Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

EsinIslam Media: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Search on This Topic:   
[ Go to Home | Select a New Topic ]

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Illolin zina da luwadi da madigo (1)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Illolin zina da luwadi da madigo (1)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin Manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam) tare da alayensa da sahabbansa. Bayan haka, wannan tsokaci ne a kan ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncin kowanensu a karkashin shari'ar Musulunci da Dokta Muhammad Rabi'u Umar Rijiyar Lemo ya rubuto kuma muka ga ya dace a sanya a wannan fili don amfanin jama'a. Ina rokon Allah Ya sa abin ya yi tasiri a kan kowane Musulmi. Bismillah!

Ma'anar zina da hukuncinta:

Lafazin zina a shari'ance yana nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure, ko an mallake ta a matsayin baiwa ba. Sai dai akan yi amfani da lafazin zina a kan abin da bai kai saduwa ba, kamar yadda ya zo a Hadisin Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ) ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "An rubuta wa dan Adam rabonsa na zina, babu makawa sai ya same shi, zinar idanu ita ce gani, zinar kunnuwa ita ce ji, zinar harshe ita ce magana, zinar hannu ita ce damka, zinar kafa ita ce taku, zuciya kuwa tana kwadayi tana fata, farji kuma shi yake gaskata haka ko ya karyata." Muslim.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Layya da hukunce-hukuncenta
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Layya da hukunce-hukuncenta

Abin da ake cewa Layya shi ne duk wani abu da aka yanka domin neman kusanci ga Allah. Layya na da asali a cikin Alkur'ani da Hadisin Annabi (SAW). Allah (TWT) Yana cewa: "Ka yi Sallah ga Ubangijinka kuma ka yi yanka." (Kausar: 2) A Hadisi kuwa Anas Bin Malik (RA) ya ruwaito cewa: "Manzon Allah (SAW) ya yi Layya da raguna biyu bakake, masu kahonni. Ya yanka su da hannunsa, ya yi bisimillah ya yi kabbara, ya kwantar da su ta gefensu." (Muslim).

A shekara ta biyu Bayan Hijira aka shar'anta yin Layya kuma sunnah ce mai karfi a kan:

1. Musulmi da, namiji ko mace. Tana zama sunnah a kan mutum ga kansa da iyayensa, idan talakawa ne, da 'ya'yansa maza da ba su balaga ba ko mata da ba su yi aure ba. Ba sunnah ba ce mutum ya yanka wa matarsa ko dansa da aka haifa a ranar Layyar.

2. Kada ya kasance mahajjaci, domin shi mahajjaci, hadaya ce a kansa.

3. Ya zama ba matalauci ne ba, da ke cikin tsananin bukata. Amma zai iya cin bashi ya yi Layyar, idan ya san zai iya biya, ba tare da takura ba. Wasu malamai sun ce kada mutum ya ci ba shi domin yin Layya.

Dabbobin da ake yin Layya su ne: Rago wanda ya shekara, taure sai ya shiga shekara ta biyu. Sa, wanda ya shekara uku, rakumi sai ya kai shekara biyar. A wajen Layya, rago ya fi falala, sai taure, sai sa, sai rakumi. A cikin dukkan dabbobin an fi fifita maza a kan matansu da lafiyayyunsu (wadanda suke yin barbara) a kan fidiyayyuns, sai idan fidiyayyun sun fi kitse sai a yi da su.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Ya da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne (SAW). Allah Ya dada tsira da aminci ga ManzonSa da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa Ranar karshe.

Bayan haka, yau 6 ga watan Sha'aban, shekara ta 1437 Bayan Hijira, mukalarmu za ta yi tsokaci ne kan kwadaitarwa game da yin azumi a cikin wannan wata, kamar dai yadda kanunta ya nuna.

Shi watan Sha'aban, kamar yadda ya kamata kowane Musulmi ya sani, shi ne wata na takwas a cikin jerin watanni 12 na shekara, wata ne da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya kasance ya fi yawaita yin azumin tadawwu'i a cikinsa.

A cikin littafin Sahihu Fikhus Sunnah Wa Adillatihi… na Abu Malik Kamal bn Assayyid Salim, an gabatar da bayani a karkashin kanun "Azumin Tadawwu'i," wanda ya kamantu da yadda dan uwa mai daraja, Usamatu Abdul'aziz (Allah Ya ba shi lada), ya yi a littafinsa "Azumin Tadawwu'i: Falala da Hukunce-hukunce."

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah, Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni zuwa ga samun alheran duniya da Lahira; (Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsa cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta, amin.

Bayan haka, mun kwana a wannan mukala bayan gabatar da amsar tambayar da aka yi wa marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam a kan haka, to yau, in Allah Ya so, za mu ga amsar shehunan malamai biyu kamarhaka:

Yayin da ya amsa tambayar mene ne hukuncin daga hannaye da addu'a bayan Sallah, a cikin littafinsa Fatawal Akidah wa Ma'aha Fatawas Siyam wal Hajji waz Zakkah was Salah, Sheikh Muhammad bn Salihul Usaimin ya ce:

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, mun kwana a karshen bayanin manuniya kan cewa kofar tuba a bude take, yau, saboda mu samu armashin kawo karashen mukalar, za mu gabatar da ita ne daga farkon maganar tuba, kamar haka:
kofar Tuba A Bude Take

Wani ko wata zai ko za ta iya tunanin cewa, "Yanzu na ji wa'azi, to yaya zan yi in tuba in daina, kuma shin ma Allah zai karbi tuban nawa, bayan dukkan wadannan abubuwa da na aikata?" Sai mu ce:

Babu wani zunubi a bayan kasa da Allah ba Ya gafarta shi, matukar dai mai yin sa ya tuba, tuba ingantacciya, saboda Allah Yana cewa, "Ka ce, ya ku bayiNa wadanda suka yi wa kansu barna kada ku debe kauna ga rahamar Allah, hakika Allah Yana gafarta zunubai gaba daya, lallai shi Allah, Mai gafara ne, Mai jinkai". (Surar Azzumar, aya ta 53). Sannan Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Allah Ya sanya wata kofa a wajen mafadar rana, fadinta tafiyar shekara saba'in ce, saboda tuba, ba kuma za a rufe wannan kofar ba, matukar dai rana ba ta bullo daga inda kofar take ba". Tirmizi ne ya rawaito wannan hadisi.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, mun karanci bayanai kan ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu, to yau ga ci gaba daga manuniya ne kan:

Hanyoyin Kare Kai Daga Zina Da Luwadi Da Madigo

Saboda hikimar Ubangiji da rahamarSa, duk abin da Ya haramta wa bayi, to za a bude wata kofar da mutum zai biya bukatarsa ba tare da ya afka wa wancan abin da Allah Ya hana din ba. Wannan abu haka yake a nan ma, domin dai mun ji irin tarin illolin da suke tattare da yin zina da luwadi da madigo, to amma babu yadda namiji ko mace za su rayu ba tare da sun sami inda za su zubar da sha'awarsu idan ta taso ba, saboda haka sai Musulunci ya halatta wadannan abubuwa masu zuwa don kauce wa afkawa cikin zina:

1. AURE: Allah Madaukakin Sarki Ya halatta wa maza su auri mata, inda yake cewa: "To ku auri abin da kuke so na mata, bibbiyu (ko) uku-uku (ko) hurhudu. Idan kuwa kuna tsoron ba za ku iya adalci ba, to ku auri daya, ko kuma abin da damarku ta mallaka. Wannan shi ne abin da zai sa ba za ku karkace ba." (Annisa'i: 3).

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, mun kwana a karshen illa ta 5 daga cikin illolin luwadi, yau ga ci gaba daga illa ta:

6. Luwadi yana haifar da munanan cututtuka, irin su rashin rike bayan gida, kuraje, sanya zuciya ta yi baki wuluk, bacewar basira da kyakkyawan tunani, rashin kunya da sauransu.

7. Luwadi yana kawo kaskanci da wulakanci da tozarta, a duniya da Lahira.

8. Saduwa da mace ta dubura mummunan abu ne, wanda Ibnul kayyim – Allah Ya yi masa rahama – yake cewa, "Ba a taba halatta saduwa da mace ta dubura a harshen wani Annabi da Allah Ya aiko ba."

9. Mai luwadi bai kai darajar dabbobi ba, saboda dabba ma ba ta haka.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu maibatar da shi, wanda kuma Allah Yabatar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta wa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne (SAW).

Allah Ya dada tsira da aminci ga ManzonSa da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa Ranar karshe.

Bayan haka, mun kwana bayan mun gabatar da nau'in azumi na hudu da aka yi hanin yin sa, a karkashin kanun ‘Kwanakin da aka haka azumi a cikinsu', yau ga ci gaba daga:

5. Azumin Shekara (Daharu -Tutur): An samo daga Abdullah Ibn Amr (Allah Ya yarda da shi), cewa yayin da labari ya iske Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), cewa Abdullahi yana azumi tutur, sai ya ce, "Babu azumi ga wanda yake azumi tutur; babu azumi ga wanda yake azumi tutur; babu azumi ga wanda yake azumi tutur." Sahihin Hadisi ne na Buhari, Hadisi na 1,977 da Muslim, Hadisi na 1,159.

Haka nan a Hadisin Abu kattadah, inda Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce, "Ya Ma'aikin Allah, me kake gani ga wanda ya azumci shekara gaba daya?' Sai ya ce, "Bai yi azumi ba, kuma bai sha ruwa (bai ci abinci) ba." Sahihin Hadisi ne na Muslim, a Hadisi na 1,162.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Menene Hunkunci Azumtar Watan Rajab??
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Menene Hunkunci Azumtar Watan Rajab??

Amsa: Babu wani hadisin da ya tabbata daga bakin Manzon Allah ko aikinsa wanda ya nuna cewa Manzon Allah (saw) ya lazimci azumin watan Rajab tun daga farkonsa har qarshensa. Kuma ba a samu wani daga cikin sahabbai ko tabi'ai ko tabi'uttabi'ina ko kuma wadanda suka biyo bayansu daga cikin magabata na qwarai da suka lazimci yin wannan ba. Kai bari ma, abin da ya zo a hadisin da ya tabbata shi ne cewa Manzon Allah ya lazimci yin azumi mai yawa ne a cikin watan Sha'aban, amma ba a cikin watan Rajab ba. Saboda haka duk wanda yake son bin ingantacciyar sunnar manzon Allah (saw) sai ya lazimci yin azumi mai yawa a cikin watan Sha'aban, kamar yadda manzon Allah (saw) ya lazimce shi.

Sai dai akwai hadisai masu yawa da aka qago su kuma aka jingina su ga manzon Allah (saw) musamman a kan azumtar watan Rajab baki dayansa, da yin salloli a cikin dararensa baki daya, da kuma yin wadansu zikirai daban dabam da bikin daren Isra'i da Mi'iraji wadanda dukkaninsu ba su tabbata daga manzon Allah (saw) Kuma akwai qage-qagen ma da aka qara a kan wadancan hadisan, wandanda ake yinsu a wadansu wuraren, kamar abin da ake kira AZUMIN TSOFAFFI. Shi ma bai tabbata ba a cikin Al-qur'ani ko hadisin manzon Allah (saw) ko kuma aikin magabata na qwarai. Kai qarewa ma, lafazin ma babu shi a cikin rubutun arabiyya, a gan shi a rubuce cewa AZUMIN TSOFAFFI, ko da na qarya ne.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

044 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 44
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

044 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 44

✺✺FASALI NA GOMA (10)✺✺
.
Malam Ya cigaba da Bayani akan Hukunce-Hukuncen da suke kiyayewa Mace Martabarta, kuma suke tsare mutuncinta.
.
4● Daga cikin matakan da suke sawa a tsare farji hana kad'aituwa tsakanin mace da namijin daba Muharraminta ba.
.
● Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: ''Wanda ya kasance yana imani da ALLAH da ranar Lahira to kada ya kuskura ya kad'aita da mace ba tare da muharraminta na tare da ita ba, domin na ukunsu shine shaid'an.''
.
● Amir Ibn Rabi'ah Yace: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: ''Kada wani namiji ya kad'aita da macen da bata halatta gare shi ba, domin shaid'an shine na ukunsu, sai dai muharrami.''
.
Al-Majid ya fad'a acikin Al-Muntaqa cewa: Imam Ahmad ne ya ruwaito wad'annan hadisan, kuma an ruwaito ma'anarsu daga hadisin Ibn Abbas acikin Bukhari da Muslim.
.
→ Imam Al-shaukani Yace: ''Kad'aituwa da mace ajnabiya ga mutum (wato matar da ba muharrama ba ga namiji) abu ne da malamai suka gamu akan haramcinsa, kamar Yadda Al-hafiz ya fad'a acikin Fat'h.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

043 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 43
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

043 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 43

✺✺FASALI NA GOMA (10)✺✺
.
Malam Ya cigaba da Bayani akan Hukunce-Hukuncen da suke kiyayewa Mace Martabarta, kuma suke tsare mutuncinta.
.
3● Har wa yau yana daga cikin matakan taimakawa ga tsare farji, hana mace tayi tafiya in bada muharrami ba, wanda zai tsare ta, ya kareta daga kwad'aice-kwad'aicen­ lalatattu da fasiqai, ingantattun hadisai sunzo wad'anda suke hana mace tayi tafiya ba tare da muharrami ba, daga ciki akwai:
.
● Hadisin Abdullahi Ibn Umar (RA) Yace: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: ''kada Mace tayi tafiyar kwana uku sai da muharrami tare da ita.''
.
[Bukhari da Muslim suka ruwaito]
.
● Kuma Abu Sa'idul khudriy (RA) Yace: Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya hana mace tayi tafiyar kwana biyu ba tare da mubarraminta tare da ita ba.''
.
[Bukhari da Muslim suka ruwaito shi]
.
● Daga Abu-hurairah (RA) Yace: Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: ''Bai halatta ba ga mace tayi tafiyar kwana d'aya da wuni d'aya ba, sai tare da muharrami agare ta.''
.
[Bukhari da Muslim suka ruwaito]

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

042 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 42
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

T042 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 42

✺✺FASALI NA GOMA (10)✺✺
.
BAYANIN HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKE KIYAYEWA MACE MARTABA, KUMA SUKE TSARE MUTUNCINTA.
.
1● An umurci mace, kamar yadda aka umurci namiji, data kame ganinta, ta kuma kiyaye farjinta, ALLAH (SWT) Yace:
.
قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَٰلِكَ أَزْكَىٰ لَهُمْ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ * وَقُل لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ
.
Ma'ana: ''Kace da Muminai maza su kame ganinsu, kuma su kiyaye farjinsu. Wannan shi yafi tsarki agare su, haqiqa ALLAH masanin abunda suke aikatawa ne. * Kace da Muminai mata su kame ganin su, kuma su kiyaye farjinsu.'' [Suratul Noor aya ta 30-31]
.
→ Malaminmu Sheikh Muhammad Al-Amin Al-shanqid'i (Rahimahullah) Yace acikin Tafsirinsa Adawa'ul Bayan [6/186-187]:

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

DAUKAN GAWA A MAKARA DA KAITA MAQABARTA DA BINTA ABAYA
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

DAUKAN GAWA A MAKARA DA KAITA MAQABARTA DA BINTA ABAYA

Bayan an gama yiwa gawa wanka anmata likkafani wajibine adauketa tareda binta abaya zuwa maqabarta wannan yana daga cikin hakkin musulmin akan musulmi.

BIN GAWA DA KAITA MAQABARTA KALA BIYU:-
1-Binta da kaita tun daga gidan ahalinsa zuwa wajan da zaa yi masa sallah.
2-Binta da kaita tun daga gida da yi mata sallah har zuwa binneta a maqabarta.
Manzan Allah (saw) yace:Duk wanda ya raka jana iza tun daga gida har akai mata sallah dan Allah. Allah zai bashi qiradi daya.wanda kuma ya wuce har aka bunneta yanada qiradi biyu sai habbai sukace manene qiradi? Sai yace:qiradi daya yana daidai da dutsan uhudu.

AKULA DA ABUBUWA KAMAR HAKA:-
1-Mata basa kai gawa Kuma falalar akan maza take kawai.

2-Bai halatta akai gawa anayin abin ya sabawa shariaba kamar DAGA MURYA DA KUKA DA BINTA DA BINTA TURARE KO WUTA.

3-Bai halatta ariga yin zikiri ba ana (LAILAHA ILLALLAHU) agaban gawa ko bayanta bidia ne hakan.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

07 SHIN KASANCEWAR SAYYIDUNA MU'AWUYYA DAN ALJANNA NE ?
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

KASHI NA HUDU

07 SHIN KASANCEWAR SAYYIDUNA MU'AWUYYA DAN ALJANNA NE ?

SHIN ZAKA IYA YIMUSU HUKUNCI ?

ﺍﻟﺤﻤﺪﻟﻠﻪ ﻭﺻﻼﺓ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﻟﻠﻪ .

HAQIQA ACIGABADA KAWO DALILAI NA ALQUR,ANY DA KUMA INGANTACIYAR SUNNAR MA,AIKI AKAN KASANTUWAR ZAMANTOWAR
S.MU,AWUYYA DAYA DAGA CIKIN YAN
ALJANNAH TO YAU ZAMU KAWO WANI DALILI DA ZAMU NEMI WANDA ZAI IYA
WARWAREMANA SHI.

MUTUQAR ZAKA ZARGI S.MU,AWUYYA TO ZAKA ZARGI S.ALI .

HAQIQA DUKKAN WANDA YAKASANCE MAI QAUNAR MA,AIKI TO YAYARDA DA MAGANAR MA'AIKI INDA YAKECEWA .

ﻭﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻣﻮﺳﻰ . ﺭ . ﻋﻦ ﺍﻟﺤﺴﻦ .ﺭ . ﺃﻥ ﺍﺑﺎﺑﻜﺮﺓ . ﺭ . ﻗﺎﻝ ﺳﻤﻌﺖ ﺍﻟﻨﺒﻲ . ﺹ . ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻨﺒﺮ ﻭﺍﻟﺤﺴﻦ ﺇﻟﻰ ﺟﻨﺒﻪ ﻳﻘﻮﻝ ﺇﺑﻨﻲ ﻫﺬﺍ ﺳﻴﺪ ﻭﻟﻌﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﺼﻠﺢ ﺑﻪ ﺑﻴﻦ ﻓﺌﺘﻴﻦ ﻋﻈﻴﻤﺘﻴﻨﻲ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ .

> ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ٣٧٤ >.

TO TABBAS MA,AIKI .S.A.W. YACE WANNAN DAN NAWA SHUGABANE MAIYUWUWA ALLAH YASANYA YAZAMA WANDA ZAI SULHUNTA
TSAKANIN MANYA MANYAN BANGARORIN MUSULMAI GUDA 2.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

06 SHIN KOKASAN CEWA SAYYIDAUNA MU'AWUYYA DAN ALJANNA NE ???
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

KASHI NA UKU

06 SHIN KOKASAN CEWA SAYYIDAUNA MU'AWUYYA DAN ALJANNA NE ???

ﺍﻟﺤﻤﺪﻟﻠﻪ ﻭﺻﻼﺓ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﻟﻠﻪ .

ACIGABAN KAWO DALILAI NA, AYOYI DA KUMA HADISAI DAKE NUNI DA KASANTUWAR ZAMOWAR S. MU,AWUYYA .RD. A GIDAN
ALJANNAH.

TO YAU ZAMU CIGABA.

DAGA INDA MUKA TSAYA.

ﻋﻦ ﻳﺰﻳﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﻌﺴﻢ ﻗﺎﻝ .:ﺳﺌﻞ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ > ﺭ ﺍﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﺷﻴﺐ ٣٩٠٣٥ >

ANTANBAYI S.ALIYU DANGANE DA YAQIN DA YAFARU A SUFYIN TSAKANINSA DA DAN UWANSA S. MU'AWUYYA NAGAME DA WADANDA
AKAKASHE ACIKIN YAQIN SAI S. ALIYU YAKE CEWA WADANDA AKAKASHE DAGA CIKIN MU DA WADANDA AKA KASHE DAGA CIKIN SU S. MU,AWUYYA DUKA YAN ALJANNA NE.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

05 SHIN KASANCEWA SAYYIDUNA MU,AWUYYA DAN ALJANNANE ??
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

KASHI NA BIYU

T05 SHIN KASANCEWA SAYYIDUNA MU, AWUYYA DAN ALJANNANE ??

ﻭﺻﻼﺓ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﺧﻴﺮﺧﻠﻖ > ﻣﺤﻤﺪ ﺹ

ﺍﺣﻤﺪ ٤ /١٢٧ ﻭ ﻓﻀﺎﺋﻞ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ١٧٤٨ ﻭﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ﻓﻲ
ﺍﻟﻜﺒﻴﺮ ١٨ /٦٢٨ ﻭﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ ﺗﺎﺭﻳﺨﻪ ٧ /٣٢٦ ﻭﺍﺑﻦ ﺧﺰﻳﻤﺔ
١٩٣٨ ﻭﺍﻟﻬﻴﺜﻤﻲ ٩ /٣٥٦ ﻭﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺹ ٣٢٢٧ .

TO MA,AIKI GASHI DAKANSA YANA NEMAN ALLAH DA YASANAR DA SAYYIDUNA MU, AWUYYA ILIMIN
ALQUR, ANI DA KUMA IYA LISSAFI.

KUMA YATSARESHI AZABAR WUTA.

KAGA KUMA WALLAHI ALLAH YA,ANSHI WANGA ROQO NA MA,AIKI.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

04 SHIN KASAN CEWA SAYYIDUNA MU, AWUYYA DAN ALJANNA NE ?
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

KASHI NA DAYA

04 SHIN KASAN CEWA SAYYIDUNA MU, AWUYYA DAN ALJANNA NE ?

ﻭﺻﻼﺓ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﻟﻠﻪ .

HAQIQA SAYYIDUNA MU,AWUYYA DAN GIDAN ABU SUFIYAN DA GA S.HINDU DAN ALJANNA NE .

KUMA BISA DALILI NA AYA DA HADISI.

KAFIN IN,FARA ZANYI WANI DAN TANBIHI AKAN WANGA KALMA

ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﻲ

SABODA NAGA WASU BASU SAN MAI AKE NUFI DA ITA BA.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

HUKUNCIN CIN YANKAN AHLUL KITABI CIKIN WANNAN ZAMANI NAMU
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

By Dr. Ibrahim Jalo

HUKUNCIN CIN YANKAN AHLUL KITABI CIKIN WANNAN ZAMANI NAMU

kullum Ahlus Sunnah wal Jama'ah a duk inda suke suna gina addinsu ne a kan abin da ya tabbata daga Alkur'ani Mai girma da kuma ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah masu daraja. Amma sabaninsu su kan gina addininsu ne kawai a kan abin da ya dace da son zuciyarsu.

Wani dan'uwa ya yi tambaya game da mas'alar da ya kamata a ce kusan yawancin al'ummar Musulmi suna sane da cewa tana rubuce cikin Alkur'ani mai girma cikin suratul Ma'idah, wannan kuwa ita ce mas'alar cin abinci ko yankan Ahlul Kitabi, watau Kafurai Yahudawa, da Kafurai Kiristoci.

Domin takaita amsar wannan tambayar za mu kawo maganar da biyu daga cikin manyan malaman duniyar Musulunci suka fada game da mas'alar.

(1) Ya zo cikin littafin fatawa na Sheik Bin Baz Shugaban majalisar malamai ta kasar Saudia a zamanin shi, littafin shi mai suna Majmu'u Fatawa Ibni Baz 5/396 kamar haka:-

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Hukuncin wanda yayi Sallah ba zuwa ga Alqibla ba A mantuwa
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Hukuncin wanda yayi Sallah ba zuwa ga Alqibla ba A mantuwa

Tambaya: Meye hukuncin mutumin da yayi sallah, sai bayan ya gama sannan ya fahimci cewa wannan sallah da yayi ba Alqibla ya fuskanta ba?

Amsa: yana daga cikin sharadin sallah mutum ya fuskanci Alqibla matukar ba wata matsala aka samu ba wadda zata hanashi hakan, inhar ko mutum yaki fuskantar Alqibla alhalin yana da dama toh sallarsa batacciya ce, sabida Allah yace ''Ka juya da fuskarka zuwa ga masallaci Tsararre'' (Baqara 144). Da umarnin da annabi(Sallallahu alaihi wasallam) yayi yace ''Sannan ka fuskanci alQibla kayi kabbara) Bukhari 6667.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Hukuncin wanda kabbara daga cikin kabbarorin sallan gawa ko sallar idi suka wuce
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Hukuncin wanda kabbara daga cikin kabbarorin sallan gawa ko sallar idi suka wuceshi

Mutum ne yazo sallan gawa sai ya tarar da liman ya riga yayi kabbara biyu ko fiye da haka meye hukuncinsa? zai yi kabbara ya fara daga karatun fatiha ne ko kuma zai fara daga inda limamin yake ne sannan daga karshe ya rama kabbarorin ko kuma bazai rama su ba?

Amsa:

idan mutum wasu kabbarori suka wuceshi daga cikin kabbarorin sallan gawa toh in yazo zaiyi kabbara ne sannan ya fara karanta fatiha, zaiyi lura da cewa wannan kabbarar itace farkon kabbararsa, sannan in limami ya kammala sallan shikuma zai tsaya ya kammala kabbarorin da suka wuceshi da sauri, in har ba'a dauke gawar ba, amma in aka dauke gawar to kawai zaiyi kabbarorin da suka wuce masa ne ajere ba tare da bata lokaci ba ko yin addu'oi bayansu, dalilin da yasa malamai sukace wanda wasu kabbarori suka wuceshi na sallan gawa zai cikesu shine umumin fadin manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam),

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Hanyar Neman Tsari Daga Sharruka
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Hanyar Neman Tsari Daga Sharruka

Assalamu Alaikum 'yan'uwa, a takaice zamu dubi wasu hanyoyi na neman tsari daga sharruka ta duniya da lahira, wanda addinin musulunci ya koyar damu. kaman yanda kowa ya sani ne da yawa daga cikin mutane suna cikin tsoro, da rashin kwanciyar hankali, musamman a wannan zamani da fitintinu sukayi yawa, wasu mata zaka samu sukuma suna fama da matsaloli na bugun Aljannu. Duka wannan insha'Allah ana iya yin riga kafinsa Da yardar Allah,

Da farko abinda musulmi ya kamata ya gane shine komai ya sameshi daga Allah ne, babu mai iya cutar dashi ko amfanar dashi sai da yardar Allah, sabida haka in matsala ta sami musulmi abinda zai fara yi shine komawa zuwa ga Allah, kada yaje wurin boka, ko malamin tsubbu koma wace tarkace, domin ba abinda wannan zai iya masa.

Hanyoyin neman tsari:

1.Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace wa sahabinsa uqbah(Radiyallahu anhu) kulhuwallahu, falaq, da nasi, babu wani abinda mutum zai nemi tsari dasu fiye da wannan. Musulmi ya kamata ya lazimci karanta wa'innan surori uku safe da yamma da kuma in zaiyi bacci

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Wani lakani ne zan bayar wanda nake fatar in samu lada mai wanda yayi aiki da sh
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Wani lakani ne zan bayar wanda nake fatar in samu lada mai wanda yayi aiki da shi shima ya samu lada

Wanda kuma ya turawa dan uwansa shima ya samu lada.

HADISI NA FARKO Manzon Allah (S.A.W) ya na cewa Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad kafa 10x Allah ya yi masa Alkawarin zai gina masa kata faren gida a gidan Aljanna sai Sayidina Umar ya ce Ai to in haka ne sai mu dinga yawai tawa sai Manzon Allah ya ce Allah shine mai yawaitawa Allah shine mai tsabtacewa.

HADISI NA BIYU Manzon Allah ya na cewa duk wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar jumaa Allah zai cika masa hasken sa har zuwa wata jumaa mai zuwa yana cikin haske yana cikin farin ciki.

HADISI NA UKU Annabi Muhammad (S.A.W)

ya ce duk wanda ya haddace ayoyin goma na farkon kahfi Allah zai kiyayeshi daga fitinar dujal.

HADISI NA HUDU Manzon Allah yana cewa Wanda ya karanta ayatal kursiyu bayan kowace Sallah ta farillah ba abinda zai hana shi shiga Aljanna sai in bai mutu ba.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

ABUBUWAN DA ANNABI (SAW) YA NEMI TSARI DA SU
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

ABUBUWAN DA ANNABI (SAW) YA NEMI TSARI DA SU

WADANNAN ABUBUWA DA SUKAZO A HADISAI ANNABI SAW YA NEMI TSARI DA SU.

1, ZUCIYAR DA BATA TSORAN ALLAH.

2, FITINAR ZUCIYA 3, SHARRIN, JI ,DA GANI 4, TSORO 5, ROWA 6, BAKIN CIKI 7, DAMUWA 8, BACIN RAI 9, HASARA 10, SABON ALLAH 11, KASALA 12, GAJIYAWA 13, KASKANCI 14, KARANCI 15, TALAUCI, 16, FITINAR KABARI, 17, ZUCIYAR DA BATA KOSHI 18, YUNWA 19, CIN AMANA 20, TABEWA 21, MUNAFINCI 22, BASHI 23, FITINAR WADATA 24, FITINAR DUNIYA 25, SHARRIN MAZAKUTA 26, KAFURCI 27, BATA 28, RINJAYAN MAKIYA 29, DARIYAR MAKIYA 30, MUMMMUNAN TSUFA 31, MUMMUNAR HUKUNCI 32, TABEWA A RAYUWA 33, CIWON HAUKA 34, KAMBUN BAKA 35, KASKANCIN RAYUWA 36, KOMAWA BAYA A RAYUWA 37, ADDU'AR WANDA AKA ZALUNTA 38, MUMMMUNAR MAKOMA 39, MUMMUNAN MAKOCI 40, RINJAYAN MAZAJE 41, FITINAR DUJAL 42, AZABAR JAHANNAMA 43, SHARRIN SHEDANUN MUTANE 44, FITINAR RAYUWA 45, FITINAR MUTUWA 46, AZABAR KABARI, 47, SHARRIN ABINDA AKA SANA ANTA.

48, SHARRIN ABINDA AKA AIKATA 49 , SHARRIN ABINDA MUTUM BAIYI BA 50, SHARRIN GIRGIZAR KASA 51, GANGAROWA DAGA TUDU 52, RUSOWAR GINI AKA 53, NEMAN TSARI DA YARDAR ALLAH DAGA FUSHIN SA.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

IMANI DA RASSAN SA GUDA 67, NAWA KAKE DA SU A CIKI.?
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

IMANI DA RASSAN SA GUDA 67, NAWA KAKE DA SU A CIKI.?

Manzon Allah saw yace: Imani yana da rassa guda Sitttin bakwai , ko sabain da bakwai, mafi daraja, shine ,Lailaha illalahu, mafi karanta dauke abu mai cutarwa daga hanya, kunya tana daga cikin imani. Muslum ya ruwaito Malamai sunyi bincike domin gano wadannan rassa, sun wallafa littafai da dama akan haka, abinda suka kawo, daga Alkur'ani mai girma, da ingatattun hadisai, kuma sun gaya mana cewa wadannan rassa sun fito daga aiyukan zuciya, da aiyukan harshe, da aiyukan gabbai, kuma imani yana karuwa yana raguwa.

1- Imani da Allah, shi yayi halitta, shi ya mallaka. shi yake gudanarwa.shi ya cancanci bauta. Da sunayansa da siffofinsa.

2- Imani da Mala'ikun Allah, da siffofin su da aiyukan su, da sunayansu.

3- Imani Da Manzannin Allah swt.

4- Imani da littafan Allah swt, 5- Imani da ranar Lahira.

6- Imani da kaddara mai dadi da mara dadi.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

FARKON SHIGA ALJANNAH (SAWW)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

FARKON SHIGA ALJANNAH (SAWW)

Farkon wanda zai shiga Aljannah aranar Alqiyamah shine Annabinmu Muhammadu (saww)
kamar yadda Imamu Muslim ya ruwaito daga Sayyiduna Anas bn Malik (rta) yace Manzon Allah (saww) yace:

"ZAN ZO KOFAR ALJANNAH ARANAR ALQIYAMAH, SAI IN KWANKWASA, SAI MAI TSARONTA (WATO MALA'IKA RIDHWAN)
YACE : "KAI WANENE?".

ZAN CE MASA "MUHAMMADU NE". SAI YACE : "SABODA KAI AKA UMURCENI KAR IN BUDE MA WANI KAFIN KA".

Acikin wata ruwayar kuma yace: "NINE NAFI DUKKAN ANNABAWA YAWAN MABIYA, KUMA NINE FARKON WANDA ZAI KWANKWASA (KOFAR ALJANNAH)." (Muslim ne ya ruwaitoshi).

Acikin ruwayar Abu Hurairah kuma Annabi (saww) yace: "MUNE NA KARSHE KUMA MUNE NA FARKO ARANAR ALKIYAMAH. KUMA MUNE FARKON WADANDA ZASU SHIGA ALJANNAH".

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

TAMBAYOYI DA AMSA MUTUMIN DA KE DA MATA 4 SANNAN YA YI WA DAYANSU YANKAKKEN SAKI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

DR. IBRAHIM JALO JALINGO

TAMBAYOYI DA AMSA MUTUMIN DA KE DA MATA 4 SANNAN YA YI WA DAYANSU YANKAKKEN SAKI KO ZAI HALATTA YA AURI WATA MATAR KAFIN IDDAR WANNAN TA CIKA?

1. Babu sabani tsakanin Malamai cewa: ba ya halatta ga namiji ya hada Ya da Kanwa karkashin aurensa a lokaci guda. Haka nan ba ya halatta gare shi ya daura wa mace ta biyar aure koda kuwa akwai wacce ya saka saki na kome matukar dai ba ta gama iddarta ba. Wannan mas'ala babu sabani a cikinta tsakanin Malaman Sunnah; saboda dalilai da yawa daga cikinsu akwai: Fadar Allah cikin surar Nisaa'i aya ta 23 ((Kuma kada ku hada tsakanin Ya da Kanwa saifa abin da ya riga ya wuce)). Da kuma wasu hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah, daga cikinsu akwai hadithi na 2243 da Imam Abu Dawud ya ruwaito, da hadithi na 1952 da Imam Ibnu Majah ya rueaito, da hadithi na 4631 da Imam Ahmad ya ruwaito, da hadithi na 4156 da Imam Ibnu Hibban ya ruwaito dukkansu da isnadi sahihi cewa Sahabi Wahb Al-Asadiy ya musulunta alhalin yana da mata 8 sai Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce da shi ya zabi 4 kawai daga cikinsu. Haka nan ya faru da sahabi Gailan Bin Salamah, haka nan ya faru da sahabi Qais Bin Al-Harith.

2. Amma su Malaman Sunnah sun yi sabani game da idan mai mata 4 ya saki guda a cikinsu saki yankakke watau: saki na 3 ko kuwa sakin Khul'i, ko yana da damar ya daura wa wata matar aure kafin iddar wannan da ya saken ta kare? Akwai mazhabobi biyu na Malamai cikin wannan mas'ala:-

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [19]
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

I'ITIKAFI DA HUKUNCE- HUKUNCENSA ....[3]

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [19]

ABUBUWANDA BAYA HALATTA GA MAI I'ITIKAFI

1• JIMA'I: Yin jima'i da sumbatar mace da wasa da ita baya halatta ga mai i'itikafi da dare ko da rana, idan kuma har hakan ya faru to i'itikafin ya 6aci, saboda hani akan wannan yazo cikin alqur'ani mai girma, ALLAH (SWT) Yana cewa: "kada kuyi mubashara da mata alhali kuna masu i'itikafi acikin masallatai" .

(Surah ta 2 aya ta 187)

2• FITA DOMIN GANIN MARAR LAFIYA: Ba ya halatta ga mai i'itikafi ya fita zuwa ganin marar lafiya a gida ko a asibiti.

3• JANA'IZA: Ba ya halatta ga mai i'itikafi ya halarci sallar gawa sai dai idan sallar gawar ta kasance acikin masallacin da yake i'itikafi ne to zai iya yin sallar gawar tare da Liman. Kar ya fita sai fitar da bata da makawa, saboda Aisha (RA) tace:

"Abunda yake sunnah ga mai i'itikafi kar ya gaida marar lafiya, kar ya halarci jana'iza (sallar gawa) kar yayi jima'i da mace, kuma kar ya shafeta shafar jin dadi" .

(Abu-dawud ya fitar dashi)

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [18]
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

I'ITIKAFI DA HUKUNCE- HUKUNCENSA ....[2]

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [18]

SHARUDAN I'ITIKAFI

1• MASALLATAI: Yin i'itikafi baya inganta sai acikin masallatai.

Saboda ALLAH (SWT)
Yace: "Kada ku yi mubashara da mata alhali kuna masu i'itikafi acikin masallatai" .

(surah ta 2 aya ta 187)
Amma ba kowane masallaci ake i'itikafi acikinsa ba, domin yazo acikin Hadith cewa:

"Babu i'itikafi (cikakke)
sai a masallatai uku" wato Masallacin Makkah, Masallacin Qudus da Masallacin Madina" (Hadith ne ingantacce malamai sun inganta shi)
Amma wannan Hadith ba yana kore yin i'itikafi bane acikin wanin wadannan masallatai bane, sai dai yana kore cikar ladar i'itikafi a wani masallacin na daban.

2• MUSULUNCI: sharadi ne mai i'itikafi ya kasance musulmi domin ba'a kar6an i'itikafin Kafiri.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [17]
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

I'ITIKAFI DA HUKUNCE- HUKUNCENSA ....[1]

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [17]

•I'ITIKAFI: malamai sunyi bayanin ma'anar i'itikafi cewa shine tsayuwa akan wani abu, ta wannan ma'anar ne ake cewa wanda ya zauna masallaci yana ibada acikinsa, wanda ya ke6e domin bautar ALLAH (SWT).

•••HIKIMAR YIN I'ITIKAFI••• .

Haqiqa ALLAH (SWT) Ya shar'antawa bayinsa yin i'itikafi, wanda manufar hakan ita ce komawar zuciya ga ALLAH (SWT)
domin neman kusanci da neman yardarSa, Kuma ALLAH ne ke debewa mai i'itikafi kewa a lokacin da ya nisanci mutanen dake debe masa kewa domin zai ke6antu ne da ambaton ALLAH, kuma haqiqa ALLAH yana son masu ambatonsa.

•••ZAMAN I'ITIKAFI••• .

ALLAH (SWT) Yace:

"Kada ku yi mubashara (hada jiki) da mata alhali kuna masu yin i'itikafi a masallatai" .

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [16]
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

FALALAR KWANA GOMA (10) NA QARSHEN WATAN RAMADAN !!!

MARABA DA WATAN RAMADAN [16]

Kwanakin watan Ramadan dukkansu akwai falala acikinsu, sai dai mafi falalarsu sune kwanaki 10 na qarshe. Saboda ayoyin Alqur'ani da Hadithai ingantattu sun zo da bayanin falalarsu. Daga cikin falalar wadannan kwanaki akwai:-

1• Acikinsu ne ake dacewa da daren Lailatul Qadr, ba a nemansa acikin sauran kwanaki face acikin kwana 10 na qarshen Ramadan, saboda Hadithin Aisha (RA)
tace:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Ku nemi Lailatul Qadr acikin marar kwanaki 10 na qarshen watan Ramadan" .

(Bukhari 4/225, Muslim 1169)
2• Lallai Manzon ALLAH (SAW) Ya himmantu kuma ya kula sosai da wadannan kwanaki 10 na qarshen watan Ramadan, saboda idan suka zo Manzon ALLAH (SAW) Yana daura gyautonsa (damara) ya dage da ibada ya nisanci iyalansa, yayi ta ayyukan alkhayri da Da'a zuwa ga Ubangijinsa a Masallacinsa.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: