Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

EsinIslam Media: Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Search on This Topic:   
[ Go to Home | Select a New Topic ]

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Falalar Darare Goma na Zul-Hajji
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Falalar Darare Goma na Zul-Hajji

Allah Madaukaki Ya ce: "Ina rantsuwa da Alfijir. Da Darare Goma." (Alfajr:1-2). Malamai sun kai sun kawo kan wadanne ne Darare Goma. Kuma mafi rinjaye sun tafi a kan darare goma na farkon watan Zul Hajji ne, kamar yadda Ibnu Kasir ya ce: "Darare Goma: Ana nufin goman Zul Hajji ne kamar yadda Ibnu Abbas da Ibnu Zubair da Mujahid da malamai da dama na Salafus Salih da Khalafus Salih suka fadi." (Tafsirul ku'anil Azim, mujalladi na 4 shafi na 539-540).

Ibnu Sa'adi (Rahimahllah) ya ce, "A bisa mafi ingancin magana su ne dararen goma na Ramadan ko darare goma na Zul Hajji. Su darare ne da suka kunshi ranaku masu falala, ayyukan ibada da neman kusanci ga Allah suna aukuwa a cikinsu fiye da wasunsu… A cikin darare goma na Zul Hajji ne ake tsayuwar Arfa wanda Allah Yake yin gafara ga bayinSa, gafarar da Shaidan ke bakin ciki da ita, domin Shaidan bai taba ganin kaskanci da tozarci irin na Ranar Arfa ba, saboda abin da yake gani na sassaukar Mala'iku da rahama daga Allah a kan bayinSa, kuma ayyukan Hajji da Umara na gudana a cikinsu. Wadannan abubuwa masu girma sun cancanci Allah Ya yi rantsuwa da su." (Taisirul Karimir Rahman, mujalladi na 7 shafi na 621-622).

An karbo daga Ibnu Abbas (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: "Babu ranakun da ayyuka nagari suka fi soyuwa a wurin Allah daga wadannan ranaku goma (na Zul-Hajji). (Sahabbai) Suk ce, Ya Rasulullahi! Ko da jihadi a tafarkin Allah? Ya ce, "Ko da jihadi a tafarkin Allah, sai dai in mutum ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai daga cikinsu ba." (Buhari). Ibnu Rajab ya ce: "Wannan Hadisi ya nuna aiki a cikin ranakunsa (Ranaku 10 na Zul-Hajji) ya fi soyuwa a wurin Allah daga aiki a sauran ranakun duniya ba tare da toge komai daga gare su ba. Kuma idan ya kasance mafi soyuwa ga Allah, to shi ne mafi falala a wurinSa." (Lada'iful Ma'arif, shafi na 458).

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Dabbobin Layya da kwanakin 10 na farkon Zul-Hajji
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Dabbobin Layya da kwanakin 10 na farkon Zul-Hajji

Babban Limamin Masallacin Nagazi-Ubete, Okene, Jihar Kogi

Mukaddima:

Bayan haka ya bayin Allah! Daga cikin muhimman lokuta na yin ibada akwai ranaku 10 na farkon watan Zul-Hajji – wata na 12 na shekarar Musulunci, wadanda Allah Ya fifita a kan sauran kwanaki na shekara.

Ibn Abbas ya ruwaito cewa: "Annabi (SAW) ya ce: "Babu wani aiki da ya fi alheri irin wanda aka yi a ranaku 10 na farkon Zul-Hajji." Sai wadansu sahabbai suka ce: "Koda jihadi a tafarkin Allah?" Annabi (SAW) ya ce: "Koda jihadi a tafarkin Allah, sai dai in mutum ya tafi da kansa da dukiyarsa bai dawo da komai ba." (Buhari).

Wadannan kwanaki goma manya ne kuma mafiya soyuwa ne a wurin Allah. Ibn Umar (RA) ya ruwaito cewa: "Annabi (SAW) ya ce: "Babu wasu ranaku da suka da girma kuma suka fi soyuwa a wurin Allah fiye da wadannan kwanaki goma na farko Zul-Hajji, don haka ku yawaita tahlili da takbiri da tahmidi a cikinsu" (Musnad Imam Ahmad). Kuma Sheikh Ahmad Shakir ya inganta shi.

Daga cikin darajojin da wadannan kwanaki goma suke da su akwai cewa:

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)

Shi kuma Salam bin Abu Mudi'u ya ce: "kattada yana sauke Alkur'ani a (kwana ko dare) bakwai, amma idan Ramadan ya zo a kowane uku. Idan goman karshe suka zo, sai ya rika saukewa a kowane dare." (Siyar A'alamin Nubla'i, 5/276).

Rabi'u bin Sulaiman ya ce: "Imam Shafi'i ya kasance yana sauke Alkur'ani sau sittin a cikin watan Ramadan." (Siyar A'alamin Nubla'i, 10/36). Akwai misalan haka da dama.

Tsayuwar Ramadan:

An karbo daga Abu Huraira (RA) cewa: "Lallai Manzon (SAW) ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar Ramadan (Sallar Tarawihi ko Asham) yana mai imani kuma domin Allah kawai, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa." Buhari da Muslim suka ruwaito.

Aliyu bin Al-Madani ya ce: "Suwaidu bin Ghafalata ya rika yi mana limanci a tsayuwar Ramadan har ya kai shekara 120 a duniya." (Siyar A'alamin Nubla'i, 4/72).

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah, Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni zuwa ga samun alheran duniya da Lahira; (Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsa cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta, amin.

Bayan haka, yau mukalarmu za ta gudana ne kan amsar tambayar da aka yi wa marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam kamar haka:

Mene ne hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla? – Daga baya kuma sai mu ga abin da wadansu malaman suka ce, in Allah Ya so.

Amsa: Addu'a bayan an kammala sallar farilla (ta danganci) nau'in addu'ar da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake yi, (wanda) shi ne ‘Du'a'u Ibada,' ba Du'a'u Mas'ala ba.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya ce duk wanda ya gode wa ni'imarSa, zai samu kari. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni gare su wajen samun abubuwan more rayuwar duniya da Lahira. Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, yau za mu ci gaba da mukalar tamu ne daga bayanin:

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)

Makircin Shaidan wajen hana gode wa Allah

Yayin da makiyin Allah, Shaidan ya san girman matsayin godiya, wadda tana daya daga cikin mafi daukakar lamarin ibada (bauta) ga Allah kuma mafi muhimmancinta, sai ya sa matukar zirga-zirgarsa da kokarinsa wajen kange mutane daga barin ta.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya ce duk wanda ya gode wa ni'imarSa, zai samu kari. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni gare su wajen samun abubuwan more rayuwar duniya da Lahira. Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, mun kwana bayan kawo misali da yabon da Allah Ya yi wa ManzonSa na farko Annabi Nuhu (Alaihis Salam), wanda aka ce bawa ne mai godiya. Sai kuma Hadisin da aka samo daga Anas bin Malik (Allah Ya yarda da shi), inda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, "Allah Yana murna da bawanSa, wanda idan ya ci ko ya sha wani abu, sai ya gode wa Allah saboda haka."

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Buhari Da Muslim: Babi Na Hudu 140 - 142 & 148
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Buhari Da Muslim: Babi Na Hudu 140 - 142 & 148

Tare da Sheikh Yunus Is'hak Almashgool, Bauchi

Yanda aka halitta taurari Kattada ya ce: Bisa faDar Allah MaDaukaki cewa: "Hakika Mun kawata saman duniya da taurari…(67:5)." Kuma dalilan halittar taurari ya kasu kashi uku: Na farko saboda kawata sama, na biyu saboda jifar sheDanun Aljnnu, na uku saboda shiryadda mutane da su. Wanda ya yi fassara fiye da haka to lallai ya yi kuskure ya tozarta rabonshi, kuma ya Dora wa kanshi Abin da bai sani ba." Saboda haka harba mutum zuwa taurari vata dukiya ne da karfi.

BABI NA HUDU:-

Siffar Rana da Wata bisa lissafi. Mujahid ya ce: Suna juyawa kamar mulmulin dunkuli. Wasu sun ce: "Suna kewaya bisa lissafi da masaukai wani bai ketaran wani. Kuma ana kiran jama'a da suna Husban: Kamar yadda ake faDar shihab da shuhban….har zuwa karshe duba littafin Tafsiri.

140. An karvo daga Muhammad DanYusuf ya ce: "Sufiyan ya ba mu labari daga A'mash daga Ibrahim Ataimi daga babansa daga Abu Dharri (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Annabi (SAW) ya ce wa Abu Darri lokacin da rana ta vuya: Shin ko kasan inda wan nan rana take zuwa? Na ce, "Allah da ManzonSa suka fi sani ya ce: "Lallai ita tana tafiya ne zuwa karkashin Al'arshi tayi sujuda, sai ta nemi izini sai ayi mata izinin. Kuma ya yi kusa in tayi suujuda ba za'a karvan mata ba. Kuma za ta nemi izinin, ba za'a yi mata izininba. Sai a ce mata: Ki koma in da kika fito, sai ta rika vulla in da take vuya. To wan nan shine fassarar faDar Allah MaDaukaki cewa: "Rana tana gudana ce ga matabbacinta wan nan shine kaddarawa Mabuwayi Masani. (36:38)."

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Buhari da Muslim: Babi na Talatin da Biyu 114 - 124
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Buhari da Muslim: Babi na Talatin da Biyu 114 - 124

Tare da Sheikh Yunus Is'hak

Almashgool, Bauchi

Babi na Ashirin da Takwas: Yadda shugaba ke aikawa ga wanda ya warware alkawari:

114. An karbo daga Abu Nu'aman ya ce: "Sabit dan Yazid ya ba mu labri ya ce, Asim ya ba mu labari ya ce: "Na tambayi Anas (Allah Ya yarda da shi), game da kunuti yaushe ake yi? Ya ce, "Kafin ruku'u ne." Sai ya ce: "Lallai wane yana riyawa ka ce: "Bayan ruku'u ne." Sai ya ce: "karya ya yi." Sa'an nan ya bayar da labari daga Annabi (SAW) cewa: Lallai shi ya yi kunuti kamar wata daya bayan ruku'u yana addu'a a kan kabilun Bani Sulaim." Ya ce, "Kuma ya taba aikawa da wadansu mutum arba'in ko ya ce, saba'in, makaranta Alkur'ani zuwa ga wadansu mutane daga mushirikai. Daga baya suka juya baya suka kashe su, saboda tsakaninsu da shi (Annabi SAW) akwai sulhu. Kuma ban taba ganin abin da ya bata wa Annabi (AS) rai ba kamar mutuwar wadannan mutane ba."

Babi na Ashirin da Tara:

Karbar amanar da mata suka dauka da karbar makwabtakarsu:

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Buhari da Muslim: Babi na Goma Sha Tara & Babi na Ashirin 90 - 102
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Buhari da Muslim: Babi na Goma Sha Tara & Babi na Ashirin 90 - 102

Tare da Sheikh Yunus Is'hak

Babi na Goma Sha Tara: Abin da Annabi (SAW) ya kasance yana bayarwa saboda lallashin wadanda suke wajen Musulunci daga daya cikin biyar na ganimar yaki. Abdullahi dan Zaid ya ruwaito shi daga Annabi (SAW):

90. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: "Auza'iyyu ya ba mu labari daga Zuhuri daga Sa'id dan Musayyib da Urwatu dan Zaubair cewa: "Lallai Hakim dan Hizam (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Na taba rokon Manzon Allah (SAW) ya ba ni. Sa'an nan na sake rokonsa ya ba ni. Sa'an nan ya ce mini: " Ya Hakim! Lallai wannan dukiya kamar 'ya'yan itace ne mai zaki (koriya ce mai saukin ci), wanda duk ya karbe ta da neman wadutawa daga roko Allah zai sanya masa albarka. Wanda ke karba don tarawa da neman daukaka ba a sanya masa albarka. Sai ya kasance kamar wanda ke cin abinci bai koshi. Kuma hannu madaukaki (mai mikawa) ya fi alheri a kan hannu makaskanci (mai karba)." Sai Hakim ya ce, "Sai na ce, "Ya Manzon Allah! Ina rantsuwa da Wanda Ya aiko ka da gaskiya ba zan sake rokon wani ba a kan komai a bayanka har in bar duniya. Daga nan Abubakar (RA) ya kasance yakan kira Hakim don ya ba shi kyauta sai ya ki karbar komai. Sa'an nan lokacin Umar (RA) ya kira shi domin ya ba shi kyauta sai ya ki karba sai ya ce: "Ya jama'ar Musulmi! Ku shaida na gitta (ba shi) hakkinsa wanda Allah Ya raba daga wannan ganimar yaki sai ya ki karbarsa. Hakim ya bar rokon komai daga wajen mutane bayan Annabi (SAW) har ya rasu."

91. An karbo daga Abu Nu'aman ya ce: "Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Ayyub daga Nafi'u cewa: "Lallai Umar dan KhaDDab (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Ya Manzon Allah! Lallai na taba alwashi a lokacin Jahiliyya cewa zan yi I'itikafi yini daya, sai ya umarce shi da ya cika alwashinsa. Ya ce, "Umar ya samu 'yan mata biyu daga fursunan Yakin Hunain sai ya sanya su daga cikin gidajen Makka. Ya ce, "Manzon Allah (SAW) ya yi baiwa ('yanta) wadansu fursunonin Yakin Hunain sai suka rika tafiya cikin hanya (babu wanda ya ce musu komai). Sai Umar ya ce da Abdullahi duba mene ne wannan? Ya ce, "Manzon Allah ne ya saki fursunonin yaki." Sai ya ce, "Tafi ka 'yanta (sake) yaran matan nan biyu." Nafi'u ya ce, "Manzon Allah (SAW) bai yi Umara daga Ji'iranata ba, da kuwa ya yi da haka bai buya ga Abdullahi dan Umar ba."

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Buhari da Muslim: Babi na Tara, Babi na Goma Sha Uku & Babi na Goma Sha Biya
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Buhari da Muslim: Babi na Tara, Babi na Goma Sha Uku & Babi na Goma Sha Biyar 61 - 63 & 72 - 79

Buhari da Muslim: Babi na Tara, Babi na Goma Sha Uku & Babi na Goma Sha Biyar 61 - 63 & 72 - 79

Tare da Sheikh Yunus Is'hak Almashgool, Bauchi

61. An karbo daga Sa'id dan Muhammad Aljarmiyyu ya ce: "Yakub dan Ibrahim ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba mu labari cewa: Lallai Walid dan Kasir ya ba shi labari daga Muhammad dan Amru dan Halhalatu Addailiyyu ya ba shi labari cewa: Lallai dan Shihab ya ba shi labari cewa: Lallai Aliyu dan Husain ya ba shi labari cewa: Lallai su lokacin da suka iso Madina daga wajen Yazid dan Mu'awiyya inda aka kashe Husain dan Aliyu (Allah Ya yi masa rahama), sai Miswar dan Makhramat ya iske shi ya ce masa: Shin ko kana da wata bukata da za ka umarce ni da ita? Na ce masa, "A'a, sai ya ce: "Shin ko za ka ba ni takwabin Manzon Allah (SAW) ina jin tsoron kada mutane su rinjaye ka a kansa yau? Ina rantsuwa da Allah idan ka ba ni ba za su samu ikon karbarsa face in sun kashe ni." Kuma ya ce: "Lallai Aliyu dan Abu Dalib (RA) ya taba neman 'yar Abu Jahil bisa ga nemansa ga Fadima (AS) (wato suna tare). Sai na ji Manzon Allah (SAW) yana huduba ga mutane a mumbarinsa wannan. Lokacin na balaga sai ya ce: "Lallai Fadima tawa ce, kuma lallai ni ina tsoron a fitine ta cikin addininta (bisa ga 'yar Abu Jahil). Sa'an nan ya ambaci surukuntarsa da kabilar Abdu Shams ya yabe shi bisa ga surukuntarsa da shi. Ya ce: Ya yi mini magana ya yi mini gaskiya, ya yi mini alkawari ya cika. Kuma lallai ni, ban zamo mai haramta halal, ko kuma mai halatta haram ba. Amma wallahi 'yar Manzon Allah (SAW) ba ta haduwa da 'yar makiyin Allah har abada."

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Buhari da Muslim: Babi na Biyu, Babi na Hudu 43 - 52
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Buhari da Muslim: Babi na Biyu, Babi na Hudu 43 - 52

Tare da Sheikh Yunus Is'hak Almashgool, Bauchi

Babi na Biyu: Bayar da daya cikin biyar na ganimar yakin Musulunci yana daga cikin addini:

Littafin bayanin hukuncin farillan daya cikin biyar na ganimar yaki. Bisa fadar Allah Madaukaki:

43. An karbo daga Abdan ya ce: "Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Aliyu dan Husaini ya ba ni labari cewa: Lallai Husain dan Aliyu (AS) ya ba shi labari cewa, lallai Aliyu ya ce: "Ya kasance ina da wani rakumi da na samu daga rabon ganimar Badar. Kuma Annabi (SAW) ya ba ni wani rakumi daga daya cikin biyar na ganima. Lokacin da na yi nufin aure da Fadima 'yar Manzon Allah (SAW) sai na yi wa'adi da wani makerin zinari daga kabilar Kainuka'u yakan tafi tare da ni sai mu yiwo kayan tsaure. Ina nufin in rika sayarwa ga makera. Saboda in yi amfani da kudin wajen walimar aurena. Ina cikin wannan halin tanadi da sai na debi wasu kaya da sirdin taguwa na gurfana da su kusa da gidan wani mutumin Madina. Sai na komo lokacin da tara abin da nake son tarawa. Sai kawai taguwoyin nan nawa biyu na iske an yanke musu tozo an soke kwibinsu biyu an debe hantarsu. Sai na kasa (gaza) tsare idona daga kuka, saboda abin da na gani. Na ce, "Wa ya aikata mini wannan? Sai suka ce mini, "Hamza dan Abdul Mudallib ne ya aikata, yana cikin wannan gida na mutanen Madina inda ake shan giya. Sai na tafi har sai da na shiga Annabi (SAW) yana tare da Zaid dan Harisa, Annabi (SAW) ya fahimci abin da ke cikin fuskata na bacin rai. Sai Annabi (SAW) ya ce, me ya faru da kai? Na ce, "Ya Manzon Allah! Ban taba ganin bakin ciki irin wannan yini ba, Hamza ya fada wa taguwoyina biyu ya katse musu tozo, ya huda cikinsu. Ga shi can a wani gida na shan giya. Annabi (SAW) ya kira aka kawo masa alkyabbarsa ya yafa ta. Sa'an nan ya tafi da kafa na bi shi ni da Zaid dan Harisa har sai da ya isa ga gidan da Hamza ke cikinsa, ya nemi izini suka yi masa izini sai ga su cikin maye. Sai Manzon Allah (SAW) ya rika zargin Hamza bisa abin da ya aikata, sai ga Hamza idanuwansa sun yi ja, Hamza ya yi dubi ga Manzon Allah (SAW) sa'an nan ya daga idonsa, ya yi dubi zuwa ga gwiwarsa. Sa'an nan ya dubi zuwa cibiyarsa sa'an nan ya daga ganinsa zuwa fuskarsa. Sa'an nan Hamza ya ce: "Shin ku ba komai ba ne face bayin babana." Sai Manzon Allah (SAW) ya fahimci cewa lallai shi ya bugu: Sai Manzon Allah (SAW) ya juya bisa duga-duginsa da sauri zuwa baya, muka fita tare da shi."

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Buhari da Muslim: Babi na Dari da Tamanin da Uku, Babi na Dari da Tamanin da Biy
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Buhari da Muslim: Babi na Dari da Tamanin da Uku, Babi na Dari da Tamanin da Biyu, Babi na Dari da Tamanin da Shida, Babi na Dari da Tamanin da Bakwai, Babi na Dari da Tamanin da Takwas

Tare da Sheikh Yunus Is'hak Almashgool, Bauchi

Babi na Dari da Tamanin da Biyu: Lallai Allah zai karfafa wannan addini ko da ta karkashin fajiri ne:

15. An karbo daga Abul Yaman ya ce: "Shu'aib ya ba mu labari daga Zuhuri, Hawwala Sanad.

16. An karbo daga Mahmud ya ce: "Abdurrazak ya ba mu labari ya ce, Ma'amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Dan Musayyab daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Mun halarci wani yaki tare da Manzon Allah (SAW) sai ya ambaci wata magana ga wani mutum da ke da'awar Musulunci (Annabi SAW) ya ce: "Wannan yana daga cikin mutanen wuta. Lokacin da ya halarcin yakin nan, mutumin nan ya yi yaki mai tsanani sai aka yi masa rauni. Sai aka ce ya Manzon Allah, wanda ka fadi wata magana game da shi dazu cewa yana daga cikin mutanen wuta, ya mutu." Sai Annabi (SAW) ya ce: "Wuta zai tafi," har sai da wadansu mutane suka kusan su yi kokwanto (bisa ga abin da Annabi SAW ya fada). Ana cikin haka sai aka ce, bai mutu ba amma dai yana da rauni mai tsanani. Lokacin da dare ya yi sai ya gaza hakuri bisa raunin sai ya kashe kansa. Da aka ba Annabi (SAW) labarin haka sai ya ce: "Allahu Akbar, na shaida lallai ni bawan Allah ne kuma ManzonSa ne." Sa'an nan ya umarci Bilal ya yi shela ga mutane cewa: "Babu wata rai da za ta shiga Aljanna face rai Musulma. Kuma lallai Allah zai daukaka wannan addini ko da ta karkashin mutum fajiri."

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Hakuri Baya Baci
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Hakuri Baya Baci

Gaskiya ne rayuwa makaranta ce, Amma wanda zai fi cin jarrabawar wannan makarabta shine mai hakuri da hankalta don kiyaye gaba.Pls ka matashiya game da rayuwa da fatan Allah ya kara mana hakuri da Junan mu, amin

1. Wanda ya ganka a cikin matsala ko bukata a rayuwar ka, ya tsaya ya taimaka maka har aka dace ka fita daga wannan damuwa hakika masoyin ka ne, Don haka abin so shine kayi ta masa addu'a da fatan samun damar ka saka masa, amma ka kiyaye kada kayi masa Butulci, Kuma kayi hakuri dashi kada ka kosa da shi in ya bukaci agajin ka.

2. Wanda ya ganka a cikin matsala ya rabu da kai, wato ya fita sha'anin ka, yaki tausaya maka ko agaza maka. Shi wannan in ka samu dama ka yi kokarin koya masa darassi mai kyau wajen yi masa alheri, kada kayi watsi dashi in yazo nema gun ka, hasali ma abin so shine ka yafe masa abinda yayi maka, insha Allahu hakan zai zamo darassi gareshi a rayuwa ya gane yin hakan ba dai-dai bane ya gyara a gaba.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

018 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 18
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

T018 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 18

Malam ya cigaba da bayani game da HUKUNCIN DA'AWAH A MATSAYIN AIKIN ALKHAIRI:
.
Kuma don a sake fito da alkhairin dake cikin wannan aiki na da'awah, sai ALLAH (SWT) yayi yabo ga al'ummar Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) ta fuskar siffanta al'ummar da muhimmin aikin ta na umurni da kyawawan ayyuka da hani zuwa ga munana a inda yake cewa:
.
كُنتُمْ خَيْرَ أُمَّةٍ أُخْرِجَتْ لِلنَّاسِ تَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَتَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنكَرِ وَتُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَلَوْ آمَنَ أَهْلُ الْكِتَابِ لَكَانَ خَيْرًا لَّهُم مِّنْهُمُ الْمُؤْمِنُونَ وَأَكْثَرُهُمُ الْفَاسِقُونَ
.
''Kun kasance mafi alkhairin al'umma wadda aka fitar ga mutane. Kuna umurni da alkhairi kuma kuna hani daga abunda ake ki, kuma kuna imani da ALLAH, kuma da mutanen littafi sunyi imani, lallai ne da haka ya kasance mafi alkhairi agare su, daga cikinsu akwai muminai, kuma mafi yawansu fasikai ne.'' [Ali-imran:110]

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

017 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 17
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

017 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 17

Malam ya cigaba da bayani game da HUKUNCIN DA'AWAH
.
3● DA'AWAH A MATSAYIN AIKIN ALKHAIRI:
.
Duk da kasancewar aikin da'awah Fardul-kidayah ne, bisa mafi rinjayen magana a tsakanin malamai. Wato idan wasu suka rungumi aikin da'awah nauyin wajibcina ya saraya akan sauran jama'a, amma dumbin alkhairi dake cikin wannan aiki ya bayyana a fili karara.
.
Wasu malamai suna ganin babu yadda musulmi zai tsame hannunsa daga cikin aikin da'awah domin kawai wasu sun dauke masa wajibcin gabatar da wannan aiki. Domin duk da kasancewar aikin da'awah yana bukatar ilimi da fahimtar abunda ke kunshe cikin ilimin, amma ba a shardanta cewa sai mutum ya tara wani adadi na ilimi kafin yayi da'awah ba, asali ma ana bukatar kowa yayi kokarin isar da sakon musulunci gwargwadon iyawarsa, gwargwadon abunda ya fahimta, saboda fadin Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa: ''Ku isar daga gare ni koda kuwa aya daya ce.'' Sannan kuma ba a yarda musulmi ya jahilci addininsa ba, wajibi ne ko wani musulmi ga kowane musulmi yayi kokarin fahimtar dokokin addininsa, kuma ya kasance mai isar da abunda ya fahimta ga wasu idan halin yin hakan ya bayyana.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

016 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 16
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

016 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 16

Malam ya cigaba da bayani game da HUKUNCIN DA'AWAH.
.
2● DA'AWAH A MATSAYIN FARDUL KIFAYAH:
.
Mafi yawan malamai sun raja'a akan cewa da'awah aiki ne na fardul kifayah wato aiki ne da ya wajaba akan dukkan musulmai, amma idan wasu yanki na jama'a zuka rungumi gabatar da wannan aiki, wajibcin yin aikin ya sauka akan sauran jama'a.
.
Wannan ra'ayi ya ginu ne bisa hujjar cewa: ALLAH (SWT) acikin ayar da yayi umurnin aikin da'awah, cikin suratul suratul Ali-imran cewa yayi: ''Kuma wata jama'a daga cikinku ta kasance…'' wato yankin jama'a ba kowa da kowa ba.
.
Ibnul Arabi yana da ra'ayin cewa fadin ALLAH cewa: ''Za'a samu wasu al'umma daga cikinku'' wanda ishara ne da wajibcin yin da'awah, yana nuni ne da kasancewar da'awah Fardul kifayah ne.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

015 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 15
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

013 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 15

Malam ya cigaba da bayani akan HUKUNCIN DA'AWAH bisa aiki na wajibi ga dukkan musulmai.
.
Amma malamai sunyi sabani akan cewa shin wannan wajabcin ya game kowa da kowa ko kuma wasu al'umma daga cikin musulmai zasu iya daukewa sauran awajen wajibci.
.
Daga cikinsu akwai masu ganin cewa wannan Umurni ya game dukkan musulmai, don haka wajibcin da'awah gamamne ne ba a daukewa kowa ba.
.
Alal Misali Sheikh Muhammad Abduh wani shahararren malami da ya rayu a Misra yana cewa acikin tafsirinsa ''Da'awa zuwa ga aikin alkhairi, umurni da kyawawan ayyuka da hani zuwa ga munana farilla ne da ya game dukkan musulmai, kamar yadda zahirin ayar alkur'ani ya nuna.
.
Masu irin wannan fahinta suna ganin cewa Umurnin da ALLAH ya bayar cewa '' Kuma wata jama'a daga cikin Ku'' yana nufi ne Yaku al'ummar musulmi Ku kasance masu da'awah zuwa alkhairi, ku zama masu umurni da kyawawan ayyuka da hani zuwa ga munana. Wato wannan umurni daga ALLAH gamammen umurni ne kuma kalmar daga cikinku ko ﻣﻨﻜﻢ (Min kum) a larabce, an kawo ta ne don Karin bayani amma badon takaitawa ko kebancewa ba, suka ce irin wannan salo yazo acikin alkur'ani a suratul Hajj aya ta 30 a inda ALLAH (SWT) Yake cewa:

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

014 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 14
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

014 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 14

HUKUNCIN DA'AWAH
.
Kamar yadda bayani ya gabata, da'awah aiki ne na Annabawa da Mursalai. Haka kuma aiki ne na dukkan wadanda suka yi imani da sakonnin da suka zo dashi acikin al'ummimin su. Don haka, gabatar da aikin kira Da'a, yana iya daukan hukunce-hukunce daban-daban bisa la'akari da masu Isar da sakon da kuma irin sakon da ake isarwa. A bisa wannan dalili ne, malamai suka yi maganganu akan hukuncin yin da'awah acikin al'umma. Wato yin da'awah yana iya daukan hukunce- hukunce mabanbamta bisa banbamcin yanayin aikin. Bisa wannan ne malamai suka zo da hukunce-hukuncen da'awah kamar haka:
.
1● DA'AWAH A MATSAYIN AIKI NA WAJIBI GA DUKKAN MUSULMAI:
.
Aikin da'awah ko isar da sakon ALLAH ga bayinsa wajibi ne ga dukkan Annabawa da Manzannin ALLAH, domin shine aikin da ALLAH ya turo su bayan kasa domin isarwa. Kasancewar Manzanni da Annabawan ALLAH zasu iya isar da sakonni ne kai tsaye ga wadanda suka riska a zamanin rayuwarsu, don haka ake bukatar wadanda zasu daukaka muryar su saboda isarwa ga sauran al'ummomin su. Domin ta hanyar da'awah ne sakon ALLAH zai mamaye duniya.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Sharrudan da suke halasta wa mutum yayi tafiya zuwa garin kafirai
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Daga Sharhin riyaadussaliheen na Ibn Uthaymeen

Sharrudan da suke halasta wa mutum yayi tafiya zuwa garin kafirai

•Sharadin Farko: ya zamto mutum yana da ilimi da zai iya kawar da shubuhohi da za'a iya bujuro masa dashi, domin kafirai sukan bijuro wa musulmai shubuhohi dabam dabam, Shubuhohi kan Dabi'un musulmai, da koma meye, domin musulmi ya zamto cikin shakka a koda yaushe, ya zamto bashi da Alqibla, kuma abune sananne inhar mutum yayi shakka kan abinda yake wajibi ne a kudurce ta hakika, toh bai kawo wajibin abinda yake akansa ba,Su kafirai kullum suna shigar wa musulmai shakka, wani daga cikin shuwagabanninsu yake cewa:

kada kuyi kokarin fitar da musulmi daga addininsa zuwa addinin kirista, ya isheku idan ku ka sanya masa shakka kan addininsa, domin idan kuka sanya masa shakka kan addininsa toh kun cireshi daga cikin addinin, wannan ya isar.

Wannan sharadi na farko kenan, ya zamto mutum yana da ilmi gwargwado da zai iya mayar da shubuhohin da zai iya fuskanta in yaje can.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

TAKAITACCEN TSOKACI A KAN JAWABIN SHEIK DAHIRU BAUCHI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

TAKAITACCEN TSOKACI A KAN JAWABIN SHEIK DAHIRU BAUCHI

Jawabin da Malam Dahiru Bauchi ya yi a shirin safe na BBC hausa a yau 21/5/2015, hakika ya fadi daidai cikin wani sashi nasa, ya kuma kasa fadin daidai cikin wani sashi nasa.Ya fadi daidai a inda ya kafirta 'yan Tijjaniyyar nan da suka yi bukin maulidin Sheik Ibrahim Inyas a garin Kano, sannan a wajen wannan buki nasa wasunsu suka yi ta furta kalaman batunci ga Annabi Mai tsira da amincin Allah.

Amma bai fadi daidai ba a inda ya ce babu abin da ake kira Ahlul Hakikati cikin Darikar Tijjaniyyah, ya kuma fadi hakan ne duk kuwa da cewa a cikin Darikar tijjaniyyah a kwai yarda da abin da ake kira Wahdatul Wujudi, shi kuwa Wahdatul Wujudi tabbas yana daga cikin lazimin wannan akida yarda da irin maganar cewa Ibrahim Inyas Allah ne.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

'YAN TIJJANIYYAH DA CIN MUTUNCIN ALLAH DA MANZONSA
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

'YAN TIJJANIYYAH DA CIN MUTUNCIN ALLAH DA MANZONSA

Bismillahirrahmanirraheem.

Yau inaso in share din wani sauti ne wanda wasu 'yan tijjaniyyah suka zagi Allah da manzonsa acikinsa, wannan ya faru ne kaman yanda na sami labari awurin wani mauludin inyass. Inda suke nuna cewa shi inyass ya wuce gabar kowa, da dai kalamai munana na shirka da kafirci da fitsaranci.Kaman yanda kowa ya sani ne maluman Ahlussunnah sunyi kokari kuma suna kai wurin wayar da kan al'ummah akan tafarkin sufaye wanda wannan tafarki gurbatacciyace kuma Tana kaiwa ga halaka.

Amma wani lokaci in ana bayanin hakikanin sufanci da abinda ta kunsa sai mutane su rika ganin kaman sharri ake musu, hatta wa'inda suke bin wannan tafarki ta sufancin sai surinka ganin abin karyane tsagoronta sabida su ba'a fada musu ainihin haqiqanin abin ba, su anrudesu ne dason annabi da kuma zikiri da salatin annabi, wanda ahakikanin lamari ba haka abin take ba.

Amma yanzu ansami wanda suka yunkura daga cikin mabiya wannan tafarkin sufanci sukaje suka karanto hakikanin lamarin kuma suka dawo suna bayyana wa mutane gaskiyarta bawai don suka da bayyana aibinta ba, a'a don nuna wa mutane haqiqa subi.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

WANENE YAKAMATA YAFARAYIN SALLAMA.... WANDA YABUGO WAYA KO WANDA AKA BUGAWA??
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

WANENE YAKAMATA YAFARAYIN SALLAMA.... WANDA YABUGO WAYA KO WANDA AKA BUGAWA??

Babban Malamin nan kuma Masanin Ilimin Hadith a Wanna Zamanin Ash-sheikh Al-Allãmah Muhammad Nasiruddeen Albãny Yace :

Acikin Littafin :

Al-aqeedatu Auwalan Lau kãnu ya'almun Mujalladi na 1 Shafi na 16-17.

MALLAM Yace :

Abinda Yakamata ga wanda aka bugawa (waya) shine Idan yadauka Yace : NA'AM..... sai shi wanda yabugo wayar idan yaji andauka sai yafarayin SALLAMA, sai kuma wanda aka bugowa wayar shima Ya amsa sallamar..... Ba wai shi (wanda aka bugawa wayar) ne zai farayin sallamar ba.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

HAKKIN MIJI AKAN MATANSA
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

HAKKIN MIJI AKAN MATANSA

Ya ''yar uwa mai daraja hakika mijinki yana da matsayi mai girma akanki kamar yadda Annabi SAW Yafada saboda haka kiji tsoron Allah SWA acikin zaman takewarki da mijinki.

MANZON ALLAH SAW YACE:-

Da zan umarci wani yayi sujjada ga wani, dana umarci mace tayi sujjada ga mijinta.

《Tirmizi ya rawaito》 MANZON ALLAH SAW YACE:-

Idan miji ya kira matarsa zuwa ga shimfidarsa amma bata zoba, mala'iku suna tsinemata har saita tafi.

《Bukhari da muslim 》 MANZON ALLAH SAW YACE:-

Wace macece ta mutu mijinta na mai yarda da ita, zata shiga aljanna.

《Abu daud da tirmizi》 MANZON ALLAH SAW YACE:-

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

AL KITAB WAL ''ITRA'' KO AL KITAB ''WAS SUNNAH
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

AL KITAB WAL ''ITRA'' KO AL KITAB ''WAS SUNNAH''? 4

Riwayoyin Hadisin ''ITRA'' Ruwaya ta Farko:

Ruwayar sayyidina Abu Huraira Radiyallahu Anhu wadda Imam Al Baihaki ya zo da ita a cikin SUNAN AL KUBRA (10/144), Hadisi na 20124 da Imam Al Bazzar a cikin MUSNAD (2/479), Hadisi na 8993.

Ga nassin Hadisin Abu Huraira:

''ﺍﻧﻲ ﻗﺪ ﺧﻠﻔﺖ ﻓﻴﻜﻢ ﺍﺛﻨﻴﻦ ﻟﻦ ﺗﻀﻠﻮﺍ ﺑﻌﺪﻫﻤﺎ ﺃﺑﺪﺍ :

ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻨﺘﻲ، ﻭﻟﻦ ﻳﺘﻔﺮﻗﺎ ﺣﺘﻰ ﻳﺮﺩﺍ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﺤﻮﺽ ''.

Fassara:

''Hakika na bar maku ababe biyu da ba zaku bace ba idan kun yi riko da su KITABULLAHI WA SUNNATI. Kuma ba zasu taba rabuwa da juna ba har su same ni a tafki (Al Kauthar).

Ruwaya ta Biyu:

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

AL KITABU WAL ''ITRA'' KO ALKITABU ''WAS SUNNAH
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

AL KITABU WAL ''ITRA'' KO ALKITABU ''WAS SUNNAH'' 3

Bari mu soma magana kan Hadisin da muke nufi:

Wannan Hadisi ya zo ta hanyar sahabbai da dama. Dukansu suna cikin wadanda 'yan Shi'ah suka jingina ma ridda bayan wafatin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam.

Kamar su Abu Huraira da Zaid bin Arqam da Jabir bin Abdillah da Amr bin Auf da Abu Sa'id Al Khudri. Amma kuma suna azzama Hadisin kwarai da gaske da ruwaya guda daya daga cikin ruwayoyinsa wadda suke ganin ta karfafi akidarsu. Haka kuma sukan hautsina ruwayoyin hadisin don su fitar da wacce suke bukata.

Zamu tattauna kan wannan Hadisi – cikin yardar Allah – ta fuska uku:

Fuska ta farko ita ce, hanyoyin da aka samo Hadisin da su. Domin abinda bakin malamai ya hadu a kansa ne cewa, Hadisi ba ya zama hujja a addinin Allah, har a iya jingina shi ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam sai an amince da hanyar da aka samo shi. Ma'ana sai maruwaitansa sun zamo masu sheda ta kwarai daga bakunan wadanda suka san su, suka yi hulda ta ilimi da su. Wannan ma shi ya sa aka kai matsaya kan amsar hadisan sahabbai baki daya ba tare da wariya ba. Tunda yake muna neman wanda muka amince ma ne, sai muka sami su Allah ya ce ya amince masu. Mun kuwa sani wannan maganar ba karama ba ce, kuma Allah Ta'ala da ya yi ta ya san abinda take nufi, kuma bai taba warware ta ba.

Saboda haka Ahlussunnah sun wadatu da shedar mahaliccinmu a kan su.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

AL KITABU WAL ''ITRA'' KO AL KITABU WAS ''SUNNAH&#
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

DR MANSUR SOKOTO

AL KITABU WAL ''ITRA'' KO AL KITABU WAS ''SUNNAH''? 2

kashi na Uku shi ne hadisan da malamanmu suka yi sabani a kan ingancinsu ko rauninsu.

Ka'idarmu a nan ita ce hujja, ba Malam wane ya fada ba. Amma da zaran an samu haka sai su yi fararat su ce, ai Malaminku wane ya inganta shi. Daga nan sai su gina abinda shi malamin da an tambaye shi zai ce ba haka ne ba.

Idan mun zo fitar da Hadisin ''ITRA'' zamu ga wannan baro baro.

Kashi na Hudu shi ne hadisan da suke sukar mu a kansu, alhalin yadda suke a littafanmu haka suke a nasu. Kamar Hadisin fitsari a tsaye, da yawa sukan zage mu a kansa, su ce bamu san girman Manzon Allah ba, alhalin Hadisin yana a cikin littafansu su ma! Da kuma Hadisin cewa, ba a gadon Annabawa. A kullum sai ka ji suna zagin sayyidina Abubakar a kansa suna cewa ya shara ta, alhalin Majilisi da wasu Malamansu sun kawo shi ta nasu hanyoyi kuma sun inganta shi.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

AL KITABU WAL ''ITRA'' KO AL KITABU WAS ''SUNNAH&#
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

DR MANSUR SOKOTO

AL KITABU WAL ''ITRA'' KO AL KITABU WAS ''SUNNAH''?

Bismillahir Rahmanir Rahim Abinda muka sani ne cewa, daga cikin manyan ginshikan Shi'a da suka dogara gare su kuma suka gina akidarsu a kai shi ne, cewa Annabinmu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya yi wasici da abi Alkurani da ''ITRA'' wato iyalan gidansa. Sa'annan kuma sai suka dauka cewa, bin jikokin sayyidina Husaini shi ake nufi domin su ne magadan ilimin annabta. (mutum tara ne daga cikin zuri'ar Husaini suka sa a cikin imamansu goma sha biyu amma babu na Hasan ko guda!). A kan wannan fahimta tasu sun hakikance cewa an saba ma umurnin Manzon Allah tun da farko, don haka tafiya ta gurbace tun daga asalinta, musulmin farko – almajiran Annabi da masu bi masu – duk sun bar tafarkin shiriya, a fahimtar 'yan Shi'ah.

Muna so mu tattauna a tsanake dangane da wannan Hadisi da ruwayoyinsa, domin mu gano ingancinsa ko rashin haka. Sannan mu yi tsokaci game da ma'anarsa wadda ta yi daidai da abinda aka sani na koyarwar ma'aiki Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam.

Kafin mu shiga wannan bayani, zai yi kyau muyi nuni ga matsalar da take shiga a cikin rubuce-rubucen malaman Shi'a idan suka zo magana a kan hadisai. Wannan bayani a hakikaninsa na masanan Hadisi ne, yana yiwuwa ya dan yi nauyi ga wasu daga cikin masu karatu.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

ARBA'UNA HAADITH (36) HADISI NA TALATIN DA SHIDA
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

ARBA'UNA HAADITH (36) HADISI NA TALATIN DA SHIDA

An karbo daga Abu hurairata (R.A) daga Annabi yace, wanda duk yakutar wa mumini wani bakin ciki daga bakin cikin duniya to Allah zai kautar da masa da wani bakin ciki daga bakin cikin irin bakin kiyama duk wanda ya kawo sauki ga wanda yake cikin tsanani, Allah zai kawo masa sauki a duniya da lahira, wanda ya suturce musulmi to Allah zai yi masa sutura a duniya d alahira lallai Allah yana cikin taimakon bawa matukar bawan ya kasance mai taimakon dan uwansa musulmi wanda duk ya kam wani tafarki yana neman ilmi a wannan tafarkin Allah zai saukaka masa hanyar shiga aljanna babu wasu mutane da zasu taru a cikin wani daki cikin dakunan Allah sun karanta littafin Allah, sun darasinsa a tsakaninsu da juna, face sai nutsuwa ta sauka kansu, rahama ta lullube su, (mala'iku sun kewaye su) sai kuma Allah ya ambace su fadarsa. Wanda duk aikinsa ya yi sanda da shi, to dangatakarsa ba zai ta yi gaggawa ba zatayi gaggawa da shi ba.

Muslim ne rawaito shi (2699) da wanan lafazi.

SHARHI; Manzon Allah yace, wanda duk ya kautar wa mumini wani bakin ciki daga dangin wani bakin ciki da ke iya samun mutu ma duniya to Allah zai kautar masa da wani bakin cikin daga cikin bakin cikin da kan iya riskar bawa a gobe kiyama misali wni mutum mumini yana fama da matsala ta rayuwa sai ka taimaka masa ka yaye masa wannan bakin cikin ; an rubuta masa magani a asibiti bashi da kudin da zai saya sai kaje ka sayo ka bashi, an bashi notis a gidan haya sai kazo ka bashi kudin da ake binsa ka kara masa kudin ko aka sallame shi daga gidan haya, sai kazo ka bashi kudin da ake binsa ka kara masa kudin hayar na wata hudu a kai masu zuwa. Duk wanda yayi wannan Allah zai yaye masa wani bakin ciki daga cikin bakin cikin dangin bakin cikin da ke iya samun mutum a ranar tashi kiyama.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji

ARBA'UNA HAADITH (35) HADISI NA TALATIN DA BIYAR
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

ARBA'UNA HAADITH (35) HADISI NA TALATIN DA BIYAR

An karbo daga Abu Hurairata (R.A) y ace Manzon Allah Annabi (S.A.W). y ace ''Kada ku rika yi wa juna hassada, kada ku yi kore kada ku kiyayya da juna, kada ku juya wa juna bayanku, kada sashenku ya yi ciniki a cikin cinikin dan uwansa. Ku kasance bayin Allah 'yan uwan juna. Muslim dan uwan muslim ne, kada ya zalunce shi, kada ya kuntatar da shi, kada ka yi masa karya, kada ya wulakantar da shi. Tsoron Allah yana nan (har sau uku).!! Yana nuna kirjinsa,'' Ya ishi mutum sharri, ya rika tozartar dad an uwansa musulmi. Jinin kowanne musulmi da dukiyarsa da mutuncinsa, haramun ne a kan musulmi.(1) Muslim ne ya rawaito shi (# 2564).

SHARHI; Abin da ake nufi da hassada shi ne ka rika burin ina ma ni'imar da wane yake cikinta taho ta barshi ina ma dukiyar wane ta ragu jarinsa ya lalace ka rinka jin ina ma mukamin da ka baiwa wane yazo ya rasa to wannan itace hassad kuma siffa ce ta yahudu sun fi kowa sanin Annabi da siffofinsa amma hassada ta hana su yin imani dashi don haka, kayi kokarin ka wanke zuciyarka daga yi wa dan'uwanka musulmi hassada. Ko da mutum yana kokarin yin takara da kai kan wasu al'amura na duniya kai kar kayi takara dashi lallai mutum ya kasance ya tarbiyatar da kansa da haka.

(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: