Topic: Ya Mutu Ya Dawo! Martabar Iyaye: Yaushe Ne 1000000=1000???!!! (Kalu-Bale Ga Wasu Iyale)
Timeline: 2012-05-13 05:59:40
A Rubuce Da Nura Abdullahi Madina
Ya Mutu Ya Dawo! Martabar Iyaye: Yaushe Ne 1000000=1000???!!! (Kalu-Bale Ga Wasu Iyale)
Ya ce na dawo daga kwas din aikin soja kenan ina mai cike da farin ciki, ina ta tunanin yadda zan je na samu yara da sauran mutanen gida da masoya.
Bayan na isa gida da ’yan sa’o’i, kowa yana ta murna, manya da yara.
Kwatsam sai na ji ana dukan kofa da karfin gaske, da na fita sai na ga jami’an tsaro, suka kira ni da cikakken sunana, kuma suka ce ni suka zo nema, don haka shige mu je!
Suka tasa keyyata zuwa ofishin ’yan sanda. Har zuwa wannan lokaci ban wani damu ba; don na san ban yi wani laifi ba.
Amma ba zato ba tsammani sai na ji wai ana tuhuma ta da wani mugun laifi, wanda wannan ya sa ba ki daya na rude, na firgice, na dimauce, har na kasa magana.
Ana tuhumar ka da kisan ganganci! Mataimaki D.P.O ya ce min! kai ne ka kashe wane dan wane, kuma kana da sammaci a kotu!
Sai na rasa abin da yake min dadi a duniyan nan, hankalina ya dugunzuma, na kasa gasgata abin da nake ji, na yi ta hakilon gamsar da kaina kan cewa wani ake tuhuma ba ni ba, sunan ne dai ya yi kama, ko wani kuskuren fahimta.
Amma daga karshe na fuskanci abin babba ne, bayan an ta bincika ta ba ji ba gani. Abin ya kara dagulewa bayan masu binciken sun sanar da ni cewa inkarina ba shi da wani amfani; don ga shedu nan duk sun rantse suna masu tabbatarwa cewa kai ne makashin wannan mutum! Ya ce haka na yi ta fafutukar kare kaina, har karfina ya kare, musamman lokacin da na ga an mika ala’amarina zuwa gurin alkali.
Nan wasu mutane suka bayyana gareni suka ba da sheda cewa lallai ni ne na yi kisan nan, kuma Wallahi Billahillazi La Ilaha Illa huhu ban taba ganin shedun nan ba, kuma ban taba sanin mutumin da suka ce na kashe ba!
Haka na zauna tsahon shekaru goma sha biyar a kurkuku! Saboda ’ya’yan mutumin nan kanana ne, bayan sun balaga suka ki yin afuwa, suka ce su kawai kisasi suke nema! Bayan bakin ciki da damuwa, da zaman dar dar da na yi tsahon shekarun nan sha biyar a ciki, rannan da sanyin safiyar ranar Juma’a sai ga jami’an tsaro sun shigo inda nake daure, suka miko min takarda don na rubuta wasiyyata, kuma suka sanar da ni cewa yau ita ce ranata ta karshe a duniya! Suka lakkana min Kalmar shahada.
Bayan na gama rubuta wasiyya da dan lokaci, sai suka sani a gaba zuwa filin sare kai, muka samu filin makare da jama’a, ga jami’an tsaro nan iya ganinka sun yi masa kawanya. Har zuwa wannan lokacin ambaton Allah ba ya yankewa daga bakina.
Aka karasa da ni gurin fille kai bayan an rufe min idanuwana, mai shela ya fara shelanta laifin da aka ce na yi, da madogarar da aka dogara da ita wurin yanke min hukuncin kisa. A daidai wannan lokaci sai na dada tunawa da Allah, kuma na kara dagewa wurin ambatonsa, da addu’a, na ce: “Ya ubangiji zalunta ta aka yi! Ya ubangiji ni zalunta ta aka yi!! Kuma ka yi alkawari, kuma alkawarinka gaskiya ne, kuma kana amsa addu’ar wanda aka zalunta, ya ubangiji ni zalunta ta aka yi, kuma kai ne masanin dukkanin abubuwan da suke boye, na mika lamarina gareka, ba bu abin bautawa da gaskiya sai kai!!!… WALLAHI ban kammala addu’ata a lokacin da ake karanto wancan bayani ba, sai kawai na ji ana hayaniya ana ihu da karfi, na kuma jiyo sautin wani mutum yana cewa da karfi: “Kada ku kashe shi! Ni ne na yi kisan!! kada ku kashe shi! Ni ne na yi kisan!! Sai guri ya rude aka ta hayaniya, karanta bayani ya tsaya cik, sai na ji daya daga cikin jami’an tsaron yana cewa: Ga shedun nan sun yi ikrari cewa su ne suka yi kisan, na ji wasu kuma suna neman a gaggauta zartar da hukunci, haka aka dauki lokaci mai tsaho ana ta cece ku ce, ni kuma ina durkushe, ido a rufe, hannu da kafa a daure! A karshe dai Allah ya fallasa su. Hukuncin kisasi ya fadi daga kaina. Na dawo duniya kai ka ce ranar aka haife ni….
Ina masu bukatu, ina masu fama da bakin ciki da damuwa, ina masu neman waraka… dss. Kun ga yadda addu’a take tasiri? Don haka kar ku sake. Wannan abu ya faru a Saudiyya kamar yadda Badr Almishary ya fada a kaset dinsa قرع لأبواب السماء. Shi kuma ya dakko daga littafin الفرج بعد الشدة
MARTABAR IYAYE: YAUSHE NE 1000000=1000???!!!
MARTABAR IYAYE
• “Ya ku wadanda kuka yi imani ku ji tsoron Allah, kuma kowa ya yi tunanin me ya tanada ranar gobe (kiyama) ku ji tsoron Allah, hakika Allah sanau ne game da abubuwan da kuka kasance kuna aikatawa” (Suratul Hashr: 18)
• Annabi (SAW) ya ce: “Allah wadaransa! Allah wadaransa!! Allah wadaransa!!! Sai aka ce wa kenan ya manzon Allah! Sai ya ce: wanda ya riski tsufan iyayensa duka ko daya daga cikinsu, kuma ya kasa shiga aljanna” (Muslim: 6674)
YAUSHE NE 1000000=1000???!!! (KALU-BALE GA WASU IYAYE)
Wata rana wani matashi ya dawo gida sai ya ga tarin jama’a a kafar gidansu, gabansa ya yanke ya fadi; ya dauka ko rasuwa aka yi, daga baya sai ya ga ashe wai kannensa biyu mata ake daurawa aure, bai san ma an ba da su ba ballantana daurin aurensu! da ya yi magana sai aka ce masa: “To in an gaya maka me za ka iya yi, (Shi da yake fama da taluci me ya yi wa kansa ballantana wasu)?!” Bbai san lokacin da hawaye ya fara shatato masa ba, ya fito waje hawaye shabe-shabe yana cewa: “Allah ya raba mu da talauci!”
Bugu da kari, wata baiwar Allah ita ma ta koka da yadda mahaifanta suke watsi da ita, saboda mijinta ya talauce! Ta ce: A da, da suke da abin hannunsu, komai sai abin da ta ce a gidansu, musamman ma ga shi ita ce babba a gidan, amma da “yau” ta ci su da yaki sai ya zamana, wani lokaci ko sa ranar kannenta da suke ciki daya sai dai ta ji a sama! Ta ce wannan abu yana damu na fiye da misali, a ce talauci ya zabge mata daraja haka a idon iyayenta!
Shi kuma wannan wani karamin ma’aikaci ne, kwatsam sai ya bar wannan aiki ya buge da wata kaskantacciyar sana’a da yake zaton zai yi saurin samun kudi ta ita, da aka tambaye shi, sai ya ce, ya yi haka ne saboda gudin fushin mahaifiyarsa, saboda kannensa da yayyensa duk mawadata ne, don haka idan sha’ani ya taso– kamar biki ko suna– su kan ba ta kudi da yawa, shi kuma abin da yake iya ba ta bai taka kara ya karya ba, ita kuma sai ta yi ta fada har barazanar tsine masa take yi in bai yi mata irin yadda ‘yan’uwansa suke yi mata ba, ya yi mata duk wani bayani amma bata yarda ba, shi ya sa ya yanke shawarar shiga wannan sana’a takaskanci ko shi ma ya samu kudi don ya kara kima a idon mahaifiyarsa, kuma ya huta da zagi da tozartawa a gaban kannensa ba iyaka!
Dorawa ‘ya’ya abin da ba za su iya ba, ko fifita wasu akan wasu don kawai suna da kudi, ko suna auren masu da-akwai, ya sabawa koyarwar manzon Allah (SAW).
Ya zo a cikin (Bukhari da Musulim) Wata rana wani sahabin manzon (SAW) ya ba wa dansa wata kyauta, sai ya zo ya ce da Annabi ya yi masa shaida a kai, sai ya ce masa ragowar ’ya’yanka ma duk ka yi musu irin wannan kyauta?”
Sai ya ce A’a. sai ya ce:
“Kuma kana son su yi maka biyayya kamar yadda zai maka?
Sai ya ce: Sosai kuwa!
Sai ya ce masa: “Ku ji tsoron Allah ku yi adalci tsakanin ’ya’yanku!” a wata ruwayar: “Kar ka kuskura!” a wata ruwayar “wannan kyautar a fasa ta!” a wata ruwayar “Ka je wani ya yi maka shaida ni ba na shaida akan zalunci!” shikenan sai ya fasa.
Kuma a hankalce idan muka duba za mu ga da wanda ya mallaki milyan goma, ya bai wa mahaifansa kyautar milyan daya, da wanda ya mallaki dubu goma ya ba su kyautar dubu daya ba wani bambanci tsakaninsu; don kowanne 10% na dukiyarsa ya ba su!
**{Legacy activities, comments etc counter: 2279; topic series: 6; forum: MediaHausa; legacy score: 8; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 6- /*}