Topic: Maraba da Shekarar 1433 BH: Nazari kan shekarar Musulunci da hijira (4)
Timeline: 2012-03-27 18:56:34
Maraba da Shekarar 1433 BH: Nazari kan shekarar Musulunci da hijira (4)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Bidi’o’in da aka shigar cikin ranar Ashura:
1. Bidi’ar nuna bakin ciki da maida ta Idi: Bidi’ar bakin ciki da maida ta tamkar Idi, ita ce bidi’ar da Rafidawa ’yan Shi’a suka kirkiro. Daga cikin alamunta akwai marin fuska da keta sutura da koke-koke irin na Jahiliyya da zagi ko bata sahabban Annabi (SAW) yardaddun Allah.
Ibnu Taimiyya ya ce: “A dalilin kashe Sayyadi Husaini (RA), sai mutane suka kirkiro bidi’o’i nau’i biyu: (Bidi’ar nuna bakin ciki da maida ta Idi da bidi’ar nuna farin ciki da yin ado): 1. Bidi’ar nuna bakin ciki da kuka a ranar Ashura, wadda ta hada da dukan jiki da iface-iface da kuka da sanya wa kai kishin ruwa da rera wakokin ta’aziyya da abin da ya hada da zagi ko bata magabatan kwarai da la’antarsu da sanya marar zunubi cikin masu zunubi har a zagi magabatan kwarai na wannan al’umma, a rika karanta labarai na tatsuniya wadanda da dama daga cikinsu karairayi ne. Manufar wanda ya kirkiro wannan bidi’a ita ce ya bude kofar fitina da rarraba kan al’ummar Musulmi. Domin wannan abu ba wajibi ba ne, ba mustahabbi ba ne, a bisa ittifakin Musulmi. A’a, sake tayar da hankali ne da sanya mutane kuka kan masifun da suka gabata na daga manyan abubuwan da Allah da ManzonSa ya haramta.” (Minhajus Sunnah, Mujalladi na 4 shafi na 554).
Kuma ya kara da cewa: “Sai wata kungiya jahila, azzaluma, imma saboda ilhadi da munafunci, ko bacewa da tabewa, ta fito tana bayyana jibintarsa (Sayyadi Husaini) da jibintar Alhlul Baiti, ta mayar da ranar Ashura ranar Idi da bakin ciki da koke-koke. Ta rika bayyana abubuwan Jahiliyya na daga dukan jiki da keta tufafi da yin koke-koke irin na Jahiliyya. Alhali abin da Allah da ManzonSa Ya yi umarni kan masiba, in sabuwa ce, shi ne a yi hakuri a nemi lada tare da istirja’i, kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce: “Ka yi bushara ga masu hakuri. Su ne wadanda idan wata musiba ta same su, sai su ce: Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Wadancan akwai jinkan Allah a gare su da kuma rahama. Kuma wadancan su ne masu shiryuwa.” (k:2:155-156).
A cikin Sahihu daga Annabi (SAW) ya ce: “Ba ya cikinmu wanda ya mari fuskarsa ko ya yaga tufafinsa kuma ya yi da’awa da irin da’awar Jahiliyya.” A cikin Musnad an karbo daga Fadima ’yar Husain daga Mahaifinta daga Annabi (SAW) ya ce: “Babu wani mutum da musiba za ta same shi ya tuna musibar ko da wadda ta gabata ce, ya tuna ta ya yi istirja’i face Allah Ya ba shi lada misalin ladarsa a ranar da aka shafe shi da musibar.” Wannan yana daga cikin karramawar Allah ga muminai. Don haka lallai musibar Imam Husain da waninsa, idan aka tuno da ita bayan dogon lokaci, ya wajaba ne ga mumini ya yi istirja’i a kanta kamar yadda Allah da ManzonSa Ya yi umarni, domin a ba shi lada irin ladar wanda aka shafa da musibar a ranar da musibar ta auku. Idan ya kasance Allah Madaukaki Ya yi umarni da yin hakuri da neman sakamako a wurinSa a kan aukuwar musiba a daidai lokacin aukuwarta, to yaya lamarin zai kasance bayan dogon lokaci? Abin da Shaidan ya kawata wa ma’abuta bata da tabewa na daukar ranar Ashura Idi da abin da suke yi na mustahabbantar da yin kuka da rera kasidun bakin ciki da ruwaito labaran da ke cike da karya, gaskiyar abin da ke cikinsa, ba komai ba ne face jaddada bakin ciki da ta’assubanci da tayar da husuma da wutar gaba da fitina a tsakanin ma’abuta Musulunci. Kuma suna yin hakan ne don samun hanyar zagi da bata magabatan farko da yawaita karya da tayar da fitina a duniya. Kuma a tarihi, ba a san wata jama’a da yawan karya da taimakon kafirai a kan Musulmi ba fiye da wannan kungiya batacciya tababbiya, su ne mafiya sharri daga Khawarijawa karkatattu.” (Majmu Al-Fatwa, Mujalladi na 25 shafi na 307-309).
1. Bidi’ar farin ciki da ado a ranar Ashura Idi: Wannan bidi’a ita ce bidi’ar da Nawasib (wata kungiya ce daga cikin Khawarijawa da suke kafirta Sayyidina Aliyu bin Abu dalib (RA) suke fasikantar da shi, suke nakasa martabar Ahlul Bait, kamar masu adawa da su kan mulki ko suke zurfafawa wajen girmama Yazid dan Mu’awiyya ba tare da hakki ba), suka kirkiro ta. (A duba Majmu Al-Fatwa, Mujalladi na 28 shafi na 492-493). Daga cikin abubuwan da ake yi akwai bayyana farin ciki da jin dadi da yin wanka da ado da sanya tozali da turare da tanadar abinci iri-iri da yanke-yanke da yalwata wa iyalai da sauransu.
An tambayi Shaihul Islam Ibnu Taimiyya kan abin da mutane suke aikatawa a ranar Ashura na sanya tozali da yin wanka da taya juna murna da yin musafaha da bayyana farin ciki da makamanta haka, shin haka ya samo asali ne daga Annabi (SAW) a cikin Hadisi ingantacce ko a’a? Idan babu Hadisi ingantacce kan hakan, shin aikata shi bidi’a ne ko a’a? Sannan abin da daya kungiyar take yi na taron bakin ciki da sanya wa kai jin kishi da sauransu da mustahabbantar da yin iface-iface da koke-koke da keta tufafi, shi hakan yana da asali ko a’a?
Sai ya amsa da cewa: “Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Babu wani Hadisi ingantacce da aka samu daga Annabi (SAW) kan haka. Kuma ba a samu haka daga sahabbai ba, sannan babu wanda ya mustahabbantar da haka daga cikin shugabannin Musulmi, ya alla shugabannin nan hudu ko waninsu. Kuma duk littattafan da ake dogaro da su ba wanda ya ruwaito hakan ko daga Annabi (SAW) ko sahabbai ko tabi’ai, sahihi ko da’ifi a cikin littattafai Sahihai ko Sunan ko Masanid. Ba a san wani abu ba game da wadannan hadisai a zamanin karonin nan masu daraja. Sai dai wadansu daga cikin mutanen da suka zo daga baya sun ruwaito Hadisai kan hakan, kamar wanda ya ruwaito cewa wanda ya sanya tozali a ranar Ashura ba zai yi ciwon ido ba a wannan shekara. Ko wanda ya yi wanka a ranar Ashura ba zai yi rashin lafiya a wannan shekara ba, da misalan wadannan. Sai aka ruwaito falalolin Sallah a ranar Ashura, aka ruwaito cewa a ranar Ashura ce aka karbi tubar Annabi Adam (AS) da daidaituwar jirgin Annabi Nuhu a kan dutse da maido Annabi Yusuf ga Annabi Yakub da tserar da Annabi Ibrahim daga wuta da musanya layya da Annabi Isma’il da rago da sauransu. Aka ruwaito Hadisi na kirkira da karya a kan Annabi (SAW) cewa ya ce: “Wanda ya yalwata wa iyalinsa a ranar Ashura, Allah zai yalwata masa a sauran shekarar.” Wannan ruwayar gaba dayanta karya ce aka yi wa Annabi (SAW). Kuma wannan ruwayar sananniya ce daga ruwayar Sufyanu bin Ayyinah daga Ibrahim bin Muhammad bin Almuntashir daga babansa ya ce: “Ya riske mu cewa wanda ya yalwata wa iyalinsa a ranar Ashura Allah zai yalwata masa a abin da ya saura na shekarar.”
Ibrahim bin Muhammad bin Almuntashir mutumin Kufa ne, kuma mutanen Kufa sun kasu biyu: bangaren Rafidawa ’yan Shi’a da suke bayyana jibinta ga Ahlul Bait, wadanda a boye imma masu ilhadi ne, zindikai, ko jahilai ma’abuta son zuciya; da bangaren Nasiba masu nuna kiyayya ga Imam Aliyu da mutanensa sakamakon abin da ya faru na yakin fitina. Sai ya zamo a Kufa a tsakanin wadannan da wadancan akwai fitina da kashe-kashe. Lokacin da aka kashe Sayyadi Husain bin Aliyu (RA) a ranar Ashura, kungiya azzaluma mai wuce haddi ce ta kashe shi, kuma Allah Ya girmama Husain da shahada, kamar yadda Ya karrama wanda Ya karrama daga Ahlul Bait, irin su Hamza da Ja’afar da Babansa Aliyu da sauransu.
Shahadarsa ta kasance daga cikin abin da Allah Ya daukaka matsayinsa da darajarsa da ita. Kuma lallai shi (Husain) da dan uwansa Hasan Shugabannin Samarin Aljannah ne. Kuma matsayi madaukaki ba a samunsa sai da jarrabawa…..
**{Legacy activities, comments etc counter: 946; topic series: 4; forum: MediaHausa; associated: 4- /*}