Muhawara Hausa
 

 
EsinIslam Media: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

Bincike Akan Wannan Batun:   
[ Jeka Gidan Dandalin Watsa Labarai | Zaɓi Sabon Taken ]

Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

Sabuwar Shekarar 1439 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi (2)
(Labarin Cikakkun... | 6369 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Sabuwar Shekarar 1439 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi (2)

Bayyanar Musulunci ke da wuya sai watanni masu alfarma suka koma kamar yadda suke a farkon halitta inda Allah Madaukakin Sarki Ya haramta wannan al'ada ta jinkirtawar cikin fadinSa: "Lallai ne kidayayyun watanni a wurin Allah wata goma sha biyu ne a cikin Littafin Allah a ranar da Ya halicci sammai da kasa daga cikinsu akwai hudu masu alfarma. Wannan shi ne addini madaidaici. Saboda haka kada ku zalunci kanku a cikinsu. Kuma ku yaki mushirikai gaba daya kamar yadda suke yakar ku gaba daya. Kuma ku sani cewa lallai ne Allah Yana tare da masu takawa. Abin sanni kawai "Jinkirtawa" kari ne a cikin kafirci ana batar da wadanda suka kafirta game da shi: suna halattar da wata a wata shekara kuma su haramta da shi a wata shekarar domin su dace da adadin abin da Allah Ya haramta. Saboda haka suna halattar da abin da Allah Ya haramtar. An kawace musu munanan ayyukansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai." (k:36-37).

Kuma Ma'aiki (SAW) a Hajjinsa na Ban-Kwana ya ce, "Ku saurara! Lallai zamani ya juyo kamar yadda Allah Ya tsara shi a ranar da Ya halicci sammai da kasa,(1) shekara wata goma sha biyu ne; hudu daga cikinsu masu alfarma ne. Uku suna jere – Zul-kida da Zul Hajji da Muharram; na hudun shi ne Rajab na Mudar, wanda yake zuwa a tsakanin Jimada Akhir da Sha'aban." Wato yana nufin cewa sunayen watanni sun komo kamar yadda suke a farkon halitta, kafin al'adu su shigo su jirkita su. Kuma ga shi an haramta amfani da al'adar nan ta jinkirtar wani wata don ya fada wata shekara bayan tsawon zamani da aka share ana yi a matsayin abin da mutane suka yi imani da shi tare da mayar da shi addini kaka da kakanni.

Yadda aka fara kidayar shekarar Musulunci:


(Labarin Cikakkun... | 6369 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

Sabuwar Shekarar 1409 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi
(Labarin Cikakkun... | 8405 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Sabuwar Shekarar 1409 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi

Godiya da yabo da tsarkakewa sun tabbata ga Allah wanda Ya sanya dare da wuni su kasance ma'aunan gane lokuta. Kuma Ya sanya su domin gane kwanaki da shekaru da kuma lissafi.

Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa wanda aiko shi ya zama salsalar fitar da mutane daga duffan zalunci da shirka da tabewa zuwa ga hasken adalci da imani da shiriya.

A yau Juma'a ce muka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1409 Bayan Hijirar Annabi (SAW), kuma muna fata Allah Ya yi mana dandazon alheri a cikinta. Kuma Ya raba mu da sharri da bala'in da duk wata cutarwa da suke cikinta.

Bayan haka, hakika mafi yawan Musulmin Najeriya, suna gafala daga al'amarin sabuwar shekarar Musulunci, sun fi sanin watanni da kidayar shekarar Nasara wadanda ka gina su kan kalandar Gregory. Wannan ya sa da yawan Musulmi ba su ma sanin yaushe shekarar Musulunci ke shigowa ba, wani ma ba ya sanin kwanan watan Musulunci nawa ne sai lokacin azumi ko Sallah. Musulmi da dama a yau da za a tsare su a ce su lissafa watannin Musulunci sai dai su shiga kame­kame, ba su san su ba, kuma ba su nufin su sani!


(Labarin Cikakkun... | 8405 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

Me Ya Sa Yan Shi'a Suke Kin Banu Umayya?! -Dr Mansur Sokoto
(Labarin Cikakkun... | 3794 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Dr Mansur Sokoto

Me Ya Sa Yan Shi'a Suke Kin Banu Umayya?! -Dr Mansur Sokoto

Me ya sa Yan Shi'a suke kin Banu Umayya?!

Daga SHEIKH DR MANSUR IBRAHIM SOKOTO
(Rubutun Babban Masanin Tarihi, Dr. Ali as-Sallabiy).

Ibnu Kathir (r) yana cewa:

''Kabilar Banu Umayya sun ci kasuwar Jihadi; ba su da abin yi sai shi. Sun kaskantar da kafirci da kafirai. Kwarjinin Musulmi ya cika zukatan kafirai. Ba sakon da Musulmi su ka sa a gaba face sun ci shi da yaki.''

Ba a san wata Kabila da ta yi mulki ta yi wa mutane abin da Kabilar Banu Umayya (r) ta yi musu ba. Banu Umayya suna da falala a kan al'ummar Musulmi tun kafuwar Musulunci har zuwa ranar al-kiyama.

* Uthman dan Affan dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne ya tattara al-Kur'ani.


(Labarin Cikakkun... | 3794 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

**WA YA KASHE HUSSAIN?**(8)
(Labarin Cikakkun... | 4296 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Adam Sani Abu Umayrah

**WA YA KASHE HUSSAIN?**(8)

Assalamu alaikum! Yan'uwa a rubutuna da ya gabata, na soma kawo maganganun Ahlul-Baiti kai tsaye daga Littafan shi'a, wadanda ke tabbatar da kasantuwar Shi'ar Imam Ali da Hassan sune makasan Hussain,

zan ci gaba ayau insha-Allah!

*Ummu Kulsum Bnt Aliy r.a Yar'uwar Hussain r.a tana cewa:

'Yaku Mutanen Kufah Tir daku! Meyasa kuka wulaqanta Hussain kuka kasheshi, kuka turmusa dukiyarsa kuka gajeta, kuka kama matansa, kuka wulaqantashi, tir daku Allah wadaranku, wace ruduce ta rudeku, kuma wani irin zunubine a bayanku kuka dauka? Wani jinine kuka zubar?

(Al-Malhuf:91, Nafsul Mahmum: 363).


(Labarin Cikakkun... | 4296 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

IBN TAIMIYYAH GWARZON NAMIJI. (Misbahu Abdullahi)
(Labarin Cikakkun... | 2927 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

IBN TAIMIYYAH GWARZON NAMIJI. (Misbahu Abdullahi)

Shaikul islam Ahmad bn Abdulhalim ibn Taimiyyah Alharrany Addimashky ya rayu akarshen karni na bakwai zuwa farkon karni na takwas, ana kiran wannan lokaci da USURUL WUSDA. Shaihin musulunci ya taka mahimmiyar rawa aduniyar ta'alify, yai rubutu akan sufanci, yai akan kiristanci,yai akan shi'anci dsrns a janibin firak da sauran bangarori, malam ya gadarwa duniyar ilmi rubututtuka masu tarin yawa wanda bazai gusheba yana samun ladan wannan aikin Insha'allah har Allah yanade kasa, shaihi bai bar wata shubha ta ya'n bid'ah ko ya'n shi'ah ko wasunsu face saida yai kokarin byn kanta, har saida takai ya'n bid'ah da ya'n shi'ah na shakkar yatashi byni kansu suka shiga halin tsoro da firgici, ta kai sunansa aka ambata sai gabansu yafadi. Malam ya amsa sunan dodon ya'n bid'ah, har yazama babu mai adawa dashi sai dayan biyu: 1. Jahili:shikuma baisan wane shiba dole yai adawa dashi.
2.mai son xuciya: shikuma son xuciyarsa baxai barshi yabi gaskiyaba

SHIN KO KASAN HADARIN RAYUWA??

HADARIN RAYUWA;
Mu dauki ka shekara 60 a duniya!


(Labarin Cikakkun... | 2927 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

Halin Musulmi Na kwarai Ranar Ashura, Da Halin Masu Bi'ah
(Labarin Cikakkun... | 1874 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Halin Musulmi Na kwarai Ranar Ashura, Da Halin Masu Bi'ah

Abune sananne cewa musulmai sun rarrabu kashi kashi, Wasu sun dauki tafarkin Annabi(Salllahu alaihi wasallam) abin binsu, wasu kuma sun dauki Tafarkin waninsa a matsayin tafarkin da suke bi, haka abin yake acikin lamura masu yawa na addini, daga ciki akwai wannan rana ta Ashura aciki, zamuyi bayani a takaice kan halin musulmi na kwarai acikin wannan rana, da kuma halin Masu tsaba wa Annabi(Sallallahu alaihi wasallam)

Halin 'yan Addinin shi'ah a ranar Ashura: Su 'yan shi'ah sun dauki wannan rana a matsayin rana ce ta bakin ciki domin itace ranar da aka kashe jikan manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) ''Alhussein'' sukan fita acikin wannan rana cikin bakaken kaya, Suna yanka jikkunansu suna kuka suna fadiwa a kasa, saboda nuna bakin ciki, kuma sun dauki wannan a matsayin Addini, Wanda Hakan bashi da tushe a addinin musulunci, Kuma hakan yana nuna jahilci karara ta yadda suke mancewa da cewa Ali(Radiyallahu anhu) shima Shahada yayi, amma sai suka barsa basu mishi irin wannan makoki, duk da cewa Ali(Radiyallahuanhu) yafi Hussein Daraja.


(Labarin Cikakkun... | 1874 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

AA'SHUURAA (1) BANDA BIDI'AR SHI'AH BANDA KUMA BIDI'AR NAASI
(Labarin Cikakkun... | 17924 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Daga Dr. Ibrahim Jalo Jalingo 

AA'SHUURAA (1) BANDA BIDI'AR SHI'AH BANDA KUMA BIDI'AR NAASIBAH A RANAR AA'SHUURAA

Kamar yadda yake rubuce cikin calendar Ummul Quraa Talata mai zuwa ita ce goma ga watan Muharram (10/1/1438 H ) wanda ya yi daidai da 11 ga watan Octorber Tashreen na farko (11/10/2016 M). Wannan yini na goma ga Muharram shi ne yinin Aa'shuu'raa, yinin da yin azumi a cikinsa yake Sunnah ta Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah.

Kuma dai har yanzu a dai wannan yini na Aa'shuu'raa ne Allah Madaukakin Sarki Ya girmama Sayyidina Husaini Dan Sayyidina Aliyyu Bin Abii Taalib -Allah Ya kara musu yarda tare da dukkan Sahabbai- da yin shahada a cikinsa a shekarar hijira ta settin da daya; domin shahadar tasa ta kasance wani abu da Allah Madaukakin Sarki Ya kara daukaka darajarsa da shi.

IYA YAWAN DARAJARKA IYA GIRMAN MUSIBAR DA ZA TA SAME KA

Imamut Tirmizii ya ruwaito hadithi na 2,398 da isnadi sahihi daga Sa'ad Dan Abi Waqqas cewa ya ce: Ya Manzon Allah! Wane ne daga cikin mutane masifa ta fi auka masa? Sai ya ce: ((Annabawa ne, sai kuma wanda ya fi daraja, sai kuma wanda yake biye a daraja, a kan jarrabi mutum ne a bisa gwargwadon addininsa, idan addininsa mai karfi ne sai bala'insa ya zamanto mai karfi, idan addininsa laga-laga ne, sai a jarrabe shi gwargwadon addininsa, bala'i ba zai gushe ba yana ta samun bawa, har sai ya ga cewa yana tafiya bayan kasa ba tare da wani zunubi ba)).


(Labarin Cikakkun... | 17924 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB
(Labarin Cikakkun... | 15776 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB NE SHI KO KUWA WANINSA II

1. Lalle kafirta sayyidina Abubakar da sayyidina Umar da mafi yawan Sahabbai yana daga cikin manyan aqidun Shi'awa, hakan yana rubuce cikin lattattafansu na da, da na yanzu, suna kuma fadin shi da bakunansu a duk lokacin da suka sami damar hakan, babban malaminsu mai suna Muhammadul Khulainiy ya ruwaito cikin littafinsa Al-Kafiy 8/125 daga Musal Kaazim cewa an tambaye shi game da Abubakar da Umar, sai ya ce: ((Su kafurai ne, la'anar Allah da Mala'iku da Mutane gaba daya su tabbata a kansu.

Wallahi babu wani abu na imani da ya shiga zuciyarsu, sun kasance wasu mayaudara ne, masu kokonto, munafukai ne har dai mala'ikun azaba suka dauki rayukansu zuwa bigiren kaskanci cikin gidan Zama)). Intaha.Har yau Khulainiy ya sake ruwaitowa cikin Raudah cikin littafin Kaafiy riwaya ta 341 daga Abu Ja'afar ya ce: ((Mutane sun kasance masu ridda bayan Annabi in banda mutum uku, sai na ce: wadanne ne ukun? Sai ya ce: Miqdad Bin Aswad, da Abu Zarr Al-Gifaariy, da Salmanul Faarisiy rahamar Allah da albarkarsa su tabbata a gare su)). Intaha.

Haka nan Zainud Dinin Nabaatiy ya ce cikin littafinsa mai suna As-Siraatul Mustaqeem Ila Mustahiqqit Taqdeem 3/921 ((Umar Bin Khattab ya kasance wani kafiri ne da yake boye kafirci ya kuma bayyana Musulunci)). Intaha. Haka nan Muhammad Nabiy Bin Ahmad At-Tuwaisirkaaniy ya ce cikin littafinsa mai suna La'aali'il Akhbari wal A'athar 4/29 ((Ka sani, mafi darajar gurare da lokuta da halaye, kuma wadanda suka fi dacewa a la'ance su a cikinsu -Allah Ya tsine musu- su ne a lokacin da ka kasance a inda ake fitsari sai ka ce a duk lokacin fitar najasa da kuma tsarki, ka rika maimaitawa a lokacin gama fitsarin:

Ya Allah Ka la'anci Umar, sannan Abubakar da Umar, sannan Uthman, da Umar, sannan Mu'awiyah, da Umar, sannan Yazidu, da Umar, sannan Ibnu Sa'ad, da Umar. Ya Allah Ka la'anci A'isha, da Hafsah, da Hindu, da Ummul Hakam. Ka la'anci duk wanda ya yarda da ayyukansu har zuwa ranar Kiyama)). Intaha.


(Labarin Cikakkun... | 15776 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB
(Labarin Cikakkun... | 10702 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB NE SHI KO KUWA WANINSA: (I)

1. Ya kamata a san cewa aqidar Ahlus Sunnah wal Jama'ah ita ce: Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib -Allah Ya kara masa yarda- Sahabi ne babba mai yawan daraja. A kuma san cewa abin da ake nufi da Sahabi shi ne: wanda ya samu haduwa da Annabi mai tsira da amincin Allah alhalin yana mumini kuma ya mutu yana mai imani. A kuma san cewa abin da ake nufi da munafuki shi ne: mutumin da ya bayyanar da Musulunci da nuna biyayya ga manzon Allah mai tsira da amincin Allah amma kuma yake boye kafurci cikin zuciyarsa. A kuma san cewa yana daga cikin aqidar Ahlus Sunnah wal Jama'ah nuna kauna da soyayya ga dukkan sahabban manzon Allah mai tsira da amincin Allah; saboda su ne suka fi kowa cikar imani da ihsani, suka fi kowa yawan da'ah da jihadi, Allah kuma Ya zabe su da abokantakar annabinSa mai tsira da amincin Allah, babu kuma wani da zai zo daga bayansu da darajarsa za ta kai tasu. A kuma san cewa su Sahabbai dukkansu adilai ne; saboda irin yadda Allah da manzonSa suka bayyanar da adalcinsu, kuma su waliyyan Allah ne zababbu cikin halittarSa, kuma su ne suka fi kowa daraja cikin wannan Al'ummah, babu wani da ya fi su daraja in banda manzon Allah mai tsira da amincin Allah; daga cikin abin da ke tabbatar da wannan magana tamu shi ne fadar Allah Madaukaki cikin suratut Tauba aya ta 100 inda Ya ce:

((Na farko wadanda suka tsere wa kowa daga cikin Muhajirai, da Ansarawa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautayi, Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi, kuma Ya yi musu tattalin gidajen Aljannah da korumma ke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har a bada, wannan kuwa shi ne rabo mai girma))


(Labarin Cikakkun... | 10702 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MATSAYIN MUSULMI A WAJEN 'YAN SHI'A - 2
(Labarin Cikakkun... | 7039 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

DR. UMAR LABDO

MATSAYIN MUSULMI A WAJEN 'YAN SHI'A - 2

Babi Na daya Ma'anar Ahalus Sunna A Wajen Rafilawa Mai karatun littafan Shi'a zai lura da wasu sunaye, ko kuma laqabai, da suke kiran Ahalus Sunna da su.

Wadannan lakabai suna cikin littafan malamansu na farko da malamansu na zamani. Ba safai sukan kira su da sunan Ahalus Sunna ba sai nadiran. Sunayen dukkaninsu suna nuna kazafi da vatanci da wulakanci. Zai yi kyau mu fara bayani da wadannan sunaye kafin mu shiga magana a kan ma'anar Ahalus Sunna a wajen Rafilawa.

Sunayen Ahalus Sunna A Wajen 'Yan Shi'a Akwai sunaye guda uku da Rafilawa suke amfani da su don ambaton Ahalus Sunna a cikin littafansu da maganganunsu wadanda suka hada da hudubobinsu da laccocinsu da wa'azozinsu.

Wadannan su ne:

1. Nasibawa. Asalin sunan da Larabci nasib, jam'insa nawasib, watau mai kulla gaba, ko wanda ya kafa kiyayya. Abinda suke nufi gaba da kiyayya ga Ahalul Baiti, musamman Ali binu Abi Dalib da Fadima, Allah ya kara musu yarda, da kuma imamai goma sha biyu daga zuri'arsu.


(Labarin Cikakkun... | 7039 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MATSAYIN MUSULMI A WAJEN 'YAN SHI'A
(Labarin Cikakkun... | 3333 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

DR. UMAR LABDO

MATSAYIN MUSULMI A WAJEN 'YAN SHI'A 

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ 
Gabatarwa Lallai godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, muna neman gafara tasa.

Muna neman tsari da Allah daga sharrin kawunanmu da miyagun ayyukanmu.

Wanda Allah ya shirye shi, babu mai batar da shi kuma wanda ya batar babu mai shiriya tasa. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne, kuma Ma'aikinsa ne. Tsira da aminci su tabbata a gare shi, da Alayensa, da Sahabbansa, da waxanda suka bi Sunnarsa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka, 'yan Shi'a suna yawan yin magana dangane da hadin kan Musulmi. Ba sa barin wata munasaba ta wuce ba tare da sun maimaita kira izuwa hadin kai ba, da sukan rarraba da karkasuwa zuwa kungiyoyi da mazhabobi.

Sau da yawa sukan yi kira da hadin kai tsakaninsu da Ahalus Sunna, suna masu karfafa cewa bai kamata a samu sabani ba domin hakan yana raunana Musulmi a gaban abokan gabansu. A wasu lokuta sukan nuna cewa abubuwan da suka raba su da Ahalus Sunna ba wasu muhimmai ba ne, kuma su da Ahalus Sunna duka abu guda ne tunda Shi'a ita ma mazhaba ce kamar sauran mazhabobi.


(Labarin Cikakkun... | 3333 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

ABUBUWA GUDA BIYAR RAK, WADANDA SUN ISHI MAI NEMAN GASKIYA YA GAMSU YAHUDAWA SUK
(Labarin Cikakkun... | 2102 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

ABUBUWA GUDA BIYAR RAK, WADANDA SUN ISHI MAI NEMAN GASKIYA YA GAMSU YAHUDAWA SUKA KAFA SHI'ANCI

1. A tarihin Musulunci ba a taba SAMUN WATA KASA GUDA DAYA TAK WACCE BA TA MUSULUNCI 'YAN SHI'A SUKA JE SUKA KAI MA TA MUSULUNCI BA, SU KA MUSULUNTAR DA KASAR: koda kuwa irin musuluncin su ne!.

Ai ko a nan Nigeria ma, ba za ka taba ganin dan Shi'a a garin Inugu ko Anambura ko Ikiti ya je musuluntar da wadanda ba musulmai ba, a'a wannan ba AIKIN DAN SHI'A BA NE, aiki ne na Ahlussunnah AIKIN DAN SHI'A SHI NE IDAN MUSULMAI SUN JE WATA KASA SUN MUSULUNTAR DA MUTANEN SHI KUMA YA JE YA BATAR DA SU.

2. Duk manyan MALAMAI MARJI'AI NA SHI'A babu ko daya tak MAHADDACIN KUR'ANI!

saboda Qur'ani bai da kima a addinin shi'a.

Kwanakin baya an kalubalance su aka sa kudi Riyal miliyan Daya (SR1,000,00) a tashar wesal ta Larabci akan su kawo mahaddaci a cikin Marji'an malamansu amma sun kasa, saboda babu ko daya sai dai wadanda suka kware a waka da bada tatsuniya!!!


(Labarin Cikakkun... | 2102 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

ZUMUNCI DA WAJABCIN SADARDA SHI
(Labarin Cikakkun... | 1761 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

ZUMUNCI DA WAJABCIN SADARDA SHI

ALLAH SUBHANAHU WA TA'ALA YACE:- Ku baiwa makusanta hakkinsu da miskinai da matafiyi, kada kuyi almubazzaranci, Almubazzaranci.

《Suratul isra'i》

MANZON ALLAH SAW YACE:- Wanda duk ya kasance yayi imani da Allah SWA da ranar karshe, yasadar da zumuncinsa.

《Muslim》

MANZON ALLAH SAW YACE:- Mai yanke zumunci bazai shiga aljannaba.

《Bukhari da muslim》

MANZON ALLAH SAW YACE:-


(Labarin Cikakkun... | 1761 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

BURIN MANYAN MUTANE DA MA'DAUKAKIYAR HIMMA A RAYUWA
(Labarin Cikakkun... | 5435 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Dr. Mansur Sokoto

BURIN MANYAN MUTANE DA MA'DAUKAKIYAR HIMMA A RAYUWA

Abu Nu'aim ya ruwaito a cikin "Hilya", da Ibnu Asakir a cikin "Tarikh", daga Abdurrahman Ibnu Abiz Zinad, daga babansa ya ce:

ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﺠﺮ ﻣﺼﻌﺐ ﻭﻋﺮﻭﺓ ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ، ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ :

ﺗﻤﻨﻮﺍ، ﻓﻘﺎﻝ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ ﺍﻟﺨﻼﻓﺔ، ﻭﻗﺎﻝ ﻋﺮﻭﺓ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ ﺃﻥ ﻳﺆﺧﺬ ﻋﻨﻲ ﺍﻟﻌﻠﻢ، ﻭﻗﺎﻝ ﻣﺼﻌﺐ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ ﺇﻣﺮﺓ ﺍﻟﻌﺮﺍﻕ، ﻭﺍﻟﺠﻤﻊ ﺑﻴﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺑﻨﺖ ﻃﻠﺤﺔ ﻭﺳﻜﻴﻨﺔ ﺑﻨﺖ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ، ﻭﻗﺎﻝ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ: »ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ ﺍﻟﻤﻐﻔﺮﺓ « ﻗﺎﻝ: ﻓﻨﺎﻟﻮﺍ ﻛﻠﻬﻢ ﻣﺎ ﺗﻤﻨﻮﺍ، ﻭﻟﻌﻞ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻗﺪ ﻏﻔﺮ ﻟﻪ ".


Ya ce:

"Mus'ab da Urwatu da Abdullahi bn Zubair (ra)
(duka su 3 'ya'yan Zubair bn Auwam (ra)
ne), da Abdullahi bn Umar (ra) sun hadu a Hijru Isma'ila (a jikin dakin Ka'aba), sai suka ce: kowa ya fadi burinsa, sai Abdullahi bn Zubair (ra) ya ce:


(Labarin Cikakkun... | 5435 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 17
(Labarin Cikakkun... | 9396 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 17

MEYA FARU A KARBALA? 17 Mu Koma Kan Yazid Nuni ya gabata a can baya zuwa ga irin sabanin mawallafa a game da Yazid. Bisa ga wannan ne mutane suka kasu kashi uku a kan shi. Wasu na zagi har ma da la'antar sa, wasu na yabon sa da gwarzanta shi. Kashi na uku su ne wadanda suka tsaya a tsakani suna neman ayi masa adalci a ajiye shi a matsayin sauran ire- irensa daga cikin sarakunan musulunci masu rauni wadanda suka tafka kurakurai a cikin mulkinsu. A sa su a cikin ayar da madaukakin sarki yake cewa (ﻭﺁﺧﺮﻭﻥ ﺍﻋﺘﺮﻓﻮﺍ ﺑﺬﻧﻮﺑﻬﻢ ﺧﻠﻄﻮﺍ ﻋﻤﻼ ﺻﺎﻟﺤﺎ ﻭﺁﺧﺮ ﺳﻴﺌﺎ ﻋﺴﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻳﺘﻮﺏ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻏﻔﻮﺭ ﺭﺣﻴﻢ ( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ: ١٠٢ ''Kuma wadansu sun yi ikirari da laifukansu, sun gauraya aiki na kwarai da wani maras kyawo, yana yiwuwa Allah ya yi tuba a kan su, lalle Allah Mai yawan gafara ne, mai gamammen jinkai''.

Suratut Taubah: 102 Mu saurari wani daga cikin malamai masu irin wannan matsakaicin ra'ayi, shi ne Imam Abu Abdillahi Adh Dhahabi.

Ga abinda ya ce a cikin tarihin Yazid a littafinsa SIYAR A'LAM AN NUBALA (7/36):

ﻟﻪ ﻋﻠﻰ ﻫﻨﺎﺗﻪ ﺣﺴﻨﺔ ﻭﻫﻲ ﻏﺰﻭ ﺍﻟﻘﺴﻄﻨﻄﻴﻨﻴﺔ، ﻭﻛﺎﻥ ﺍﻣﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺠﻴﺶ، ﻭﻓﻴﻬﻢ ﻣﺜﻞ ﺍﺑﻲ ﺍﻳﻮﺏ ﺍﻻﻧﺼﺎﺭﻱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ.... ﺍﻟﻰ ﺍﻥ ﻗﺎﻝ :

ﻭﻳﺰﻳﺪ ﻣﻤﻦ ﻻ ﻧﺴﺒﻪ ﻭﻻ ﻧﺤﺒﻪ، ﻭﻟﻪ ﻧﻈﺮﺍﺀ ﻣﻦ ﺧﻠﻔﺎﺀ ﺍﻟﺪﻭﻟﺘﻴﻦ، ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻓﻲ ﻣﻠﻮﻙ ﺍﻟﻨﻮﺍﺣﻲ، ﺑﻞ ﻓﻴﻬﻢ ﻣﻦ ﻫﻮ ﺷﺮ ﻣﻨﻪ ..

Tare da tubatubansa yana da alheri guda daya, shine yakar Qustantiniyah. Kuma shi ya jagoranci yakin, alhali a cikin rundunar akwai manya irin su Abu Ayyub Al Ansari mai masaukin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam.. Har dai inda Dhahabi ya kai ga cewa, ''Yazidu na cikin wadanda ba ma zagin su, ba ma kuma kaunar su. An yi ire-irensa da dama daga cikin halifofin daulolin guda biyu (yana nufin Umawiyyawa da Abbasiyyawa), haka ma a cikin gwamnoni an yi ire-irensa da ma wadanda shi ya dara su dama.


(Labarin Cikakkun... | 9396 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 16
(Labarin Cikakkun... | 5215 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 16

MEYA FARU A KARBALA? 16 Matsayin Malaman Sunnah a kan Wadannan Fitinu Game da tawayen mutanen Madina malamai magada Annabawa ba su ja bakinsu ba suka yi shiru.

Sun bayyana ma mutane abinda Allah ya wajabta na da'ar shugaba ko da fasiki ne.

Maslahar da ke cikin wannan ita ce, kauce ma abinda zai zubar da jinainan jama'a da kawo tashin hankalin da ba a san karshe ko iyakarsa ba. Littafan Sunnah na hadisi da na Akida a cike suke da wadannan hadisan. Sheikh Abdus Salam Bin Barjis ya tattara su tare da maganganun magabata a cikin littafinsa MU'AMALATUL HUKKAM FI DAU'IL KITAB WAS SUNNAH, bugun Riyadh 1415H.

Misalai biyu kawai zamu kawo don bayyana matsayin malaman Sunnah a wancan lokaci.

1. Matsayin Abdullahi bin Umar:

Kamar yadda muka gani a baya, Abdullahi bin Umar Radiyallahu Anhuma na daga cikin wadanda ba su yi na'am da nadin Yazidu ba.


(Labarin Cikakkun... | 5215 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 15
(Labarin Cikakkun... | 4419 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 15

ME YA FARU A KARBALA? 15 Mutuwar Sarki Yazid Ga dukkan alamu Yazidu ya bar duniya da juyayin abu guda daya da yake fargaban gamuwa da Allah a kan sa. Wannan lamarin kuwa shine kisan Husaini da danginsa. An fadi cewa, karshen kalaman da ya furta a duniya su ne:

''Ya Allah! kada ka rike ni da abinda ban so ba kuma ban bada umurni ba. Ya Allah! Kayi hukunci a tsakani na da Ibnu Ziyad – yana nufin gwamnansa na Kufa wanda ya sa aka kashe Husain. Yazid ya rasu a ranar 14 ga Rabi' Awwal na shekarar 64H. Duka duka mulkinsa bai cika shekaru hudu ba amma al'ummar musulmi ta samu ja da baya matuka daga karfinta da kwarjininta a cikin wannan bakin lokaci.

Rundunar Husain bin Numair wacce take tsare da Ibnuz Zubair da jama'arsa suna dako a wajen Makka ba su samu labarin mutuwar Yazid ba sai bayan sati uku cur. Abu kadan ya rage wannan runduna ta hada kai da Ibnuz Zubair bayan sun samu wannan labari. Amma abinda ya kawo cikas shi Bin Numair ya nemi ya dora hannunsa a kan na Ibnuz Zubair ya yi masa mubaya'a da sharadin a yafe duk jinainan da suka gudana a baya. Ya ce kuma idan an yi haka na lamunce ma kasar Sham gaba daya zan sa su yi maka mubaya'a. Shi kuma sai ya ki karbar wannan sharadi. A nan ne Bin Numair ya juya yana nadama, ya ce, ''Dubi yadda nake kiran sa zuwa sarauta yana neman ci gaba da fitina''. Ashe dai Allah bai kaddare shi da zama sarki ba. A can kuma birnin Dimashka ta Sham an sha takaddama sosai a kan wa za a nada bayan Yazidu tun da shi bai bar wani wasici a kai ba.


(Labarin Cikakkun... | 4419 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 14
(Labarin Cikakkun... | 4877 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 14

ME YA FARU A KARBALA? 14 Me ya biyo bayan kashe Husaini?

Bayan da mutanen Kufa suka ga abinda ya faru a ranar Ashura sai suka hakikance sun ci amanar sayyidina Husaini tun da su suka gayyato shi amma kuma suka tozarta shi. Sun fito da shi daga amintaccen gari kuma sun yi biris da zuwansa har mai aukuwa ta auku. To, sannan ne fa suka fara tunanin yadda zasu kankare ma kansu wannan laifi. A nan ne wata kungiya ta bayyana mai suna ''Jaishut Tawwabin'' rundunar masu tuba.

Babbar manufar wannan kungiya tasu ita ce yin gangami don fada da gwamnatin Banu Umayyah da ta zama gwamnatin 'yan ta'adda wadda ba ta kiyaye alfarmar jinin gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ba. Manufa ta biyu ita ce daukar fansar jinin 'ya'yan gidan Manzon Allah da aka kashe. To, sai dai wannan fargar jaji da 'yan Shi'ah suka yi ba ta yi wani tasiri na azo a gani ba. A maimakon haka sai ta ida dagula lamurra, ta kara auka al'ummar musulmi cikin rikici. Duk abinda 'ya'yan wannan kungiya ta 'yan tuba suka yi bai wuce kamfe ne da furofaganda ba ta batunci ga gwamnatin Yazid da kokarin wanke hannun 'yan Shi'ah daga wannan ta'asa. A cikin wannan kungiyar ne aka samu wani dan ta'adda mai suna Mukhtar bin Abi Ubaid Ath Thaqafi wanda ya lashi takobin sai ya ga bayan duk masu hannu ga kisan Husaini.


(Labarin Cikakkun... | 4877 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 13
(Labarin Cikakkun... | 5291 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 13

ME YA FARU A KARBALA? 13 Labarin Kisan Husaini Ya Game Duniya Da sauri kuma ba da bata lokaci ba wannan mugun labari ya game duniya. Ana mamaki ya aka yi musulmi mai neman ceton Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya iya kashe jikansa, farin cikin rayuwarsa?! Wannan labari ya mantar da musulmi sauran musibu da fitinun da suka gabata. Daman an ce, ba a jin warin bera in ana babbakar giwa.

A hedikwatar halifanci Sham, Yazidu ya samu wannan labari mai ban mamaki. Sai dai kamar yadda muka fadi a baya, ruwayoyi sun sha banban game da irin tarbon da Yazidu ya yi ma wannan labari.

Riwayoyi mafi kusa da gaskiya sune wadanda suka ce, Yazidu ya firgita da jin wannan labari, ya yi taslima.

Sannan ya yi rantsuwa shi bai ce a kashe Husaini ba, kuma bai ji dadin kisan ba. Ya la'anci gwamnansa Ubaidullahi, ya ce bai kiyaye alfarmar Manzon Allah ba.

Wannan magana ba a cikin littattafan Sunnah kawai ba har a cikin na Shi'ah akwai ta. Misali, a cikin KITABUL IHTIJAJ na Tabarsi cewa ya yi:


(Labarin Cikakkun... | 5291 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 12
(Labarin Cikakkun... | 8223 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 12

ME YA FARU A KARBALA? 12 Wa ya kashe sayyidina HUSAINI?

Bayan duk bayanin da ya gabata na abinda ya faru, muna son amsa wannan tambaya. WA YA KASHE SAYYIDINA HUSAINI? Amma a wannan karon littafan Shi'ah kadai muke son su bada amsa.

1. Ga abinda Allamah As Sayyid Muhsin Al Amin ya fada a cikin A'yanus Shi'ah (1/34):

ﺑﺎﻳﻊ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻋﺸﺮﻭﻥ ﺃﻟﻔﺎ ﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻌﺮﺍﻕ، ﻏﺪﺭﻭﺍ ﺑﻪ ﻭﺧﺮﺟﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺑﻴﻌﺘﻪ ﻓﻲ ﺃﻋﻨﺎﻗﻬﻢ ﻭﻗﺘﻠﻮﻩ '''Mutane 20,000 daga 'yan Iraqi sun yi ma Husaini mubaya'a, sun YAUDARE shi kuma suka fito a kansa, alhali mubaya'arsa na ga wuyansu, kuma suka kashe shi''.

2. Ga kuma abinda Hurru bin Yazid – daya daga cikin 'yan rakiyar Husain -ya ce ma rundunar da take kokarin kashe HUSAINI a Karbala:

ﺍﺩﻋﻮﺗﻢ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ، ﺣﺘﻰ ﺍﺫﺍ ﺟﺎﺀﻛﻢ ﺍﺳﻠﻤﺘﻤﻮﻩ، ﺛﻢ ﻋﺪﻭﺗﻢ ﻋﻠﻴﻪ ﻟﺘﻘﺘﻠﻮﻩ، ﻓﺼﺎﺭ ﻛﺎﻻﺳﻴﺮ ﻓﻲ ﺃﻳﺪﻳﻜﻢ؟ ﻻ ﺳﻘﺎﻛﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻈﻤﺎ .


(Labarin Cikakkun... | 8223 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 11
(Labarin Cikakkun... | 4515 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR. MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 11

ME YA FARU A KARBALA? 11 Husaini Ya Isa Karbala Da sayyadi Husaini ya kusa isa Kufa sai ya gamu da Umar bin Sa'ad dauke da sakon kaninsa Muslim wanda sai yanzu ne ya san cewa an kashe shi. Muslim ya nemi Husaini da ya koma abinsa tunda mutanen Kufa ba da gaske suke ba. Shi dai Umar bin Sa'ad daman yana cikin 'yan Shi'ar Ali kamar yadda shi ma wannan sabon gwamna Ubaidullahi bin Ziyad yake. Duba KITABUR RIJAL na TUSI Shafi na 54 don haka Bin Sa'ad sai ya bada labarin kashe Muslim yana kuka ta yadda ya zaburar da 'yan uwansa, ya kuma ja hankalinsu ga daukar fansa. Husaini ya so ya komawarsa amma sauran dangi na ganin dole ne a isa Kufa zuwa daukar fansar jinin dan uwansu.

Duk mai hankali zai iya lura da hannun kaddara a cikin wannan lamari.

Domin kuwa ya za a iya daukar fansar wanda hukuma ta kashe shi?

Kuma a kan wa za a dauki fansa? Sannan su waye zasu dau fansar?

Husaini ba wani shirin yaki da ya zo da shi. Bil hasili ma kaffatanin na tare da shi mata ne da kananan yara.


(Labarin Cikakkun... | 4515 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 10
(Labarin Cikakkun... | 3651 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR. MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 10

ME YA FARU A KARBALA? 10 Husaini Ya Kama Hanyar Kufa Safiyar 8 ga watan Dhul Hajji a shekara ta 61H ita ce ranar da alhazai suka kama hanyar zuwa Minna don fara aikin hajji. Ita ce kuma ranar da kaddarar Allah ta gargada Husaini da iyalansa zuwa darajar da madaukakin sarki ya ajiye masu ta samun shahada a Karbala. AL BIDAYAH WAN NIHAYA na Ibnu Kathir (8/171).

A kan hanyarsa ta zuwa Iraqi sayyidina Husaini ya gamu da shahararren mawakin nan Firazdaq, ya tambaye shi labarin inda ya fito, sai ya ce Kufa.

Da ya tambaye shi halin da ya baro a can sai Firazdaq ya ce masa, ''Na bar zukatan mutane na tare da kai, makamai na ga masu mulki, sanin gaibu na wurin Allah''. Da ya karasa gaba kuma sai ya gamu da Hurru bin Yazid At Tamimi wanda ya fito fili ya ba shi shawarar ya koma Makka. Har sayyidina Husaini ya karkata ga wannan ra'ayi sai kuma hukuncin Allah ya rinjaya, Husaini ya ci gaba da tafiyarsa.

A wani wuri kuma da ya yada zango sai ya hadu da Abdullahi bin Muti' shi ma yana dawowa daga Kufa. Dan Muti'u bai yi wata wata ba ya shawarci Husaini da komawa Makka yana ce masa ''Ka ji tsoron Allah ya kai Husaini, ka tsare martabar gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam kada ka sa a keta ta. Kada ka je Kufa, kada kuma ka gitta ma mulkin wadannan mutane. Idan ka yi haka wallahi zasu kashe ka. Allah ne kuwa kadai ya san karshen wannan lamari idan ya faru''. AT TARIKH AL ISLAMI na Mahmud Shakir (3/124).


(Labarin Cikakkun... | 3651 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 9
(Labarin Cikakkun... | 3105 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR. MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 9

ME YA FARU A KARBALA? 9 An ci gaba da shawartar Husaini Kamar yadda muka gani a baya mutanen Iraqi sun riga sun bada amincin Allah a kan tarbon sayyidina Husaini da halifantar da shi a madadin Yazid. Kuma sun aike masa wasiku masu dinbin yawa a kan haka. Haka ma zuwan da Muslim bin Aqil ya yi bai sa liki ya balle aka gano mugun nufinsu ba, amma dai masu nazari sun yi ta ba Husaini shawara kada ya amince musu. Akwai kuma wadanda suka aike masa da wasiku na rarrashi da ban hakuri don hana shi fita kamar Abdullahi bin Ja'afar bin Abi Talib da Amru bin Sa'id bin Al Ass da wata mashahuriyar malamar hadisi ta wancan lokaci ana ce da ita Amrah.

Shi Abdullahi bin Umar wanda da farko suka dauki matsayi daya da Husaini a yanzu sai da ya bi Husaini ko bayan fitar sa yana rarrashin sa kan ya dawo.

Kwanan sa biyu a tare da shi a kan hanya yana kokarin shawo kansa, yana ce masa ''ka tuna rashin kirkin mutanen Iraqi da rashin cika alkawarinsu. Wace irin wahala ce mahaifinka bai sha a hannunsu ba?


(Labarin Cikakkun... | 3105 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 8
(Labarin Cikakkun... | 3094 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR. MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 8

ME YA FARU A KARBALA? 8 Yarima Ya Zama Sarki Tun daga hudubar farko da Yazid ya yi ya fara sauya siyasar mulki daga ta babansa kamar yadda hausawa suka ce Sarki Goma Zamani Goma. Yazid ya soma da jajanta ma jama'a game da mutuwar sarkin musulmi Mu'awiyah, Sannan ya bada sanarawar game ma mutane albashin wata uku (a wancan lokaci talaka albashi gwamnati ke masa, sunnar da sarkin musulmi Umar Dan Haddabi ya fara), Sannan Yazidu ya ce ya jinkirta yaki a bangaren teku saboda shigowar lokacin sanyi. Daga juyayi sai mutane suka koma murna.

Ba a Sham kadai aka yi wa Yazidu mubaya'a ba, a'a har da Makka da Madina da sauran garuruwan musulmi.

Amma mutum biyu da muka sani cewa ba su yi mubaya'a ba suna nan a kan matsayinsu.

Kuma ganin kamar gwamnan Madina Al Walid bin Utbah zai yi yunkurin tilasta su sai suka sauya mazauni su biyun suka koma Makka.


(Labarin Cikakkun... | 3094 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 7
(Labarin Cikakkun... | 3494 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR. MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 7

ME YA FARU A KARBALA? 7 Nadin Yarima Mai jiran gado Kamar yadda muka fadi a baya, HUSAINI Radiyallahu Anhu ya bi umurnin wansa Al Hasan wajen yin biyayya ga gwamnatin sayyidina Mu'awiyah har sanda Allah ya kawo karshenta a shekara ta 60H. To, amma kafin haka Mu'awiyah ya ayyana Yazid a matsayin Yarima wanda zai gaje shi idan ajalinsa ya cim masa. A nan ne Husaini ya cije ya ce ba zai bada goyon baya ba.

Husaini ba shi kadai ya dauki wannan matsayi ba. Akwai masu mutane uku da suka hada da Abdullahi Dan Umar da Abdurrahman dan Abubakar da kuma Abdullahi dan Zubair. Su hudun basu bada goyon baya ba, kuma dukkansu 'ya'yan manya ne kamar yadda muka gani. Ko wannensu babansa na cikin mutane goman da aka yi amanna 'yan aljanna ne don sanarwar da bakin da ba ya karya ya bayar a kansu. Amma HUSAINI ya dara sauran don shi yana da tasa bushara ta kashin kansa. Amma dai duk da haka wannan lamarin ya ci gaba yadda aka tsara shi.

Me ya sa sayyidina Mu'awiyah ya nada Yarima? Kuma don me ya zabi dansa YAZIDU?

Amsa ita ce, Sanin gaibu sai Allah. Amma dai ba za a rasa dayan wadannan abubuwa ba ko dukansu bisa ga hasashen masu iya kyautata masa zato a matsayinsa na sakataren Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam, wadanda ba su dauke da ''Gilli'' a zukatansu dangane da shi. Ga su:


(Labarin Cikakkun... | 3494 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 6
(Labarin Cikakkun... | 2746 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 6

ME YA FARU A KARBALA? 6 Matsayin Sayyidina Hussaini game da gwamnatin Yazid Kafin mu je can, yana da kyau muyi waiwaye game da gwamnatin da ta kawo shi mulki, ina nufin gwamnatin babansa Mu'awiyah.

Abinda aka sani ne cewa, har zuwa lokacin wafatin sayyidina Ali ba wani nadadden sarkin musulmi in ba shi ba.

Babu kuma wanda yake da'awar son ya karbi wannan mukami daga wurinsa. Amma bayan da sayyidina Ali ya samu shahada ta hannun Abdurrahman bin Muljam (daya daga cikin 'yan Khawarij wadanda suka yi tawaye daga rundunarsa – Shi'arsa), sai mutanen Iraq suka nada dansa AlHasan, a yayin da mutanen Sham suka nada gwamnansu Mu'awiyah. Ba kuma wani bangaren da ya tuntubi wani a wajen aiwatar da muradinsa.


(Labarin Cikakkun... | 2746 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 5
(Labarin Cikakkun... | 4302 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 5

MEYA FARU A KARBALA? 5 Har yanzu dai a kan Yazid Mun riga mun fadi cewa, akwai rikici mai yawa a tsakanin mawallafa game da sha'anin Yazidu har mun soma bada wasu 'yan misalai a kan haka.

Daga cikin abin da ke nuna haka zamu ga zancen wasiyyar da Mu'awiyah ya yi masa Dinawari da Ibnu Abdi Rabbihi duk sun ruwaito ta. Amma Dinawari cewa ya yi Mu'awiyah ya yi masa wannan wasici ne baka da baka, amma shi Ibnu Abdi Rabbihi sai ya ce Mu'awiyah ya rubuta ta ne a yayin da Yazidu yake can yana farauta da wasanni kuma bai dawo ba sai bayan mutuwar uban nasa.

Duba Al Iqdul Farid na Ibnu Abdi Rabbihi (4/372) da kuma Al Akhbarut Tiwal na Dinawari, shafi na 225.

To, wace ruwaya ce ta gaskiya a cikin wadannan?


(Labarin Cikakkun... | 4302 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 4
(Labarin Cikakkun... | 3541 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 4

ME YA FARU A KARBALA? 4 ASHURA, HUSAINI, YAZIDU DA KARBALA 4 A cikin babban kundin tarihin da Ibnu Asakir ya wallafa ya kawo hadisai masu dinbin yawa a kan zagin Yazid kamar yadda ya al'adanta a duk wadanda yake kawo tarihinsu. Sai ka ga ya kawo ruwayoyi masu yawa a kan yabon mutum, sai kuma ya kawo wasu irin su na sukar sa. Muradin mawallafa a wancan lokaci shi ne tabbatar da riwayoyin kowane bangare na masoya da masoka. Don haka ya zama dole kowace ruwaya a jingina ta ga inda aka ji ta don mai karatu ya zan cikin basira. Basu san za a kai ga irin wannan lokaci da nassin kawai ake kallo ba, ba a ma san su wane ne maruwaitansa ba.

Wannan shi ya sa sai ka ga mai yabo ya damfare ma wadannan riwayoyi, mai suka kuma yana ta cika baki da wadancan.

Malaman Sunnah kadai ne ke iya tantancewa, su cire aya su raba ta tsakuwa, kowane mutum kuma suyi masa adalci, su ajiye shi inda ya cancanta.

Wannan ya sa suka kasance mafi adalcin al'umma.


(Labarin Cikakkun... | 3541 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 3
(Labarin Cikakkun... | 2595 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 3

ME YA FARU A KARBALA? 3 Rikicin mawallafa a game da YAZIDU Yana da wahala kwarai ka samu mutum a tarihi wanda aka yi ta takin saka a kansa, ruwayoyi kuma suka rinka cin karo da juna a kan sa kamar YAZIDU. Yawan masoyansa masu yabon sa, da makiyansa masu sukar sa na sanya mai karatun tarihi a cikin rudani ba na wasa ba. Zan bada wasu 'yan misalai don mu gane wannan.

Misali na Daya: A yayin da Ibnu Abdi Rabbihi ya ruwaito cewa, YAZIDU ya damu da nadin da aka yi masa a matsayin kwamanda wajen yakin Qustantiniyah kuma har ya zargi babansa da son halaka shi. Kai har ma wai zambo ya yi ma baban nasa! (Duba Al Iqdul Farid na Ibnu Abdi Rabbihi 4/367)
Shi kuma Ibnu Tolon cewa ya yi YAZIDUn ne ya nemi a ba shi wannan mukami.


(Labarin Cikakkun... | 2595 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

ME YA FARU A KARBALA? 2 Wane ne YAZIDU?
(Labarin Cikakkun... | 3032 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

ME YA FARU A KARBALA? 2 Wane ne YAZIDU?

Sunansa YAZIDU Dan Mu'awiyah Dan Sakhr (Abu Sufyan) Dan Harb Dan Umayyah Al Umawy Al Qurashie.

Ana yi masa alkunya da Baban Khalid.

Mahaifiyarsa ita ce Maisun 'yar Bahdal daga kabilar Kalbu, daya daga cikin kabilun Kuraishawa masu karfi a wancan lokaci. Ta rabu da mahaifinsa tana dauke da cikinsa, sai ta yi mafarkin wata ya fito daga jikinta. Masu Fassara suka ce mata in har mafarkinki ya tabbata za ki haifi sarki.

Hakan kuwa aka yi.

An haifi YAZIDU a shekara ta 26H a zamanin halifancin sayyidina Usmanu Dan Affan. YAZIDU ya tashi a gidan sarauta, domin ko da aka haife shi mahaifinsa yana gwamnan Sham. Ya samu tarbiyyar jihadi domin tun yana matashi dan shekaru 24 ya jagoranci runduna mafi girma da ta fatattaki Rumawa kuma ta kwace hedikwatarsu ''Qustantiniyah''. Daga nan ne kuma sunan YAZIDU ya fara fitowa har ya yi tashe a tsakanin matasa. A nan ne kuma ya samu tasa daraja daga Hadisin Ummu Haram bint Malhan Matar sayyidina Ubada bin As Samit wacce ta ce ta ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam na cewa ''Rundunar farko da zasu yi yaki a teku daga cikin al'ummata Allah ya gafarta masu''. Ta ce, Manzon Allah ina cikin su? Ya ce, eh. Kina cikinsu. Sannan ya ce ''Rundunar farko da zasu ci birnin Qaisar daga cikin al'ummata su ma Allah ya gafarta masu''. Ta ce, Manzon Allah ina cikin su? Ya ce, a'a. (Sahihul Bukhari, Hadisi na 2924).


(Labarin Cikakkun... | 3032 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com