a so mutum?

-Mene ne rabe- raben so?

-Mece ce alamar so?

Daga nan kuma sai musan mece ce hakikanin soyayyar Manzon Allah (S.A.W)?

Mece ce soyayya?

Hafiz Ibin hajar babban malamin hadisin nan da yayi sharhin sahihul bukhari yace:


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH YAUSHE NE YA FI DACEWA A YI SAHUR?
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH YAUSHE NE YA FI DACEWA A YI SAHUR?

Alhamdu lillahi rabbil A'lamin, Wa sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammad wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Amma ba'ad; Lallai wanda yake son Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama zai fifita shi akan duk abin da yake da girma ko daraja ko tsada a gunsa.

Domin son Allah da manzonsa sune imani, kuma imanin bawa bazai cika ba sai da su. Allah subhanahu wa ta'ala yace:

'' kace idan har iyayenku da 'ya'yanku da 'yan uwanku da matanku da danginku da dukiyar da kuka tsuwurwurta da kasuwancin da kuke jin tsoron tasgaronsa da gidaje da kuke yarda dasu sune suka fi soyuwa a gareku daga Allah da Manzonsa da jihadi saboda Allah ;to ku zauna har Allah ya zo da al'amarinsa, allah baya shiryar da fasikai'' {Tauba :24} Wannan ayar nassi ce karara a bisa wajibcin kaunar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama,da wajibcin gabatar da wannan kaunar akan duk wani abin kauna.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH IDAN MUTUM YANA CIKIN YIN SAHUR, SA
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH IDAN MUTUM YANA CIKIN YIN SAHUR, SAI YA JI KIRAN SALLAH YAYA ZAI YI?

SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

AMSA:

A irin wannan hali mutum zai qarasa abin da ke hannunsa ne.

Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira radhiyallahu anhu ya ce:

Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce:

Ma'ana:

Idan dayanku ya ji kiran sallah alhali qwarya tana hannunsa, kada ya ajiye ta, har sai ya biya buqatarsa .


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: