Topic: Bukatar Samar Da Shugaban Kasa Nagari
Timeline: 2010-11-18 15:39:05
Bukatar Samar Da Shugaban Kasa Nagari
A Rubuce Da Musa Ismaeel
Lokaci ya yi da za’a tace aya daga tsakuwa. Najeriya ayau ta cika shekaru hamsin da samun `yancin kai, ga kuma zabe na gabatowa a mataki daban-daban. Sanin kowa ne `yan Najeriya na mutukar neman samun shugabanni da wakilai nagari a matakai domin cigaba da kasancewa kasa mai arzikin masana`antu da tattalin arziki.
An dade ana wakar yadda za`a samar da nagartattun mutane domin shugabanci da wakilci, amma abin ya gagari kundila. Matsalolin kasar nan na da nasaba da rashin wakilai da shugabanni na gari. Wannan ya samo asali ne daga rashin samun hukumar zabe sahihiya wadda za ta tsaya wajen tantance gaskiya, sannan kuma akwai rashin gyaran dokoki da zai zamo zabe ya inganta bisa gaskiya da kauce wa magudi. A cikin wannan yanayi na rudani da kasar nan ke ciki aka samu namiji jan gwarzo da ya kawo canje-canje da za su saka kasar nan bisa tafarkin cigaba, domin kuwa wannan canje-canjen su ake bukata tuntuni.
Abu na farko shi ne samar da gyaran dokokin zabe na kasa ta yadda za`a rage ko kuma a yi maganin magudi gaba daya. Kusan tuntuni ake da bukatar wadannan sauye-sauye domin a tabbatar da zabe nagari, amma hakan ba ta samu ba, sai da shugaba Goodluck ya yi namijin kokari wajen samar da wannan dokoki wanda tuni ya rattaba hannu a kansu.
Baya ga gyaran dokokin zabe, shugaban bai tsaya nan ba sai da ya zakulo mutumin da da yawa daga ’yan Najeriya su na da yakinin zai yi gaskiya kuma zai samar da yanayi da za a yi zabe na gaskiya.Wani abin duba shi ne wadannan canje-canje da shugaba Goodluck ya yi sun faru ne duk da ya na da niyyar fitowa takarar shugabancin kasa. Akan gane mutum nagari daga yadda ya ke gudanar da al’amuransa. Sanin kowane a bisa al`adar shugabannin Afirka da Najeriya duk wanda ya ke kan kujerar mulki kuma ya ke son ya cigaba, yakan yi iyakar iyawa domin ya kawar da duk wani abu da zai iya kawo masa nakasu, ko da kuwa abin bisa doron gaskiya ya ke.
Sanin kowane titunan kasar nan sun zama yadda su ka zama, domin kuwa ana asarar rayuka da dama a kullum sanadiyyar lalacewarsu. Ba da jimawa akan kujerar mulki ba shugaba Goodluck ya samar da kwangiloli domin gyaran manyan hanyoyin kasar nan da kuma ware makudan kudade domin gina sabbi. Ba a nan abin ya tsaya ba, shugaban ya yi yunkuri mai kyau domin farfado da hanyoyin jirgin kasa a kasar nan. Yin haka zai saukaka sufuri da samar da hanyar fitowa da amfanin gona zuwa kasuwanni cikin sauki.
A bangaren ilimi kuwa, wanda }asar nan ke koma- baya idan aka yi duba ga kasashen duniya, shugaban ya yi namijin kokari wajen sam ar da ministan ilimi ta farko mace `yar asalin Arewacin Najeriya domin a wannan yanki ake fama da }arancin karatun zamani koma baya ga Kudancin kasar nan. Saka wannan talika zai taimaka wajen gyara tsarin ilimi a matakai daban-daban, kasancewar masaniya ce a wannan fanni sosai kuma yankin da ta fito shi ya fi fama da matsalolin ilimi.
**{Legacy activities, comments etc counter: 783; topic series: 5; forum: MediaHausa; associated: 5- /*}