Topic: Fatawoyin Aikin Hajji Da Umra Da Ziyara (2)
Timeline: 2012-06-19 02:37:53
Fatawoyin Aikin Hajji Da Umra Da Ziyara (2)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Daga Sheikh Abdulwahhab Abdullah Tambaya ta 5: Mene ne hukuncin wanda Allah Ya ba shi damar zuwa aikin Hajji, amma ya yi sakaci bai je ba?
Amsa: Wanda ya yi sakaci bai je aikin Hajji ba, bayan kuwa Ubangiji Ya ba shi iko, to, hakika ya saba wa Allah, kuma ya yi sakaci a kan rukunin da Allah Ya wajabta masa. Saboda haka, akwai barazana da narko a kansa idan har ajali ya zo masa a wannan hali. Dalili kuwa shi ne fadinSa Madaukaki “… Kuma wanda ya kafirta, to lallai Allah Mawadaci ne daga dukkan talikai.” (Al-Imran: aya ta 97).
Wannan shi ne abin da Ubangiji (SWT) Ya fada, bayan Ya yi bayani a kan wajibcin aikin Hajji. Haka kuma an karbo Hadisi daga Abdullahi Ibnu Umar (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku nemi jin dadin (bautawa Allah) da wannan dakin: Hakika an rushe shi sau biyu, kuma a na ukun za a dauke shi. (Sahih at-Targhib wat-Tarhib (2/1110) da Kitabul Hajji).
Tambaya ta 6: Shin wanda ya mutu bai samu damar yin aikin Hajji ba, za a iya yi masa?
Amsa: Na’am, hakika za a iya yi masa, ba tare da wani sharadi ba, ko ya bar wasiyya ko bai bari ba. Dalili kuwa shi ne, Hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibnu Abbas cewa “Hakika wata mace daga kabilar Juhaina ta zo wajen Manzon Allah (SAW) sai ta ce: “Hakika mahaifiyata tayi bakancen yin Hajji, amma ba ta samu damar yin Hajjin ba har ta mutu, shin zan iya yi mata? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: Na’am! Ki yi mata Hajjin. Sai kuma (Manzon Allah (SAW) ya ce: Shin da bashi ake bin mahaifiyarki za ki biya mata? To, ku biya hakkin Allah, domin hakkin Allah shi ne ya fi cancantar a cika masa.” Sahihul Bukhari: Kitabu Jaza’is Saidi, Babul Hajji Wan Nuzuri Anil Mayyiti, Hadisi na 1852.
Haka kuma wani hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibnu Abbas (RA) ya ce: Hakika Manzon Allah (SAW) ya ji wani mutum yana cewa: Labbaika an Shubrumah (wato yana daukar niyyar Hajji ga dan uwansa mai suna Shubrumah). Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: Wane ne Shubrumah? Sai ya ce: makusancina ne. Sai (Manzon Allah SAW) ya ce: Shin kai ka taba yin Hajji? Sai ya ce: Ban taba yi ba. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: Ka fara yi wa kanka, sannan ka yi wa (dan uwanka) Shubrumah.” (Sunan Abu Dawud: Kitabul Manasik, Babur Rajuli Yahujju An Gairihi, Hadisi na 1811; da Sunan Ibnu Majah: Kitabul Manasik, Babul Hajji Anil Mayyiti, hadisi na 2903; da Irwa al-Ghalil (mujalladi na 4 shafi na 994). Kuma Sheikh Albani ya inganta shi.)
Wannan hadisi ya nuna cewa: Manzon Allah (SAW) bai tambaye shi ko Shubrumah ya bar wasiyya ko bai bari ba. Sharadin kawai shi ne, lallai ne wanda zai yi wa mamaci aikin Hajji, ya kasance ya fara yi wa kansa.
Haka kuma duk mutumin da ya tsufa ba zai iya yi aikin Hajji ba saboda larurar rashin lafiya ko tsufa, to, za a iya yi masa. Dalili kuwa na cikin Hadisin da aka ruwaito daga Abdullahi Ibnu Abbas cewa: “Hakika wata mace daga kabilar Khas’am ta zo wurin Manzon Allah (SAW), sai ta ce: Ya Manzon Allah (SAW)! Hakika babana ya tsufa kuma ya yi rauni, ga shi farillar Allah ta aikin Hajji a kan bayinsa ta same shi, kuma ba zai iya yin aikin Hajjin ba, shin zan iya yi masa? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: Na’am! Za ki iya yi masa.” (Sahihul Bukhari: Kitabu Jaza’ussaid, Babu Alhajju Amman La Yastadi’u, Hadisi na 1854, da Sahih Muslim: Kitabul Hajji, Babul Hajji Anil Ghairi, Hadisi na 133; da Sunan Abu Dawud: Kitabul Manasik, Babur Rajuli
Yahujju An Gairihi, Hadisi na 1809; da Sunan Ibnu Majah: Kitabul Manasik, Babul Hajji Anil Hayyi Iza Lam Yastadi’i, Hadisi na 2908; da kuma Irwā al- Ghalīl: (Mujalladi na 4 shafi na 992). Kuma Sheikh Albani ya inganta shi). Wannan na nuna sauki da tausayawar da Musulunci yake da ita.
Tambaya ta 7: Iyaye da ’yan uwa da suka rasu, shin za a iya yi musu Hajji?
Amsa: Iyaye ko ’yan uwa da suka rasu za a iya yi musu Hajji ko Umra da niyyar Allah Ya kai musu ladan, ko da ba su bar wasicin a yi musu ba. Wannan shi ne zance mafi rinjaye a wurin malamai magabata.
Amma yi musu dawafi sau daya ko sau bakwai bai tabbata ba a sunnar Manzon Allah (SAW) ko aikin magabata na kwarai. Amma muna ganin iyayenmu mata suna yawan yin dawafi da niyyar Allah Ya kai ladan ga iyayensu ko ’yan uwansu da suka rasu maimakon su yi musu addu’ar Allah Ya yi musu gafara. Allah Ya fahimtar da mu mu tsaya a kan sunnar Manzon Allah (SAW).
Tambaya ta 8: Shin ya halatta a biya wa mutum Hajji da kudin da aka sata (kamar daga aljihun gwamnati) ko kudin haram (kamar riba ko kudin giya)?
Amsa: Bai halatta ba, saboda fadin Ubangiji (SWT) cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku ci daga dadadan (abubuwan) da Muka azurta ku (da su), kuma ku gode wa Allah idan kun kasance Shi kuke bautawa.” ( Bakara: aya ta 172).
Haka kuma an karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: Ya ku mutane! Hakika Ubangiji (SWT) Tsarkakakke ne, kuma ba Ya karbar aiki sai tsarkakakke. Hakika Ubangiji (SWT) Ya umarci muminai da abin da Ya umurci Manzanni da shi. Ya ce: Ya ku Manzanni! Ku ci daga dadada, kuma ku yi aiki nagari, hakika Ni masani ne game da abin da kuke aikatawa. Kuma Ubangiji (SWT) Ya ce: Ya ku muminai! Ku ci daga dadadan abin da Muka arzuta ku da shi.” Sannan sai (Manzon Allah (SAW) ya ambaci wani mutum matafiyi, mai gizo, ya yi kura, yana daga hannayensa zuwa sama, (yana addu’a yana cewa) Ya Ubangiji! Ya Ubangiji! Alhalin abincinsa (daga) haram ne, abin shansa (daga) haram ne, tufafinsa (daga) haram ne, kuma an ciyar da shi da haram. (Sai Manzon Allah SAW ya ce:) Ta yaya za a amsa addu’arsa?”
(Sahih Muslim: Kitabuz Zakati, Babu kubulis Sadakati Minal Kasbid dayyibi Wa Tarbiyatiha, Hadisi na 1015).
Abin fahimta a wannan hadisin shi ne, duk da cewa addu’ar matafiyi karbabbiya ce, amma Manzon Allah (SAW) ya nuna ba za a karbi addu’arsa ba saboda cin haram. Domin haka, idan mutum ya yi aikin Hajji da dukiyar haram, Hajjinsa ba karbabbe ba ne. Wallahu a’alām.
Amma akwai wadansu malamai da son zuciya ya sa suke ba da fatawar cewa, mutum zai iya satar kudin hukuma, ya yi aikin alheri da shi. Wadannan malamai ba su da wani dalili a cikin littafin Allah ko sunnar Manzon Allah (SAW). Sai dai kuma shugaba mai adalci, wanda baitulmali ke hannunsa, zai iya amfani da wani bangare na kudin da aka tanada don tsaron shugaba, ko alawus, ko sallamar baki, ko daga cikin albashinsa, ya biya wa wadanda suka cancanta. Zai yi haka ne, ba tare da ya tauye hakkin talakawa ba, kamar yadda wadansu hukumomi ke barnatar da dukiyar al’umma wajen biya wa wadanda ba su cancanta ba, saboda manufa ta siyasa.
Ya kamata malamai su rika fadakar da shugabanni game da hadarin amfani da dukiyar da Allah Ya sa a hannunsu, ta hanyoyin da ba su dace ba. Malamai su tuna cewa ilimi da karantar da shi amana ce da Allah zai tambaye su a Ranar kiyama. Don haka, wajibi ne su zamanto masu fadin gaskiya ba tare da la’akari da jin dadi ko rashin jin dadin shugabanni ba. Allah Ya shiryar da mu zuwa tafarki madaidaici, amin.
**{Legacy activities, comments etc counter: 475; topic series: 2; forum: MediaHausa; associated: 2- /*}