Topic: Layya da hukunce-hukuncenta (1)
Timeline: 2012-03-27 18:36:18
Layya da hukunce-hukuncenta (1)
A Rubuce Da Muntasir Umar Fagge
Godiya ta tabbata ga Allah UbSakamakon gabatowar Babbar Sallah mun dakatar da bayanin da muke yi kan tuba da istigfari don kawo wani abu kan layya, insha Allah za mu qarasa bayani kan darasin namu bayan Sallah.
Abin da ake ce wa layya shi ne duk wani abu da aka yanka domin neman kusanci ga Allah. Layya tana da asali a cikin Qur’ani da Hadisin Annabi (SAW). A cikin Qur’ani Allah (TWT) Yana cewa: “Ka yi Sallah ga Ubangijinka kuma ka yi yanka.” (Kausar: 2) A Hadisi kuwa Anas Bin Malik (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya yi layya da raguna biyu baqaqe, masu qahonni. Ya yanka su da hannunsa, ya yi bisimillah ya yi kabbara, ya kwantar da su ta gefen wuyansu” (Muslim ya ruwaito). Akwai Hadisai masu yawa kan layya. A shekara ta biyu Bayan Hijirar Annabi (SAW) aka shar’anta yin layya.
Ita layya sunna ce mai qarfi, tana hawa kan wanda ya cika sharuxxa masu zuwa:
1. Ya kasance xa ba bawa ba, namiji ko mace. Tana zama sunna a kan mutum ga kansa da iyayensa, idan talakawa ne, da ’ya’yansa maza idan ba su balaga ba, da ’ya’yansa mata idan ba su yi aure ba. Ba sunna ba ce a kan mutum ya yanka wa matarsa ko xansa da aka haifa a ranar layyar.
2. Kada ya kasance mahajjaci, domin shi mahajjaci, hadaya ce a kansa.
3. Ya zama ba matalauci ne ba. Ma’ana kada ya zama yana buqatar kuxin yin layyar domin biyan wasu buqatu nasa. Amma idan zai iya cin bashi ya yi layyar, to ya yi, idan ya san zai iya biya, ba tare da takuruwa ba. Wasu malaman suka ce kada mutum ya ci ba shi domin yin layya.
Dabbobin da ake yin layya da su
Dabbobin da ake yin layya da su kaxai su ne: Raqumi, sa, rago da taure da matansu. Rago sai wanda ya shekara, taure kuwa sai ya shiga shekara ta biyu. Sa kuma sai wanda ya kai shekaru uku. Shi kuwa raqumi sai ya kai shekara biyar.
A wajen layya, rago ya fi falala (sai tunkiya), sai taure (sai akuya), sai kuma sa (sai saniya). Bayan sa sai kuma sai raqumi (sai taguwa). A cikin kuma dukkan dabbobin da aka ambata an fi fifita mazansu a kan matansu, lafiyayyunsu (waxanda suke iya yin barbara) kuma a kan fixiyayyunsu (wanda ba sa iya yin barbara). Sai dai idan fixiyayyun sun fi kitse ne sai a yi da su.
Sharuxxan ingancin layya
1. Dole ne a yi yankan da rana, bai inganta a yi shi da daddare ba. Rana tana farawa ne daga ketowar alfijir. Amma a game da layya sai liman (shugaba) ya yanka tasa layyar sannan kowa ma zai yanka. Ba wai da an wayi gari ne kawai sai a yi ta yanka ba. Idan mutum ya yanka kafin liman ya yanka tasa, layyarsa ba ta yi ba.
2. Mai yin yankan dole ne ya zama Musulmi,yankan kafiri bai halatta ba. Koda kuwa ma’abocin littafi ne “Ahlul-Kitabi”. Amma ya halatta a ci yankan ma’abocin littafi “Ahlul-Kitabi”.
3. Kaxaituwa da sayen dabbar layyar. Bai halatta mutane da yawa su haxu a cikin kuxin dabbar layya xaya ba. In kuma suka haxa kuxi suka sayi dabba suka yanka, ba ta zama layya ba. Amma idan xaya daga cikinsu ya biya saura kuxinsu, shi ya kaxaita da dabbar, a wannan lokacin ya halatta ya yi layya da ita.
Duk da haka ya halatta ga mai yin layya ya sanya wani ko wasu cikin ladan layyar, kafin ya yanka, ba bayan ya yanka ba. Koda kuwa waxanda zai sa a cikin ladan sun wuce bakwai. Yin hakan kuma sai da sharuxxa uku:
a) Ya kasance wanda zai saka cikin ladan na kusa da shi ne. kamar xa, xan uwa, xan ammi ko matarsa.
b) Ya kasance wanda zai shigar cikin ladan layyar, wanda ciyar da shi ya wajaba a kansa ne. Ko kuma dai shi yake ciyar da shi. Wato ko ba don ciyar da shi xin ya wajaba a kansa ba.
c) Ya kasance suna zaune tare a gida xaya.
Idan waxannan sharuxa suka tabbata, layya ta faxi daga kan wanda aka shigar cikin layyar wani xin. Ana buqatar waxannan sharuxxa ne idan zai shigar da wasu mutane cikin layyarsa ne. Amma idan su kaxai zai yi wa layya a ware ban da shi a ciki, ya inganta ya yi. Ba sai da cikar waxancan sharuxxa da aka ambata ba.
Ya halatta a yi gamayya a cikin layya idan dabbar layyar ta zama raqumi ko saniya. Sannan kuma kada adadin masu gamayyar ya wuce bakwai. Idan suka wuce bakwai, bai halatta su yi gamayya a dabba xaya ba. Dalili a nan shi ne Hadisin Jabir (RA) da yake cewa: “Mun yi layya tare da Manzon Allah (SAW) a shekarar Hudaibiyya, kowace taguwa mutane bakwai, saniya ma mutane bakwai” (Muslim ya ruwaito).
4. Dole ne dabbar layyar ta kasance ta kuvuta daga cututtuka ko aibubbuka da suke a fili qarara. Saboda Hadisin da Bara’u (RA) ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya miqe tsaye a cikinmu ya ce: “Dabbobi huxu bai halatta a yi layya da su ba. Mai ido xaya wadda rashin idon ya fito fili. Marar lafiya, wadda rashin lafiyarta fito fili. Gurguwa, wadda gurguntakarta ta fito fili, wadda ta karye a qafa da kuma wadda ba ta da vargo” (Abu Dauda ya ruwaito), da kuma Hadisin da aka ruwaito daga Aliyu (RA) cewa: “Annabi (SAW) ya hana a yi layya da dabba mai gutsurarren kunne da gutsurarren qaho” (Abu Dauda ya ruwaito).
Ba zai yiwu a yi layya da dabba ba, idan ta zama mai ido xaya, ko mara ido. Koda kuwa akwai alamun idon. Haka nan ba za a yi da mai gutsurarriyar qafar gaba ko ta baya ba, ko marar ji ko mai warin baki ko wadda ba ta yin kuka ko marar vargo ko mai gutsurarren bindi ko marar lafiyar da rashin lafiyarta ya fito fili ko mahaukaciya, madauwamin hauka, ko gurguwa ko ramammiyar da ramarta ta fito fili. Dukkan abubuwanda aka ambata a baya, idan masu sauqi ne, babu laifi, sai a yi layya da ita.
Haka nan bai halatta a yi layya da dabbar da qahonta ya karye yake yin jini ba. Ko wadda kashi xaya daga cikin uku na bindinta ya gutsure. Amma idan wanda ya gutsure bai kai kashi xaya cikin uku ba, babu laifi. Haka nan kuma wadda ta rasa haqora biyu ko fiye ba domin yarinta ko tsufa ba. Amma idan haqori xaya ne ta rasa, babu laifi. Haka nan idan fiye da kashi xaya cikin uku na kunnenta ya tsage, ba a layya da ita.
Kuvutar dabba daga dukkan aibubbukan da aka ambata sharaxi ne a ingancin layya. Idan mai yin layya bai lura da wani aibi da yake jikin dabbar layyarsa ba, sai bayan ya yanka, sai ya yi sadaka da kuxin lamunin da zai amso daga wajen wanda ya saida masa da dabbar ko kuma qimar kuxin lamunin. Domin ita layya sai an yanka ta take wajaba. Ba ta wajaba da niyya ko warewa.
**{Legacy activities, comments etc counter: 1667; topic series: 4; forum: MediaHausa; legacy score: 10; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 4- /*}