Topic: Yahudu da Nasara ba za su taba yarda da kai ba (2)
Timeline: 2012-03-27 18:43:05
Yahudu da Nasara ba za su taba yarda da kai ba (2)
A Rubuce Da huxubar Sheikh Saleh bn Abdullahi Al-Hazlul Huxuba ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su kara tabbata a bisa bawanSa kuma ManzonSa Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad Manzon Allah da wanda ya jibince shi, ya bi sihriyarsa har ya sadu da Allah.
Bayan haka, ya ku Musulmi! Idan har mun ce mu Musulmi ne to yakin da ya gudana a Bosniya da Kosobo da wanda ke gudana a Kashmir da Philipines da Checheniya da makamantansu ba za mu ce yaki ne na basasa ba. A’a yaki ne da makiya suka kai farmaki kan Musulmi. Kuma saboda su Musulmi ake watsi da maganarmu ake tuhumarmu da karkata ga wani bangare. Shin me za ku ce idan aka ce wannan bayani ya fito ne daga rahoton sirri na daya daga cikin wakilan kungiyoyin leken asiri na duniya, kamar yadda aka watsa a wata jarida ta duniya. Jaridar ta ce: “Lallai zaton cewa abin day a faru a Bosniya yakin basasa ne babbar karya ce, akwai hujjoji tabbatattu a hannun Amurka na samun siyasa Sabiyawa da aka tsara aka kintsa shafe Musulmi ta hanyar kisa da azabtarwa da sanya su a kurukuku...”
Kuma a ayan wannan an ga yadda Yammacin Turai ta yi kokarin mu’amala da shugaban Sabiya don nuna shi a matsayin wani mai kiran zaman lafiya. Yana ta kai-kawo tsakanin nan da can don nuna bay a goyon bayan yakin tatre da neman kusanci ga Yamma yana nuna musu kyakkyawar niyyarsa, alhali niyyarsa ta boye it ace gamawa da Musulmi. Mu Musulmi mun san inda da gaske Yammacin Turai suke yi suna son kama shugaban Sabiya ne da makamantansa da sun kama shi a raye ko a mace.
Ya ku Musulmi! Abin da yake faruwa a Checheniya ya fi fitowa fili daga abin day a faru a Bosniya, koda ta hanyar cewa ba yadda za a yi a nuna shi a matsayin yaki ne na basasa. Jama’ar Checheniya al’umma ce da ake yi mata mulkin mallaka sama da shekara 200. Sun fafata da Rasha lokacin tana karkashin sarakuna, kamar yadda suka fafata da tsohuwar Tarayya Sobiyet, kuma ta sha bakar azaba a hannunsu.
Sai dai al’ummar Checheniya ba su sami sa’a irin na al’ummar Bosniya bat a wata fuskar. Domin a yanzu haka suna mutuwa ba tare da ana yi musu jana’iza ko ta’aziyya ba, kamar yadda ya auku a Bosniya da Kosobo. Ta yiwu wadansu su ce: “Mun san dukkan wadannan abubuwa ko ma fiye da haka, kuma babu abin da yake boye a yanzu, jaridu bas u boye komai ba game da makaman da ake amfani das u a kansu, komai yana fitowa a kafafen labarai musamman intanet domin mai bincike ya dada bincikawa, sai dai abin tambaya ta yaya za a warware matsalar? Mene ne abin yi? Me za mu iya yi mu da muke neman a warware shi ko a daki mataki a kai. Baya ga bakin ciki me za mu iya yi saboda kowa ya san gazawarmu?”
Amsar wannan batu shi ne:
Na farko lallai ne mu gane cewa kafirai duk yadda suke makiyanmu ne. Musamman wadanda suka bayyana adawarsu ga Musulunci a fili dare da rana. Ya alla suna adawar ce da kansu ko suna sanya wadansu su yi, ko suna taimakawa da bayar da goyon baya da tallafi ga masu adawa da Musuluncin? Duk wata da’awa da Turawan Yamma suke yi ta zaman lafiya duk karairayi ne. Ta yaya za a gaskata su bayan Bankin Duniya yana taimaka wa Rasha a lokacin da take cikin tsananin yakar Checheniya, kuma a samu kungiya NATO tana goyon bayanta?
Ta yaya za a gaskata su a hali ba sa kare hakkin dan Adam a Checheniya kamar yadda suke da’awa, kuma ba sa la’antar cin zarafi da halaka dan Adam da ake yi a can sai bayan sun tabbatar Rasha ta gama halaka wadanda take so? Kuma koda sun fito da wani bayani da ke Allah wadai da Rasha za a iske ihu ne bayan hari, kuma ba za a aiwatar da komai da zai dakile ta a gaba ba.
Yaya za mu gaskata su bayan ga garuruwan Checheniya da alkaryunta suna fama da aukawar miyagun makaman Rasha, ana halaka mazaunansu da mujahidansu ana yi musu ruwan azaba iri-iri? Shin ko wannan al’amarin cikin gidan Rasha ne kamar yadda kafirai suke son su nuna, kuma wani ba ya shiga cikin harkar cikin gidan wata kasa?
Dubi yadda Turawan Yamma suka dauki matsalar Taymor ta Gabas da Kudancin Sudan. Dubi yadda suka yi ta karaji da iface-iface suka kasa zaune, suka kasa tsaye lokacin takaddamar Taymor ta Gabas har sai da suka tabbatar an dauki matakin tura sojojinsu yankin tare da tabbatar da ta sami ’yancin ballewa daga kasar Indonusiyya! Don me suka amince a ba Jojiya (Georgia) da Armeniya mabiya addinin Nasara ’yancin ballewa daga Mosko amma suka hana wannan ’yanci ga bangaren Musulmi? Dukkan wadannan suna gaskata fadin Allah Madaukaki ne: “Yahudu ba za su yarda da komai daga gare ka ba, haka ma Nasara, har sai ka bi akidarsu.” (k:2:120). Wannan maganar Allah ce da ya wajaba a yi imani da yakini da ita. Kuma wajibi ne ya kai Musulmi ka tsayu wajen kiyaye wannan ka’ida ta addini.
Na biyu: Bayyanar hanyar mujirimai da bayani kan hanyarsu ta yadda ba zai boyu ga kowa ba, abu ne da shari’a take bukata. An kallafa wa Musulmi fahimtarsa da kiyaye shi ta yadda shu’urin Musulunci ba zai zuganye ba, ko kimar Musulunci ya yi sarara, ya zamo ana yi wa Musulunci rikon sakwa-sakwa har da’awar samar da daidaito tsakanin addinai ta sami gindin zama, ko a kaddamar da yaki da tsananin kishin addini da ta’addanci da sababbin kalmomin cin zarafin addini da suka bullo da su.
Fahimtar haka da tabbatarsa a zukatansu Musulmi abu ne da shari’a take nema kuma lalura ce ta akida da ya wajaba a kira mutane a kai da yaki da abin da ya saba mata. Wannan fage da ake neman kai Musulmi ka nuna karfin imaninka. Kuma daga abin day a gabata za mu ga irin kuskuren wadanda suke kusantar kafirai suke zabarsu tare da ba su aiki a ma’aikatu ko kamfanoninsu, har ma suke fifita su a kan Musulmi bisa hujjar cewa sun fi Musulmin kwarewa da son aikin! Suna mance cewa wadannan kafirai suna kwana da tashi da mugun kulli a zukatansu kan yadda za su ga bayansu ne a duk lokacin da suka sami dama! Zaba da kusanto da Musulmi a jika abu ne da kowa zai iya yi, kuma hakan yana da nasa tasirin.
Ya Ubangiji Ka daukaka Musulmi da Musulunci, Ka darkake mushirikai da makiya addini. Ya Allah wanda ya nufi Musulunci da Musulmi da cutarwa a addininsu da duniyarsu da kasashensu Ka shagalatar da shi ga kansa, Ka sanya kulle-kullensa su zama silar halakarsa.
**{Legacy activities, comments etc counter: 1046; topic series: 1; forum: MediaHausa; associated: 1- /*}